Showing 48001 words to 51000 words out of 74786 words
Ta maida 'kofar asanyaye tarufe ta ce, "to ALLAH yakaimu, saman gado tafaďa ta kwanta, tayi addu'ar barci dan Nawaf bai kiraba ita kuma wlhy bazata kirashiba.
Ta kammala addau'ar ta lumshe idanu amma badan barciba, dan tana bu'katar jin muryar Nawaf, kamar daga sama wayar tafara 'kara alamar kira, tayi Burus da wayar harta tsinke, yasake kira, saida yakira sau uku, nanma ta'ki ďauka, sai ana huďu ta ďauka zuwa sanan Nawaf yacika fam da haushi.
Ta ďauka kuma tayi shiru, shima shiru yayi sai huci yake kamar yana gabanta, cikin masifa ya ce, "waike wace irin "'yar rainin wayoce, dan wula 'kanci tunďazu nake kiran wayarnan kika 'ki ďauka kuma nasan kina kallonta.
Yasmeen ta ta ta6e baki, tayi shiru kuma, wannan yasa Nawaf 'kara hawa sama, yacigaba da masifa, "k wlhy kishiga hankalinki dani, karkiga ina kwance a gadon asibiti kice zaki raina mini wayo, kinsanni kinsan halina, kodan kinga ina kulaki shine zaki min hauka, daga yanzu idan kinga na sake shiga harkarki kiyimini abinda kika ga dama, tsowww yaja tsaki tareda yanke wayar.
Yasmeen ta dafe kai tana hawaye, wai ita miyasama ta 6atama Nawaf rai, miyasa bata ďagaba tun akiran farko, gashinan wajen jan aji ta 6ata komai, itada take fata tajawo hankalinsa gareta, gashi nan ta na 'ko'karin nisantasu da juna, sai kawai tahau kuka.
Na ce, "tofa kaga wani ďigimi, wai dukan sauro da 'kota.
Shikam Nawaf wurgi yayi da wayar ta fashe, yamaida kansa ya kwanta yana hargitsa sumarsa, zuciyarsa cike da ba'kin ciki, yarasa wane irrin 'kiyayya yasmeen take masa haka, wace irin tsana take masa wai, ya rintse idununsa yana fitar da huci, dolene yaďauki mataki akan yarinyarnan, yakamata yafita harkarta gaba ďaya, dan yakula 'yar kulawar dayake bata ta kwana biyunnan ce takeson jawo masa raini a wajenta.
Zai tureta daga zuciyarsa yacigaba da harkokinsa, inyaso yamutu da sonta azuciyarsa mana, ahaka doctor yazo yasameshi.
Bayan yaďan dubashi ya ce, "yana bu'katar ya kwanta yahuta, dan haka allurar barci zai masa.
Nawaf ya ce, "A'a baya so.
Doctor ya ce, "aii tazama dole, babu 6ata lokaci ya zurkuďa masa, barci kuwa yay awon gaba dashi.
To itamadai yasmeen barcin ne ya saceta bayan tagama koke kokenta.
_________________________________ a yau aka fara koyama Nawaf tafiya, yana ri'ke da sanda guda biyu likitoci guda biyu suna gabansa saikuma wasu ma'aikatan abayansa, a harabar asibitin suke, dan haka su yasmeen suna gefe suna kallo.
Nawaf sai matse idanu yakeyi yana dogara sanduna, ga zufa daketa tsatstsafo masa, sunďanyi nisa da tafiya, aka kar6e sanda ďaya, to dagananfa Nawaf ya 'kara shan wahala, zufa kuwa aii kamar ana kwara masa ruwa.
Yasmeen tai 'kasa da akai tana hawaye, suma su Anwar haka, aka 'kara kar6e ďayar sandar, yafara tafiya da 'kafafunsa, daganan jikinsa yafara rawa, dauriyarsa ta 'kare, hawaye suka fara ambaliya a fiskar Nawaf, gsky koni yabani tausayi, gashi mugaye likitocinnan sun'ki cewa ya zauna.
Tun yana daurewa yana ďaga 'kafar har yakoma janta, daga bayama saiya faďi, daga nan suka ďaukesa aka maidashi ďakin dayake, zuwa sanan yafita hayyacinsa.
Momcy ta rungume yasmeen tana rarrashi, dukda itama hawayen takeyi.
Harzuwa dare an hana kowa ganinsa, sai ha'kura sukayi suka koma masauki.
Washe garima dasukaje basu ganshiba, sai lokacin da aka fito dashi domin motsa jiki, yaukam yamafi jiya shan wahala, saboda 'kafar tayi tsami jiya, haka suka kwasheshi suka maida.
