Showing 21001 words to 24000 words out of 74786 words
kusada ita ta zauna ta ce, "wai yasmeen mike damunkine??, ko bakida lafiya ne??.
Yasmeen ta bud'e ido tana kallon umma, ta ce, "kaina yake ciwo tunjiya umma!.
Umma ta ce, "o, ni kharima!! shine kuma bazaki fad'aba saidai kuka?, shidai d'an fari duk inda yake saiya nuna halinsa, to kitashi akwai magani ad'akin abbanku ki d'akko kisha.
Jiki a sanyaye ta tashi taje ta d'akko maganin, koda tadawo sai ta tarar umma bata falon danhaka saita wuce d'akinta.
Bayan madubi ta watsa maganin tana fad'in umma wannan bashi bane maganin ciwona, maganin ciwona yana hannun wancan mugun, ta 'karashe maganar da hawaye masu zafi.
Na ce, "ALLAH sarki yasmeen yazakiyi aure kenan.
------------------------------------
A6angaren Nawaf kuwa ko ajikinsa, yanzu hakama yana kwance a d'akin momcy bisa gado yanata barcinsa hankali kwance, dan tun asuba dayaje gaishesu ya kwanta.
Dama wata sa'in yakanyi barci a d'akin momcy.
Momcy ta kalli agogo 'karfe 9:30am ta ce, "modebbo yakamata katashi hakanan, gaban gadon ta 'karasa tana tashinsa, yad'an bud'e ido yana kallonta, saikuma ya maida ya lumshe.
Ta ce, "Abbuna yakamata katashi hakanan kaga rana tayi, tafad'a tana jan baban yatsan kafarsa.
Ahankali yatashi yana murza ido, ya ce, "momcy har 'karfe nawa nakai ina barci yau?, ta ce, "kalli agogo kagani mana, koda ya kalla saiya zaro idanu waje, ya ce, "kai ashe nadad'e ina barci, yaufa ko motsa jiki ban fitaba.
Momcy ta ce, "hala kadad'e bakayi barciba jiya.
Yad'anja tsaki, mara kunyar yarinyar nan ce ta hanani barci da da wuri.
Yarinya kuma? a ina kenan?, momcy ta tambaya tana yatsine fuska, Nawaf yad'an sosa gefen wuyansa yana fad'in yasmeen fa momcy.
Murmushi momcy ta saki ta ce, "o, ai nazata watace kuma.
Mi'kewa yayi yana murmushi yanufi 6angarensa.
Wanka yashiga yayi yafito yashiga shafa can, dangwala can, yagara jikinsa tsaf, yad'ora 'kananun kaya ba'kin wando da green d'in riga mai 'karamin hannu, yakawo ba'kar rigar sanyi mara hannu ya d'ora, yasaki hular abaya, yad'anja zif d'in sama kad'an amma baikai 'kirjinsaba, yayi 'kau sosai gsky, yafito yanata zabga 'kamshi.
Gefen momcy ya koma, tana kichin suna aiki itadasu talatu, suka russun suka gaisheshi, sai satar kallonsa sukeyi, dan ita ladidi a haukanta har yanzu son Nawaf takeyi.
Momcy ta ce, "modebbona sai ina kuma, yashafa sumar kansa data sha gyara, ya ce, "momcy wajen mas'ud zanje.
Ta ce, "to break fa??, ya ce, "uhmm!!! Kumafa inajin yunwa gsky, bari nayi break sanan.
Momcy ta ce, "to ladidi jeki had'a masa.....da sauri ya ce, "no, my sweet mom, tabarsa zanyi dakaina kawai, yafad'a yana yatsine baki, dan ganin ladidin awani hargitse, kuma momcy tana 'ko'kari wajen kula dasu da saimusu sutturu masu daraja, amma a banza.
Shiyyasa bakomai Nawaf yakeso asakasu suyi masaba.
danning yanufa yazauna abinci kad'an yaci yami'ke, lokacin momcy ta fito, ya ce, "mata yawuce.
Ta ce, "adawo lafiya babban mutum.
Nawaf yafita yana murmushi yanaso momcy ta ce, "masa abbu! ko babban mutum!, dayake sunan mahaifinta aka saka masa, shiyyasa papa yasaka masa modebbo saboda yana yima momcy kara.
Kai tsaye gidansu mas'ud yanufa, dukda yasan yana asibiti yanzu, wajen mami yashiga tana zaune afalo tana break dan yaran duk suntafi school, ta ce, "oyoyo my son!.
