Showing 18001 words to 21000 words out of 74786 words
bud'e motar yafito.
Cikin gidan suka danna kai, har zuwa 'kofar falon abba dake harabar gidan ta baya, babu yanda za ayi kaga masu gidan dan 'kofar falonsu tana can cikin lungu, Tunda suka shigo 'kamshin turare falon da abinci yake dukan hancinsu, suka zazzauna.
Babu dad'ewa yaseer ya shigo da sallam suka amsa, 😳idanu ya zaro waje dan mamaki, ya 'kara murza idaninsa, yagadai kwarai dgsk modeebbo ne, ya ce, "yaya mas'ud dan ALLAH dgske ida nuna sukeyi??.
Murmushi mas'ud yayi dan yagane me yaseer yake nufi, ya ce, "gsky suka nuna maka yaseer, modebbone dai daga kasani yana gara mana kwallo a afili.
Nawaf yay murmushi shima ya ce, "zonan 'kanina!, jiki a sanyaye yaseer ya 'karasa wajensa, hannunsa yakama ya zaunar dashi kusadashi, kasannine??, yaseer yay dariya, aiko shekaran jiya saidanaga wasanka, wlhy narasa irin murnar dazanyi danna burge kaina, amma ALLAH ngd maka daka nuna min wanda nake 'kauna ido da ido.
Nawaf yaji dad'i sosai, danhaka ya rungume yaseer shima.
mas'ud ya ce, "yaseer sisto d'inkafa?.
Yaseer yami'ke yana fad'in kuyi ha'kuri farinciki ne ya mantar dani bari na kirata!!.
Mas'ud ya ce, "to karka gaya mata abinda kagani fa.
Cikin dariya yaseer ya ce, "bazan fad'aba ALLAH.
yasmeen zaune afalo tana jiran yaseer yazo yakirata, tayi 'kyau cikin les green ta d'ora farin mayafi dukda ba kwalliya tayiba amma tayi bala'in 'kyau.
Muskarsa cike da fara'a ya ce, "sisto kije suna jiranki, bai jira amsartaba yashige d'akin umma domin kai mata rahoton farin ciki.
Jiki a sanyaye ta tashi tanufi falon, tad'an dad'e a 'kofar falon 'kirjinta yana dukan tara2, daga 'karshe tayi kundun bala tashiga da sallama, cikin siririyar muryarta.
Mas'ud ne kawai ya amsa, dan Nawaf yana wayane.
Ta zauna suka gaisa da mas'ud yabata ha'kuri akan kwana biyu basu zoba, tayi d'an mumushi tana fad'in babu damuwa aii.
Mas'ud sai dariyar mugunta ya ke k'asa2, ya'kagara yaga yanda za'a had'u.
To nimadai 'yar rahoto abinda nake jira kenan.
Bayan Nawaf yagama waya ya juwyo yana kallon mas'ud, mas'ud ya ce, "lafiya dai ko??.
Harar sa Nawaf yayi ya ce, "ban saniba.
Mas'ud ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "Amarya ga angonki na kawo miki yau dai.
Kan yasmeen a'kasa ta ce, "ina yini?,
Lafiya. kawai Nawaf yafad'a yana wani yatsine fuska.
Yasmeen ta mi'ke domin ta basu ko ruwane dan takula ko bud'e abincin basu yiba.
Ta 'karaso kanta a'kasa, shi Nawaf ma waya yake latsawa, gabansu ta dur'kusa ta tsiyaya lemon kwakwa ta mi'kawa mas'ud.
Ta zuba wani ta mi'kawa Nawaf dake latsa waya abinsa.
Mas'ud ya ce, "malam ana baka abufa, ayatsine Nawaf yad'ago zaiyi magana, saiya daskare a gurin.
Cikin in ina ya ce, "kai ba dai ke ba ce.....
Itama cikin tsoro take kallonsa, sudukansu 'kirjinsu yana bugawa da tsananin 'karfi, hannun yasmeen sai rawa yake, gashi takasa ajiye lemon.
Shima Nawaf cikin rawar hannu da baki yake nuna yasmeen👉🏻👩🏻amma yakasa cigaba da furta komai.
Shiko mas'ud sai dariya yakeyi yana tafa hannaye😆😜.....................✍🏻
©2016
💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞Luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:55 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💞
Page👉🏻19
....Lokaci d'aya suka mi'ke kowa yana kallon kowa, idan kagansu saika d'auka kallon soyayya sukema juna, yasmeen ce tafara janye idanunta tana zubar da hawaye, saikuma tad'ago da sauri tana kallonsa.
