Showing 51001 words to 54000 words out of 74786 words
jiki yana 6ari tayi abinda yace, ta gyara ďaurin ďan kwalinta.
Fuska aďaure ya ce, "kizo ki shafa mini mai, ta bishi da kallo tana mazurai, ta daure ta ce, "bafa hannunka bane mai ciwon?, cikin rawar murya tafaďa.
Idanunsa alumshe ya ce, "nasani, koban isa nasakaki aiki bane??.
Ta ce, "ni ba haka nake nufiba, amma.......
Yay saurin katseta da faďin amma mi???, tai shiru tana shirin yin kuka, yay sauri faďin karki yarda waďan nan hawayen su zubo, idan kuma ba hakaba zan aikata miki abinda ba'kya so,, kuma kiyi maza kizo ki shafa mini mai idan ba hakaba hummmmyim ya 'kare maganar dayin kwafa.
Da sauri tazo ta zauna gefensa, ta ďibi mai ahannunta tana murzawa, amma takasa shafa masa, sai mulmulashi take ahannu, yagaji da mi'ka mata hannu ya buďe idanunsa dasuke lumshe akanta.
Tai 'kasa da idanunta, ya ce, "kin za6i komai yafaru kenan........? kafin yarufe baki ta kama hannun tafara shafa masa mai, ya lumshe idanu yana murmushi jiyake kamar tana masa susa, tagama ya mi'ka mata ďayan hannun, dahaka dai aka gama shafa man, ya ce, "saura kaya.
Ta marairaice fuska tana faďin dan ALLAH kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba ka tausaya mini.
Yami'ke yana murmushi bataredaya tanka mataba, cikin 'kananun kaya yashirya, yagama ya ďauki waya yay musu odar abinda zasuci, itadai tana zaune tana kallonsa.
Babu daďewa aka kwankwasa 'kofar yabada izinin shigowa, mai kawo abincine, ya ajiye yafita.
Ya ďauki nasa ya tura mata nata gabanta yana faďin minti20 nabaki kiyi maza kici abincin nan, daga nan ya hau cin nasa batareda ya sake bi takantaba.
Itama saitaja abincin taci, dan dama yunwa takeji, kusan tare suka gama, ya ďauki magungunan sa yasha, yana gamawa yatashi yadawo kujerar datake zaune, kusada ita yazauna, itakuma taďan matse jikinta kamar tana jinsanyi.
Yaďan murmusa tareda zamewa ya kwanta yaďora kansa bisa cinyarta yana faďin matsoraciya kawai, ya lumshe idanunsa tamkar zaiyi marci.
Aka kwankwasa 'kofar yasmeen tayi shiru kamar batajiba, Nawaf ya ce, "kowaye yashigo.
Abdallah da mas'ud da Anwar ne, suka shigo da sallama, yasmeen tashiga ture kan Nawaf, amma ko motsi baiyiba, suka zauna mas'ud ya ce, "a lallai mara lafiya ansamu harda so............, da sauri Nawaf ya buďe ido yana harararsa, kaifa mas'ud ďan iskane wlhy zaka fara ko??, mas'ud yay dariya to nabari bro's.
Su Anwar suka gaisheshi da tambayar yajiki??, ya ce, "musu da sau'ki, suka gaisa da yasmeen, itadai duk kunya ta isheta amma Nawaf ko ajikinsa, hirarsa yaketa zubawa.
Ana haka momcy da papa suka shigo, azatonta Nawaf zai tashi, amma saitaga ya 'kara gyara kwanciyama, yasmeen ta rissina tana gaishesu, Nawaf ma ya gaishesu, suka tanbayeshi ya 'karfin jikin ya ce, "da sau'ki, Papa ya ce, "to ALLAH ya'kara afuwa, mu bari muje wani wuri saimun dawo..
Suka ce, "to adawo lafiya", Anwar ya ce, "papa dan ALLAH zanje.
Papa ya ce, "A'a kabari zuwa jibi zamuje tareda ku, saimun dawo, suka fice.
Abdallah yashiga tuntsura dariyar mugunta, Anwar ya fashe da kukan shagwa6a, yana faďin yaya kagansa ko.
Nawaf yadakama Abdallah tsawa dallah malam yima mutane shiru, ubanmiye abin dariya anan, Abdallah ya tsaya da dariyar yan toshe baki, wayar mas'ud tayi wringing yami'ke yana faďin ina zuwa.
Nawaf ya ce, "malam babu wani kana zuwa kace kawai katafi soyayya.
