Showing 36001 words to 39000 words out of 74786 words

Chapter 13 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

368

bedroom ya wuce ya kai kallonsa ga yasmeen dake saman gado 'kudun dune a bargo, ya đaukr kansa daga kallonta, cigaba yayi dayin harkokinsa, yagama komai na al'adar rayuwarsa.
Yay tsaye abakin gadon yana faďin ke wai mikike nufi da kwanciya a gado, kinsandai bazan kwanta saman kujeraba ko??.
Jin tayi banza dashi yasa kai hannunsa ya yaye bargon, wani hucin zafi ya dakeshi, yay sagare yana kallonta, zama yayi abakin gadon yakai hannu ahankali saman wuyanta, idanunsa ya runtse tareda fitar da huci mai zafi.
Baisan sanda yakai hannu yana shafa gashintaba ahankali, ta buďe ido tana kallonsa, da sauri ta tashi zaune tana jujjuya ido.
Ya gimtse fuska yana faďin mike damunki, cikin rawar murya ta ce, "zazza6i.
Mi'kewa yayi batareda yayi magana ba, ya buďe durowar gefen gadon ya ďakko magani harya mi'ka mata saikuma ya janye hannunsa yana faďin kunci abinci??.
Ta girgiza kai alamar A'a, maganin ya mayar ya fita, babu daďewa yadawo hannunsa ďauke da kofin shayi, ya mi'ka mata, yatsine fuska tayi tana faďin nifa na'koshi.
Batareda yayi magana ba ya zauna kusada ita, yaja filo yajingina mata ajikin gado, kamata yayi ya jinginata da filon, itadai sai kallon ikon ALLAH takeyi, kofin yasaka mata abaki, dole ta buďe bakin ta kur6a, haka yayta bata tana sha, amma babu magana tamkar wasu kurame.
Saida tasha rabi sanan ta ce, "na'koshi, harararta yayi ya ce, "kar6a bana son yawan magana.
Kar6a tacigaba dayi harta shanye tas, sanan ya ďako maganin yabata, ta yatsine fuska kamar zatayi kuka dan bata son magani.
Ya 'kara ďaure fuska, "k ni ki kar6a kona tashi na kwanta dan barci nakeji, tana hawaye ta kar6a ta shanye tana rintse idanu.
Tana gama sha tafara yun 'kurin amai, da sauri ya rungumota zuwa jikinsa yana shafa bayanta kamar wata jaririya, saida aman ya lafa sanan ya ďagota yana faďin kin daina jin aman ko??.
Kai ta kaďa masa.
Ya gyara mata kwanciya ya lullu6eta da bargon, dandanan barci yay gaba da ita, shikuma yakoma saman kujera ya kwanta, aiko yadaďe baiyi barciba.
Nima na lalla6o na firo🚶🏼.
_________________________________ da asuba tunda yafita bai dawoba sai wajen 'karfe 7:30am tare suka shigo da mas'ud, zuwa sanan masu aiki sun gama gyara gidan tsaf, ita kuma tana kichin tana haďa break.
Yashiga bedroom bata nan ya fito yana faďar kaga yarinyarnan ko yanzu haka tana wajen su momcy.
Mas'ud ya ce, "A'a, kadai duba kichin naji kamar motsi.
Nawaf yanufi kichin batareda yayi magana ba, bakin 'kofa ya tsaya yana kallonta saidai fuskarsa babu walwala, da sauri ta juyo danjin tamkar mutum abayanta.
Karaf suka haďa ido da Nawaf ta kauda kai daga kallonsa, ya ce, "keda bakida lafiya miye nawaniyin girki.
Kanta a'kasa ta ce, "aii naji sau'ki.
Ya ďan ta6e baki, wannan ba hujja bace, ki sauke abinda kika ďora kizo ga mas'ud yazo zai dubaki, yana gama faďa yafice.
Ta sauke abinda ta ďora dama ya nuna, falo tafito, ta gaida mas'ud, ya amsa tareda tambayarta ya jikin??, ta ce, "da sau'ki.
Tambayoyi yay mata tana bashi amsa yana rubutawa, bayan ya gama ya ce, "bari naje zuwa anjima zan kawo miki magunguna, ta ce, "to, ka gaishemini da Ameenar, yafita yana faďin zataji.
Kichin ta koma bayan fitarsu, dan tare suka fita da Nawaf.
Mas'ud ya kalli Nawaf ya ce, "mutumina gsky yasmeen tana cikin damuwa, dan damuwarce ta haddasa mata zazza6in.
Nawaf ya ce, "badole damuwa tasa ta zazza6iba tunda gangar jikinta ce a gidana zuciyarta tana wajen tsohon mijinta.
