Showing 3001 words to 6000 words out of 74786 words
gayyato babban abokin ango zuwa wannan waje.
Batare da musuba takarb'a takardar tafara kiran NAWAFF SA'ED MODEEBBO.
Takira yakai sau biyar amma bai ko motsaba daga inda yake, tajuyo dan ganin wai waye wannan d'an rainin wayon abokin angon.
Karaf idanunsu suka had'u a k'ar kashin inuwa d'aya, zumbur NAWAFF yamik'e tsaye.
Yasmeen ta ce, "taf tsuntsu daga sama gasashe, azuciyarta take maganar.
shima dai NAWAFF raya abinda zai faru yakeyi dan yasan dole sukwashi 'yan kallo, amma yasan maganin ta..........................โ๐ป
Hahahha yauda budiri tsakanin YASMEEN DA NAWAFF.๐๐๐๐๐
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐LUV U OLL๐๐๐๐๐๐
ยฉ2016
[1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: โโโโโโโ
๐พ NAWAFF ๐พ
โโโโโโโ
NA BILKISA IBRAHIM๐
Assalamu alaikum.
Alhmdllh 'yan uwana kamar yanda nafad'a muku natsaya da rubutu sabida wani dalili.
To Alhmdllh yanzu komai ya dai daita, in farincikin kasancewa daku๐๐๐.
Page๐๐ป5
.....Nawaff ya tsuke fuska, itama yasmeen ta tsuke tata fuskar.
Yak'araso gareta cikin wani taku na isa da tak'ama, wajen yayi tsit ana kallonsu, yayinda masu hotuna suketa haskasu.
Yak'araso daf da ita, tamkar zai shige jikinta, tayi saurin ja baya, ya had'a yatsunsa biyu yana bugawa, yay k'asa da murya yanda ita kad'ai zata iya jinsa, ya ce, "wlhy kika yimini hauka awajennan saina aikata miki abunda 'yan jaridu da mujallu zasu buga a safiyar gobe juma'a.
Dukda tsoro mai tsanani yashigi yasmeen wannan bai hana ta hararar saba, ta rik'e k'ugi cikin tsiwa ta ce, "kai baka isa kasa 'yan jarida yad'aniba, kuma ALLAH shizaimin tsari da sharrinka.
Nawaff modeebbo yad'an d'ago yana kallon yanda hankalin mutane yadawo kansu, saiya saki murmushi na basarwa.
Gaba d'aya gurin yad'auki sowa da fad'in sun dace da juna.
Nawaff yaja tsaki tareda fad'in shashashu kawai, ta ina na dace da wannan mai kama da aljanar.
Yasmeen ce kawai taji furicinsa saikuma mai gabatarwa dayake kusada su tsaye.
Yasmeen tai murmushin takaici ta ce, "ai basu bane shashashun kaine babban shash............kafin tarufe baki ya damk'o hannunta ya murd'a da k'arfi, wani tsananin zafi yaratsata har kwakwalwa, ALLAH yasota fitilar gurun Blue ce tana kuma kunnawa ta kashe, dan haka ba kowa yaga muguntar da Nawaff yake mataba.
Zafin ya ratsata sosai, afusace ta watsa masa mari, da sauri yasaketa yana murza kumatu, itama takoma kusada amarya da sauri ta zauna tana haki.
Nawaff yad'ago da sauri danjin andafa shi, mas'ud yagani tsaye.
Mas'ud ya ce, "plz my bro's ka share kawai, karka bari wani yagane wani abu dake faruwa.
Nawaff ya kalli mas'ud da idanunsa dasukayi jaa, ya ce, "wlhy Mas'ud saina yima yarinyarnan abinda zatayi dana sani arayuwarta, kamar yanda ka buk'ata zan barta ammafa had'uwarmu tagaba batada k'yau ko kad'an, kuma ka rubuta ka ajiye.
Yana gama fad'a yakoma mazauninsa dake kusada ango, mas'ud ne ya wakilcesa, wajan fad'ar duk abinda ake buk'ata.
Asmy ta ce, "yasmeen wai miye had'inki da modeebbo??, yasmeen ta share hawayen fuskarta, ta ce, "karki damu zan sanar miki, amma ba yanzuba.
To shikenan asmy tafad'a, tacigaba da lallashin yasmeen, yasmeen ta ce, "Asmy kiyi hak'uri zan tafi gida, dan kaina yana mini ciwo.
Asmy ta ce, "babu damuwa dear kije gobe ma had'u, ngd da k'ok'arinki.
