Showing 69001 words to 72000 words out of 74786 words
musu ďaki, dariya Abdallah yayi, ya ce, "Ablah aiko bazasu raba muku ďakiba, dan momcy ma idan sukazo itada papa wlhy ďaki ďaya suke zama.
Idanma na faďa momcy koroni zatayi, kiyi ha'kuri kawai kuyi zaman ku, dan shima Abii ba yarda zaiyiba,, yasmeen ta ce, "ALLAH inajin kunya Abdallah, Abdallah ya fice yana mata dariya.
Bai daďe da fitaba Nawaf yashigo ita harma ta kwanta sannan,, ya shigo yana faďin sorry fancy face nabarki ke kaďaiko, ina wajensu isma'il muna shan hirar zuminci, bayi yashige yay wanka dan azatonsa tayi barci ne..
Bayan ya fito yay shirin barci sannan tayi barcin gsky, sai kawai ya rungume matarsa suka hau barci.
Da asuba tunda yatafi sallah bai dawoba, ta nanan zaune tana laximi saiga wata 'yar yarinya takawo mata dabino guda bakwai, ta ce, "taci, yarinyar ta burge yasmeen, ta zaunar da ita saman cinyarta tana tambayar ya sunanta, yarinya ta ce, sunanta fateema,, woow!! Yasmeen tafaďa, sunanmu ďaya kenan ko, yarinya ta ďaga kai,, duk suna magarne da turanci saikuma larabci ďai2 da yasmeen take sakawa wanda ta iya.
Suna nan zaune Nawaf yashigo dagudu fateema taje ta tarosa ya ďauketa yaďaga sama, suna dariya, yazau bakin gadon yana yana tambayarta tasan yasmeen tace eh, nan sukaita hira shida ita da larabci, yasmeen ta ce, "o ni yar yarinya 'karama ta iya larabcun.
Nawaf yay dariya kajifa xarah da wani zance, to itada yarenta , ke sanda kina 'karama baki iya hausaba, da yaren buzaye??.
Yasmeen ta ce, "na'iya mana, sukai dariya gaba ďaya, ya ce, "fateema jeki amso min dabino nima, tako 'ki'kira da gudu amso dabino, Nawaf yasakko kusada yasmeen yaďan kwantar da kansa a bayanta, cikin taushin murya yace nifa da matsala nazo, yasmeen ta ce, "matsala kuma wace iri??, yay mata zobe da hannayensa cikin kunne ya gwar gwaďa mata suna cikin yin dariya fateema tadawo da dabino, da sauri yasaki yasmeen yana ďan sosa kai, tazo ta haye cinyarsa tana bashi dabinon abaki,, yasmeen ta ce, "kaganka kuwa kuna kama kamar kaika haifeta.
Yay murmushi mai 'kayatarwa yana shafa kan fateema ya ce, "karki damu nima tawa tana nan zuwa,, yasmeen tai 'kasa dakai tana murmushi,, ta ce, "ďiyar waye??, Nawaf ya ce, "ďiyar uncle zaid ce, tunda mamansu tarasu wajen haihuwar 'kanin fateema aka kawosu nan wajen hajja.
Ayya ALLAH yagafarta musu, wlhy harta bani tausayi, su nawane??, su ukune, akwai Nawaf mai sunana, sai muh'd Ariff, sai fateema Wanda tarasu wajen haihuwarsa shima yarasu,, ALLAH sairki ALLAH yaji'kansu.
ameen fancy face.
nansukaita hirarsu harsaida hajja ta aiko su fito suyi break sannan.
Bayan sun kammala break suka ďau gayu, Nawaf yatafi zagawa da yasmeen gidajen dangi, gidansu ummuhabeeba ne na farko, antarbesu da mutunci, ummuhabeeba sai rawar kai ake anga masoyi, yayinda yasmeen ta cika tayi fam, Nawaf ne kawai ya gane halin datake ciki, dayaga zata fashe saiyace ta tashi su tafi,, ummuhabeeba kuma ta ce, "zata bisu itama tayo ziyara, tofa.
Koda suka fito yasmeen saita shige baya, Nawaf ya ce, "k miye haka??, banza tayi masa bata amsaba,, itako ummuhabeeba ko a kwalar rigarta ta buďe gaban mota tashige abinta,, da hausa Nawaf ya ce, "fancy face wai miye haka kikeyi??, baki ta murguďa masa😏batareda ta tankaba.
