Showing 30001 words to 33000 words out of 74786 words

Chapter 11 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

358

durowar gefen gadon ya buďe yaďakko wasu magunguna ya watsa abaki ya kora ruwa, gefen gadon ya zauna yana faďin ya salam!!.
Ahankali yasmeen ta sauka daga gadon ta koma saman kujera ta kwanta.
Yakai minti5 azaune kafin yatashi yahau shirin barci.
Yabi yasmeen dake kwance saman kujera da kallo, ahankali yafurta kin taimaki kanki yarinya, gadonsa ya haye yay kwanciyarsa harda jan bargo.
Yasmeen tana kallonsa taďan ta6e baki, itama ta maida kanta ta kwanta, babu daďewa barci yay gaba da ita.

WASHE GARI
da safe yasmeen ta tashi ta gyara ďakin tsaf ta wake bayi sannan tayi wanka, dan Nawaf tundaga sallar asuba bai dawo ďakin ba, yana ďakin motsa jiki.
Gayu ta ďauka cikin atamfa siket da riga tayi 'kyau sosai, bawata kwalliya tayiba fauda kawai tashafa.
Ta le'ko falo azatonta Nawaf yana nan, saitaga babu kowa ta fito ta lalle'ka ko ina, komai ya burge ta, tagama zagayawa tazo tashare falon duk da bawani datti yayiba, amma taďan 'kara gyarawa.
Har waje ta fito ta gyara tsaf, alokacin Nawaf yafito daga ďakin motsa jiki yashiga bedroom, wanka kawai yashiga yadaďe sosai kafin yafito, bayan fitowarsa ya shirya.
Yasmeen tana zaune afalo tayi shiru tana tunani.
'Karar takunsa yasata juyyo da sauri, Nawaf tagani cikin shadda orange color, ďinkin zamani yayi masa 'kau sosai, amma fuskarsa babu walwala.
Ta ďauke kanta daga kallonsa, dan ganin gurinta ya nufo.
Cikin takun 'kasaita ya 'karaso gareta dan iña ganin yau sarautarce ta motsa, ya ce, "k ki tashi muje mu gaida mutane.
Banza tayi masa.
Hannu yasa ya fincikota "k 'karamar mara kunya har kin isa ina miki magana kimin banza.
Ta ce, "anyi maka ka ďauki mataki mana, ta murguďa masa baki😏.
Shi dariyama tabashi, amma saiya gimtse, ya ce, "zanyi maganinki ki bani lokaci.
Tayi wata dariyar rainin hankali, aii ba saina baka lokaciba yanxu yadace kaďauki mataki.
Ya zaro wayarsa dake wringing momcy ce, cikin girmamawa ya ce, "momcy ina kwana??.
Daga can ta ce, "lafiya lao abbuna kun tashi lafiya.
Ya ce, "lafiya lao my momcy, ta ce, "ina ďiyar tawa bata mugaisa.
Ya ce, "momcy ai yanzu zamuzo gaisheku ma.
A'a modebbo karka wahalarmin da ďiya kabarta ta huta.
Haba dai momcy yazamu zauna bamu gaida su hajjaba, bawani wahalar da ita daza ayi.
To shikenan bata mu gaisa.
To, juyowa yayi domin yabata wayar, saiyaga bata nan, bin bayanta yayi zuwa bedroom, batareda yayi mata maganaba ya manna mata wayar kawai a kunne.
Tabuďe baki zatayi magana saitaji maganar momcy tana faďin ďiyata kin tashi lafiya??.
Cikin girmamawa ta zamo daga kujera ta ce, "momy ina kwana??, lafiya lao ďiyata ya ba'kunta.
Ta ce, "lafiya lao.
Masha ALLAH momcy ta faďa, ta ďora dafa ďin babu wata matsala dai ko??.
Eh babu komai momy.
To shikenan gasu talatu nan zasuzo suďan gyara miki inda aka 6ata kinji.
Lah momy ai bama sai sunzoba nariga na gyara.
Kai ďiyata damme??, daga yau karki 'kara wahalar da kanki akan aiki, akwai masu yi kinji.
Ta ce, "to momy ngd ALLAH ya'kara girma.
Momcy ta ce, "amin ALLAH yay muku albarka.
Ta ce, "amin.