To ayau rana ta uku sai ya kasance da sau'ki, dan yau baisha wahalarba, dakansama ya koma ďaki.
haka rayuwar tacigaba da tafiya, Nawaf yana samun sau'ki, kuma kullum ana fita dashi dan motsa jiki safe da yamma, saidai yafita harkar yasmeen gaba ďaya, ko zuwa sukayi dubashi daga gaisuwa babu abinda yake shiga tsakaninsu, saima 'yar harara da murguďa baki, amma kowa yana ma'kale da son ďan uwansa, babu wanda yafahimci halin dasuke ciki sai mas'ud, dan basayi gaban su papa, da su Abdallah, amma gaban mas'ud yin abunsu sukeyi.
To yaudai an sallami Nawaf, gidan dayake zaune suka nufa, ya haďa duk abinda zai bu'kata suka koma hotel ďin inda su momcy suke.
Papa ya ce, "akai masa kayansa inda matarsa take, gaban yasmeen yashiga faďuwa, miyasa baza'a kama masa ďakiba, kosu zauna da mas'ud, itako batason su kasance đaki đaya da Nawaf, bare yanzu daya tsaneta, ta lura ko ganinta baya sonyi, amma babu yanda zatayi tunda umarnin papa ne.
Nawaf ya mi'ke yana dogara sanda yanufi ďakin yasmeen yana faďin bari naje nayi wanka saida safenku, kowa ya ce, "ALLAH yakaimu, momcy ta ce, "yasmeen tashi kema kije saida safe.
Badan tasoba ta mi'ke dan cika umarnin momcy.
Ta tura 'kofar tashiga jiki a sanyaye kamar wadda kwai yafashemawa aciki, Nawaf yana zaune bakin gado yana cire kaya, kallo ďaya yasmeen tayi masa ta kawauda kai.
Shiko aii ko kallon inda take bayyiba, tayi tsaye a tsakkiyar ďakin tana wasa da yatsun hannunta.
Ya mi'ke yanufo inda take dagashi sai ďaurin guntun tawul, ahankali takeja baya azatonta wajenta yataho, daya matso saita matsa, yamatso ta matsa, haka sukaitayi har zuwa jikin 'kofa, ta rintse idanu dan sunje 'karshe, ta manne da 'kofa sosai ga idanunta a runtse, ya'karasa takowa ahankali gurinta yakai jikinsa kusada ita kamar zai ringumeta fuskarnan murtuk ya tsare gida...........................✍🏻
Assalamu alaikum
Nagode da sakwannin gaisawa da addu'ar samun lafiya dakuketa ďawai niyar turomini, harma dama su kirana, , Nagode kwarai da 'kaunarku gareni, nima ina 'kaunarku a duk inda kuke, ALLAH ya barmu tare, ya bar mana zuminci😍😍😘😘💓💓💚💜💖luv u oll!!!!!!!!!!!!!!👌🏻👌🏻
©2016
💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😍💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆
NA BILKISA IBRAHIM💓
Page👉🏻41 & 42
.....Yasmeen ta ďauke numfashi, sai 'kirjinta ke dukan tara2, ga jikinta yana rawa, tamaba Nawaf dariya kwarai da gsk, amma saiya gimtse.
Kaďan yara6u da jikinta, yakai hannu bisa key ďin dake 'kofar ya kulle.
Tanaji yana sakama 'kofa key sai rawar jikinta ta 'karu, tazame 'kasa ta zauna da6as, ta tura kanta tsakiyar cinyoyinta, tana ambatar sunan ALLAH.
Ya bita da kallo bayan yagama kulle 'kofar, kai ya girgiza yan ta6e baki, kamar wanda yaga wani abin daba'a so.
Bayi yashige domin yin wanka abinsa.
Bayan wasu 'yan mintina taji motsin ruwa, amma tsoro yahanata tashi daga wajen, tama kasa ďago kanta, itafa har yanzu ta zata Nawaf yana awajen tsaye😜.
Shima yana wanka yana murmushi, ashema yarinyar nan matsoraciya ce?, to ita da mitake tunanin zan mata ne?, yay wata 'yar dariya, ashedai ana tsoron iya iya inji 'yar mayya, yarinya kamar farar kura, ga tsoro ga jan faďa, dahaka yagama wankan yana zancen zuci, yafito
Abin yabashi mamaki daya ganta a inda yabarta, kuma kanta a6oye har yanzu, ya murmusa yana dogara 'yar sandarsa, abakin gado yazauna yana cije le6e dan har yanzu 'kafar tana ďan masa zafi, tunda bata gama sakiba gaba ďaya, ya shafa mai tareda shirin barci, harkokinsa yaketayi batareda ya'karabi takan yasmeen ba, yagama shirinsa tsaf, ya haďa shayi yasha da magungunan sa.