Ummuhabeeba ta ce, "my luv muje mana, wani haushi ya'kara turni'ke zuciyar yasmeen, wai agabanta akecema mijin ta my luv,, Nawaf yana kallonta tana hawaye ta madubu,, kai kawai ya girgiza dan baisan miya dace yayiba.
Ummuhabeeba ta ce,, A'a yanaga kana nufar ka'aba🕋damune?, muda zamu ziyara,, batareda ya kalletaba ya ce,, "aidama can zamuje nida fancy face, mungama ziyara sai kuma gobe idan ALLAH yakaimu.
Ummuhabeeba taji haushi ta 'kara maimaita sunan wai fancy face, wani ďan 'karamin tsaki taja wanda Nawaf ne kawai yaji, itafa tabiyosune dan azatonta dangi zasu zaga tana kuma bu'katar dangi su tabbatar da soyayya takeyi da Nawaf, tasan dolene asakashi ya aureta.
Amma shine dan wula'kanci yayo masallaci dasu.
Yasamu guri ya tsaida motar, suduka suka fito fuska babu walwala, Nawaf ya ce, "lokacinma sallah yayi, saimushiga muyi sallah idan mun fito saina zagaya dake kiga guraren tarihi ko fancy face??,, bataso tabashi kunya agaban ummuhabeeba dan haka tayi far da idanu ta ce, "hakane habibina,, ummuhabeeba tayi gefe dakanta zuciyarta tana zafi,, yayinda yasmeen ta harari Nawaf,, yay mirmushi yana mata jinjin😃👍🏻.
Haka suka shiga sukayi sallar la'asar,, bayan sunfito yashiga nuna mata wajajen tarihi hannunsa yana ri'ke da nata,, daga baya ummuhabeeba ta ce, "tagaji ya maidata gida.
Ya kalli agigon hannunsa yana murmushi, aii inaga mu bari muyi sallar magriba kawai dan ta gabato, zata iya riskarmu a hanya.
Badan tasoba dole ta ha'kura sukayi sallar magriba accikin masallacin🕋sannan ya maidata gida suma suka koma inda suka fito, yasmeen tanata wani zuzun6ura baki, ita adole kishi ya motsa.....................✍🏻
©2017
💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘💓
[1/12, 9:11 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💓
Page👉🏻57 & 58
.......Nawaf yanaso yay dariya amma saiya gimtse, idonsa na kan titi ya ce, "matar NAWAF SA'EED MODEBBO ya yadai??.
Yasmeen taimasa banza kamar bata jishiba, yay murmushi tareda kamo hannunta ďaya ya rumtse anasa, yana tu'ki da ďaya, yaďan kalleta kaďan yanda taketa zum6uro baki saida ya dara,, ya ce, "waishin yazanyi da shagwa6ar fancy face ne yayinda yarana sukazo duniya??, sai asannan ta kalleshi ta murguďa masa baki, ya sake murmusawa dan yaganta ta madubi, antuna baya kenan yafaďa yana shiga kwanar dazata sadashi dagindansu hajja.
Ta zame hannunta daga nasa tana cewa kadaiji dashi na ummuhabeeba,, tofa harkin sadakar dani fancy face, lallai kinason ummuhabeeba wannan irin 'kyauta da rana tsaka, aiiko muna sauka zan kirata na sanar mata kin barmatani tasamu miji a sanga.
Yasmeen fa ta sha'ka da yawa danhaka tayi tsit, yanayin parking tafice batareda ta jirashiba, a'katon falon gidan ta tarar da ahalin gidan harma da ba'ki waďanda bata saniba,, tunda tashigo suke murmushi damata sannu da zuwa, itama saita daure take murmushin ya'ke, amma tuni momcy ta harbo jirginta, ta gaisheda kowa dake falon, waďanda ta girma suka gaisheta, hajja ta mi'ka mata hannu alamar tataho wajenta, kusada ita taje ta zauna sai asannan Nawaf yashigo yana cilla makullin mota sama yana ca6ewa, kai kai lallai ashe yau munada manyan ba'ki, waďanda yakecema manyan ba'ki suka shiga dariya suna faďin kainedai babban ba'ko, shekararka nawa rabonka da saudia, shima ďayan gefen hajja yaje ya zauna suka sakata tsakki shida yasmeen, ya ce, "ablah kibari kawai wallahi sana'ar nan tamu itake hanamu wani motshi, amma waccan shekarar nazo saidai kwanana biyu naduba hajja na tsere, ya madina?.