Nawaf yagyara tsayuwarsa tareda 'kara d'aure fuska ya ce, "lallai yarinya dama kece papa ya 'ka'kaba mini, tofa ina mai baki shawara 'yammata tun wuri ki hanzarta fad'a musu su warware wanan auren ankuwa ba hakaba wlhy zaki gwammace kid'a da karatu, ya 'kare fad'a yana huci, kamar wanda yake afilin danbe.
Cikin tsiwa yasmeen ta harareshi ga hawaye share2 a fuska, ta ce, "ai basai nasha wahalar sanar dasuba malam, wannan damar tana hannunka, idan kaso nanda minti d'aya saika datse igiyar da aka d'auramini ta 'kaddara dakai, tsowww... taja tsaki.
Wani 'kududun ba'kin ciki ya tokare ma'koshin Nawaf, wlhy badan yanajin tsoron fushin mahaifansaba da agurinnan zai saki yarinyarnan, ya had'iye wani mugun yawu jikake 'kudddd.
Idanunsa sun kad'a sunyi jajur,, yasmeen ta ce, "aikin banza ashema kai matsoracine??..........kafin tarufe baki ya dam'ki hannunta na dama ya murd'e tabaya, tako kware baki zatayi ihu dan azaba, da sauri yasa d'ayan hannunsa ya toshe mata baki, saida ya tabbatar hannun ya murd'u sanan ya saketa yana dariyar mugunta, ya ce, "nida ke za'a tantance matsoraci.
Yasmeen ta durkushe tana zubar da hawaye, jitake kamar hannunta baya jikinta, kwatakwata takasa d'agashi.
Mus'ud yale'ko dan yaga wainar da ake toyawa tunda yasan ba shiri sukeyiba.dan tund'azu yafita yabarsu su biyu kawai.
Da sauri ya'karaso ganin yasmeen tsugunne tana rusar kuka, a hanxarce ya ce, "Nawaf!! mikayi matane??.
Banza Nawaf yay masa ya koma saman kujera ya zauna yana shan lemon kwakwarsa wanda yayi masa dad'i.
Ran mas'ud ya6aci sosai ya ce, "waikai Nawaf wane irin mugun mutumne yau kuma mizakace tayi maka??.
Nawaf ya yatsine fuska, katanbayeta abinda taimin sai nikuma nagaya maka abinda nayi mata, kawani d'ora mini laifi ni kad'ai, tsowwww ya 'karashe maganar da tsaki.
Mas'ud ya ce, "kiyi hakuri yasmeen ALLAH zai saka miki,, yasmeen tad'ago jajayen ida nunta ta ce, "karka damu mas'ud nima dakaina zan rama, dan wlhy bana barin bashi, karya d'auka dan yayi mini wanan muguntar zan barsa, shima ya saurari ranar ramuwa..
Tana kaiwanan ta mi'ke zata tafi, mas'ud ya ce, "plz karki tafi ki dawo, kinga su umma bazasuji dad'iba.
Batayi musuba tadawo ta zauna dan tana ganin darajar mas'ud.
Nawaf kam ko kallo basu isheshiba, yanata danne2 awaya hankalinsa kwance, yana kora lemon kwakwa.
Na ce, ji 'kafin hali azo gidanku a cuceka.
Afalon umma kuwa faisal ne da hajiya jummai da alhaji buba, zuwansu kenan suma, umma bata nuna musu komaiba ta tarbesu da mutunci, harda ruwa ta zauna suka gaisa sanan ta ce, "gashi kunzo malam baya nan amma yana hanya, dama jiya yake magana akan akwatuna, ya ce, "azo akai muku kafin ku biyo.
Hajiya jummai tayi dariya, A'a mu ba kar6ar akwatuna muka zoba, munzo mu baku ha'kuri akan abinda yafarune, wlhy makircin wani abokin faisal ne, shikuma babu bincike yaje ya aikata wanan aika aikar, amma wlhy tunda aka gane makircine hankalinsa ya tashi, nan dai hajiya jummai ta labartawa umma komai daya faru.
Umma ta ce, "ALLAH sarki ai bamu saniba damunzo mun dubashi, ALLAH yasa kaffarane faisal.
faisal ya ce, "amin umma, yafad'a yana wani sissinkuyar dakai 'kasa, adole shi mai kunya.