Mas'ud ya fice yana dariya, aii dai ba haramun zanyiba, kuma na fika, Nawaf ya murmusa azuciyarsa ya ce, "nima ina hanya, afili kuma sauya kalli yasmeen, suka haďa ido, tayi saurin janye idanunta daga kallonsa.
Shima saiya kauda fuska yana murmushi.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya da sauri, jikin Nawaf yana sau'ki yanda yakamata, sannan agefe ga son yasmeen yana ďauwainiya dashi, saidai yakasa furta mata, dukda kwayar idanunsa da aiyukansa suna 'ko'karin fallasa asirin zuciyar tasa.
Mas'ud ne kawai ya fahimci halin dayake ciki, amma shima bai nuna masaba tunda bai fito fili ya sanar masaba.
Itakuma yasmeen dayakeyi dan ita takasa fahimtar ainahin gskyar sa, saboda kallon maza datakeyi abai bai, saka makon hare2 dasuka kawoma rayuwarta abaya, sai take kallon kowane namiji da irin wannan sigar yake kallon mace, dukda itama tana fama da dakon soyayyar tasa azuciyarta, amma ita takan gwada 'ko'kari, konace jarumtar 6oyewa, wannan yasa gwarzon nata yakasa fahimtarta yake mata kallon kitse afannin san maso wani, (wato yana sonta tana son faisal) wannan yasa yake kasa fallasa sirrin zuciyar tasa saboda tu'ku'kin ba'kin cikin kishi dakanyi ďawauniya dashi aduk lokacin da kwarin gwuywar faďa matan ya iso kwakwalwarsa.
Shaiďan yakan kawo masa taswurar bazata amshi soyayyarsaba, dan tanada wanda takeso, 'kaddarace kawai tarabasu, shikuma ta haďasu.
Aduk lokacin da shaiďan yagama masa wannan karatun yakanji baya son ganin yasmeen akusadashi, shikansa yakanji haushin kansa yanda yabari sonta da 'kaunarta suka yimasa kamun kaxar kuku, shikam ya yarda ALLAH ne ya yanka masa kazar wahala, shiyyasa yaketa faman figarta, gashi kuma gashinta yagaza 'karewa, yarintse ido yana fitar da huci mai zafi daga bakinsa. A haka yasmeen tafito daga bayi tasamesa.
Tabishi da kallon mamaki, wannan irin huci haka kamar wanda yake filin gwada 'kwanji.
Yajuwyo yana kallonta shima, taďan kauda idonta daga kansa, cikin sar'kewar murya ya ce, "lafiya dai?", yasmeen ta ce, "'kalau mika gani??, ya girgiza kai yana faďin babu komai.
Ta juya tana linke kayansa daya cire yabajesu akan gadon, wayarsa dake bisa dirowar gefen gadon tahau kara alamar kira, ta ďauka tanufi inda yake ta mi'ka masa, ya ce, "waye?, batareda ya kar6aba.
Ta kalli fuskar wayar sannan ta kalleshi ta ce, "number ce babu suna,, yaďan ďaga kafaďa shikenan kowaye bazan ďaukaba.
Cikin mamaki yasmeen ta ce, "saboda mi??, yaďan tsura mata idanu, ya ce, "saboda bana ďaga ba'kuwar number, kuma wanan layin nawa kowa zai iya samunsa, dan shine number gama gari,, yasmeen ta ta6e baki, to kasan bazaka rin'ka ďagawaba miyasa karin'ka bada number??.
Nawaf yaďan zaro ido waje tofa 'yar jarida akaina zaki fara aikin nakine??, A'a ALLAH yabaka ha'kuri malam niba faďa nake nemaba.
Nawaf ya murmusa, ainima ba faďan nake nemaba, ni dan ALLAH ma zokimin tausa.
Tausa kuma?, aiini idan zaka saka bindiga akaina bansan yanda aikeyin tausaba.
Nawaf ya ce, "hummyimm aiko dole ki koya, dan ni mutumne maison idan yagaji amin tausa, ya 'kare maganar yana wani kanne ido ďaya, yasmeen ta kauda kai tana ta6e baki, ta ce, "dan kuma kanaso sai akace dole nice zan maka.
Yay wata sassanyar dariya yana faďin, yarinyarnan nakula har yanzu 'kuruciya tana damunki wlhy, amma karki damu, nakusa kaiki makarantar hankali, kuma nine malamin.......bai gama rufe bakiba aka 'kara kiran wayar.
Yasmeen ta ce, "babu 'kyau wula'kanta mutanedai.