Cikin mamaki Mas'ud ya ce, "ban ganeba, Nawaf ya zayyana masa duk abinda ya faru jiya.
Mas'ud ya ce, "bawai ban yarda bane, amma yakamata ka sake yin bincike, danni amina tabani labarin komai.
Nawaf yay shiru baice komaiba, mas'ud ya ce, "bari nawuce saina dawo.
Sanda Nawaf yadawo yasmeen tana wanka, ya zauna saman kujera yana jiran fitowarta, ta daďe abakin 'kofa tana tunanin yanda zata fito da tawul, kamar ance Nawaf ya juyo suka haďa ido da yasmeen da sauri ta koma cikin bayin.
Ďan 'karami tsaki Nawaf yayi, tareda mi'kewa yanufi hanyar bayin, ahankali ya ce, "kifito ki shirya ni na koma falo, ki kuma shirya kayanki kala huďu dan zamuje anguwa, yana gama faďa yafice.
Saida taji batajin motsinsa gaba ďaya sanan ta fito, agurguje ta shirya dan bataso yazo ya ritsata.
Saida ya daidaici tagama sanan ya shigo, ya ce, "kin haďa kayan dana ce??, ta ce, "A'a, bayi yashige batareda ya sake maganaba.
'Karamin akwatinta ta ďakko ta haďa kaya biyar da duk abinda zata bu'kata, tai sauri ta koma falo, taďanyi break kafin ya fito.
Shima daya fito saiya shirya kayansa a ďan akwatinsa irin na maza, falo yafito ya isketa ya zauna yaci abinci, tana zaune a gefe tana kallonsa.
Yagama tsaf yami'ke, ya ce, "tashi muje muyima su momcy sallama.
Yasmeen ta ce, "azuciyarta wai wanan wace irin tafiya ce babu shiri???, na ce, "yasmeen yazakiyi, mulkin kenan aii.
Sallama sukaiyima su momcy, anan takejin garin da zasuje, kafin Nawaf yagama tattaunawa da papa yasmeen tadawo ta gyagygyara abinda ya dace, sanana su talatu suka kaimata akwatinan wajen mota, saida suka jira mas'ud yakawo mata magungunan ta sanan, suka tafi su momcy suna ďaga musu hannu.
_________________________________ tunda suka fara tafiya babu wanda ya tankama wani, saida suka kusa fita kano sanan ya tsaya gidan mai, aka cika musu tankin mota taf, ya shigo suka ďauki hanya bayan yayi addu'oi, itadai nata ameen.
Gudu Nawaf yashiga shararawa kamar zai tashi sama, cikin awa ďaya da rabi suka isa tsanyawa, fitsari ya 'kullema yasmeen mara amma takasa gayama Nawaf, saida suka ďauki hanyar katsina sanan Nawaf ya kalli Yasmeen, cikin ďaure fuska ya ce, "waike motse2n mi kikeyine haka??.
Tayi 'kasa da kai tana faďin babu komai, ya ďauke kansa ya maida bisa titi, ahaka suka isa safana, harta fara murna sunzo, saitaga ya ďauki wata hanyar kuma, tun suna bin birji mai 'kyau har suka koma mai ramuka, yasmeen tagadai tafiyar bamai 'karewa ba ce, harta fara zargin kodai sayar da ita Nawaf zaiyi, ga azababben fitsari yana cinta, haka ta daure, suka wuce wani 'karamin 'kauye tazata nanne, amma saitaga sun wuce, saida suka wuce 'kananun 'kauyuka uku, sanan sukaje wani 'kyauye amma babban garine shi saidai shima 'kyauyene sosai.
Tunda suka shigo garin yara ke binsu abaya suna faďin ga mota ga mota.
Yasmeen ta ce, "tofa.
Nawaf yanajinta yay mata banza.
A'kofar wani gida suka tsaya, amma shi shafe yake da suminti, dukda ginin 'kasane, Nawaf yabuđe mota yafito batareda yayima yasmeen maganaba.
Itama saita buďe ta fito, ya danna kai cikin gidan tabi bayansa.
Suna shiga gidan aka taresu da murna, dan har yara sunkai labarin zuwansu, yasmeen ta ce, "ma wata 'yar buduwa dan ALLAH ina bayi yake 'kanwata, yarinyar ta ce, zona rakaki.
Buta ta ďakko ta rakata, cikin hanzari yasmeen tashige, babu daďewa ta fito suka koma inda aka shimfiďa musu tabarma, a 6angaren wata 'yar tsohuwa.
Sai asanan yasmeen ta lura da muta nen gidan suna kama dasu Nawaf musamman ma Abdallah dan shi yake kama da papa sosai.......................✍🏻





Kuyi ha'kuri yau babu yawa, ina busy ne.










