Showing 42001 words to 45000 words out of 74786 words

Chapter 15 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

364

bata farkaba sai cikin dare, tajuya taga Nawaf agefenta kwance yana kwasar barci, ta lumshe ido ahankali ta sake buďewa, sakkowa tayi tashiga bayi tayi wanka dan jikinta duk ciwo yakeyi.
Jin motsin ruwa yasa Nawaf farkawa shima, ya laluba gefensa saiyaji babu yasmeen yatashi yanufi bathroom ďin, ahankali ya tura 'kofar saiyaji ta a buďe, yako tura kai cikin bayin batareda neman iziniba.
Dasauri yasmeen tajuyo danjin motsi, ta kwalla 'kara dan ganin Nawaf tsaye yana kallonta, ta rarumi tawul ta 'kudundune jikinta.
Da sauri Nawaf ya'karaso gabanta yana faďin "k dallah karki taramin mutane.
Da'karfi ta ce, "to kafita mana, miye haka zaka wani shigo mini ina wanka.
Tsaki Nawaf yayi ya ce, "ubammi zan kalla ajikinki, aikin banza kawai, yafaďa yana ficewa.
Yasmeen tazauna jagwaf tana maida numfashi da'kyar, ta runtse idanu gam tana hawaye.
A6angaren Nawaf madai hakan take, jagwaf yafaďa saman gadon yana fitar da huci mai zafin gaske.
Yasmeen tadaďe bata fitoba, saida ta daidaici Nawaf yayi barci sannan tafito, ta saka riga mai ďan kauri ta kwanta saman kujera.
Nawaf yana kallonta, yaja Numfashi ahankali, gsky shikam yana bu'katar matarsa, amma yarasa hanyar dazaibi yacika burinsa, dawanan tunanin barci yakwasheshi ___________________________________ haka rayuwa taci gaba da gudu da sauri, Nawaf yanata shirin komawa Spain.
Yauma yana wajen papa suna tattaunawa, papa ya ce, "yanzu idan katafi sai yaushe??.
Nawaf yay 'kasa da kai yana faďin papa da'an gama kakar wasanni insha ALLAHU zamuzo hutu.
To shikenan, ammafa idan kadawo da matarka zaka koma, dan bai daceba ace kana can matarka tana nanba, tunda kana daďewa baka 'kasar.
Kan Nawaf a'kasa ya ce, "to shikenan papa, ALLAH yakaimu lokacin.
Papa ya ce, "amin.
Daganan Momcy tashigo itama suka cigaba da tattaunawa, sun daďe suna hira saida papa ya ce, "yatashi yaje wajen matarsa, Nawaf yami'ke badan yasoba yatafi.
A falo ya isketa tana waya da umma tana hawaye, ya zauna kujerar dake kallonta jiki a sanyaye, itako bama tasan ya shigoba, tacigaba da wayarta, umma wlhy iya gsky ta nake gaya miki, nikam nagaji wlhy.
Tai shiru zuwa wani lokaci, tasaka hannu tana share hawaye, ta ce, "to shikenan umma nagode sosai, to ALLAH yakaimu.
Sai asanan takula da Nawaf, ta kauda kai daga kallonsa.
Nawaf ya ce, "k dawa kikeyin waya?, kuma wayace ki ďaukarmin wayata kiyi kira?.
Banza tayi masa kamar batajiba, tamaida kanta tsakanin cinyoyinta tana kuka, haushi ya tokare ma'koshin Nawaf, jiyake kamar ya doketa agurin, dan bayason kuka musamman kukan mace, yami'ke cikin haushin rashin amsa masa maganarsa datayi, kujerar datake zaune yadawo, yasa hannu yaďago fuskarta.
"K!!! Wai wane irin iskancine zaki zauna kinama mutane kuka, kamar wadda akaima wani abu, kuma kinaji ina tambayarki amma kikayimini banza.
Cikin rawar murya ta ce, "tomi kakeso nace maka?, aidai kasan babu wanda zankira a wayarka sai 'yan gidanmu ko, kuma aiga wayarnan kaďauka kakira number dana kira saikaji waye??.
Kuma wayarka dake faďin wayace na ďauka, kai wayace ka fasa mini tawa wayar??.
Nawaf ya zazzaro idanu yana faďin "k!! Wlhy ki kiyayeni, kar 'kuruciyar ki tajaki ki ďakko mini zancen wani 'kato anan, dan wlhy zan iya zaneki!!!.
Yasmeen ta tsorata da Nawaf sosai, amma bataso ta nuna masa tana jin tsoronsa, dan zai samu lagontane.
Itama ta zazzaro nata idanun, ta ce, "aikai kajika, sai ba'kin kishin tsiya, wlhy kayi wasa sai zuciyarka ta tarwatse abanza, nikam an cuceni wlhy da aka haďani aure da kai, shiyyasa bazan ta6a sonkaba kuwa har.........