Hajiya jummai ta ce, "nibanga 'yar tawaba.
Umma ta ce, "tana nan wlhy, tayi ba'kine, ALLAH sarki d'iyar albarka.
Alhaji buba yaga hajiya jummai tanata wani kewaye2 takasa furta komai, sai kawai ya wage baki yashiga bayanai.
Maman yaseer dama abinda yakawomu shine dan ALLAH ayi ha'kuri da abinda yafaru baya, tunda faisal yayi nadama ayi ha'ku amayar masa matarsa, munyi muku al'kawari hakan bazai sake faruwaba.
Cikin mamaki umma take kallonsu, ta ce, "alhaji ai yasmeen yanzu tanada aure, ko baku saniba??.
Hajiya jummai ta kar6e, munsani mmn yaseer, abinda dama mukeso muce shine dan ALLAH abama wancan mijin ha'kuri sai a war ware adawoma da faisal matarsa.....
Da sauri yaseer ya shige falon abba, batareda yaji furicin ummaba, kai tsaye wajen Nawaf yanufa, yayinda mas'ud da yasmeen suke d'an ta6a hira.
Akunne yaseer ya gwargwad'ama Nawaf abinda yajiyo.
Idanu naga Nawaf yazaro ya ce 'kanina da gsk, yaseer ya kad'a kai tareda fad'in sunama falon umma,, kafad'ar yaseer Nawaf yadafa ya ce, "karka damu bazamu barima Mafita ba ka kwantar da hankalinka, yaseer ya ce, "to bara naje naji yanzu mi ake tattaunawa.
To Nawaf ya cema yaseer.
Maganar ta girgiza Nawaff, amma shi atunaninsa yasmeen tana son failal ne, yazata makircinne da gsk.
Dan haka yake ganin ai bama saiya saketaba yasamu hanyar yima yasmeen abinda yaso kenan.
Awajen su umma kuwa, umma ta ce, "musu to wanan ba maganarta bace sai abba yadawo zasuyi shawara.
Alhaji buba ya ce, "to bari suje suna saurarensu idan sunyi shawarar.
Umma ta ce, "to mungode ku gaida gida.
Har ga ALLAH faisal yaso ganin yasmeen amma babu dama, danko mai kama da'ita bai ganiba,, jiki a sanyaye yatashi yabisu hajiya jummai yanata raba idanu dan son ganin yasmeen😜😜.
Tafiyarsu babu dad'ewa abba yadawo, bayan ya huta yasha ruwa yashiga suka gaisa da su Nawaf, har 'kasa suka tsugunna suka gaidashi, Nawaf sai wani sisinkuyar dakai yakeyi.
Yasmeen ta ce, "munafinci banza, wlhy indai nice zaka gane kurenka.
Sun d'an dad'e suna hira da abba, daga nan umma tashigo suka gaisa, su duka sun yaba da hankalin surikin nasu, gashi 'kya'ky'kyawa laillai d'iyarsu ta more saidai subita da fatan alkairi, dan auren miji nagari bababar ribace.
Sai gab da magriba suka tafi, abba yamatsa saita yimusu rakiya.
A 'kofar gida mas'ud ya ce, "yasmeen yakamata nima ki samar min mata a anguwarnan gsky.
Yasmeen tad'anyi murmushi, ai indai wannan ne takwana gidan sau'ki, nabaka ameena.
Ya ce, "woow!! Kice harna samu?, yasmeen ta ce, insha ALLAH.
to yakamata afara yimini kamfen daga yau.
Nawaf yaja tsaki yana fad'in malam nifa kana 6ata mini lokaci kaji, tsaki mas'ud yaja, ya ce, "matsalarka ce kuma wannan, d'an rainin wayo kodan kaga ka kama taka a hannu, to nima tawa nake nema.
Baki Nawaf ya ta6e ya ce, "kaine mata ke gabanka aii.
Maganar tayi mugun 6atawa yasmeen rai, dan haka taja wani dogon tsaki tana fad'in wandama ya ce, "basa gabansa munafinci ne kawai...
Da sauri Nawaf ya ce, "ke waye munafikin??, saida ta murgud'a baki😏sanan ta ce, "damai aikatawa nake.
Nawaf yay wata 'yar dariya, yarinya kin taimaki kanki dakika kauce, wlhy dasai na ida 6alla wananan hannun mai kamada sillen kara.