Ta ce, "madina lafiya lau, ya amarya tunda bansamu zuwa bikiba sannan jawad yana fama da rashin lafiya muna kwance a asibiti, ayya ablah karki damu aisu ummulkhairi sunje shima ya wadatar, su jawad suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya karatunsu, sukace lfy law, yamaida kallonsa ga jawad ya ce, "zo na ganka my boy, jawad yazo suka gaisa lallai kayi girma sai aure ko? , gaba ďaya falon suka saka dari, ablah ta ce, "aure kam, Anwar fa ya girmi jawad jikinne kawai ALLAH yabashi haka.
Koh ablah?, amma yanzu sai ace shine babba, ga Anwar ďan 'karami,, gsky kam, shima yanzu yagama tsokanarsa aii.
Ablah tacanja maganarta zuwa larabci danda da turanci sukeyi, ta ce, "Nawaf wannan matar taka kamar ba 'yar Najeria ba?, Nawaf ya kalli yasmeen ya ce, "ablah saboda mi kikace haka??, Ablah tayi dariya naganta 'kya'ky'kyawane,, lallai Ablah kin samemu mu 'yan Najeria bamuda 'kyaune??
Kunada 'kyau mana amma dai ku ba'ka'kene, inkuwa 'yar Najeria ce ka iya za6e, nanma dariya sukayi, banda yasmeen dabatasan misuke cewaba, Nawaf ya ce, "kai ablah ammafa kin samemu mungode,, saidai yakamata ki shirya kije Najeria kigammu muma akwai kala.
Ta maida maganar zuwa turanci, Karka damu zanzo Najeria da bikin Abdallah insha ALLAHU.
tabďi bikin Abdallah kuma?, kice da sauran lokaci kenan??, kai haba wane sauran lokaci?, aii kamar yaune,, ablah yanzufa yake shekara ta biyu a school, yaushe aka gama aka samu aiki, yarinyarma dayakeso ko secondary bata gamaba.
Hajja ta ce, "aiko Abdallah aure yakeso kaida kadage kanata kwaso masa shekaru, kallifa yanda yake haďe fuska yaji kace da sauran lokaci.
Abdallah yay saurin cewa hajja karkisa yanzu abii ya hau kaina fa, momcy tai masa dakuwa kaci gidanku ai gsky hajja ta faďa nima ina kallonka.
Dayaga za'a tasoshi gaba saiya tashi ya shige đaki yana kunkune, lallai abii kaika kama matarka ahannu kunata shan soyayya saini zaka ringa lodamin shekaru, wlhy halimatu tana gama secondary aure zamuyi, dannikam aure nakeso.
Na ce, "da gsky ka Abdallah wlhy kayi aurenka kaima kasha soyayya😜.
Afaloma hirarsu suketa sha, dayake da turanci akeyin hirar yasmeen tanajinsu saidai bata saka musu baki, iyakarta daria ko murmushi, dahaka aka kira sallar isha'i mazan suka fita masallaci sukuma matan sukayi agida, bayan sun dawo akaci abinci sannan su Ablah suka tafi gindan iyayenta dayake anan suka sauka.
Momcy ta kalli yasmeen datayi shiru cikin kujera ta ce, "ďiyata zonan, yasmeen ta tashi ta nufi wajen momcy, harzata zauna 'kasa momcy ta ce, "A'a takamota ta zauna kusada ita, tajawo kan yasmeen gefen kafaďarta tana shafa bayanta ďiyata miyake damunki?, yasmeen ta ce, "momy babu komai.
Momcy ta saka hannunta gefen wuyan yasmeen ta ce, "bakijin dađi yasmeen tun jiya ina kula dake bakisan faďane kawai komuje asibitine??, A'a momy bama sai munjeba, to faďamin mike damunki??, mom jikina ne kawai yakeyimin nauyi sai kuma wani lokacin inaďan ganin jiri, amma banajin zazza6i, saidai jikin yayi ďumi kawai.
Momcy ta shafa kanta amma shine baki faďaba ďiyata, kuma mijinkima bai saniba ko?, eh yasmeen tafaďa,, humm ďiyata zurfin ciki ko??, ALLAH mom niban ďauki abin serious ba shiyyasa., aiko wannan serious ne ďiyata, gobe idan ALLAH ya kaimu ummuhabeeba saitazo ta dubaki kinji, dam gaban yasmeen ya faďi, badai wacan maikama da aljanarba ko tafaďa a zuciyarta.
Nawaf dake gefe yana kallonsu ya ce, "momcy waimi ake tattaunawane haka?, sai kus2 kukeyi babu maiji.