Kafin ta rufe baki ya matse bakinta da 'karfi, yasa ďayan hannunsa ya matse gashinta, ya ce, "k!! karki ďauka kishi nake akanki, karki ďauka nima zan soki, dana soki gara naso dijangala, domin koba komai 'yar uwatace, inada waďanda suka fiki komai dayawa yarinya, ki kalli ummu habiba, yarinya 'kya'ky'yawa jinin larabawa, mai ilimin addini dana boko, akwai irinsu dayawa dasukeson na kasance mijinsu, tundaga turawa har ba'ka'ken fata, dan haka ki daina ďaukar kanki "k wata tsiyace awajena.
Ya fisga gashin sanan ya hankaďata ta bigi kujera, yabuga yatsun hannunsa biyu yana faďin "k ba komai bace, face 'yar aiki, mai jiran tsammani, ki ďauka darajar iyayenace tasa nake zaune dake, kuma ina ganin mutuncin iyayenki, domin muta nen kirkine, amma daba hakaba hummmmm ya 'karashe zancen acikinsa.
Yasaki bakinta yashige bedroom, sai asannan tasamu damar yin kuka, takoyi kuka mai isarta harta koma bani tausayi.
Ranar afalo ta kwana,.
Washegari Nawaf tunda yafita daga gidan bai dawoba sai dare.
Afalo ya isketa zaune ko kallo bai ishetaba shima ďin haka, yay wucewarsa bedroom.
Tsaki yasmeen taja tana faďin mugu kawai mai ba'kin hali, koda yashiga ďakin kayansa yashiga haďawa dan gobe zai ďage zuwa Spain, amma bai sanarma yasmeen ba.
Yagama haďa komai sannan ya kwanta yana tunanin yanda zaiyi da yasmeen dan shidai bazai sanar mata zai tafi gobe ba, kuma bayaso papa ko momcy suji cewar bai sanar mataba.
Yajawo ledar daya shigo da ita, yaciro wata haďaďďiyar waya akwali, yabuďeta ya'kare mata kallo, sannan ya ďakko biro da takarda yafara rubutu📝yagama ya ninke yasaka acikin wayar ya ajiye yay kwanciyarsa.
Saikuma wata dabara ta faďo masa, yaďauki waya yana surutu kamar yanayi dawanine, harfalo yafito yana faďin karka damu insha ALLAH gobe zan iso Spain, zan biyo jirgin 'karfe bakwai nasafe da ixinin ALLAH.
okey babu damuwa nagode zataji saina iso.
Yasmeen tanajinsa, sai abin yabata mamaki, wai kana tareda mijinka amma yagagara sanar dakai zai tafi, wanan wace irin rayuwace, wasu hawaye suka wanke mata fuska, shikuwa tuni yakoma bedroom abinsa.
Haka takwana rabi barci rabi tunani, aiko dasafe ta makara, sanda ta tashi 7:30am tadiro dasauri daga kujera tanufi bedroom wayam tagani Nawaf yatafi, hawaye suka shiga yimata ambaliya a fuska, jiki asanyaye tayi alwala tayi sallar asubahi.
Tana zaune saman sallaya momcy tashigo, yasmeen taďago da sauri tazata Nawaf ne saitaga momcy, batasan sanda sabon kuka yazo mataba.
Momcy tazauna ta rungumota zuwa jikinta tana lallashi, yihakuri barkuka, shiyyasa mijinki ya ce, "kar'a tadaki daga barci, dan tunjiya kike kuka, to kiyi ha'kuri aiba daďewa zaiyiba zai dawo, kuma idan yadawo tare zaku koma kinji.
Azuciyar yasmeen ta ce, "wato 'karyar daya shirya muku kenan?, ba komai zanyi maganin shi dakaina agidannan, komai yanada lokaci, nasan nima nawa lokacin yana zuwa.
Nan momcy tayita lallashinta, daga 'karshe ta ce, "idan kinajin tsoro kishirya kayanki, ki koma ďakina, idan yadawo saiki komi nan kinji, idan kuma ba'kyajin tsoro tokiyi zamanki anan ďin.
Da sauri yasmeen ta ce, "momy zanbiki can.
Toshikenan tashi ki shirya kayanki kinji, bari na turo miki Anwar yatayaki ďauka, ta ce, "to.
Ta shirya duk kayan dazata iya bu'kata, sai asanan taga ledar daya ajiye, yarubuta nakine idan kina bu'kata.
Kai kawai ta girgiza taďauki ledar tasaka cikin kayanta, Anwar da Abdallah sukazo suka tayata ďaukar kayan, suka kashe duk wani kayan wuta na wajen, suka rurrufe ko ina.