Nawaf yazauna yana murmushi, yarissina yana gaida mami, ta amsa cikin fara'a, ta ce, "ina amarya?, saida yay 'kasa da kai yana wani sosa gefen wuya ya ce, "tana nan lafiya mami.
Ta ce, "masha ALLAH agaishe mini da'ita, amma yakamata akawo mana ita mugani kafin ka koma, dukda muma zamuje muyima iyayenta godiya, dan ba kowane zaiyi kasadar bada d'ansa batareda yasan wanda yabamawaba.
Nawaf ya ce, "karki damu mami za'a kawota insha ALLAHU.
To ALLAH ya yarda.
Amin Nawaf yafad'a yana mi'kewa, ya ce, "mami bari na iske mas'ud a asibiti.
To shikenan ALLAH ya tsare shima aii yau bai dad'e da fitaba dan ya makara.
Nawaf ya fara tafiya yana fad'in ALLAH sarki, to bari na 'karasa.
To Modeebbo nagode ALLAH yayi muku albarka kaji.
Amin yafad'a yana fita.
Asibiti ya nufa wajen mas'ud, lokacin dayaje Nawaf yana duba marasa lafiya.
Guri yasamu yazauna mutane sai kallonsa sukeyi, dan wasu sun riga sun sansa a magiji๐๐ป๐ฅ, saidai suna kokwanton shine koba shibane.
Ga Nawaf baya son kallo dan haka sai yaji dukya takura, mota yatashi ya koma ya zauna, yad'an dad'e zaune amota yanata chattinga a awaya.
Wata wayarsa tahau wringing, banza yay da wayar yaci gaba da chatting d'insa, saida aka 'kara kira sanan ya d'auka.
Marakunya yaga ansaka, dan haka yay save d'in sunan yasmeen, saida ya ta6e baki sanan yad'aga, amma baiyi maganaba.
Yasmeen ta ce, "assalamu alaika, muryarta can 'kasa tafad'a kamar mai mura.
Sanin muhimmancin sallama yasa ya amsa.
Sukayi shiru suduka harna tsawon minti2, ita a tunanintama yakashe saitaji ya ce, "dan wula'kanci kinsan bakida abin fad'a kika kirani!!.
Cikin rawar murya ta ce, "plz dan ALLAH kabarni naje school d'innan wlhy idan kahanani zan cutu, kaga nayi asarar shekara d'aya da wata hud'u danayi ina zuwa kenan abaya.
Plx duk abinda zakamin karka had'a da maganar karatuna.
Banza yay mata kamar bazai tankaba, saikuma ya ce, "K!" Nifa ba'a sakani nayi abu dole, nafison idan na ce, "banason abu a 'kaleni, aii karatu ba dole bane ko?, duk kinbi kin wani dameni, kodai so kike kifita zuwa gidan tsohon mijinki daya sakeki ne??, yaja tsaki yana fad'in matsalar auren bazawara kenan!!!.
Yasmeen ta rintse idanu dan jin yakirata bazawara, maganar tadaki zuciyarta sosai, wasu hawaye sukabi kumatunta, tayi shiru batarda ta 'kara firta komai ba.
Shimadai shiru yayi baisake cewa komaiba, daga 'karshema saiya ajiye wayar batareda ya kasheba, kuma yana kallo itama bata kasheba.
Daga baya yasmeen ta yanke wayar tana cigaba da kuka, ahaka ameena tashigo ta sameta, cikin mamaki take kallonta.
Yasmeen ta ce, "ki zauna mana kika tsaya, Ameena ta ce, "ina naga tazama kina kuka, waike bazaki yarda da 'kaddaraba ne??, yasmeen ta share hawaye ta ce, "Ameena bazaki ganeba ne.
To ganar dani Ameena tafad'a tana zama akusada yasmeen,, yasmeen ta gayama ameena yanda sukai da Nawaf tun jiya dasukazo, da kiran datayimasa da daddare, dakuma na yanzu, ta ce, "Ameena waini zai kira bazawara!!.
Ameena ta ce, "kekam kinada abin haushi wlhy, to miye nawani kiransa saikace wadda take karatu aljanna, dammi bazaki share karatunba, idan kinada rabo nan gaba saikiyi, kuma ni banga abinyin kuka danya ce miki bazawara!!, aii kowa yasan keba bazawarar baceba ko??.
To ki kwantar da hankalinki, dolefa kema saikin nuna masa baki damu dashiba sanan zaisan darajarki.
Saidaifa 'kawata na tayaki murna, dan gay d'in handsome ne wlhy, saima yana gara kwallo a fili, gashi daga gani zaiyi soyayya.
