Showing 15001 words to 18000 words out of 74786 words

Chapter 6 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

354

Yasmeen ta girgiza masa kai batareda tayi maganaba.
Murmushi yaseer yasaki, ya ce, "tomiya farune?? Ko zasuzone??, nanama kai ta kad'a masa alamar eh.
Yaseer yami'ke yana fad'in bari nasanarma umma to.
Da sauri yasmeen ta ce, "malam ban saka kaba, ko saurarenta bayyiba ya fice, yanaji tana kwala masa kira amma yay mata banza.
'Dakin umma yanufa, tana zaune tana linke kaya, ya zauna kusada ita.
Umma ta ce, "autana lafiya dai ko??, yaseer yay murmushi yana fad'in lafiya lao umma, dama aunty ce zatayi ba'ki shine na ce, "bari nasanar miki, dan kinsan itadai ba fad'a zatayiba.
Umma ta ce, "gsky ne d'an albarka, amma wad'anne irin ba'kine??, mijinta ne zaizo.
Umma tayi murmushi ta ce, "madallah, ALLAH yakawoshi lafiya, sai azo ashirya musu kayan tarba kenan.

Abuja (Trening cam).
Nawaf zaune bisa kujera agefen fili, yana zaune yana hutawa bayan sun gama trening shida sauran 'yan wasa, zaune yake amma ya kwantar da bayansa a jikin kujerar, hannunsa ri'ke da waya, da'alama yana chatting ne, dan naga saifaman murmushi yakeyi.
ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake wringing, cikin murmushi ya ce, "shegen sama sai yanzu katuna dani.
Mas'ud ya ce, "A'a dama kana raina, banaso na takura makane ko kana uzuri.
Ayya Nawaf yafad'a, kunje gida lafiya??, lafiya lao mukazo wlhy.
Zaka shigo yaune?, ito gani dai, idan na samu dama zan zo, idan kuma banzoba zan kalla anan insha ALLAHU.
wane uzuri gareka dazai hanaka zuwa kallon wasanmu na yau??.
Hhhh, zanje ganin amaryane.
Amarya kuma?, a ina??.
Hhhh lallai mutumina kana sha'aninka, to zanje ganin amryarkane, dansu papa sunce yakama naje kafin kadawo.
Tsaki Nawaf yaja, tareda gyara zama.
Tomiye najan tsakin, ko bakaso naje saika dawone?.
Kaga malam idan zaka kabar tsayani, idan kaje kabar tunawa dani, ALLAH idan wannan maganar tasa ka kirani to zan kashe wayata, inada aikinyi.
Mas'ud ya ce, "to kashe mana, idan kakashe sai akace maka zanji haushi......
Kafin mas'ud yarufe baki Nawaf yakashe wayar d'if,, dariya sosai mas'ud yakeyi, saida yayi mai isarsa sannan yami'ke yana fad'in wannan man d'in wlhy d'an yawane..