Tundaga ranar takoma ďakin momcy da zama, tanajin daďin zaman, saidai tunani Nawaf da kewarsa duk sun addabeta, har takanyi mamakin kanta, yanda tadamu da mutumin dabai damu da itaba, wanda bazaman lafiya sukeyiba sanda yana nan, taja 'karamin tsakai tareda gyara kwanciyarta, 'kilama shi yamanta dawata halitta yasmeen.
Tasan Nawaf bazai ta6a sontaba sai wani abu ga ALLAH, wanan kuma ikonsane, yakan aikata duk yanda ya so, alokacin daya so.
________《》__________
To shimadai Nawaf hakan take agareshi, tunda yasauka 'kasar Spain bashida wani sukuni, tunanin yasmeen duk yacika masa zuciya da ruhi, bashida aiki sai tunaninta, yakanyi dariya idan yatuna wani faďan nasu, yayi waya da kowa nagidan amma banda ita, yatambayi Anwar ya ce, "baiga ta haďa wayar daya saya mataba.
Yana matu'kar bu'katar yin magana da'ita amma yarasa hanyar dazaibi.
Ya lumshe manyan idanunsa masu haske, ya maida kansa jikin luntsume miyar kujerar dake falonsa yakwantar, tabbas yasan yafaďa tarkon son yarinyarnan, kuma yalura ita bata 'kaunarsa, haushinsama takeji, saboda har yanzu soyayyar tsohon mijinta tana tareda ita.
Ya'karashe maganar kamar xaiyi kuka, yashiga girgiza kai yana faďin A'a FATEEMA ZARAH karkimin haka, nine kawai yadace ki so, domin dani kika dace, jiki yana rawa yaďauki ďaya daga cikin wayoyinsa yashiga kiran Anwar, harta tsinke ba'a ďaukaba, yatuna yanzu yana islamiyya wajen karatun dare.
Yamaida akalar kiran zuwa Abdallah shikuma tashi akashe, yayi tsaki, saikuma yakira momcy, bugu ďaya biyu ta ďauka, bayan sun gaisa yatambayi lafiyar kowa.
Ta amsa dakowa yana nan lafiya, ya ce, "masha ALLAHU haka akeso, yanaso ya ce, "tabama yaameen amma yanajin kunya, dan haka sukayi shiru suduka, momcy takatse shirun da faďin Abdallah ya ce, "yau da daddare zakuyi wasa ko??.
Eh momcy insha ALLAHU, sai a tayamu da addu'a.
Babu damuwa kullum ita muke muku ALLAH yabada sa'a.
Amin momcyna ngd, bari nabarki haka ki gaida min dasu.
To sai anjima zasuji.
Yasmeen tana zaune tana jinsu, abin ya sosa zuciyarta, tunda yatafi bai nemetaba, amma kullum yana kiran iyayensa da 'kannensa, đazu datayi waya da yaseer a wayar Anwar yake gaya mata babu daďewa yayi waya da yaya Nawaf, amma ita banda ita, wasu 'yan kwalla suka taru mata agefen idonta, tai saurin sharewa kafin momcy tagani.
Su Anwar suka dawo daga islamiyya, suka zauna suka cigaba dahira, dukda ita yasmeen firar bawani daďi takemataba, danma anasako Nawaf a firarne da tuni taje ta kwanta.
Suna nan zaune har aka fara kallon wasan su Nawaf ďin, taďanji sanyi data ganshi, tunda wasan Life ne ake nunawa, sai wani murmushi takeyi najin daďi, ana haka su Nawaf sukaci kwallo kuma shine ya zura kwallon.
Su Anwar suka shiga murna da tsalle, itamadai taďanyi murnan, damma ganin momcy awajen taďan kanne saboda kunya.
Haka rayuwa yacigaba da tafiya yauda gobe sai ALLAH, yau watan Nawaf ďaya datafiya, kuma har yanzu basu ta6a gaisawa da yasmeen ba, ga kowannensu yana cikin muradin son jin muryar ďan uwansa, amma hakan ya gagara, suduka suna cikin begen juna, garama yasmeen tana ganinsa yayin dasuke wasa, takanďan rage damuwa.
________________________________ ____ yauma tana kwance aďakin momcy abin duniya duk yadameta, saitaji wayar Abdallah dake gefenta tana wringing, takai hannu taďauka saida gabanta yafaďi dataga ansa yaya Nawaf, ta rintse ido tabuďe, har wayar ta'katse, yasake kira itama ta katse, ana ukunne ta ce, "bari taďaga.
Jiki a sanyaye ta ďaga wayar, muryarsa ta daki dodon kunnenta, tarintse idanu, cikin faďa ya ce, "kai wane irin iskancine anata kiranka ka'ki ďagawaya??, ubammi kakeyi??.
Yasmeen tayi shiru takasa magana dan tsoro, shikuma jin anyi shiru yacigaba da bala'insa, ahaka Abdallah yashigo, da sauri ta mi'ka masa wayar....................................✍🏻


