Showing 33001 words to 36000 words out of 74786 words

Chapter 12 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

359

asiriba, ko makwancima ni bamu ta6a haďawaba wlhy.
Idanu mas'ud yazaro, kai amma dai kai garane wlhy.
Oho kama faďamin abinda yafi gara mana, kai kanka kasan ba son yarinyar nan nakeba, kai nama ta 'kaice maka zance, kullum saimunyi faďa.
Dariya sosai mas'ud yayi, ya ce, "lallaikam zaku barine, koda yake shima faďan duk acikin soyayyane.
Tsaki Nawaf yayi daganan yay masa banza.

________________________________ a6angaren yasmeen kuwa sai la'asar ta farka, tayi mamaki data ganta akan gado, itadai tasan ba'a nan ta kwantaba, zata iya cewama tundaga randa aka kawota batasake hawa gadon nanba da niyyar kwanciya, saidai kawai ta gyara masa.
Bayan tagama mamkinta ta sakko, wajen madubi taje tana kallon fuskarta, la66anta sunyi fushi sosai, ta ce, "ALLAH yasaka mini mugu kawai, tunda nake arayuwata banta6a ganin mugun mutum irin Nawaf ba, ruwa zafi taje ta ďebo a kichin, awani ďan bokiti, tazo tazauna gaban mudubi, tasaka wani hankacif ďinsa ta gasa bakinta,, dukda zafin datakeji haka tadaure tana hawaye ta gasa, saida taji ruwan ya huce sanan ta ha'kura, tashiga wanka.
Tafito tayi sallar la'asar, ta shirya tsaf cikin doguwar jalla biya ba'ka, mai duwatsu.
Falo tafito taci abincin, da momcy ta aiko musu, dama har yanzu bata fara abincin ranaba, saidai na safe, da daddarema ba girki sukeyiba, dan kowane daren duniya kayan fruit ne abincin Nawaf, sukaďai yakesha sai shayi na 'ka'ida, wanda saiyasha sau goma arana batareda ya isheshiba😜.
Ta kammala cin abincinta tadawo falo, yasmeen bata cika damuwa da kalloba, idan itace sai ayi sati ba'a kalli tv ba, dan haka tai kwanciyarta saman kujera tana game a waya.
Yaseer ya kirata awaya, taďaga cikin fara'a tana faďin ďan 'kanina nayi missing ďinka wlhy.
Ya ce, "nima haka sisto na, ykk?, ya gida?.
Ta ce, "komai lafiya Alhmdllh, ka'ki kazo ko??.
Karki damu zanzo, school ce ke hanani wani motsi wlhy, amma zuwa weekend zaki ganni.
To ALLAH ya kaimu lfy, yasu ummana da abba??, suma duk suna lafiya wlhy, aii yanzu su yaya Nawaf suka tafi, tun ďazu suke anan.
Yasmeen taishiru azuciyarta ta ce, "mugu, wato bayan yagama mini mugunta ashe gidanmu yaje, taďan murmusa koba komai taji ďaďi...........yaseer ya ce, "hello sisto kina jina kuwa??.
Saida tayi ajiyar zuciya sanan ta ce, "ina jinka, ka ce, "tunďazu yake anan??, eh, shida yaya mas'ud sukazo, bakiga alherin daya kawo manaba wlhy, ki 'kara yimana godiya, gsky aunty kin more miji..
Hummm to uban 'yan surutu anji, yaseer yay dariya, kai sistona daga faďar gsky, ina aunty amina??, tana gidanta itama nima bamu haďuba.
Kai aunty gida biyune fa tsakaninku.
To yaseer basai anbar mutum zuwaba?, ya ce, "hakane kuma.
Sun daďe suna hira, ta ce, "ka gaishemin da umma, itama zan kirata mu gaisa insha ALLAH, dan jiya mun gaisa da abba.
To shikenan zataji insha ALLAHU, saina zo.
Okey to saikazo.
Shiru tayi tana tunanin mijin nata, tana mamkinsa, agaban mutane yakan nuna yana sonta, amma idan su kaďaine sai muguntar tsiya.
Anwar yashigo da gudu yana faďin aunty kina ina??, yasmeen ta tsshi zaune, ganinan Anwar, ya mi'ka mata kofi, yayinda Abdallah ma yashigo da gudu, yatsaya yana hakki yana hararar Anwar.
Yasmeen tayi dariya tana tambayarsu miya faru, Anwar ya tuntsure da dariya, yaya ne ya haďa askirim na ďebo miki, shine yabiyoni zai kwace.
Yasmeen ta ce, "kai Abdallah ALLAH yashiryaka wlhy, nixaka yima rowa.
Ya 'karaso yana faďin ALLAH aunty dama nayi niyyar kawo miki, banfa gama haďawaba ya ďebo, kuma dafarko bake yay niyyar kawomawa ba, kansa ya ďebar mawa.
Anwar yay dariya kaidai yaya faďi gsky.
Dagudu Abdallah yabiyoshi suka fara zagaye falon, yasmeen tana tun tsura musu dariya.
Nawaf yashigo da sallama, bashiri suka nutsu, kowa yana hakki, yasmeen ce kawai taketa dariyarta.
Nawaf yatsaya yana kallonsu kawai, yayin da yakejin kamar kar yasmeen ta daina dariyar dan tayi 'kyau da dariyar.
Su Anwar suka ra6a ta bayansa suka fice, sum2🚶🏼🚶🏼kafin akai musu masga.
Bayan fitarsu Nawaf yay tsaki yashige bedroom, babu daďewa yafito sanye da jallabiya, ko kallon yasmeen baiyiba ya fice.
Tabishi da kallo tana ta6e baki.
Koda yadawo sallah wajen papa yawuce dan amsa kiransa, ya rissina ya gaisheshi.
Papa ya amsa yana faďin zauna sosai mana.
Nawaf ya zauna.
Papa ya ce, "dama inaso na sanar makane ka shirya kaida matarka kuje safana, ku gaishe da jama'a damusu godiyar hidima.
Da sauri Nawaf ya ce, "papa safana fa ka ce??.
Eh, safana na ce, yakamata ka kaita tasan tushenka, tasan kaiba ďankowa bane, talakane kamarta, baka fita da komaiba, wannan 'katon gidan datake gani da taimakon ALLAH aka ginashi, shima saida aka đauki shekaru ba'a gamaba, dan har aka haifeka ban gama ginin nan ba, kuma haka mahaifiyarka ta zauna dani, duk da ita tafito daga wata 'kasa, kuma gidan arzi'ki.
Nawaf ya ce, "to shikenan papa zamuje, amma aranar zamu dawo??, kai papa ya girgiza, ya ce, "A'a, kwana uku zakuyi ku zaga dangi ko'ina, kushiga ko'ina da ina.
Nawaf ya ce, to shikenan zamuje nextweek, dan inaso 'karshen watanan na koma Spain!!.
To ALLAH yakaimu lafiya, saikayi 'ko'karin shrya muku tafiyar, ALLAH yay muku albarka, yabaku zuria ta gari.
A la66ansa ya ce, "amin.
Sunďan daďe suna hira, saida papa ya ce, "yatashi ya je wajen matarsa, anbarta ita kaďai.
Akunyace Nawaf yami'ke yafice.
Papa yabishi da kallo yana murmushi.
Saida yaje wajen hajja yay mata saidai safe sanan yatafi 6angarensu.