©2016


💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘 💞
[1/12, 8:59 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻33 & 34

.....Gidan babbaban gidane, wanda za'a iya kira family house, saidai 6angare2 ne, wannan yasa yasmeen tagaza tattance adadin yawan muta nan gidan, dan danan aka cika musu gaba da nau'in kwanikan fura kala2.
Gaishe2 aka fara da tambayar juna bayan rabuwa, amma sukan haďa da fulatanci, wanda Nawaf shima yana yarawa, lamarin yabama yasmeen mamaki, bata ta6a tunanin yanajin fulatanciba.
Nawaf ya ce, "wai inasu baffa??, 'yar tsohuwa mai ran 'karfe ta ce, "suna gona, wasu kuma suna kasuwa.
Ayya ALLAH yadawo mana dasu lafiya, amin saura suka faďa, bayan wani ďan lokaci kowa yafita yabarsu dansu ďan sha furar kafin a kammala abinci.
Ita dai yasmeen bin kowa take da kallo, dan bata sansuba, tagadai wasu awajen bikinta, wasu kuma bata gane suba.
Nawaf ya juyo yana kallonta, ya ce, "wannan ita ce, hajiya iya kakarmu kenan, kowa ya mutu yabarta, ya'karashe maganar da tsokana.
Hajiya iya tayi masa da'kuwa, Nawafa kaci gidanku, kenan sokake na mutu.
Nawaf da yasmeen suka tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "nikam ba sunan Nawafa ba, shiyyasa saboda ke bana son zuwa garin nan.
Aii dama ba zuwa kakeyiba, sa'idune kawai da umma (momcy)suke zuwa, saisu Abdu, amma kai basai ka haďa shekara biyu bamu gankaba.
Nawaf ya tsaya da dariya ya ce, "bahaka bane hajiya iya, niďin nan dakike gani nafi kowa son garinnan, kawaidai yanayin sana'a tace haka, amma kiyi ha 'kuri tunda yanzu nayi amarya zan runga zuwa ganin uwargida sosai.
Yakamata kam, dan babu abinda yafi zumunci daďi, shiyyasa nakeson sa'idu fiye da kowa acikin 'ya'yan gidanan, tafaďa tana bubbuďe kwanukan da matan gidan suka tara, ko ina furace da tasha damu da nono mai 'kyau, hajiya iya ta ri'ke baki, to su waďanan ina suke nufin zakukai wanan uwar hura haka sakace masu cikin zani.
Nawaf ya ce, "karki damu duk zamu iya shanyewa kinsanni da son fura.
Tami'ke da 'yar sandarta tana faďin to saiku bada himma, kishiya kisha dayawa ďanyar fata bata fashewa.
A'a hajiya iya, sokike cikin matata ya fashe, nazama naki ke kaďai.
Hajiya iya tafita tana faďin ďan nema mizanyi da ďan ta maula.
Bayan fitarta yasmeen ta ce, wai kana nufin wannan itace ta haifi papa?.
Nawaf ya girgiza kai, wanan kishiyar kakarmu ce, duk yawan matan nan dakike gani daga matan 'ya'yanta sai na jikokinta, kakarmu papa kawai ta haifa, ALLAH yay mata rasuwa tuni itada kakanmu.
ALLAH sarki yasmeen tafaďa, ALLAH yagafarta musu sukuma.
A la66ansa ya amsa da ameen.
Yami'ke yana faďin bari naje nayi sallah lokaci yayi.
Yafice yasmeen tana binsa da kallo.
Bayan dawowarsa sukaci abinci, zuwa sanan mazan gidan sun fara dawowa, kowa yagansu saiyayi farin ciki da zuwansu, dan sunsan yau sun warke.
Zuwa dare Nawaf ya dam'kawa kowa tsarabarsa, sai murna da godiya sukeyi, har makwafta suma an kakkai musu.
Nawaf yana 'kofar gida cikin danginsa anata hira da wasa da dariya, dan kokaďan baya 'kyamarsu, yanason danginsa sosai, ya kira musu papa a waya sukasha hira, sai wajen karfe tara suka shigo kowa yanufi ďakin matarsa.
Yasmeen ma harta fara barci a ďakin hajiya iya, Nawaf yashigo da sallama hajiya iya dake gyangyaďi ta buďe ido, Nawafa ina kashiga kabar yarinya ita kaďai ga gajiya ga ba'kunta, baywar ALLAH harma ta fara barci anan.
Nawaf ya ce, "hajiya iya aii anan zata kwana dama, miyasa bataje wajensu kuluwa tayi hiraba?, A'a ni ce, "na hanata dan naga tagaji wannan garin naku mai nisan tsiya.