Masha ALLAH yasmeen tafad'a tana murgud'a masa baki, ta ce, "basai kazo ka 6allaba, kuma dakai ake zaka kashe nine???.
tana ganin Nawaf ya biyota ta tsillara da gudu cikin gida.
Nawaf ya ce, "'karamar 'yar marakunya daki tsaya mana kiga hauka.
Mas'ud ya ce, "wlhy tunda nake ban ta6a kallon film mai dad'in kamar nakuba, gsky kuna wuta alhaji.
Harara Nawaf yasakar masa, ya ce, "kaifa d'an iskane wlhy mas'ud ya ce, "iskan cin menayi maka malam??.
Nawaf ya ce, "wai mas'ud ya akayi haka, kodai kaine kayi wanan had'in yama za'ayi wanan yarinyar tazama matata, aii da sake.
Babu wani sake malam aii ka d'auka an wuce gurin kawai, domin wannan wata hikima ce daga cikin hikimomin ubangiji.
Wai mikayi mata d'azu naga tana kuka??, ko har an fara soye wane??.
Duka Nawaf ya d'akama mas'ud ya ce, "a 'konewa aka fara ba soyewa ba, rashin kunya tamin na hukuntata.
Hhhhh kaidai wlhy mugune nakula.
Koda yake wasan yana 'kyau dan nasan saita rama.
Lallai kam kokuma ta rame ba, dan wlhy yanzu ta ce, "zatamin hauka wahala zatasha ba 'karamaba, garama ka bata shawara ta kiyayeni.
Hhhhh kadaiji dashi malam, dahaka suka 'karasa wani masallaci domin yin sallahr magriba.
Yasmeen kuwa da gudi tashiga gida, a falo suka had'u da umma ta ce, "k irin wannan gudu haka lafiya?.
Gefen wuyanta ta sosa ta ce, "babu komai umma.
Girgiza kai kawai umma tayi tashige d'aki domin yin sallah.
Itama yasmeen d'aki ta shige ta kwanta domin tana fashin sallah, dan danan tashiga duniyar tunani, lallai saita dage tunda har ALLAH ya 'kaddara mata zaman aure da wanan d'an haya'ki, saidai kuma tayi farin cikin rabuwada faisal d'an is......takumayi ba'kin cikin kasancewa da Nawaf d'an kwallo🎾, wai itace matar d'an kwallo kai lamarin tamkar almara wlhy, gsky bata moreba dan ita kwallo bata burgeta bare mai yinta, amma gashi ALLAH ya jarabceta da auren d'an kwallon.
Ta kalli hannunta da har yanzu ciwo yakemata ta ce, "mugu ALLAH yasaka mini, kuma wlhy ka rubuta ka ajiye saina rama, 'kilama yayi mani targad'e azzalumin.
Haka tai ta tuna abinda yafaru d'azu tamkar a mafarki.
FAISAL
faisal kuwa koda suka tafi saiya sakama iyayenasa kuka, hajiya jummai ta hau rarrashinsa haba faisal d'in dady kayi ha'kuri, kobakaga 'ko'karin da mukeyi akanka bane, ka d'auka yasmeen tama rigada tadawo hannunka nan bada dad'ewa ba.
Alhaji buba ya ce, "bana son ganin kukanka my son dan ALLAH kabari indai yasmeen ce dan kai aka halicceta kaji.
Kai kawai yad'aga yana share hawaye.
Wlhy ni dariyama yabani😆😜.
BAYAN KWANA BIYU.
yasmeen tasake yima abba maganar makarantar ta, abba ya ce, "banace ki fad'ama mijinki idan yazoba.
Ta ce, "abba ai na manta ban fad'a masaba.
Aii wanan mai sau'kine tashi kije ki fad'a masa ta waya yanzu, idan ya yarda saiki fara zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Jiki asanyaye yasmeen ta mi'ke, ita yanzu idan ta kirashi mizatace masa, 'kilama yay mata wula 'kancin daya saba mata, itako wlhy ba 'kyaleshi zatayiba.
Tadad'e tana kullawa da kwancewa, daga baya ta d'auki wayar tafara kiransa cikin fad'uwar gaba, har wayar ta tsinke bai d'aukaba.
Ta kai dubanta akan agogo 'karfe 9:56pm, wata zuciya ta ce, "ki 'kara kira, maso d'an tsuntsu aishi ke binshi da jifa.
Ta sake kira har sau biyu bai d'agaba, jiki asanyaye tazame ta kwanta tana hawaye, shike nan an hanata zuwa makaranta tanaji tana gani.