Afalo ya iske yasmeen tana kallon hausa film, ya ďauki remote ya canja, wai shi bazai kalli wannan shashancinba, yasmeen ta turo baki gaba, a zuciyarta ta ce, "bagara hausa film ba wataran suna faďakarwa, akan 'yan kwallo da rashin aikinyi yay musu yawa...........Nawaf ya katse mata tunani da faďin "k ina shayina☕??.
Banza tayi masa, tayi kamar batajishiba, ya mi'ke, da sauri ta tashi tsaye itama, tanufi kichin da gudu.
Dariya ta su6cewa Nawaf, ya tuntsure da dariya, cikin dariya ya ce, "kai matsoracima baiji daďin kansaba wlhy.
Babu daďewa ta dire masa shayi agaban sa, tana wani zuzzun6ura baki gaba, ta ajiye zata wuce, ya ce, "k dawo nan, ta tsaya cak ita bata tafiba, kuma bata dawoba.
Cikin faďa ya ce, "wai badake nakeba??, saida ta murgiďa baki sanan ta juyyo, tazo ta tsaya akansa, ya watsa mata harara, wlhy yarinya kishiga hankalinki dani, inba hakaba kin rin'ka shan wahala kenan.
Ta yatsine fuska sanan ta ce, "wlhy saidai musha wahala, kabar ganin ďazu ka kumbura mini le6e na 'kyaleka, zan ramane.
Ya tashi zaune daga kwanciyar dayayi, yasa hannu ya fisgota ta faďo jikinsa, runtse idanu tayi kam, tana rawar jiki, ya matseta kam ajikinsa, bata ankaraba taji bakinsa cikin nata, wata mahaukaciyar sumba yake mata, ga le6enta bai gama warkewaba, dan har yanzu yana mata zafi, amma dan muginta irinta Nawaf sai yahaďe bakinta da nasa sai murza yakeyi.
Itako hawaye kaiwai take zubowa, tana tsunguninsa da hannunta ďaya, amma ko'a jikinsa, dan ya'ki sakinta.
Saida yaga taji jiki sannan yasaketa, tana hawaye, tama kasa tashi daga jikinsa.
Ya lumshe idanunsa dasukai jajir, yamaida kansa jikin kujera yana fitarda numfashi.
Ahankali ta tashi daga jikinsa ta shige bedroom, saman gado tafaďa tana kuka, saida tayi mai isarta sanan ta shiga bayi taiyi wanka, tafito tayi shafa'i da wutiri, tana nan zaune yashigo ďakin tai 'kasa da kai kamar bata ganshiba.
Shima bai kalletaba yashiga cire kayan jikinsa, tashi tayi ta haye kujera takwanta.
Yashiga wanka shima, yafito yagama komai na al'adar rayuwarsa, shafa'i da wutiri, karatun alkir'ani, sanan yaje kichin dakansa yasake dafa wani shayin dan wancan ya huce.
Falo yay zamansa saida dare yayi sosai yashigo, sanan yasmeen ta daďe dayin barci akan kujera.
Kallo ďaya yay mata ya ďauke kai, ya hau gado yakwanta.
Na ce, "mu kwana lafiya, nima wajen nawa handsome ďin nataho😘.
________________________________ WASHE GARI.
lokacin dana iso 'yan aiki harsun gama gyarama yasmeen 6angarenta, tagama haďa break a falo na tarar da Nawaf yana break na ce, "tofa yau ba'a ra'ayin dinning ďin??.
Yasmeen ta fito daga ďaki, hannunta ďauke da littatafai, ko kallon inda Nawaf ya ke batayiba, ta zauna saman kujera tana karatun ta, yaďago yana kallonta, wani abu yana ta6a zuciyarsa, amma yanaji har aransa bazaiyi fatan yafitowarsa filiba.
Yasmeen taji ajikinta ana kallonta, ta ďago tana kallon inda Nawaf yake, ta murguďa masa baki😏.
Ya 'kara ďaure fuska, "k dawa kike??, ta ce, "da wanda ya tsargu mana.
Ya ce, "toni na ysargu.
Ta ce, "matsalarkace.
Ya ce, "kema yanzu zata zama taki!".
Aii tana ganin ya mi'ke ta tashi ta fallah da gudu zuwa waje, dama shiyyasa ta zauna kusada 'kofa.
Nawaf yay kwafa zaki dawo ki sameni aii, matsoraciyar banza kawai😜.....................✍🏻