Tofa kaji wani sa ido ina ruwanka ko ka aikata wani abune dakake tsoron kar'afaďane??, Nawaf ya murmusa A'a A'a, nikam ban aikata komaiba, amma momcy wannan irin sirri haka miyasa ba'aso muji??, aiba saikunjiba shiyyasa, to shikenan idan tayi tsami maji, nikungama bari naje na kwanta, inaso mu fita da wuri gobe idan ALLAH yakaimu gara muyi ziyarar nan mugama kafin wuri ya 'kure.
Yay musu sallama ya shige ďaki, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije ki kwanta kinji ALLAH ya'kara sau'ki, tami'ke tana faďin ameen mom, itama sallamar tai musu ta shige, yayinda suma kowa ya mi'ke yanufi makwanci, dama Abdallah yana ďaki suna waya da halimatunsa.
Yasmeen ta maida 'kofar tarufe, Nawaf dake zaune bakin gado yana tu6e kaya yajuyo yana kallonta ta ďauke kai daga kallonsa,, murmushi yayi yatashi yashige bayi danyin wanka,, yaudai ba'a daďeba aka fito, yana fitowa itama tashiga, sanda ta fito yana shafa'i da wutiri, itama saitayi harama dan dama batayiba.
Bayan sun idar yazauna shan shayi itakuma ta haye gado tana mitar mutum kullun saiya sha shayi yake iya barci saikace wata kwaya, koni dana gada bana shansa haka,(karku manta yasmeen buzayene ), koda yake shima yagada awajen momcy.
Tana nan tana sa'kawa da kwancewa Nawaf yagama ya hawo gadon yakwanta, shiru tayi kamar tayi barci, ya rungumota zuwa jikinsa yana faďin yarinya kokinyi barci saikin tashi, danyau bazan iya ha'kuriba, duk abinda yake mata tanajinsa tayi shiru.
Dayaga haka saiya ďauki wayarsa ya haska mata fuska, dole taďan 'kyafta idanu sabida haske, yay dariya, oh da wasan 6urun2 akeyimini to aii na harbo jirginki, hannu tasa taďan tureshi tana faďin dakazo kana 'yar murya bagara kabiya sadaki aďaura muku aureba gobe kaida mai kama da aljana.
Tabashi dariya sosai wai mai kama da aljana wato ummuhabeeba kenan,, cikin dariya ya ce, "A'a fancy face karfa ki faďa abakin mala'iku, surubuta gobe ya tabbata, dama ďazu kince kin barmata ni.
Ta gallah masa harara tamkar yana ganinta, ta ce, "kaidai kasani.
Yasake rungumota yana faďin kema zaki sanine, tunda zaki koma raba dai2 ďina da wata.
Haushine ya 'kara turnu'ke zuciyar yasmeen saikawai tafara kwalla,, jiyayi laima tana bin 'kirjinsa da sauri ya haska danyasan 'kila kuka takeyi, ilai kuwa shitakeyi, yashiga share mata haba matana uwargidana kuma amaryata dagake aii babu 'kari, itafa mai kamada aljanar nan amatsayin 'kanwa na ďauketa, dan haka batada wani fili azuciyar habibinki, duk kinbi ki mamaye ko'ina, 'ya'yana kawai kika barma fili, plz banaso kibari kishi ya 6ata min ranki a banza, Nawaf nakine ke kaďai fancy face, ya 'kare maganar da sumbatar bakinta, daganandai ya cigaba da kwantar mata da hankali ta hanyar daya dace.
Washe gari momcy ta aika Abdallah ya đakko ummuhabeeba danta duba yasmeen, sama2 suka gaisa kowa kishi yana cin zuciyarsa, Nawaf yay dariya wato sudai mata basuda wata damuwa saita kishi.
Toshi wannan 'kaddara tasa ya haďasu aiyaga takansa.
Ummuhabeeba tanama yasmeen tanbayoyi cikin wani yanayi, itama tana bata amsa cikin jin haushi, tun a tanbayoyin datake mata da amsar datake bata tagano yasmeen ciki gareta, amma tsabar kishi bazai barta tafaďa musu yasmeen nada cikiba, saita ce, "zataje asibiti tadawo.
Momcy ta ce, "babu wani magani dazaki bata yanzu ummuhabeeba?, dan na kula batajin daďin jikinta, karki damu momcy yanzu zandawo insha ALLAHU da maganin zan dawo, to shikenan saikin dawo.
Ta kalli Nawaf abii zoka kaini muje mudawo plzzz, saida yaďan harareta sannan ya ce, "dawaya kawokine?,, ta shagwa6e fuska ALLAH mijin Ablah hidaya ne ya saukeni, toga key kije kidawo, ta zaro ido waje😳 kamanta nanba 'kasarku bane, kasanfa mata basa tu'ki a saudia........