Yay murmushi nima ba wula'kantasu nakeyiba, inada hujjar 'kin ďagawa, duk inda mutum yaga wannan no ďin ya ďauka to yaga dokokin dana kafa, na ce, "kafin ka kirani ka tabbatar katuro mini sa'kon dazan gamsu dakai, idan naso zan iya kirankama da kaina, amma haka kawai daga kirana da number saina kama ďagawa, bakisan mu sanannu anada hanyoyin cutar damuba iri2, karki manta bakowa yake sonmu dan ALLAH ba.
Yasmeen ta ďan jinjina kai tana ta ce, "hakane kuma, amma kabari ni naďaga wanan.
Da sauri ya harareta, ya ce, "wlhy koda wasa karki fara, angaya miki kowane shara ya isa yaji muryan matata ne, ALLAH kobanan kika aikata saina gane, kuma zan miki kwakwkwaran hukunci.
Yanda yake maganar cikin faďa sai abin yabama yasmeen mamaki, a zuciyarta ta ce, "badai kishina yafarayiba??, ta tuna randa ya sha'keta akan faisal, da fasa mata waya dayayi, wata zuciya ta ce, "babu wani kishi yana kare martabar igiyoyin aurensane kawai.
Ahankali tajuya tacigaba da aikinta,, yabita da manyan idanunsa farare tas, ji yake zuciyarsa tana ambaliya akogin 'kaunarta wadda shi kansa baisan lokacin daya afkaba, ya lumshe idanunsa ahankali.
Bayan kwana huďu.
Suka fara shirin komawa Najeria harda Nawaf, dan yaďauki hutu domin yin jiyya, daganan zai zarce da hutun 'karshen shekara,, suka shirya tsaf, Nawaf da Mas'ud suka shiga gari sukayo tsaraba, Nawaf ya ce, "malam wai lafiya naga tsarabarka ta 'kare akayan baby?.
Mas'ud yay murmushi, ya ce, "malam aika kusa zama dadyne.
Nawaf yazaro ido waje bro's dgsk kakeyi??, mas'ud ya sakeyin dariya, hakane wlhy bakai kana mana rowaba konace kana mana ba'kin cikin ganin baby,, Nawaf ya ce, "kai nayi farinciki ALLAH ya inganta mana, amma ni babu wani rowar baby danake muku dasauran lokacine kawai.
Mas'ud ya ce, "shikenan muna nan muna jiran lokacin, amma gsky muna bu'katar baby, dan haka ku ajiye wani girman kanku ku bamu.
Nawaf yakaima mas'ud duka, oh munema zamu baku babyn ba ALLAH ba??.
A'a ALLAH ne zai bamu amma fa da taimakonku, Nawaf ya ce, "to saika bari saina 'kara aure,, hhhhhh su aure manya, malam tuni nafara harbo jirginka, saiya faďo zan maida yanda akayi, shiru Nawaf yayi dan yasan halin mas'ud sarai.
'Kananun kaya yaďebo sosai, wanda duk azuciyarsa na yasmeen ne, dan ita kaďai yay ma tsaraba, yabama su Abdallah kuďi suyi tasu, hakama su momcy, saikuma 'kannen mas'ud daya siyomawa, daga nan suka dawo hotel ďin, ya tarar har yasmeen tagama haďa musu komai nasu.
'Karfe bakwai na dare jirginsu yataso zuwa 9ja✈................✍🏻
Assalamu alaikum
Ina muku barka da sabuwar shekara, amma ina kira gareku 'yan uwana akan mu gyara wani abu, damuke aikatawa a tsarin rayuwarmu.
Idan ban mantaba munshiga shikarar musulunci wata biyu daya wuce baya, amma banga mutane suna posting sosai akan farin cikin shigarmu sabuwar shekaraba,, wasuma basu san munshigaba,, amma abin haushi da ba'kin ciki kowa yasan anshiga sabuwar shekarar 2017, harma yana 'ko'karin yin posting ďin taya murna.
'Yan uwana mu gyara, muringa girmama addininmu da aldarmu, mudaina fifita addinin wasu akan namu, dansu basu damu da abinda muke cikiba, koda sun sani sukan nuna basu fahimtaba,, tofa lokaci yayi dazamu fara gane karatun kurma wlhy,, ALLAH yasa mugane amin..
©2017
💓bilyn Abdul💓
💓Mrs Abdus'salam💓
💓luv u oll my fan's😘💓
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💓
Page👉🏻43 & 44
.....Sun iso 9ja cikin ďokin son ganin 'kasarsu ta haihuwa, musamman ma Nawaf daya ďan daďe baya nan, da'kyar suka samu ku6towa daga hannun 'yan jarida afilin jirgin, bayan Nawaf yayiwa masoyansa godiya da irin kulawa dasuka nuna masa, yayi 'yan bayanai na gamsarwa ga masoyansa.