4:30pm
Karfe hud'u da rabi direba ya sauke su mas'ud a 'kofar gidansu yasmeen, dayake shi yakawosu papa ranar, dan haka papa ya ce, "yakawo su mas'ud gidan.
Wayarta mas'ud yakira ya ce, "munzo amarya.
Yasmeen ta ce, "to, gaba d'aya batada walwala, daka ganta zaka san tana cikin damuwa, ita azatonta harda mijin nata aka zo, dan haka gabanta yafara dukan tara2.
Yaseer ta turo ya kaisu falon abba, Abdallah ya ce, "lallai indai kaine 'kanin antyn mu, to kuwa yayanmu ya more.
Dariya kawai yaseer yayi ya ce, "musu yana zuwa.
Babu dad'ewa yacika musu gaba da kayan ciye2, saida yagama kawo komai sannan yasmeen tashigo falon 'kirjinta yana dukan uku uku.
Kujera ta samu nesa dasu ta zauna, sanye take cikin ba'kar atamfa riga da sket, ta yafa farin mayafi har saman kai.
Suduka kallonta sukeyi, ta ce, "ina yininku??, mas'ud ne kawai ya amsa, Anwar yataso yadawo gefenta, ya ce, "aunty aiimu 'kannenki ne, muzamu gaisheki, ina yini, kad'an ta d'ago tana kallon Anwar saida gaban ta yafad'i domin ganin yayi mata kama da wani data tab'a sani.
Ta amsa tana murmushin ya'ke, Abdallah ma yadawo d'ayan gefenta ya gaisheta, nanma ta amsa masa cikin murmushi.
Mas'ud ya ce, "amaryarmu!!.
Na'am ta amsa tareda d'ago kai tana kallon mas'ud, suduka sukaima juna kallon mamaki, kardai ace wanan ne mijin nawa yasmeen tafad'a a zuciyarta.
Saida kama tatuna daya kirata ya ce, "shi abokin mijintane, toko ina mijinki oho? ?
Mas'ud ya ce, "dama kece amaryar tamu, lalali nayi matu'kar farin ciki da faruwar hakan ALLAH ya sanya alkairi.
Ita dai yasmeen ta kasa furta komai, amma idanunta sun cika da kwalla, dan batasan waye zai kasance mijintaba, tunda gashi har abokinsa yazo shi yakasa zuwa.
Kamar mas'ud yasan tunanin datakeyi, ya ce, "megidanki yana neman afuwarki, shima ya nan zuwa nan bada dad'waba, dan yanzu haka yana abuja, amma nanda nextweek zaizo insha ALLAH.
'Dan murmushi yasmeen tayi tareda fad'in babu damuwa ALLAH yakaimu.
Sukace amin dai.
Nan Abdallah da Anwar suka shiga zuba mata surutu, har saida mas'ud ya ce, "su tashi su tafi.
Bayan sun shiga sun gaida su umma sannan suka tafi.
Ji sukayi kamar karsu tafi, dan matar yayan nasu ta burgesu, gata 'kya'ky'kawa, ko amota hirarta sukayi tayi har suka isa gida.
Nanma sukaita bama momcy labarin surukarta, da karramasu da akayi musu agidansu yasmeen.
Momcy taji dad'i sosai, itama ta 'kagara taga surukar tata.
Yaseer yataya yasmeen kwashe manyan ledoji dasuka kawo cike da sayayya ta birgewa.
Lamarin yabama yasmeen mamaki, amma taji har azuciyarta zata iya zama da mas'ud amatsayin miji, inhar dashine mijin nata, dan alamunsa suna nuna mutumne mai ha'kuri.
Yau ko abincin dare bata ciba tana d'aki kwance abinta.
Abba ya ce, "aje akira masa ita, koda yaseer yashiga d'akin saitayi kamar tana barci.
Yaseer yadawo ya ce, "barci takeyi..
Bayan fitar yaseer babu dad'ewa wayarta tahau wringing, tayi kamar bazata d'aukaba, saida takusa tsinkewa sannan ta d'auka ta kara akunnenta.
Amma daga can an'ki yin magana, ta daure tayi sallama, nanma akayi mata shiru, a'kufule ta ce, "wai dan ALLAH wanene??.
Cikin gadara taji ance, zaki baya fad'ar kansa, saidai risinawar namun daji ta bayyanar da matsayinsa.
Yasmeen ta ce, "huuuum saidai kayi rashin sa'a ni mutum ce ba dabba ba.
Tana kaiwa nana taja tsaki ta kashe.
To shima dagacan tsaki Nawaf yaja, yana wani yatsine, fuska, shifa dama papane ya takura masa akan saiya kirata, shine zata wani kashe masa waya, lalaima yarinyar nan zanyi maganinki kwarai da gsk.
Juyawa yayi wajen 'yan uwansa 'yan wasa dan dama wasa zasu fara, yakirata kafin lokaci yacika.

9:00pm
Yauma dai Abuja international stadium cike take da 'yan kallon wasa.
Yau Najeria zasu buga da kamaru.
Bayan shigowarsu Nawaf cikin fili, sukayi addu'oi da sauran abinda yadace, aka fara wasa.
Yaukam wasan yana tafiya dai dai, dan 'yan Najeria suna nuna kwazo, cikin kwarewa suke gara kwallon, yayinda 'yan bayan fage suketa zugasu da ihu.

Har d'aki yaseer yaje yataso yasmeen wai tazo ta kalli kwallo, hararasa tayi takoma ta kwanta, dan tana cike da haushin rainin hankalin da'aka yimata yanzu a waya.
Dayaga zata b'ata masa lokaci saiya fito kawai dan ya kalli wasansa.