Nawaf yaji daďin yanda yasmeen ta girmama mahaifiyarsa, amma sai ya kanne dan yasan matar tasa 'yar haya'kice.
jallabiya ya ďakko ya cilla mata, gashi nan kisaka mu tafi.
Kai taďago daniyar yimasa rashin kunya, amma saitaga ya tsare gida kamar bai ta6a dariyaba, bata ta6a jin shakkar yimasa rashin kunyaba irin yau, ďauka tayi tana zum6ura baki tanufi bayi ta canja, tayi mata matu'kar 'kyau dan rigar ta haďu, shi kansa saida ya yaba amma bai nuna mataba, ya ce, "muje, yafaďa yana nuna hanya👉🏻.
Batayi musuba suka tafi, 6angaren papa suka fara zuwa yayi farincikin ganinsu, yasmeen ta zube tana kwasar gaisuwa wajen surikin nata, shima Nawaf yakai tashi gaisuwar, papa yay musu nasiha mai shiga jiki.
Daga nan wajen momcy sukaje suka gaisheta, itamadai nasihar tayi musu.
Sai 6angaren dasu hajja suke, cikin farinciki hajja ta rungume yasmeen itako sai kunya takeji.
Nawaf kuwa tsakkiyar kakanninsa yaje ya zauna yana gaishesu cikin harshen larabci, suka shiga tambayarsa ya amarya.
Ya ce, "gata nan lafiya lau.
Taďan yi 'ko'kari wajen gaishesu da larabci, saboda islamiyya datake zuwa, daga nan sai Nawaf yakoma yimusu tafinta, idan sunyi magana da larabci ya fassara mata, idan tayi da hausa ya fassara musu, Nawaf sai dariya yake mata wai bata iyalarabci ba.
Momcy ta ce, "rabu dashi yasmeen kema zaki iya indai larabcine.
Yasmeen ta ce, "momy sainama fishi iyawa insha ALLAHU.
Nawaf ya harareta wazakifi iyawar??,
Ta ce, "kaimana.
Haka dai sukaita hirarasu, saida hajja ta ce, "su tashi suje 6angarensu.
Tun ahanya aka fara faďa, na ce, "kai ALLAH ya shirya waďannan gays ďin.
Talatu da ladidi suka shigo da kayan break suka jere a dinning, sanan suka tafi.
Nawaf yatashi yanufi dinning batareda yabi takan yasmeen ba, abincinsa yaci ya 'koshi kunsandai 'yan kwallo sun iya ci😜.
Yasmeen tana zaune a falo ko kallo bai ishetaba, saida yagama yafita sanan taje taci nata, ta gyara wajen.
Falo tadawo ta ďauki wayarta tahau chatting dan tarage kaďaici, dama kallo bai cika damun yasmeen ba.

``````````````````````````````````
Sai bayan sallar la'asar Nawaf yashigo gidan lokacin tasake wanka cikin sket da riga na shadda tayi 'kyau, tana bedroom bayan ta idar da sallar la'asar, zaune ta ke kawai tunani fal zuciyarta.
'Karar buďe 'kofa yasata juyowa da sauri tana kallonsa, kallo ďaya yay mata ya ďauke kai, itama kanta ta maida gefe, tana ganin yafara cire kaya tatashi ta fice, yarakata da harara.
Tana nan zaune afalo saiga 'yammatan danginsa na saudia, suka zauna ana hira harda ummu habeba, yau tasaki jiki anayin hirar da'ita.
Suna nan zaune Nawaf yafito sanye da 'kananun kaya sai zabga 'kamshi yakeki, kan hannun kujerar da yasmeen take zaune ya zauna, suka shiga gaidashi, daga nan aka ďora da hira, ummu habeba sai kallonsa takeyi, ita dai tana 'kaunar Nawaf, amma gashi ya zagaye yayi aurensa ya barta, kwata2 ta kula ma shi nunawa yake baisan tana sonshiba.
Sai gab da magriba suka tafi 6angaren momcy.
Shikuma Nawaf yatafi sallahr magriba masallaci.

____________________________
Yau jirgin muta nen sudia ya ďaga, hajja kawai aka bari zatayi ďan kwana biyu sanan ta tafi, da'kyar tayarda ta zauna.
Yau gidan shiru babu kowa saisu kaďai.
Nawaf yadawo daga motsa jiki ya zube afalo saman doguwar kujera yana faďin wash ALLAH na nagaji yawa yau.