A family falo suka baje kowa yana maida numfashin gajiya, aka kawo musu lafiyayyen abinci daga gidansu mas'ud, kowa yaci ya 'koshi.
Nawaf ya ce, "momcy nifa barci nakeji wlhy.
Momcy ta ce, "to mai sunan manya kujira papanku ya sakko, dan yay muku tanadin wani abu dazai sakaku farin ciki,, Nawaf yay murmushi, ALLAH sarki my sweet papa, to muna jiransa.
Babu daďewa papa ya sakko cikin jallabiya fara, momcy ta ce, "kamar kasan jiranka kuwa akeyi,, murmushi papa yayi ya ce, "to gani miya faru?, momcy ta nuna masa Nawaf, wai barci yakeji, papa yay dariya to kutashi muje, amma saikun ďaure fuskarku, momcy ta ce, "gsky ne Alhaji.
Nawaf da yasmeen suka ďaure idonsu da hankici momcy takama hannun Yasmeen, papa yakama na Nawaf, su Abdallah suka take musu baya.
Woow!! Nafaďa danganin inda suka dosa.
Anwar yabuďe 'kofa suka shiga, saida sukaje tsakkiyar falon san nan papa ya ce, "subuďe idonsu, kowa yazaro ido 😳😳dan mamaki, cikin farin ciki Nawaf ya rungume papa yana sambatun farinciki, sai dariya suke masa.
6angaren da Nawaf yafara ginawane ya daina, papa ya 'karasa ginin aka zubama wajen kaya masu 'kyau da tsari, abin sai wanda yagani komai zam2, papa ya ce, "to kowa ya za6i bedroom ďin dayakeso, Nawaf ya ce, "papa ni zan fara za6a.
A'a modebbo yasmeen ce 'karama ita zata fara za6a, yasmeen tafakaici idonsu papa tayima Nawaf gwalo, ya ďaure fuska tamau yana harararta, momcy ta ce, "za6i kinji ďiyata, tako nuna wanda Nawaf yakeso acikin zuciyarsa, da sauri Nawaf ya ce, "tab yarinya wlhy nima shinakeso.
A'a modibbo kayi ha'kuri kaci girma kaifa babbane, kuma aii ďakin mai gida a ciki akesonshi, dan haka kaine zaka ďauki na ciki, Nawaf yay wani murmushin mugunta ya ce, "na amince papa.
To ALLAH yay muku albarka kunji, suka dawo falo akayi addu'oi sannan su papa suka tafi nasu waje.
Bayan fitarsu yasmeen ta tashi tayi shigewarta ďakin data za6a batareda tabi takan Nawaf ba, yabita da kallo yana murmushin mugunta, takai minti goma da shiga sannan yabi bayanta, har yaje 'kofar ďakin saikuma ya fasa ya wuce ďayan ďaki, wanka yashiga .
Itama yasmeen wanka tayi, tana fitowa ta zira kaya ajikinta marasa nauyi ta haye gado, harta kwanta saikuma ta tashi ta sakko 'kofar ta sakama key tabar key ďin aciki, dan tanada tabbacin wannan mugun zai i ya biyo bayanta tunda tabashi haushi, dan tunda tace tana son ďakin nan ya canja fuska yana harararta, ta haye gadon tana wata 'yar dariya, babu daďewa barci yay gaba da ita.
Shima dai Nawaf bayan yafito kwanciya yayi domin yin barci, amma saiya kasa, tunanin yasmeen yazo ya kanaynayeshi abubuwa dayawa yake kissimawa a cikin zuciyarsa, yanzun kam gsky bazai iya đaga mata 'kafaba, yariga yashirya. komai tafanjama fanjam, shima yana bu'katar ďanďana za'kin rayuwar aure, yanason sanin banbancin da da yanzu, to amma tawace hanya zaibi domin mallakar wadda yadaďe yana muradi da bege??, taya zai fahimtar da yasmeen cewa ya fara 'kaunarta tun lokaci mai tsawo daya wuce?, to anyama zata fahimcesa??, idan ta fahimcesa zata amshi uzurinsa??, waishinma zata soshi??, ko har yanzu tana ma'kale da son tsohon mijintane??, yaja wani dogon tsaki, ko a mafarki bayason tuna anta6a ďaurama yasmeen aure dawani kafinshi, yakaima iska naushi yana huro hanci tamkar mai shirin danbe.