Yasmeen ta mik'e tana neman Ameena, bayan ta ganta suka fice, duk abinda take Nawaff yana kallonta, suna fita yarufa musu baya, shima mas'ud binsu yayi.
Yasmeen tana k'ok'arin neman balarabe saitaji an fisgota ta baya, tajuyo da sauri, gabanta yafad'i rass dan ganin NAWAFF,
Ya had'e fuska kamar bashiba, yasmeen ta ce, "lfy konaci bashinkane??.
Nawaff ya damk'i gashin yasmeen data d'aure abaya, ya murd'e da karfi, tako kwalla k'ara, saidai babu maijinta saboda hayaniyar wajen tayi yawa, gakuma kid'a yana tashi, gashi a tsakankanin motoci suke.
Cikin sark'ewar murya ya ce, "nikika mara ko??, to wlhy ki rubuta ki ajiye, wannan marin saiya zama FANSAR BUDURCINKI, NA MELODY , saikinyi dana sanin aikata hakan agareni, ya hankad'ata tadaki motar bayanta.
mas'ud dake bayansu yabi NAWAFF da kallon mamaki, shin miyake nufi da marin datayi masa saiya zama FANSAR BUDURCINTA!!!!????.
Da sauri yarufa masa baya, yayinda ameena ta k'araso takama yasmeen dake kwasar kuka, hannunta kawai taja batareda tace mata komaiba, mota suka shiga bala yajasu suka tafi.
Ahanyama yasmeen sai kuka take, dan furicin NAWAFF yayi matuk'ar gigitata,
ya dawomata da tunanin rayuwarta ta baya, lallai itakam tana cikin tarkunan maza azzalumai, shiyyasa takema maza KALLON KITSE na @UT@R H@JIYA@",, shin wai ita haka rayuwarta zata k'are, kowane NAMIJI burinsa yarabata da Abu mafi muhimmanci ARAYUWAR ta, miyasa haka???, mina musu???, miyasa suke son su rabani da mutuncina???, ta fad'a tana wani irin kuka mai ban tausayi,, Ameena da balarabe duk tausayin yasmeen ya cika musu zuciya, dan afili take maganar batareda ta saniba.
Ameena ta rungumeta tana lallashi, dahaka suka k'arasa gida..........................โ๐ป
ยฉ 2016
๐Bilyn Abdul๐
๐Mrs Abdus'salam๐
๐LUV U OLL๐๐๐
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: โโโโโโโ
๐พNAWAFF๐พ
โโโโโโโ
NA BILKISA IBRAHIM๐
Page๐๐ป6
........Nawaff kuwa tafiyarsa yayi yabar mas'ud, mas'ud bai damuba dan dama batare suka zoba, komawa yayi wajen taron dan baikama ta ace suduka sun tafi ba.
NAWAFF kwance afalonsa dayaji kayan more rayuwa iri2 yana kwance saman doguwar kujera idanunsa lumshe, tamkar maiyin barci, amma idanunsa biyu, yana cikin tsananin b'acin raine kawai, tunani yake mizaima yarinyar nan ya huce haushinsa, dan ya tsaneta, hangota kawai yake lokacin data maresa, yakai hannu yashafa fuskarsa.
Yay kwafa, wlhy sai yarinyarnan ta raina kanta inhar yana numfashi.
Kofa aka kwankwasa, ya ce, "kowaye ya shigo.
Wata 'yar aikin gidansu ce, d'auke da tiren kayan marmari, ta d'ora asaman tebirin dake tsakiyar falon, tad'an jawo tebir d'in gaban kujerar da Nawaff yake kwance.
Watama tashigo da kuloli, ta d'ora inda 'yar uwarta ta d'ora, sannan suka duk'a suna kai gaisuwa wajen oga Nawaff!!.
Hannu kawai ya d'aga musu sannan yay musu nuni dasu tafi.
Da sauri suka wuce dan sunsan halinsa baya son wargi.
D'aya acikinsu ta ce, "wlhy talatu yaya Nawaff yana burgeni, dama zaice yana sona!,
Talatu ta rik'e baki, lallai ladidi yau na tabbatar bakida hankali, garama tu wuri ki fidda wannan tunanin a ranki, tun kafin wanima agidannan yajiki, in banda wuce gona da iri, yazaki had'a kanki da wannan had'ad'd'en mutumin, mai ilimi da kud'i, ga k'yau, wanda duniya tasan da zamansa.
Ladidi tayi dariya kujimin wannan talatun, to kika San abinda ALLAH zaiyi ne??.
Talatu ta ce, "A'a.