Saida ya kwanta sannan ya ce, "k anan zaki kwana ne??, tayi shiru babu amsa, yay tsaki waike ba'kya jina ne?, yay maganar cikin tsawa.
Da sauri yasmeen ta ďago tana kallonsa baiwar ALLAH ashe barci takeyi ahaka, ya ce, "bazaki tashi a 'kofar nanba nane??.
Yanda yay maganar yana zaro idanu gashi ya haďe girar sama data 'kasa, saitaji bazata iya maida masaba, dan Nawaf yanada kwarjini, idan ya haďe fiska ko kai waye dole kaji tsoronsa, ta mi'ke jiki na rawa ta shige bathroom.
Nawaf ya girgiza kai yana lumshe fararen idanunsa, gaba đaya kansa a kulle yake, yakamata yanemi shawarar mas'ud, amma kuma bayaso kowa yasan sirrinsa, to kenan zai cigaba da zama da damuwa azuciyarsa, gashi wadda yakeyi dan ita batasan yana yibama, yafitar da huci maizafi daga bakinsa,, lallai lokaci yayi dazai gwada karfinsa yacije le6ensa na 'kasa, yakai hannu bisa 'kafarsa mai ciwo yana girgiza kai, afili ya furta akwai sauran lokaci!!!👌🏻.
Tadaďe a bayin zaune dan babu abinda takeyi, saima duniyar tunani data lula, ta manta da inda take zaune.
Nawaf sarkin saurin jin haushi har ya sha'ka, ya mi'ke yana masafa, yaja sandarsa zuwa 'kofar bayin, da 'karfi ya buga 'kofar bathroom ďin, "k wai wane irin iskancine wannan?, mikikeyi a cikin bathroom ďin??.
Yasmeen ta ce, "wankafa nakeyi.
Yaja tsaki yana faďin A'a iyo kikeyi 'karewar wanka, wlhy idan baki baki fitoba saina 6alle 'kofarnan, kuma jikinki saiya gaya miki.
Ta murguďa baki kamar tana gabansa, a zuciyarta ta ce, "wlhy idanma wani abu kake 'kullawa to kama kwance sa, dan ALLAH bazai ta6a baka sa'a a kainaba, mugu kawai, amma afili sai ta ce, "aii dai ganinan fitowa ko.
Kwafa Nawaf yayi yakoma kan gadon yakwanta yana jan 'kafa, yana mamakin miskilanci irin na yasmeen.
Na ce, " kunji wani 'karfin hali, tomiye na damuwa da fitowarta, kuma shi ya manta da nasa miskilancinne??,😏
Yakai kusan minti goma da kwanciya sannan yasmeen ta buďe 'kofar ta fito, babu wani alamar wanka datayi, zuwa sanan Nawaf ya daďe dayin barci, saboda magungunan daya sha.
Ta bishi da harara tana 'kun'kunai, saman kujera ta zauna, ta tsurama 'kya'ky'kyawar fuskarsa idanu, barci yake amma tamkar yana murmushi, ko afili bazakaga fuskarsa hakaba, lalle tayarda mijinta handsome ne, kuma Gentle man ne, domin komai nasa mai ajine, tafiyarsa, maganarsa, bare idan yana 'kayataccen murmushinsa mai kashe zuciyar 'yammata.
Yanada kwarjini na musamman wanda dole ma'abota tarayya dashi su girmamashi, gashi da tausayi da son jama'a, tunda take tareda shi bata ta6a ganin ya wula'kanta waniba dukda ďaukaka da ALLAH ya bashi, jarumi wanda duniya tasani, kuma take alfahari dashi, tunda yasamu ciwonnan gidan radio da tv mujallu da jaridu suketa yayatama duniya, yanzu ta'kara tabbatarwa Nawaf sananne ne a duniya, yakan girmama masoyansa, gashida 'kyauta, yakan taimakawa na 'kasa dashi bashida rowa ko kaďan, tasaki wani lallausan murmushi yayinda taga fuskar Nawaf ma tana bayyana murmushin. Yajuya kwanciyarsa zuwa ďayan 6angaren.
Tazame ta kwanta saman kujerar dan ganin ya 6oyema ganinta, babu daďewa barci yay awon gaba da'ita.