⚽har aka tafi hutun rabin lokaci, babu wad'anda suka zura kwallo.
Dan haka da'aka dawo kowa yayta 'ko'karin akan son yaga yazura kwallon, amma har lokaci yarage saura minti10 babu abinda ya canja.
Ana saura minti1 atashi Nawaf yasami nasarar antayawa Najeria kwallo a raga⚽😃😀😘☺👍🏻🖐🏻nantake 'yan Najeria suka hau ihun murna gurin ya kwaure da hayaniya.
Da'kar aka lafa, bayan 'kara minti 7 da akayi.
Acikin minti na 5ne kamaru suka so zira kwallo⚽amma golan Najeria ya cireta.
Antashi 1-0
Najeria tanada 1 & kamaru 0

Can na hango Nawaf yad'aga gorar ruwa yana kwan kwad'a, yayinda suke tafawa da hannu d'aya da sauran 'yanwasa, kowa yazo akad'an tafa saiya wuce, wasu kuma sai an d'an rungumi juna.
'Yan kallo kuma sunata d'aga 🇳🇬Najeria suna wa'ka.
Yayinda muta nene kamaru kowa fuska ahad'e😟🙂😒😞😜😜.
....................✍🏻







© 2016


💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻18

BAYAN KWANA BIYU
Najeria suka buga wasa da gini, sai dai wanan wasa baiyima Najiria dad'iba, dan antashi 1-1 amma yau ba Nawaf ya zura mana kwalloba.
Dana kalli Nawaf d'inma sainaga baya cikin walwala, na ce, "yau miskilanci 'yan mazan ya motsa.

KANO
faisal ma an sallamesa saidai har yanzu yana zuba sambatunsa, duk ya rame yayi ba'ki, sai ro'kon iyayensa yake akan subarshi yaje gidansu yasmeen, 'kila idan yabata ha'kuri ta ha'kura tadawo gareshi.
Tun iyayen na d'aukar lamarin nasa wasa har suka koma tausayinsa, idan yana surutai hajiya jummai har kuka takeyi masa, gabad'aya sun rasa kansa, bayada wani zance saina yasmeen.
Hajiya jummai ta ce, "Alhaji kodai zuwa zamuyi mu ro'ki iyayen yasmeen ne?, 'kila su tausayamana su warware wancan auren, subama faisal.
Alhaji buba yay shiru yana nazarin maganarta, zuwa can ya ce, "kina ganin hakan zata faru?, kuma idan sun yarda shi wanda ya auri yasmeen d'in zai amince??.
Hajiya jummai ta ce, "to Alhaji saimu gwada, kuma ko biyansa yakeso muyi ai sai mu biyasa ko nawane, indai zai saki yasmeen faisal ya aura, karmuzo d'anmu ya susuce akan abinda baifi 'karfin saba.
Na ce, "hummm aikodai wannan tafi 'karfinsa, dan ba kowacce mace kud'i ke iya sayaba.

KIRA
mu mata munada al'adar cewa sai mun auri mai kud'i, kuma hakan ba daidai bane, kedai amatsayinki na d'iya mace kamata yayi kiyi addu'a ALLAH yabaki miji nagari mai 'kaunarki da gsky.
Wlhy masu kud'innan damuke hari ba kowane yadamu da fita ha'k'kin iyalinsaba.
Musamman ma mazan hausawa, idan suna samun kud'i sunfi maida hankalinsu ga neman kud'in fiyeda 'ya'yansu da matansu.
Wani saiya had'a wata uku zuwa hud'u baya 'kasar, yabar matar cikin damuwa da kewa, shikuma yanacan tareda karuwai a hotel, to dan ALLAH miye ribar auren irin wanan mai kud'in.
Idan baki kai zuciya nesaba saiki fara bin mazan waje da aurenki, ALLAH ya kiyayemu.
Idan kuwa kika auri talakannan daba kiso, duk inda yafita zuwa yamma yadawo, zai kula dake zai kula da 'ya'yanku, UBANGIJI ALLAH yasa mu gane amin.