Harara yasmeen ta galla mata, ta ce, "kin ganki ko zaki fara๐.
Ameena tayi dariya sorry my dear!, ammafa gsky nafad'a.
Yasmeen ta ce, "Ameena yanzu kenan nayi wahalar banza a school.
Bakiyiba wlhy tunda kin 'karu da wasu abubuwan,, kuma na tabbata zai barki kicigaba yana dai latsakine kamar yanda yasaba.
Aiko saidai ya latsa kansa!, dan insha ALLAHU bazan sake yimasa maganarba.
Hakan shine daidai 'yar uwa, nandai sukayita hira abinsu, Ameena tana 'kara koya mata dabaru.
,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
To shima dai Nawaf bayan wasu 'yan lokuta tashi yayi yashige office d'in mas'ud batareda muta ne sun gama ganin mas'ud d'inba.
Mas'ud yay murmushi, angon yasmeen kaine kake tafe.
Harararsa Nawaf yayi ya ce, "kaifa sai ahankali, kulum saikaita abu kamar wanan 'katon kan naka baya kawo maka wuta.
Dariya mas'ud yayi ya ce, "nida kai za'a tantance wanda kansa baya kawo wuta.
Firij Nawaf ya bud'e yad'akko gwangwanin Moltina yazauna yanasha.
Saida mas'ud ya gama sallamar mutane sanan ya juyo gareshi.
Nawaf ya ce, "likita bokan turai, dama haka mata suke safa da marwa a office naka.
Mas'ud ya ce, "tomiye aciki?, baneman lafiya sukazoba?.
Nawaf ya ce, "sunzo neman lafiya kukuma kuna kallesu ko?, ALLAH likitoci ma 'yan duniyane!!!.
Hhhhh ku kuma 'yan kwallo 'yan lahira, malam kada kayi mana mummunar fassara kaji.
Nawaf ya ce, "babu wani fassara alhaji, nikam gsky bazan bari 'katon banza yaduba mini mataba.
Hhhhh mutumina har kafara kishi kenan?, lallai na yasmeen bada kanka asare kaje gida kace ya fad'i.
Tsaki Nawaf yaja ya ce, "banza kawai wanda ba'a maganar arzi'ki dashi, ni kagama katuna min wai jiya da daddare saiga marakunyar nan takirani.
Mas'ud yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, kai malam dgsk?, to mitace maka??.
Nawaf ya ce, "magulmaci harda wani tasowa kai kaji gulma.
To ai kaine magul macin tunda kaine ka kawo maganar, plz bani nasha bana son jan rai.
Nawaf ya ta6e baki yashiga bama mas'ud labarin jiya, harda kiran data masa yanzu amota.
Ido mas'ud yazaro, kai amma bakada kirki, dammi ka ce, "mata bazawara??.
Nafad'a ba bazawarar ba ce?, A'a malam yasmeen ba bazawar bace, tunda ba a kaita gidan mijiba, anan aka d'aura yasaki aka baka.
Nawaf ya kur6i moltina yana fad'in malam babu wani kwaskwarima daza kamin na yarda.
Ai dama basai ka yardaba, d'an rainin hankali kawai.
Yakamata yauma kashirya da yamma muje, ko da daddare.
Dawa zaka?, Nawaf yafad'a.
Dakai mana, ba matarka bace.
Tsaki Nawaf yaja ashe zaku dad'e banjeba kuwa, jiyanma dan papa ya takura mini ne wlhy.
Hhhhh malam wataran bama zansan ka lalla6a kajeba.
Kai dallah saikace wani mara gsky.
Dariya mas'ud yaytayi masa, ya ce, "malam inzaka fito fili ka fito kafad'a kana son yarinya, zaka wani zauna kana kauce2.
Banza Nawaf yay masa ya d'au wayarsa yana dan danne............โ๐ป
Assalamu alaikum
Kuyi ha'kuri yaudai babu yawa, 'yan nefa suna tamana iskanci da wuta.
ยฉ2016
๐bilyn Abdul๐
๐Mrs Abdus'salam๐
๐ โคluv u oll my fan's๐
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: โโโโโโโ
๐พ NAWAFF ๐พ
โโโโโโโ
NA BILKISA IBRAHIM๐
Page๐๐ป21 & 22
......yau tun farar safiya faisal yazo gidansu yasmeen, tana tana shara a tsakar gida yashigo, zumbur tami'ke tana fitar da numfashi cikin sar'kewa, saikace wadda tayi gudun fanfala'ke.