Na ce, "mukwana lafiya.
Da asuba yarigata tashi kona ce, "tare suka tashi, badai ta nuna ta farka bane, tana kallonsa yami'ke yana dogara sandarsa zuwa bayi, alwala yayo yafito, ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya fara, ya ďauki abun sallah ya shinfiďa, saida taga ya kabbara sallah sannan ta tashi ahankali itama tayo alwalar, abayansa ta kabbara tata sallar.
Bayan sun idar kowa ya zauna yana addu'a, Nawaf yajuyo da zummar tada yasmeen tayi sallah, sai kuma yaganta abayansa, ya ďauke kai tamkar bai gantaba, itama tayi burus dashi kamar batasan da zaman wani ďan adam a wajenba.
Ya tashi ahankali yana dogara sandarsa, yafice batareda yabi takanta ba, murmushi yasmeen tayi tatashi ta haye gado ta kwanta abinta.
Shikam wajan motsa jiki yanufa dake a hotel ďin.
Yasmeen tasha barcinta sosai, dan Nawaf bai dawoba, yanacan wajen motsa jiki, har saida ma'aikaciya tashigo, yasmeen ta fito waje dan bata damar gyara ďakin, saida tagama sannan tadawo tashiga wanka.
Tafito ta shirya tsaf cikin siket da riga na golden brown ďin material, ta naďa ďaurin ďankwali mai tsari, dukda bawata kwalliya tayiba tayi 'kyau sosai, tana fesa turare Nawaf yashigo sai hura hanci yakeyi daka gansa kasan yagaji matu'ka.
Momcy tashigo itama, da sauri yasmeen ta tsugunna tana gaisheta, momcy ta amsa cikin fara'a, ta ďora da faďin ďiyata, ga mijinki nan nakula yagaji matu'ka, daga wajen motsa jiki yake, kisamu ruwa mai zafi ki gasa masa jikinsa danya samu ďan'karfi kinji.
Yasmeen taďaga kai atsorace kuma cikin kunya, momcy tadafa kan Nawaf tana masa sannu, ya amsa yana ďan murmushi, karki damu momcyna komai zai dawo normal insha ALLAH, wannan motsa jikin shine zai taimaka mini sosai.
Momcy ta ce, "to shikenan abu na ALLAH ya'kara lafiya kaji, amin my dear mom, momcy ta ce, "bari naje, ďiyata agasa 'kafarnan sosai, dan ya ce, "jiya da daddare ba'ayiba.
Yasmeen ta ce, "to mom.
Momcy tafice taja musu ďakin.
Yasmeen tana tsaye inda momcy tabarta ko motsawa batayiba, shikuma Nawaf yana zaune a kujera yana mata kallo kasa2, tayi masa 'kyau sosai yau, kayan sun dace da jikinta, jiyyake tamkar yaje ya rungumeta.
Yaďan gyara zamansa yana faďin wash ALLAHNA!!.
da sauri yasmeen taďago tana kallonsa, ya haďe fuska kamar bashiba, ya ce, "kije ki haďa ruwan mana.
Ta ďan hararesa kafin tawuce bayi, ta haďa ruwa mai zafi sosai, wanda nakula harda mugunta, dan da alama zaiyi zafi sosai.
Tafito tana goge hannu da 'karamin tawul, kallo ďaya tamasa ta ce, "na haďa, ya kalleta yana ta6e baki to dakika haďa sai akayi yaya?, itama bakin ta ta6e sanan ta ce, "idan kana bu'kata saikaje kayi wankan.
Yami'ke yana kwafa, gabanta yaje ya tsaya kerere, ta ce, "lafiya?, ya ce, "ita takawo haka, hannunta yaja kawai suka nufi hanyar bayi, ta ce, "wai miye haka ne??.
Bai tanka mataba har saida sukaje cikin bathroom ďin sannan ya ce, "bakiji mi momcy tace mikiba kenan??, catayi ki gasa mini jiki.
Yasmeen ta zaro idanu waje, tokai saika amince nagasa maka jiki ďin??, yay wani bazawarin murmushi yana faďin toke ba matata bace, miye aciki??.
Yasmeen tajuya zata fice tana faďin nikam bada niba wlhy.
Da sauri ya dam'ke hannunta, "k momcy kika raina kenan??.
Yasmeen ta ce, "kata6a ganin mutum ya raina mahaifiyarsa, kodawasa bazan raina mahaifiyataba aii.