Tunda suka fita baiko motsaba bare yaga abinda suka kawo masa, wayarsa tashiga k'ara cikin sauti mai dad'i, idonsa arufe ya mik'a hannu ya d'auka, ahankali ya bud'e idanu dan ganin wake kiransa, momcy yaga ansaka.
Wayar ta k'atse aka sake kira.
Cikin ladabi ya ce, "momcy barka da dare.
Daga can ta ce, "barka dai, wai lfy banga kashigoba?, kuma ance mini kadawo.
Wlhy babu komai momcy ina d'akine, nagajine shiyyasa kika ga ban shigoba, inaso nayi barcine da wuri, dan gobe d'aurin auren SAFWAN, banaso nak'i zuwa gashi kuma na safene.
Okey to shikenan, dama nazata ko bakada lfy ne??.
A'a lfyta k'alau momcy na!!.
To shikenan saida safe.
ALLAH yakaimu my sweet mom!!!!.
Saida takashe sannan ya kashe.
Number mas'ud yakira, batareda yayi sallamaba ya ce, "waikai malam kana inane??.
Gani nanma shigowa gidan mas'ud yafad'a.
Kashe wayar yayi batareda ya ce, "komaiba.
Mas'ud yaturo k'ofan yashigo da sallama, bai saurari amsaba, dan yasan bazai samuba, saboda mutumin yau cikin fushi yake.
Kujera yanema ya zauna, tareda fad'in gani neman mi kake mini??.
Nawaff yatashi zaune, yad'an tsurama mas'ud idanu, bayan kamar minti d'aya ya ce, "bro's plz inaso ka taimaka mini??.
Mas'ud ya ce, "to wane irin taimako kenan??.
NAWAFF yad'an cije leb'ensa na kasa, ya ce, "na nemo yarinyar nan, inaso nasan ita wacece?, 'yar kuma wacece?.
Dan wlhy idan banyimata rashin mutunciba zuciyata zata iya fashewa, ALLAH na tsaneta, kuma saina koya mata hankali, daga kaina bazata sake rashin kunyaba, ko kuskurwn marin wani.
Mas'ud yay masa kallon tsaf dan ganin yanda yafita hayyacinsa yau d'aya.
Yaja numfashi, Nawaff! Yakamata kadawo hayyacinka, karka manta kaifa kafara tsokanar yarinyarnan, kamareta, kayimata dariya.
To dankuma yau tarama saikaji haushi, yakamata ku tsaida fad'annan haka tunda kowa yayima kowa, sannan ka janye k'udirinka na d'azu, dakace marin data yimaka shine zai zama fansar budurcinta, Nawaff bansanka da irin wannan halinba, kar ka aikata abinda zaizo ya dami kowa, wannan ba hanyar bullewa bace, kai dama soyayya kuka koma dan wlhy kun dace da juna sosai.
Harara Nawaff ya watsama mas'ud, wadda dama tun d'azu ita yake masa bai ganiba.
Ya ce, "ALLAH kuwa mas'ud yau dawanine yafad'a mini maganar nan wlhy dasai na bubbugeshi, amma............. yay kwafa kaiwai batareda ya karasaba.
Mas'ud yay murmushi ya ce, "amma mi....?, ka karasa fad'a mana, to konima zaka bibbigeni ne?, ka huce haushinka!!,.
Tsaki NAWAFF yayi yatashi zaibar falon, mas'ud ya tuntsure da dariya, tareda fad'in sakai a wahala kenan,, duk wanda dai yaga wannan fad'an naku yasan na masoyane๐.
Har Nawaff yakai k'ofa yadawo ya ce, "kai dallah malam sauraramin!, mixanso a jikin wannan faratun yarinyar mai kama da aljana, kai dana so wannan yarinyar gara naso 'yar k'auye wlhy.
Dariya mas'ud yake tuntsurawa harda hawaye, cikin dariya ya ce, "aii kaima faratunne Nawaff, koka manta?, amma mudai 'yan kallone mijin faratu, mas'ud yafad'a cikin tsokana๐.
NAWAFF ya kula mas'ud yana neman maidashi wani sakaraine, dan haka yashige bedroom yay kwanciyarsa.
Dak'yar mas'ud ya lallab'ashi yafito sukaci abinci.
WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???????, kubiyoni danjin wannan amsar๐.
ยฉ2016
๐Bilyn Abdul๐
๐Mrs Abdus'salam๐
๐LUV U OLL๐๐๐
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: โโโโโโโโ
๐พ NAWAFF ๐พ
โโโโโโโโ
NA BILKISA IBRAHIM๐
Page๐๐ป7
......WAYE NAWAFF SA'EED MODEEBBO???.