Assalamu alaikum
Kuyi ha'kuri masoyana, kunjini shiru ko??, wlhy har yanzu banida lafiyane, saida nakwanta asibiti kwana biyu.
Ngd sosai.
Luv u oll❤❤❤😘


©2016



💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞



Page👉🏻37 & 38

......Abdallah yakara wayar akunnensa tareda faďin Abi!!.
Nawaf ya daka masa tsawa kai!! Dallah yimin shiru mana, sai yanzu kaga damar yimini magana.
Cikin rawar murya Abdallah ya ce, "Abi kayi ha'kuri wlhy bana kusada wayar, aunty ce taďaga.
Nawaf yaja tsaki wace aunty??.
Aunty yasmeen mana, wayana tana hannunta ne, yanzu nashigo shine tabani.
Nawaf yaja wani gwauron numfashi ya ce, "tana ina??.
Da sauri Abdallah yajuya inda yasmeen take zaune amma saiyaga wayam ta tashi ya ce, "Abi ta tashi, bari na duba kotana falo.
Ya duba falo batanan har waje.
Ya ce, "Abi wlhy ta 6uya yauma.
Shiru Nawaf yayi danji yake kamar zuciyarsa zata fashe, ya kula da gayya yasmeen take 6uya aduk lokacin dayace abata waya, ya yanke wayar batareda yasake cewa komaiba dan haushi..
Abdallah ya girgiza kai, yana mamakin hali irin na Abi!, shi daban yake da sauran mutane, yata6e baki tareda jefa wayar saman gadon momcy yafice.
Yasmeen tabuďe Bayi tafito, dak wanda ya kalleta yasan tasha kuka, tafaďa saman gado tana share hawe, lokaci yayi dazata nemawa kanta mafita, dukma yanda za'ayi saita cire son Nawaf azuciyarta, bazata bari sonshi yacigaba dayin tasiri azuciyar taba, takuma fashewa da kuka tana dukan 'kirjinta, cikin kuka take faďin saika fita! saika fita!! saika fita!!! Daga zuciyata bazan yi dakon son wanda baya 'kaunataba, dolene na canja kaina kota halin 'ka'ka Tacigaba da kukanta.
Nagirgiza kai kawai nafito.

Nawaf kam dafe kai yayi dan ba'kin ciki, yashiga share zufar dake kwararo masa adukkan sassan jikinsa, dukda AC dake aiki acikin ďakin, ya 6alle murfin gorar yashiga kwan kwaďa, saida ya shanye duka sannan yamaida kai ya kwanta yana fitar da huci, kamar wanda yafito daga filin danbe.
Yaďanja tsaki waishi ya akayima ya faďa tarkon son wannan yarinyar?, dayasan inda son yake datuni yacireshi ya yarda ya huta, yana zaman zamansa amma yanzu ansakashi cikin wani yanayi, ya huro huci mai zafi daga bakinsa, wayarsa yajawo yashiga bincikar ma'ajiya hotuna.
Hotunan bikinsu yashagala da kallo, duk inda yasmeen take a hoton ta 'kayatar, takuma bada ma'ana, ya sumbaci wani hoto datayi masa 'kyau sosai, gawani 'kayataccen murmushi data saki a hoton, kamar kakirata ta amsa, ya lumshe idanu ahankali yana murmushi, tareda rungume wayar a 'kirjinsa tsam, jiyake kamar ya rungume yasmeen.
Na ce, "lallai su Nawaf modebbo an faďa tarkon SO!!!!!!.😜
_______________________________
Haka rayuwar take tafiya, kowannensu yana dakon soyayyar ďan uwansa, amma batareda sun sanar da junansuba.
Dan har yanzu yasmeen bata amince sunyi waya da Nawaf ba, dukda yana tsananin bu'katar hakan, yabi duk wata hanyar dazasuyi magana da juna amma yasmeen ta tosheta, hanya ďaya tarage masa itace momcy, itakuma yanajin kunyar tunkarar ta, yana gudun kuma kar allura ta tono garma.