Yasmeen tafito hannunta ďauke da kofin kunun gyaďa dan tana sonsa sosai, tundaga lokacin da Nawaf ya ce, "bayasan 'yan aiki awajensu idan bazatayiba tabarshi.
Momcy ta ce, "bata yardaba yasmeen ďin nawa take daza a sakar mata aiki, dayaga momcy ta dage saiya ce, "to saidai ita ta rin'ka musu girki, dan bazaici girkin 'yan aikiba.
Momcy ta ce, "wanan mai sau'kine, yasmeen kiringa yimuku girki tunda ku biyune kafin yatafi, dan tuni mijinki baya cin abincin 'yan aiki.
Yasmeen ta ce, "to momy hakanma yayi, nima nafiso nayi da kaina.
Yabita da kallo danganin shigar dake jikinta, wandone iya guywa da 'karamar riga mara nauyi, rigar ta fallasa asirin jikinta sosai, kanta yasha gyara sai wal'kiya yakeyi.
Tasan babu wanda zai shigo musu shiyyasa tayi wannan shigar, dan Tun agida yasmeen tanaso shigar 'kananun kaya damma wataran umma tana hanata ne.
Ta wuce kamar bata ganshiba.
Ya ce, "k zonan!, banza taiyi masa tunda ba "k aka raďa mataba agidansu, bedroom tashige abinta.
Nawaf ya haďiye wani mugun yawu jikake 'kuttttt, gaba ďaya ta rikita masa lissafi ya rintse ido ya furzar da huci mai zafi, ya ce, "wai sai yaushe za'a kai 'karshene??, wata zuciyar sa ta ce, "randa ka shirya kwatar ha'k'kinka dan kasan indai dan itace ayita zama ahaka.
Yay wani murmushin mugunta, afili ya ce, "aii ko ankusa zuwa 'karshen, ya mi'ke yanufi bedroom domin yin wanka.
Koda ya shiga ďakin baibi takantaba yashige wanka abinsa, ita kuma tadawo falo tana faďin ďan rainin wayo ai wlhy yanzu na daina zama kana raina mini hankali, idan zaka shekara kiran "k! Bazan amsaba tunda bashi iyayena suka raďa mini ba.
Tana nan zaune yafito shima cikin 'kananun kaya, kusada ita ya zauna, bata ko kalli inda yakeba taci gaba da shan kununta.
Gashin kanta yaja aiko ta kwala 'kara, yasa ďayan hannunsa ya rufe mata baki, tasaki kofin hannunta saboda zafi, ya ce, "k wacce irin mara kunyace ne?, kinaji ina kiranki ďazu kikai mini banza, ni tsarankine??.
Cikin kuka ta ce, "kai kasani nidai kasakeni mugu kawai.
Birkiceta yayi ya haye saman cikinta, tafara mutsu2n kwacewa.
Amma takasa saboda yafi 'karfinta, ALLAH Yabata sa'a ta gallah masa cizo.
Da sauri yasaketa danjin wani azababben zafi, mari ya kaimata ta kauce da gudu ta shige bedroom ta rufe, ya take mata baya🏃🏻🏃🏻........... ✍🏻









© 2016


💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻29 & 30

.....kafin ya 'karasa ta kulle 'kofar yashiga bugawa da 'karfi amma yasmeen tai masa banza, saida yaga batada niyyar buďewa sannan ya ha'kura, falo yadawo ya zauna zuciyarsa cike da haushi, daga baya yatashi ya fice.
Yasmeen taďan le'ko ta wata 'yar 'kofa ganin baya nan yasa ta buďe 'kofar ahankali tafito.
Hijjab tasaka tanufi 6angaren momcy, tanata addu'a a zuciyarta ALLAH yasa bacan Nawaf yajeba.
Da sallama tashiga falon, hajja da Anwar ne kawai zaune, tasaki ajiyar zuciya, gurinsu ta 'karasa hajja tanata mata murmushi, ta tsugunna har 'kasa ta gaisheta, Anwar ya ce, "aunty mu dama yanzu zanje 6angarenki hira.
Kai Anwar banyardaba kullum haka kake faďa amma komai kama dakai ban ganiba.
Anwar yay dariya, A'a aunty kinafa ganin mai kama dani baga yaya nan ba, dariya sosai sukeyi harda hajja, momcy tashigo itama tana waya, bayan ta kammala ta ce, "A'a ďiyata kece kika zomana, cikin jin kunya yasmeen ta gaisheda momcy.