Nawaf yaji daďin furicinta, yakaďa manyan idanunsa cikin muryarsa mai daďi, ya ce, "to saiki cika umarninta aii ko, yasmeen ta girgiza kai, kaima kasan bazai yuwuba 'kato dakai ka tu..............saikuma tayi shiru.
ya matsa hannunta daya ri'ke da 'karfi, nine 'katon???, jin zai murmushe mata kashin hannu abanza ta girgiza kai, nifa badakai nakeba, ya ce, "dawa kike to???.
Tuni tafara hawaye, kasakar mini hannu to zan faďa.
Bayason ganin kukanta dan haka yasaketa, amma yakoma 'kofar bayin ya tsaya, babu damar guduwa kenan.
Ta ce, "plz kayi ha'kuri wlhy bazan iyaba, inajin kunya.
Hummm dama kinada kunya 'yammata??, yasmeen ta harareshi A'a banida ita, ya murmusa ke dai bakinki baya mutuwa ko??, ta murguďa baki😏, ya ce, "yayi 'kyau 'yammata, yafaďa yana nufota, ita kuma taja baya har suka kai 'karshen bango.
Yay wata dariya yarinya ai anzo wajen kuma, ta manne da jikin bango tana mazurai.
Ahankali ya'karasa gareta, har suna jin numfashin juna, ta runtse idanu kam kamar wadda taga ba'kin aljani, yadafe bango da hannayensa biyu, itakuma tana tsakkiya har jikinta yana gogar nasa, yakai fukarsa jikin wuyanta yana shinshina.
Ta kauda kai gefe tana faďin wai miye haka??, yacigaba da shinshinar wuyanta batareda ya tankataba, tasa hannu tana ture fuskarsa.
Cikin sar'kewar murya ya ce, zanyi maganinki ne 'yammata, dan na kula kin rainani dayawan gsk, ya ďago yana kollonta, sai kauda fuska takeyi harda 'yan kwallanta, itadai aduniya ta tsani namiji yazo kusada ita, tun abinda yaso faruwa da ita a kwangwalan da wanda Faisal yaso aikata mata yasa takasa mancewa har yanzu, wasu hawaye masu zafi suka zubo akumatunta.
Nawaf yasa yatsu biyo yadawo da fuskarta tana kallon tasa, sukaima juna kallon ido cikin ido, tai saurin lumshe nata idanun dan ganin yanda nasa suka canja launi zuwa jaa, ya tsura mata idanunsa masu kalar jaa ayanzu, ahankali yakai bakinsa kan nata, shima ya lumshe nasa idanu.
Yasmeen tashiga turesa tana kuka, ganin zata iya sakawa yafaďi saboda 'kafarsa babu kwari, saiyasaka hannuwansa biyu yakamo kumatunta ya ri'ke sosai atafin hannunsa.
Sumbatarta yake kamar zaicire mata la66a, duk duka da mintsini datake masa baisa yasaketa ba, saida yayi mai isarsa ya saketa dan kansa yana fitar da numfashi, dagudu tafito ALLAH yasota bai rufe 'kofar bayinba.
Shikuma yay saurin zaunawa danjin zai faďi, yadafe kai yana jijjuyawa, yadaďe ahaka, daga bisani yasakarma kansa ruwa, yakai tsawon minti20 ahaka, saida yaji ya dai daita sannan yahaďa ruwa mai zafi yashiga ciki, dan wanda yasmeen ta haďa ya huce.
Yay lamo aciki idanunsa alumshe ruwan yana shiga dukkan sassan jikinsa musamman ma 'kafarsa mai ciwo, yadaďe ahaka sannan yay wankan sabulu yafito yana goge sumar kansa da 'karamin tawul.
Abakin gado ya tarar da yasmeen zaune ta rabga uban tagumi fuska sha6e2 da hawaye, da'alama tana duniyar tunani.
Ya zauna yana faďin "k!, shiru tayi masa, yadaka mata tsawa "k!!! Ba'kya jina?.
Afirgice ta kalleshi, ya haďe fuska kamar bashiba, cikin faďa ya ce, "nabaki minti3 kije yanzunnan ki wanke fukarki, tun kafin nayi miki abinda yafi na ďazu, 'yar rainin hankali idan momcy tashigofa basai ta zata wani abu nayi mikiba.
Itadai yasmeen ta mi'ke taje ta wanko fuska, dan bataso ya ce, "zai rin'ka mata irin haka, zata tsaneshine, duk wanda zai nuna yana son jikinta tofa yana zama ma'kiyintane.
Tafito tana wani rarra6ewa ajikin bango, ya ce, "maza ki shafa fauda a fuskarki kamar ďazu,