Zumbur yami'ke yanufi ďakin da yasmeen take, yata6a 'kofar amma saiyaji gam ankulle, mtsowwwww yaja tsaki yakoma inda yafito, babu daďewa shima barci ya ďaukeshi.
Basu farkaba sai da'aka kira sallah, yasmeen ta tashi tayo alwala, tanajin motsin fitar Nawaf, koda yadawo saiya shiga gidansu mas'ud, mami ta ce, "A'a Modebbo dakanka, muna shirin shiga anjima, nazata kunacan kuna barcin gajiya, Nawaf yay murmushi yarisina yana gaida mami, ta amsa cikin fara'a da tambayarsa yajiki??, ya ce, "jiki Alhmdllh kaďan yarage aii.
Masha ALLAHU aii haka akeso, sunďan daďe suna hira, 'kannen mas'ud sukazo suka gaisheshi dayi masa yajiki, cikin fara'a yake amsa musu,da tambayarsu ya karatu? , daga baya yanufi 6angaren mas'ud.
A falo ya iskesu anata zuba soyayya, Nawaf ya ce, "ALLAH yashiryaka malam, kana nan kana soyayya shiyyasa muna sauka kagudo ko?.
Mas'ud yay dariya yana faďin yaranka Alhaji?, Nawaf ya ce, "fari 'kal, yazauna suna gaisawa da Ameena, Nawaf ya ce, "ashe munsami 'karuwa to ALLAH ya inganta mana, Ameena ta ce, "amin tana murmushi, taje takawo masa lemo, saita koma bedroom takwanta tabasu waje.
Nawaf ya ce, "mutumina kaikam sai ahankali, ahankalinma sai sannu mas'ud yafaďa yana hararar Nawaf,, yaďora dafaďin ina yasmeen??, Nawaf ya ta6e baki tana gida mana kozan rin'ka yawo da'itane.
Dariya mas'ud yayi, to idan kayi yawon da'ita haramunne, aii yakamata ma kuzo tare yanzu.
mtsowwwww!!!! Nawaf yaja tsaki Kaifa idan ana maganar arzi'ki saika rin'ka kawoma mutane ta tsiya,, hummmmyimm!!! Maganar yasmeen ďince tatsiya?, malam idanzaka fito fili kafaďa kafito, wlhy tuni nagano ka kamu da son yasmeen, dan idanunka sun fallasa sirrin zuciyarka.
Lah mas'ud sharri kuma ka koma yima mutane da sa ido??.
Babu wani sharri alhaji gsky ce, idan kuma bakasan kakamu da sontaba to yanzu na fassara maka ba'kin.
Nawaf ya ku6i lemo yana murmushi, saida ya ajiye kofin sannan ya ce, "amma kaidai mayene!, kace dama ido kasaka mini bansaniba.
Hhhh aiba saina sha wahalar saka maka idoba, gaba ďaya sassan jikinka sun tonaka, kallon dakakema yarinyarnan kawai ya'isa agane ka kamu da sonta.
Humm kadaiji dashi, nikaga tafiyata, dama su mami nazo gaidawa daganin Ameena, dan haka mukwana lafiya.
mas'ud ya tuntsure da dariya, to angon yasmeen, mu dai muna jiran baby a daren yau.
Banza Nawaf yay masa yafice abinsa.
Afalo yatarar da yasmeen dasu talatu tana nuna musu suna gyarawa, dansuma yau suka dawo daga hutun dasuje tunda gidan babu kowa.
Da sauri suka rissina suna gaisheshi, sau ďaya ya amsa ya ďauke kai, ďakin yasmeen yashiga, cikin haushi yasmeen ta take masa baya.
Kwance ta tarar dashi akan gado yayi filo da hannayensa, idanunsa a lumshe kafafunsa kuma suna zube a'kasa yana ďan motsasu, ta tsaya cak ajikin 'kofa tana kallonsa, 'kafarsa fes2 kamar baya takata a'kasa, bakowacce 'kafa bace abin kallo, amma idan kaga ta Nawaf dolene ka kalla, taci gaba da kallon sassan jikinsa ďaya bayan ďaya.
Kamar daga sama taji ya ce, "mikike kallo ajikina??, da sauri ta kauda kai gefe, itafa azatonta idonsa arufe suke baya ganinta, ta ďan ta6e baki tomiye abin kallo ajikin naka???.
Ya buďe ido kađan yana kallonta 'kasa2, tai 'kasa da idanunta dan bazata