Momcy ta amsa cikin fara'a, tana mai 'kara jin 'kaunar yasmeen har cikin zuciyarta, itako saiwani sissinne kai take dan kunya, hajja sai tsokanarta takeyi, Abdallah yashigo shima aka fara hirar dashi.
Anwar yabata wayarsa tana kallon hotunan biki wanda yaďauka, tayi mamakin irin 'kyawun datayi, gashi wasu wuraren tana murmushi, wanda batasan lokacin datayiba, wani hoto yaďauki hankalinta awajen dinner, tatuna faďa sukeyi da Nawaf awanan lokacin shine ya harareta ta rama, amma idan kagani saika ďauka kallon soyayya sukema juna, Anwar ya ce, "kai aunty nakula pic ďinnan yayi miki 'kyau sosai, nima duk nafi sonsa wlhy.
Abdallah yataso domin yagani shima, bayan kujerar yakoma yana kallo ta bayansu.
Nawaf yashigo da sallama saida gaban yasmeen yafaďi, amamakinta saitaji ya ce, "dama kinanan inata nemanki, wani iri yasmeen taji aranta gashi yawani tsareta da mayun idanunsa masu hasken tsiya, ta daure ta ce, "yi ha'kuri bansan zaka dawoba yanzu, jinai 'kaiďaici zai dameni shiyyasa nataho nan.
Okey to nima bari nazauna ayi hirar dani, ya zauna kusada hajja, hajja ta ce, "o, sai yanzu ka tuna dani.
Nawaf yay dariya to dama na'isa na manta dake!.
Momcy ta ce, "aii daga yanzu indai yafita kiringa tahowa nan saboda kaďaici babu daďi.
Yasmeen ta ce, "to momy.
Nawaf yafaki idonsu ya harareta, ita kuma ta murguďa masa baki, ya nuna kansa wai shi👉🏻👮🏼!, ta kaďa kai alamar eh., le6enasa na 'kasa ya cije, itakuma ta maida kanta ga kallon pictures.
Haushi kamar ya kashe Nawaf, amma babu damar ďaukar mataki, dole yasaki jiki suna hira da hajja da momcy, dansu hankalinsu yana kan waya.
Saida aka kira sallar azhur suka tashi, masallaci suka tafi shidasu Abdallah, yasmeen kuma tanufi 6angarensu.
Wanka tafara shiga sanan tayi sallah, agurguje ta shirya tafito da nufin tasake guduwa 6angarensu momcy, sai sukayi kici6is da Nawaf a'kofa, kallon kallo aka tsaya yi, kowa ya ďaure fuska.
Tsaki Nawaf yayi tareda jan hannunta zuwa cikin falon, cikin tsiwa ta ce, "malam kasakeni, banza yay mata yacigaba da janta, saman kujera mai zaman mutum ďaya ya hankaďata, damma kujerar da laushi shiyyasa bataji zafi ba, yaďora 'kafarsa ďaya saman kujerar ya tsareta da idanu.
Ta kauda kai daga kallonsa, dan ita idanunsa tsoro suke bata, haskensu yayi yawa, sunkai minti2 ahaka, sanan ya ce, "wai ke na tambayeki ni sa'ankine??, banza tamasa kamar batajiba, yacigaba da faďin ďazu harda wani faďin aibansan zaka dawoba ne shiyyasa nafito, dan kaďaici yaymin yawa, yafaďa yana kwaikwayon muryarta.
abin yabama yasmeen dariya amma saita gimtse, ta ce, "oho dai naga kaine kafara, kaga kenan a wajenka na koya, agabansu hajja kayita wani kakkafi waikai mai gida, sai andawo nan kafara mazurai, ta 'kare maganar da murguďa baki😏 .
Nawaf ya ce, "niko?"
Cikin tsiwa ta ce, "eh kaiďin saime".
yasaka yatsansa ďaya ya ďago ha6arta, ta rintse ida nunta, yaja tsaki yana faďin ke nifa nafiki miskilanci!.
Sai asanan ta buďe idanu, dukda zuciyarta tana dukan uku2 saboda tsoro wannan bai hanata sake murguďa masa bakiba.
Ya ce, "ni dai ko??.
ta ce, eh, ni kadameni da tambaya? ?".