Yau yasmeen antashi da murnar zuwa gida, tanata farinciki zataga ummarta da abba, mas'ud ne ya kaisu itada Ameena, bayan momcy ta haďa mata shatara ta arzi'ki takaima su umma.
Mas'ud yanayin parking ta shilla da gudu cikin gida, Ameena da mas'ud suka tuntsure da dariya.
Da gudu tashiga kuwa, ta rungume yaseer dake zaune afalo, suka shiga ihun murna su biyu, umma tafito daga ďaki danjin ihunsu, da sauri yasmeen ta saki yaseer tanufi umma ta rungume ta.
Umma ta ce, "nikam karki karyani yasmeen, yasmeen tasaki umma tana turo baki gaba, kai umma bakiyi kewataba ma kenan??, umma tayi dariya, haba ni na isa badole nayi kewar mamana ba, taja hannunta suka zauna.
Yasmeen ta ce, "umma ina abba??, abbanku yafita amma zuwa anjima kaďan zai dawo.
Bayan mas'ud yashiga sun gaisa da iyayen Ameena saiya shigo nan suka gaisa da umma, zuwa sannanma abba yadawo, daga nan saiya tafi akan anjima zai dawo ya ďaukesu.
Anan suka wuni suna mai jin daďin kasancewar su cikin 'yan uwansu, anan yasmeen takeji ashe Nawaf dazai tafi saida yazo yay musu sallama, kuma yana kiransu su gaisa, musamman ma abba da yaseer, dan ita umma tanajin kunyarsa sosai, wato itace yaraina, yamaida sakarai, baya 'kaunarta, itama zata nuna masa baya gabanta bai dametaba, duk a zuciyarta take maganar.
Sai dare mas'ud yadawo ya ďaukesu, yasmeen harda kuka, saida abba yay ta lallashinta sanan, amota su ameena sunata mata dariya, itadai shiru tayi musu, mas'ud yakira Nawaf yasanar masa.
Nawaf bayaso ya nunama mas'ud yafara son yasmeen danzai takura masa da tsokana, dan haka ya ce, "matsalarta ce, dama tasamu akace taje zata wani yima mutane kuka, kaika zauna take maka kuka a mota.
Mas'ud ya ce, "kai malam niba abinda nakiraka kaminba kenan, sai anjima, ďif yakashe wayar.
Nawaf ya rintse idanu, jiyake kamar mas'ud ya kwala masa 'karfe akai, yadafe kai tamkar zaiyi kuka, wai miya hanashi cewa ma abama yasmeen wayar, koba komai aida yaji muryarta, yasan zai rage wani raďaďin, shikaďai yasan yanda zuciyarsa take azalzalarsa a kan son yasmeen, amma ita bata damu dashiba, dolene yaďauki matakin goge soyayyar yasmeen a zuciyarsa tunkafin zuciyarsa tabuga abanza a word. .
Su yasmeen Suka isa gida, saida suka rakata har falon momcy sanan, bayan sun gaisa da momcy suka koma gida ita kuma yasmeen tazauna suka hau hira dasu Anwar.
_________________________________ yau tunda suka tashi su Abdallah suke ďokin ganin wasan su Nawaf dazasuyi, dansunce wasan mai zafine, 'kiri2 Anwar ya'ki zuwa islamiyya saboda ya kalli wasan, Abdallah sai tsokanarsa yake, wai yau su ustaz an ajiye ustazanci saboda kallon kwallo.
Anwar yay tsaki ALLAH kaga abi kabari, inba hakaba zan haďaka da papa wlhy, dakaine yanzu saikace zaka 6ata mini rai kuma, ya 'kare maganar yana turo baki gaba.
Yasmeen ta ce, "barsa kaji auta, ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login