Yasmeen kuwa tana cikin damuwa, tanaso ta koma makaranta amma abba ya ce, "tabari mijinta yazo ta gaya masa, tayi kukan harta gaji dan tanaso takoma makaranta gashi anata wuceta a lectures.
Yau suna zaune afalo harda umma da abba, sunata hirar gida, abba yana cewa lokaci kad'an yarage suje kwangwalan dansuga dangi dangi su gansu, yaseer yanata murna, amma yasmeen ko motsi batayiba.
Abba ya ce, "mamana lafiya dai??, tai firgigit tana fad'in lafiya lao abba, ya ce, "inafa lafiya munata magana amma ba'kya tare damu, zonan mamana naji damuwarki kinji.
Jiki a sanyaye yasmeen ta tashi taje kusada 'kafafun abba ta zauna, yadafa kanta yana fad'in mike damunki? fad'amin!.
Saida ta matso hawaye sanan ta ce, "abba makaranta ta.
Tofa, abba ya fad'a, yanzunan dama saboda bokonnan kika takuri kanki, to aii na ce, "ki bari mijinki yazo saikuyi magana.
Babansa yakirani d'azu ya ce, "gobe zasuzo insha ALLAHU, dama baya nanane shiyyasa bai zoba.
Cikin sigar lallashi ya ce, "kiyi ha'kuri kinji mamana, ki d'auki duk abinda ya sameki amtsayi 'kaddara.
Yasmeen ta d'aga kai tana hawaye,. Abba ya ce, "yauwa mamana ALLAH yay muku albarka kunji, ya tsare mana ku.
Umma da yaseer sukace amin.
Daga nan yasmeen tad'an saki jikinta tana d'an saka baki a hirar tasu, amma ba sosaiba.

NAWAFF
yau da yamma Nawaf ya iso kano, zaid'an kwana biyu ya koma abuja, kafin aci gaba da wasa.
Sunyi murnan ganinsa, momcy ta shafa kansa cikin hausarta dabata gama nuna ba ta ce, "my dear duk ka rame wlhy, mike damunka haka??.
Nawaf yad'an cije leb'ensa na 'kasa ya ce, "momcy wanan auren da papa yay min mana, ALLAH bazan 6oye mikiba bana son aurenan momcy, ya'karasa fad'a cikin raunin murya.
Momcy ta kwanto dashi gefen kafad'arta ta ce, "kayi ha'kuri Abbuna ina ji ajikina wanan auren Alkairine a gareka, kuma yanda su Abdallah suke bani labarin matar taka da gidan data fito duk masu mutuncine, da tarbiyya.
Banaso akan aurennan kabari sa6ani yashiga tsaka ninka da papan ku, ka danne zuciyarka ka koyi son matarka tunkafin tadawo hannunka.
Zanta tayaku da addu'a insha ALLAHU, itama ALLAH yacusa mata sonka kaji, dukda nasa modeebbona abin sone ga kowacce mace, babu macen dazata gansa ta ce, "bataso, momcy ta 'karashe maganar da tsokana.
🙈hannu yasa ya rufe idanunsa don kunya.
Momcy tayi dariya, ato idan kuma bakaso mutafi saudia kaza6a cikin dangi, gama ummuhabeba nan kullum damuwarta tana kanka, kaga sai kawai musha biki.
Nawaf ya zaro idanu😳 ya ce, "momcy yi shiru kar papa yaji, danni bana ra'ayin zama da mata biyu, kuma ma bana son ummuhabeeba tacika 'kyau dayawa nikuma bana son macen data cika 'kyau gsky.
Tofa, momcy tafad'a, wanan kuma wani sabon idea ne na rashin son auren 'kya'ky'kyawar mace??.
Nawaf yay murmushi har fararen ha'koransa suka fito, ya ce, "A'a my sweet mom ra'ayina ne nidai!!!....
Abdallah ya shigo da sallama, Nawaf ya ce, "ka amso mini?, eh yaya na amso, na kaimaka d'akinka banyi zaton kana nanba aii.
Okey babu damuwa, amma yau miya hanaka zuwa islamiyya ne??, Abdallah yad'an sosai gefen wuyansa yagyara zama zai shararo 'karya.......Nawaf ya dakatar dashi ta hanyar d'aga masa hannu🖐🏻kaga basai kafad'aba, dan nasa 'karya zakamin.
Momcy ta ce, "aii dama jira nake kadawo na sanar maka kwata2 Abdallah baya son zuwa islamiyya, danshi bai biyo halinkaba, tun kana shekara sha biyar ka sauke ALKUR'ANI, amma Abdallah har yanzu baikai ko izufi 50 ba nakula Anwar ma yakusa kamosa.
Harara Nawaf ya watsa masa, ya ce, "wato kai nakula kaine mara ji d'in gidanan ko?, wlhy ka maida hankalinka kajiko, ku a tunaninku karatun boko shine wayewa ko??, amma ai baka ta6a fashin makarantar bokoba ko??.
Kun manta karatun bokon iyakarsa nan duniys, karatun islamiyyar dabaku basa muhimman cinba shine zai zame mana tudun dafawa awata rana mai cike da rud'ani.
Wlhy daga yau nasake jin bakaje islamiyyaba sai ranka yayi matu'kar 6aci, tashi kabani waje sakarai kawai.
🚶🏼sum sum Abdallah yatashi yashige d'akinsa yana zum6ura baki.