ALHAJI sa'eed umar modeebbo shine mahaifinsa, babban alak'aline mai gsky da rik'on amana, bashida tsoro Ko kad'an, yakan yanke maka hukunci dai2 da abinda ka aikata, duk kud'inka ko mulkinka bazaisa ka kub'uta ahannunsa ba, sai dai gskyr ka ta kub"utar dakai.
Kaifi d'ayane shi, idan ya ce, e, "baya cewa A'a.
Alhaji sa'eed bafulatanine irin na daji, dan k'yak'yk'yawane abin so dagani, d'an asalin garin safana ne dake k'aramar hukumar caranchi, safanar ma acikin wani k'yauye suke cikin rugar jauro, amma yanzu yana zaune a kano.
Matarsa d'aya hajiya ummul'khairi, balarabiya ce cikakkiya, k'yak'yk'yawar mace, mai hak'uri da ilimin addini, ga son mutane.
A Egypt ya aurota lokacin yana d'alibin ilimi a jami'ar AL'AZHAR, soyayya sukayi har ALLAH ya mallaka masa ita amatsayin mata.
Momcy Nawaff tafara haifa daga shi ta dad'e bata sakeba, sai bayan shekara bakwai ta haifi Abdallah, sai auta Anwar,
Nawaff k'yak'yawane fari amma ba tas ba, ya biyo momcy sosai, dan shikad'aine yake tsananin kama da ita, kana ganinsa kasan itace ta haifesa, sai dai ita tafishi fari.
Momcy tanada hak'uri batada hayaniya ko kad'an, amma Nawaff yanada zafi, indai wajen haline papa yabiyo Alhaji sa'eed kenan, Nawaff baya son raini ga son girman tsiya da miskilanci, gakuma ilimi, dan yanada sani wajen addini sosai, shima yanada son mutane.
Nawaff yana son k'annensa sosai, duk abinda sukeso yana musu, shiyyasa suma suke sonsa da girmamasa.
Nawaff tun yana primary yakeson kwallo har yashiga secondary, lokancin dayake a secondary sukanje gasar kwallo zuwa wasu makarantun, cikin ikon ALLAH sai sun ciyo kuma Nawaff ne mai zira musu kwallon.
Bayan ya kammala secondary saboda k'aunarsa da kwallo papa, wato mahaifinsa ya nemi shawarar momcy domin kai Nawaff wata makaranta da ake kira School Academic domin k'ara samun ilimi a fannin kwallon k'afa.
Fatan alkairi momcy tayi masa tareda addu'ar samun nasara arayuwa.
Babu dad'ewa aka kaisa wannan makaranta ta (School Academic dake jihar kwara) iyaye da 'yan uwa suka bishi da addu'ar samun nasara, aiko ansami nasarar, dan addu'ar iyaye babbar katanga ce.
In tak'aicemuku dai, Nawaff bai rufa shekara biyu ba yasamu nasarar shiga jerin wad'anda (NAJERIA's Foodboll Asocion NFF) suka gayyata zuwa abuja dan yin screening nazuwa kwallon kasa da kasa, na 'yan kasa da shekara 17, (under 17 play engle of Najeria ).
Awannan screening ansha gwagwar maya, har ALLAH yabawa Nawaff nasarar fitowa d'aya daga cikin wad'anda aka zab'a, harda muk'amin capten na k'ungiyar kwallon kafar Najeria wato ta (under 17).
Shigarsa (under 17) ta bashi damar wawuro nasarori da dama, dan sun ciyo kofin duniya na wannan lokaci, yasamu damar zurama Najeriya kwallo 9, wannan yasa yazama (here Gold scores )na wannan gasa, har aka bashi k'yautar, ( Golden but)
wannan nasace tajawo hankalin manyan club club na duniya kansa.
Samun wannan nasara yasaka family nasa cikin farinciki, yayinda shugaban k'asa na wannan lokacin ya shirya musu liyafar cin abinci tareda shi, da k'yautittikan ban girma.
Bayan dawowarsa daga kwallon k'asa da k'asa wani (club na F,C 20)dake k'asar HOLLAND yasami damar d'aukarsa.
ya rattab'a hannuโ๐ป da k'ungiyar na tsawon shekara 5, shigarsa wannan club ya k'ara fito da kwazonsa, yasamu nasarrar buga musu kwallaye masu yawan gsk.
Awannan lokacin duniyar masana kwallon k'afa suka saka idanu k'ur akan Nawaff, manyan club club suka fara jawarcinsa.