To shike nan ni bari naje na kwanta, sai da safe.
Kaga dawo ka tada ita, saitafi sakewa acan, anan aii takura zatayi, dan yaran su hanne fitsarin kwance sukeyi, kuma anan suke kwana, dan haka tada ita kuje can, itama zatafi jin daďi aii.
Batare da ya ce, "komai ba, yashiga kiran yasmeen! Yasmeen!!, ahankali ta buďe adanunta, danji take lamarin kamar amafarki, yauce rana tafarko dataji ya kira cikakken sunanta, amma "k shine sunan dayake kiran ta dashi, koyace mara kunya.
Ya ce, "tashi mana, tami'ke tana murza idanu, hajiya iya ta ce, "bita ahankali mana, saida safenku, nasa salmanu yakai muku kayanku tun ďazu.
Nawaf ya ce, "to saida safe, yay gaba yasmeen tabishi abaya tana tangaďi, ahanya tayi karo da bishshiya dalbejiya, Nawaf ya ri'ke hannunta yana faďin waike idan kina barci saiki zama tamkar 'yar kwaya??.
Itadai batace masa komaiba saima 'kara matse hannunsa datayi cikin nata.
Wani 6angare suka shiga agefe da alama shine 6angaren papa, idan kuma sunzo nan suke sauka.
Ďaki ďaya yanufa, wanda aka kunnawa fitilar kwai, 'katuwar katiface aďakin, dan haka suna shiga yasmeen ta kwace hannunta ta kwanta, dan barci takeji sosai.
Nawaf ya girgiza kai, yana faďin yarinya kamar 'yar kwaya?, ya canja kayansa zuwa na barci, "k kitashi ki cire waďannan kayan mana!.
Yasmeen ta gyara kwanciyarta dan ALLAH kabarni ALLAH na gaji barci nakeji, tsaki yayi ya ce, "dallah ca akayi kitashi ki cire waďan nan kayan, yasmeen ta tashi tana murza idanu, ya hawo katifar ya kwanta, yana mita, zaki wani ishi mutane da faďin kin gaji to waye bai gajiba?, nida nakawo mu nan bance nagajiba saike!!.
Banza tayi masa, tasaka hannu ta kashe fitilar kwan dakeci.
Nawaf ya ce, "wane irin iskanci?, ne wanan zaki kashema mutane fitila?, saida ta murguďa baki kamar yana ganinta, ta ce, "to kaya zan cire.
Tsaki yaja yakoma ya kwanta, aikin banza ubanmiye abin kallo ajikinki dazaki wani rainama mutane wayo, ya 'kare maganar da kwafa, kyaaaaaak!!!
Yasmeen ta ce, "oho dai nidai baza kayi daniba agidan mutane, shiru yayi kamar bai jiba.
Tagama shiryawa tai tsaye tana tunanin inda zata kwanta, dan bazata haďa makwanci da 'katoba, ta ce, "kabani bargon na shinfiďa a'kasa na kwanta.
Ya ce, "zoki kwata mana.
Shiru tayi bata tankaba, azatonsa ta kwanta a'kasane, yaďauki wayarsa ya kunna fitila, saiya ganta gefensa tsaye jingine da bango, ya ta6e baki yakashe fitilar ya juya mata baya.
Ta saka hannu da niyyar yaye bargon, caraf ya dam'ke hannunta, ya mirďe, ta kwalla 'kara, ya fincikota ta faďo jikinsa.
Ya ce, "ni wai sa'ankine??.
Tai masa shiru tana hawaye, fitilar wayarsa yasake kunnawa, ya haske mata idanu, ta rintse idanunta kam.
Ya ce, "matsoraciyar banza, nizaki yayema bargo, ta ce, "nifa ba ďauka zanyiba, ya ce, "to mizakiya.
To kasakeni basai na gaya makaba., ya ce, faďi ahaka mana.
ALLAH zan cijeka idan baka sakar mini hannuba,, hhhh yaro man kaza, ki cijeni mana, aii kinsan halina sarai.
Shiru tayi masa, gata ajikinsa ga hannunta amurďe, damma yau bai murďeba sosai, ganin bashida niyyar sakinta saikawai ta maida kanta saman 'kirjinsa ta kwanta, dan barci takeji.
Nawaf ya lumshe idanu tareda sakin sassanyar ajiyar zuciya, yasmeen tana jinsa.
Ahankali ya janyeta daga jikinsa, dan yanda yakejinsa ďinnan zai iya aikata mata aika2 wlhy.
Kwanciyarta yagyara tacigaba da barci abinta.
Ya haska fuskarta yana murmushi, wanda shi kansa baisan na miyeba, dahaka barci yay awon gaba dashi shima.