Kafin ta rufe baki yasa yatsunsa biyu ya kama la66anta ya matse da 'karfin tsiya, yasmeen tashiga tsungunin hannunsa tana hawaye😭, amma mugun ya'ki yasaki, gashi sai murzasu yatsun nasa yakeyi dan mugunta akan bakinta, saida yayi mai isarsa sanan yasaki, zuwa sanan la66an yasmeen sun kunbura, sunzama 'katun2n, yasaki yana dariyar mugunta.
Yasmeen sai hawaye suke zirara a fuskarta, tana shafa la66anta, har yanzu 'kafarsa tana saman kujerar, ya ce, "yammata za'a sake mini rashin kunyarne??, hararar sa tayi ga hawaye fal fuska.
Nawaf ya tuntsure da dariya, yasmeen tai sagade tana kallonsa, batayi zaton yana dariya hakaba, saida yayi mai isarsa sanan ya sauke 'kafarsa yanufi bedroom yana cigaba da dariyar.
Yasmeen ta kifa kanta saman hannun kujera tana kuka, ahaka barci yay gaba da ita.
Saida yay wanka ya shirya tsaf yafito cikin manyan kaya, wani farin yadine shara2 yay masa 'kyau sosai harda ďora ba'kar hula wanda gays ďin yanzu suke yayi, ya kai kallonsa ga yasmeen dake barci a takure saman kujera, murmushi yasaki yana faďin yarinya tayi barcin wuya.
Har yakai 'kofa kuma yadawo, ďaukarta yayi tsak yakaita bedroom, a saman gado ya kwantar da'ita, yana kallon la66anta dasuka kummbura yana murmushi, ahankali yajuya ya fice.
Saida yashiga 6angaren momcy yafito sanan yashiga mota yafice, yana bani mamaki yanda yakeson mota mai ba'kin gilas, kobayaso idan yafita agansane oho??.
A'kofar gidan su mas'ud yatsaya, ya ďauki wayarsa yakirashi, malam kafito muwuce ko??, kai haba dan baka da kirki saikace bazaka zo ka gaida Ameena ba??.
Kai mutumina ALLAH inajin kunyar zuwa haka.
Tsaki mas'ud yayi aikai kajika, dan ALLAH kashigo ku gaisa saimu wuce, yakashe wayar.
Dole Nawaf yafito yashiga gidan, da sallama yashiga falon, suka amasa.
Mas'ud yashiga tsokanarsa kaga angon yasmeen, wanan irin 'kyau haka malam, lallai amarcin ya kar6eka.
Nawaf ya zauna yana hararar sa, mas'ud kaifa ďan iskane wlhy, nazata idan kayi aure zaka canja, amma kananan yanda kake, saima 'karawa dakayi.
Kafin mas'ud yay magana Ameena tashigo hannunta ďauke da tire.
Nawaf ya ce, "amarsu ta ango!, sai dai baki more angoba, dariya tayi tana zuba masa lemo, bayan tagama ta gaisheshi ya amasa, ta ce, "ina 'kawata??.
Tana gida nabarota lfy, ta ce, "na gaidaki!.
Ameena ta ce, "ina amasawa.
Kaďan yasha lemon ya mi'ke kai malam tashi mije yamma tanayi.
Mas'ud ya mi'ke yana faďin gsky ne, saida ya sumbaci goshin ameena sanan ya fito, Nawaf yana kallonsu shiyyasa yayo gaba, dan yasan mas'ud ba kunyarsa zaijiba.
Amota mas'ud ya ce, "mutumina aure da daďi wlhy, yanasaka nishaďi da farinciki, musaman idan kasamu matar data iya tattalinka.
Nawaf ya ta6e baki, kai Alhaji kai yayima daďi, nidai bandani!, dan ni takurani akayi, dana 6ararraje nikaďai aďakina amma yanzufa??, ankawo mini wanan mara kunyar duk ta takurani.
Dariya mas'ud yayi, haba malam faďi gsky dai, kowa yaganka yasan ka 'kara 'kyau, zaka wani dozani, 'kilama mun samu baby.
Nawaf ya ce, "kai mutumina ammafa ka iya tsiya ka ce, "har resold yafito??.
Kai ďan rainin hankali ka gama wani kauce2n ka kafaďi gsky, aii dakai nake!!.
Tofa, Nawaf yafaďa yana 'kara dafe sitiyari, to indai nine wlhy kama fidda rai, bawai tonon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login