WASHE GARI
Tunda wuri umma da ameena suke hidimar had'a abubuwan tarbar ba'ki amma banda yasmeen data shige d'aki wai batada lfy.
Dan haka umma taje ta nemo Ameena 'kawar yasmeen d'in dan ta tayata.
Yasmeen kuwa tana d'aki cikin fargaba da damuwa, wai yau zataga mijinta, ko zaizo mata da mutuncine?, kokuma sa6anin hakan??.
Har zuwa azahar tana d'aki tana kullawa da kwancewa, dakuma fad'uwar gaba.

a wannan lokacin kuwa Nawaf yanacan anci kwalliya cikin 'kananun kaya, ya fito shida mas'ud sai zabga 'kamshi suke, 6an garen su momcy suka nufa, afalo suka iske momcy da papa dasu Anwar.
Papa ya ce, "kunyi 'kyau sai dai modeebbo koma ka canjo kaya wad'anan basu yiba.
Nawaf yabi jikinsa da kallo, papa miye aibun wad'anan kayan yafad'a cikin shagwa6a.
Papa ya ce, "aibunsu dasuka kasance 'kananun kaya, kai bakaga shigar da d'an uwanka yayi ba mas'ud.
Gidan surukai zakujefa, kuma yau zasu fara ganinka, sai kaiwai suganka da 'kananun kaya kamar d'an yahudawa, maza kaje ka canjo shadda ina nan ina jiranka, dan kuna 'kara 6ata lokaci.
Badan Nawaf yasoba yakoma ya sako farar shadda 'kal d'inkin zamani, harda saka hula, kai yayi 'kau wlhy, saiya fito asalin balarabensa, dan dakaga Nawaf dole ka kirashi ci kakken balarabe.
Nawaf dogone sosai yanafa jikin 'karfi sabida training dayakeyi, yana da suffa irinta kosashshen xaki, daga sama 'ka'k'karfane sosai cikinsa ad'ame tamkar baya cin abinci, farine amma ba tas ba, kalar fatarsa irinta larabawace jaa kenan zamuce, yanada suma mai yawan gske mai kuma laushi d 'kalli dukda tanashan gyara da mayuka masu tsada, yanada d'an saje wanda ya tsaya iya kumatinsa dai dai kunne, ida nunsa masu 'kyau da haske ga girar ido zara zara, kai komaidai yaji d'ammmmm.
Papa yay murmushi yauwa ko kaifa modeebbo, yanzu kaga shine mutuntawa, sai kuje banaso naji wani abinda zai 6ata mini rai, kuma ku sayi wani abu akai mata kar aje hannu rabbana, ku gashe mana dasu.
Mas'ud ne kawai ya amsa.
Abdallah ya ce, "yaya dan ALLAH zanje.
Harara Nawaf ya watsa masa wadda tasakashi saurin rufe baki.
Sukuma suka fice.
Papa ya ce, "huum d'an yanzu saka barsa da halinsa kawai.

Amota mas'ud ya ce, "mutumina baka ta6a kwalliya irin ta yauba wlhy, gashi yau ranar shan mamakice.
Nawaf ya ce, "wane irin mamaki kuma bro's??, wani murmushi mas'ud yayi, ya ce, "sai munje zaka gani!".
Baki Nawaf yad'an ta6e yana fad'in ni babu wani abin mamaki dazan gani malam.
Mas'ud ya tuntsure da dariya , banza Nawaf yay masa.
Sun isa 'kofar gidansu yasmeen, mas'ud ya ce, "ka kirata kace mun iso mana.
Harara Nawaf ya sakar masa, ya ce, "lallai ashe zamu kwana anan kuwa, indai har saina kirata ne.
Girgixa kai kawai mas'ud yayi yad'akko wayarsa ya kira yaseer ya ce, "yaseer gamu munzo.
Yaseer ya ce, "to yaya ku shigo falon Abba.
Mas'ud ya kalli Nawaf bayan ya gama wayar, ya ce, "to saika fito ance mu shiga, baki Nawaf ya ta6e ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login