Daga k'arshe wani club mai fad'a aji yasamu nasarar sayen NAWAFF.
To ayanzu haka dai girma da cigaba yazo masa, yasamu nasarar tsintar kansa a cikin club d'in (Barcelona F,C )dake k'asar Spain, wannanne ya tabbatar dashi zama babban d'an kwallon k"afa, wanda duniya tasani take kuma alfahari dashi, musamman ma k'asarsa NAJERIA.
yanzu haka yazo hutun k'arshen shekarane da sukan samu, kwanansa d'aya dazuwa suka had'u da Yasmeen, har ya takaleta.
Wannan shine tarihin NAWAFF SA'EED MODEEBBO atak'aice....................โ๐ป
ยฉ2016
๐Bilyn Abdul๐
๐Mrs Abdus'salam๐
๐LUV U OLL MY FAN's๐
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: โโโโโโโ
๐พ NAWAFF ๐พ
โโโโโโโ
NA BILKISA IBRAHIM๐
Page๐๐ป8 & 9
.....Mas'ud d'an abokin papa ne Alhaji khasim, tare sukayi karatu da papa a Egypt shima masanine ab'angaren ilimin addini danshi har isalamiyya gareshi.
NAWAFF da MAS'UD tare suka tashi tun suna k'anana, bayan sun gama secondary ne kowa yakama inda yafi wayau, Nawaff yatafi makarsantar koyon kwallo, Mas'ud yatafi kasar INDIA domin k'aro ilimi a fannin Likitanci.
Yanzu haka shi cikakken Likitane, a babban asibitin Aminu kano, Nawaff bashida wani aboki wanda ya wuce mas'ud, haka shima Mas'ud.
Sun shak'u da juna matuk"a suna kuma k'aunar juna, saidai halinsu ya babbanta, domin mas'ud mutumne mai sanyi da hak'uri, amma Nawaff yanada fad'a, kuma baya son hayaniya.
Basa shaye2 bare neman mata, hasalima shi Nawaff baya dariya gaban mata, dan ya ce, "yawan yima mace dariya yakan sa ta rainaka.
Hummm kunji son girma, naga yannda za'ayi yayi aure tunda baya son mata su rainashi๐.
A'ban garen yasmeen kuwa tunda suka shiga gida take kuka, umma bata tanbayeta abinda yafaruba, saidai tanata lallashinta, yaseer yashigo hannunsa rik'e da leda, yazauna kusada umma yana turo baki.
Umma ta ce, "kaikuma lafiya??, ya nuna mata yasmeen data d'ora kanta saman cinyar umma, waishi adole kishi, ya ce, "ALLAH umma wanima saiya d'auka itace auta!.
Umma tayi masa da'kuwa tana fad'in kaci gidanku bakaga halin datake ciki bane.
Yaseer yad'an le'ka fuskar yasmeen saiyaga hawaye, yad'an zaro๐ณidanu yana fad'i sister miya faru dake??, tad'ago tana kallonsa saikuma ta fashe da kuka, da sauri yadawo kusada ita yana share mata hawaye, ya ce, "haba auntyna yakamata ki daina saka damuwa azuciyarki haka nan, ki manta da komai na rayuwa, idan kuma wannan d'an iskanne yake saka ki kuka kiyi ha'kuri ALLAH zai mana maganinsa, kuma insha ALLAHU abinda yake burin bazai ta'ba kasan cewaba, kullum muna miki addu'oin samun nasara a rayuwa, yafad'a shima yana hawaye.
Da sauri yasmeen tatashi ta rungimeshi suka cigaba da kuka, sun bama umma tausayi, dan haka itama ta share nata hawayen, saida sukayi kuka mai isarsu, daga baya sukayi shiru.
WAI WACECE YASMEEN????.
FATIMA shine cikakken sunanata, malam Yakubu shine mahaifinta, su 'yan asalin kasar Nijar ne, awani gari kwangwalan, kwangwalan yana nan kusada jihar katsina, dan za'a iya cewa a boda suke.
Kharima itace mahaifiyarsu wato umma, malam yakubu makiyayi ne a garin kwangwalan mutumne mai tsananin hak'uri, 'yan uwansa basa sonsa, kasancewarsu 'yan ubane, shi kad'ai mahaifiyarsa ta hafa a gidansu.
Yaransa biyu Fatima sunan mamansa aka saka mata, shiyyasa suke kiranta da yasmeen, saikuma ABUBAKAR shima dai sunan baban umma ne, shiyyasa suke kiransa da