A silo ya 'karaso gareta, hannu yakai da zummar ta6ata, ta kauce da sauri tana harara sa, cikin masifa ta ce, "kai malam bakada hankaline??.
Murmushin takaici faisal yayi, ya ce, "indai akan sonkine to banida hankali yasmeen.
Ya dur'kusa agabanta tamkar uwarshi, hawaye nata zirara bisa kumatunsa, cikin raunin murya ya ce, "yasmeen plz ki taimakeni ki dawo gareni, nine kawai nake miki soyayyar gsky, wlhy abinda kikaga yafaru sharrin shaid'an ne, da makircin hisham.
Ta6e baki yasmeen tayi, ta ce, "kaga banida matsala da wannan, kuma ina mai gargad'inka daga yau karka sake koda kuskuren ta6ani, kai kanka kasan ada ban amince ka ta6a jikinaba bare yanzu danakeda aure....
Da sauri abba yafito domin jin hayaniyar tayi yawa, turus yayi domin tozali da faisal tsugunne a gaban yasmeen.
Abba ya 'karaso yana tambayar lafiya dai ko??.
Suduka suka dawo da kallonsu gareshi, yasmeen tafara zubar da hawaye tana nuna faisal, shima dai faisal d'in kuka yake, ya mi'ke ahankali yaje wajen abba, dur'kushewa yayi agabansa ya kama 'kafafunsa yari'ke yana gunjin kuka.
Hannu biyu abba yasa ya d'agoshi, haba faisal babba dakai ka zauna kana kuka?, miya faru kake kukane??.
Hannu faisal yasaka ya share hawayen fuskarsa, yashiga zayyano kalaman nadama daban ha'kuri ga abba, da ro'konsa akan yabashi yasmeen a karo nabiyu zai gyara halinsa.
Abba ya ce, "kayi ha'kuri faisal yanzu banida iko akan yasmeen, mijinta shike da iko da'ita, kayi ha'kuri ALLAH zai babaka wadda ya fita insha ALLAH.
faisal ya langa6e kai yana hawaye, itama yasmeen hawayen takeyi dan jitake tana wani son faisal d'in yanzu.
Ahaka yaseer da umma suka fito suka samesu, yaseer ya ta6e baki danshi faisal baya bashi tausayi ko kad'an.
Itama umma lalashi da nasiha takeyima Faisal, amma faisal ba gane yaren nasu yakeyiba, danshi burinshi kawai abashi yasmeen, itace kad'ai nasihar dazatayi masa tasiri.
Babu dad'ewa saiga hajiya jummai da dadyn faisal.
Suma saisuka kama hawayen dan suna tausayin d'ansu, abba ya ce, "yakamata suje ciki dan wajen akwai sanyi.
Bayan sun zazzauna afalo, su alhaji buba sukacigaba da ro'kon abba akan yabama faisal yasmeen a karo na biyu.
Abba ya ce, "bansan irin bayanin dazan muku ku fahimceniba, amma yakamata ku gane igiyar auren yasmeen ba'a hannuna takeba, bakuma yanda za'ayi nakira yaronnan na tsareshi akan yasaki yasmeen, kofa na aikata hakan tofa auren bai sakuba tunda ni ba mahaifinsa bane.
Kuyi ha'kuri muci gaba da yima faisal addu'ar fatan alkairi....
Afusace alhaji buba yami'ke yana masifa, kai malam yazaka zauna kana jamana rai akan abinda baifi 'karfinmuba, harzaka wanice bayanda zakayi kasaka yaron yasaki yasmeen, shin wai bakada tausayine, baka ganin halin da d'ana d'aya tilo yashigane??, kodan kuna ganin 'yarku tanada 'kyaune??....
Abba ya 'katse Alhaji buba ta hanyar d'aga masa hannu๐๐ป, kaga karka gaya mini magana, ai bani na ce, "faisal ya saki yasmeen bako??, ko kai ka manta da wula'kantani dayayi acikin taron jama'a ba yasaki tawa d'iyar ba!, sannan wanda kake magana na saka yasaketa shine ya share mana hawayenmu!!, to kuma saboda son zuciya saina sakashi yasaki yasmeen saboda faisal ya aureta???..
Hajiya jummai ta ce, "dan ALLAH kuyi ha'kuri, agaban yarafa muke, da'kyar suka lafa da hayaniyar dasukeyi.
Alhaji buba ya ce, "kutashi mu tafi, kuma inaso kasaka a zuciyarka ka mallaki yasmeen ka gama, yana gama fad'a yaja hannun faisal da hajiya jummai sukayi waje.