^^^^^^^^^^^^^^^^
Alokacin da yasmeen take kiran Nawaf yana wanka, yanajin wayar tana wringing, gashi yana dad'ewa awajen wanka, saida yagama komai na al'adar rayuwarsa kamar shafa'i da wutiri, karatun alkur'ani, (dan duk dare saiya karanta littafi amai tsarki,) san shayi☕, sannan ya haye gado ya kwanta, wayoyinsa yajawo, yafara duba missed calls, ya kira wad'anda suke da muhimmanci sanan, wayar da yasmeen takira itace 'karshe, 3missed call yagani saidai kuma ba'kuwar number ce, shikuma baya kiran ba'kuwar number.
Harya kwanta sai kuma zuciyarsa ta kwad'aita masa yakira, dan baisan dalilin dayasa mai number yay masa 3missedcall ba.
Lokacin har yasmeen tagama kukanta tayi barci, dayake barcin baiyi nisaba saitaji phone d'inta na wringing, sanda ta d'auka harta kusa tsinkewama.
Cikin muryar barci ta ce, "assalamu alaikum.
saida yaja ajiyar zuciya wadda shi kansa basan yayiba, ya ce, "wa'alaikissalam wacece??.
Tuni yasmeen ta watstsake domin jin muryar Nawaf, dan da farko bata duba number da aka kirata dashiba, ta tashi zaune, cikin rawar murya ta ce, "yasmeen ce!!.
Yad'an ta b'e baki dan tunda tayi sallama yagane muryarta, ya ce, "ban ganekiba, kinga kimin bayani yanda zan gane banason inda2, inba hakaba zan kashe wayata.
Saidata murgud'a baki 😏tamkar tana gabansa, ta ce, "toni wane bayani zan maka tunda nafad'i sunana baka ganeba, ni dama sonake na koma makaranta kuma abba ya ce, "saina sanar maka shiyyasama nakiraka, inba hakaba mizaisa nakiraka, ta 'kare maganar cikin mugud'a baki.
Tamkar yaganta ya ce, "mara kunyar banza, to ban aminceba inkuma kikaje ban saniba ALLAH ya isa, d'if ya yanke wayar.
Wasu hawaye suka zubo mata masu zafi, zuciyarta taita zugata akan takirashi ta ro'keshi 'kila yabarta.
Haka ta daure ta kirashi, yay buris da wayar, saida ta sake kira sanan ya d'auka, wani lallausan murmushi yasaki na mugunta kafin yad'aga, yana d'agawa ya ce, "k nifa kin dameni barci zanyi.
Ta matse hawaye ta ce, "plz dan ALLAH kabarni, kaga zamu fara EXAM ne kwanan.
Saida yagyara kwanciya sanan ya ce, "toni ina ruwana, nidai nace ALLAH ya isa ko, kuma zan kira abba na ce, "na hanaki, dan haka karki sake kirana zanyi barcine, bata ankaraba ya kashe wayar.
Dariya yashiga tuntsurawa harda hawaye, yarinya baki sanni bane, inada hanyoyin maga ninki wlhy, yafad'a yana kwanciya.
Itako yasmeen kuka tashiga rerawa kamar uwarta ta mutu, saida tayi mai isarta sanan tayi shiru, har barci ya kwasheta..
Na ce, "yasmeen asuba tagari..................✍🏻
Assalamu alaikum
Ina mi'ko d'unbin gaisuwa ga masoyana, nagode kuna 'karamin 'karfin guywa gsky, ngd ALLAH yabar zuminci.
Luv u oll😘😘😘!!!!!!.
Acigaba da gashi👌🏻!!!!!!!!!!.
©2016
💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞Luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💞
Page👉🏻20
....da safe sukuku yasmeen ta tashi batada wata walwala, umma tana kula da'ita amma batace mata komai ba.
Yaseer yagama shirin makaranta yafito bayansa goye da schoolbag, ya ce, "sisto wai mike damunki ne??.
Yasmeen tad'an yatsine fuska ta ce, "ba komai bro's.
Ya ce, "to bazakije makarantarba ne?, naji kince yau zaki koma kuma.
Kwalla suka cikama yasmeen idanu ta ce, bazanjeba na fasa.
Kin fasa kamar yaya??.
Zamewa tayi takwanta saman kujera batareda tace masa komaiba.
Dole ya 'kyaleta ya fita danshima yaga yana neman makara.
Umma tafito daga kichin tasamu yasmeen kwance tana hawaye,