Momcy ta 'katsemusu zancen da faďin kaje ka kaita mana modeebo, kaga yasmeen batajin daďin jikinta, zaku zauna gaddamar dakuka saba, saida yakalli yasmeen dake kwance ta haďe rai kamar zatayi kuka, ta harareshi, ya ďauke kai yana faďin to momcy.
Suna fita ummuhabeeba ta kamo hannunsa, da sauri ya kwace yana harararta, ta ce, "sorry bazan sakeba, batareda ya ce, "komaiba ya buďe motar yashige, itama saita buďe ta shiga, tanaso tayi masa maganar aurensu amma tanajin tsoro dan ganin yanda ya haďe rai kamar bashiba.
Har cikin asibitin ya kaita, tafito tana faďin kazo muje ciki mana, kai ya girgiza mata, A'a jeki fito ina nan ina jiranki,, asanyaye ta ce, "to, taso yashiga dan 'kawayenta su ganshi, suna shan labarinsa sosai awajenta.
Bayan tafiyarta ya kwantar da kujera ya kwanta, tuni tagama abinda takeyi amma tayi zamanta suna hira da 'kawayenta kamar babu wanda ke jiranta,, Nawaf yagaji da jira yafito, yasan matarsa tana bu'katar magani danyabaro jikinta da zazza6i, cikin asibitin yanufa, office ďinta yafara zuwa amma arufe, wanine yake gaya masa aii yau bata aiki tana hutu sai dare, ya ce, "ai tare sukazo,, mutum ya ce, "to inaga tana wajen 'kawayenta zomuje na rakaka 6angarensu, acan kuwa ya sameta tana ganinsa tafara wani kame2n binciken takardu,, ya 'karaso yana faďin ummuhabeeba wai har yanzu?,, ta mi'ke tana faďin abii yanzu na kammalane.
'Kawayena ga abiina na 9ja sunansa Nawaf,, suka mi'ke suna faďin woow!! Nice guy, dama sun sansa a hotuna datake nuna musu, suka gaisheshi ya amsa yana tambayarsu ya aiki.
Bayan sun gaggasa yayo waje, itakuma taimusu sigina da ido itama tafito tana dariya suma sunayi.
Amota ta tarar dashi, harya tada, tashigo tana faďin albishirinka abii, batareda ya kalletaba ya ce, "goro, saida taďan cije le6e ta ce, "matarka tanada ciki wata biyu, da sauri ya tsaida motar yana kallonta, ya ce, "da gsk kikeyi ko wasa?, ta ce, "wlhy da gsk, aii baisan sanda ya rungumeta yana murna ALHAMDULILLAH yaketa faďi, yayinda itakuma ta kwanta luf ajikinsa, da sauri ya tureta yana faďin wa'iyazubillah, ALLAH ka nisantamu daga sharrin shaiđan.
Shiru kawai ummu habiba tayi dan batada amsar bashi, haka suka 'karasa gida batareda ya kula dukkan maganganun datake masaba, yana zuwa ya rungume yasmeen babu ko kunyarsu momcy da hajja, ya ce, "fancy face albishirinki, da sauri ta tureshi dan kunyarsu momcy sai asannan ya kula dasu ya saketa da sauri yana sosa kai, yay 'kasa da kai yana faďin sorry mom & hajja.
Momcy ta ce, "kaidai kasani mara kunyar banza, to Albishirďin mi zakai mata??, ya sosa kai ummuhabeeba faďa musu kawai.
Ummuhabeeba dake tsaye kamar gunki tun ďazu, ta mi'kama momcy result ďin, momcy ta amsa tana dubawa, cikin murmushi ta mi'kawa hajja itama, hajja ta rungume yasmeen tana murna suka shiga mi'ka addu'oin alkairi ga cikin dabai wuce wata biyuba, kowa yana cikin farinciki da murna bare uban ginsamin Nawaf, momcy tabata shayi dakanta ta sha dayake ALLAH yasa cikin bamai saka ami bane, tanashan magunguna ta 6ingire barci abinta.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, yasmeen tana samun kulawa wajen mijinta da iyayensa, yana zagayawa da ita ko'ina guraren tarihi da gidajen dangi, sunje har kabarin fiyayyen halitta (ANNABI MUHAMMAD ,,,S A W), Tanajin daďin rayuwar saudia, kusan kullum saitayi waya dasu yaseer da ameena tanajin labarin 9ja, satinsu uku papa yazo, shima yay sati ďaya sannan