Kuka yasmeen tafasa ta zube afalo tana birgima, umma tasa hannu ta d'agota tana lallashi, abba ya ce, "mamana kiyi shurinki, babu abinda suka isa suyi miki, kuma nanda sati uku insha ALLAHU kina d'akin mijinki.
Ni ban ta6a ganin jahilan mutane irinsu alhaji buba ba, in banda jahilci yazakuce wani yasaki matarsa d'anku ya aura, bayan kuma shine yafara tozartamu agaban mutane yasiki yarinyar atake agurin da'aka d'aura musu aure.
Umma ta ce, "babu wani jahilci malam son cuciyane kawai yake damunsu, 'kila atunaninsu mu bamu san darajar 'yarba ko???.
To aiko zanyi maganin son zuciyarsu kwananan.
Yaseer kuwa d'aki yashige yashiga kiran number d'in Nawaf, saidai yayi masa kira yakai biyar bai d'aukaba, dan haka ya ha'kura yay shirin makaranta yatafi.
________________________
Alokacin da yaseer yake kiran Nawaf baya kusada wayoyinsa, yana wajen motsa jiki dayake fita akowace safiyar duniya, inhar yana 9ja.
Sai wajen 'karfe 8:00am yashigo gidan jikinsa sanye da farin JC, gajeren wando da 'karamar riga mara hannu, 'kabarsa sanye da takalmin 'yan kwallo, dad'an gudunsa yashigo gidan, yasaka robar ruwan dake hannunsa cikin bola, key yasa yabud'e d'akinsa ya shige.
Saida yasha ruwa sosai sannan yazauna yana zufa ya fitar da huci mai zafi daga bakinsa, ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe idanu, yakai minti5 ahaka daga bisani ya cire takalman 'kafarsa ya ajiye.
Bedroom d'insa yashiga, yacire kayan ya jefa cikin wani dogon kwando, ya bud'e wata 'yar durowa dake kusada bayi (bathroom) tawul ne aciki kala2, yad'akko kalar yellow ya d'aura daga 'kugu zuwa guywa.
Wanka yashiga, ammafa ya dad'e, dan nikam harna fara gajiya ma da jira, ya kai tsawon minti50 sannan yafito, d'aure da tawul d'insa, hannunsa ri'ke da 'karami fari yana goge sumarsa.
Zama yayi yashiga tsara ado, na ce, "kai gay d'inana d'an kwalisa ne gsky.
Kwalliyarma yakai tsawon lokaci yana tsarata saikace mace lol, daga 'karshe yafito sanye cikin 'kananun kaya ya d'ora tafkekiyar rigar sanyi jaa mai 'kyalli saboda yanayin sanyin garin, sai zabga 'kamshi yakeyi.
Zama yayi yay break, sanan ya jawo phones d'insa, ya kira wad'anda suka kirashi baya nan, haryazo kan number d'in yaseer, kira yashiga yi amma ba'a d'agaba, yasake kira, harta kusa katsewa aka d'aga.
Mai makon yaji muryar yaseer sai yajita yasmeen, cikin muryarta mai za'ki ta ce, "mai wayar baya nan!.
Nawaf ya ce, "ina yaje??.
Ita bata gane Nawaf bane, ta ce, "yaje school, amma idan yadawo za'a sanar masa.
Daya kula bata ganeshiba saiyayi niyyar zolayarta, ya ce, "toke wacece?.
Saida taja numfashi sanan ta ce, "yayarsace.
Saida yad'an ta6e baki sanan ya ce, "hummm kodai 'kanwarsa, dan dagajin muryarki "k, yarinya 'karamace.
Cikin 'kufula yasmeen ta ce, "kai malam sai anjima, kabi duk ishii mutane da surutu, d'if ta kashe wayar.
Dariya sosai Nawaf yayi, ya ce, "kai yarinyarnan 'yar bala'ice wlhy, dawata muryarta kamar ta gyare.
Yashiga kwaywayon muryarta yana dariya, tamkar mai kallon film ko wa'ka.
--------------''''''---------------------
Da yamma abba ya kira papa awaya yay masa bayanin komai, game da abinda yafaru da safe, maganar ta bama papa mamaki saikace a wasan kwaikwayo, kasaki mace kadawo kana hauka wai kana sonta.
Papa ya ce, "karya damu zuwa gobe zaizo suyi magana, yasmeen ta tare kawai agindasa, ta 'karasa karatun a d'akinta.
Papa