WASHE GARI
da safe hayaniyar yara ta tada ita, tunda tayi sallar asuba takoma barci, shima Nawaf tundaga sallah bai dawoba, ta tashi ta share wajen, sai asanan taga tsarin wajen, yanada girma babu laifi, akwai ciki da falo sai ďakuna ďai2 guda uku, sai kichin da bayi, ginine dai irinna 'kauye, amma shafe yake da sumunti kamar ko ina agidan.
Tayi wanka ta shirya tsaf cikin les tayi 'kyau.
Tana shirin fita Nawaf yashigo ya bita da kallo yana faďin sai ina??, ta ya tsine fuska, zanje nagaida su hajiya iya ne!, ya ce, "to sarkin zumuďi, aidai 'kya jira na dawo ko??, itadai batace masa komaiba.
Ya shiga ciki batareda yasake tanka mataba, dole ta biyoshi, amma sai tayi zamanta awaje, tana nan zaune yafito dagashi sai tawul, da sauri ta kauda kai, shima saiya ta6e baki yawuce.
Koda yafito baibi takantaba yashiga yashirya tsaf cikin 'kananun kaya, harda jibga rigar sanyi mai'kyau dan garin anaďan sanyi, yafito batareda yayi maganaba ya nufi hanyar fita, itama saita mi'ke ta take masa baya.
6angaren baffa sunusi suka fara zuwa, bayan sun gaishesu ya ce, "nanane 6angaren baffa sunusu, shida iyalinsa, shine yake bima papa.
Sanan sai 6angaren baffa lurwanu, sai 6angaren baffa Ďahiru, sai 6angaren baffa haruna.
Sanan yakaita wajen 'ya'yansu kowa da matarsa, daganan suka koma wajen hajiya iya.
Suka gaisheta, ta ce, "aiida yanzu zanzo na tasoku, sukayi dariya suna faďin aigamu mun tashi, nan yaran suka fara shishshigowa, yasmeen tana tambayar sunayensu.
Nawaf ya ce, "ashe zaki gaji, dan koni bansan yawan adadin yaran gidannan ba wlhy.
Saida suka karya sannan Nawaf ya ce, "zasuje su gaida dangi, daga nan har wasu 'yan 'kyauyika dake kusa zasuje.
Zaikai yasmeen taga dangi.
Hajiya iya ta ce, "tozata iya kuwa, dan kasan mota bata shiga.
Ya ce, "karki damu hajiya, itama aii ba'kyauyarce zata iya.
Yasmeen ta harareshi, shima ya rama.
Cikin gari suka fara zagawa gidajen dangi, duk inda sukayi sai kallonsu akeyi,, garin ya burge yasmeen, ta ce, "kai garinku ya haďu gsky, wlhy kamar karna tafi.
Murmushi Nawaf yayi batareda ya ce, "komaiba.
Bayan sun gama zaga gari, Nawaf ya 'kar6i mashin ďin salmanu ya ce, "yasmeen tahau.
Tsyawa tayi tana kallonsa, ya ce, "k nifa kina 6ata min lokaci, cikin marairaicewa ta ce, "wlhy tsoro nakeji, kaje ka kadani abanza.
Nawaf

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login