Assalamu alikum
Masoya littafin NAWAFF kwana biyu kunji Shiru hakan tafarune sakamakon rashin lafiya danayi, amma yanzu komai normal, ngd da 'kyaunarku gareni, luv u oll❤❤❤😘


[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻31 & 32

.....koda yasmeen tafita zamanta tayi a waje, tanajin motsin fitowar Nawaf ta samu wani lungu ta 6uya, 6angaren momcy yanufa tasan zaije gaishesune, ďaki takoma ta ďakko hijjab itama, tana shirin shiga yana fitowa, tamatsa masa ya wuce batareda kowa ya kalli ďan uwansaba, yasmeen ta ta6e baki tareda shigewa.
Shima mota yashiga ya bar gidan.
Yasmeen zamanta tayi a 6angaren momcy har azuhur, sanan tadawo nasu 6angaren, har sanan Nawaf bai dawoba, tayi sallah ta sake wanka, falo tadawo ta zauna zuciyarta cike da tunani, yau kwana uku ke nan kullum sai faisal ya kirata, amma bata ďagawa, gsky tana fargabar Nawaf yagani, da sauri ta ďago domin jin sallamar ameena..
Taje ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, Ameena ta ce, "kai yasmeen irin wannan 'kyawu haka, miye sirrin??.
Yasmeen ta ajiye kayan hannunta tana hararar Ameena, 'yar duniya abinma harda zagi, aii kobaki faďaba kowa yaganki yasan kina jin daďi, kodai oga mas'ud yayi ajiyane??.
Dariya Ameena tayi tareda shan lemon da yasmeen ta kawo mata, ta ce, "kin rama kenan??.
Dariya sukayi suduka.
Yasmeen ta ce, " 'yar uwa inatason shigowa wajenki amma ina tsoron na tambaya a hanani, ya amarci??.
Ameena tayi far da idanu ta ce, "amarci muna ci kam, kamar yanda nasan kuma kuna shan naku.
Yasmeen tayi murmushin takaici, ta ce, "k ni babu wani amarcin dana keci saima shan wahala, amma ba wannan bane mafi girman damuwata amina!.
Ameena ta gyara zama, yasmeen miye damuwarki???, humm amina faisal ne damuwata.
Ameena ta 6ata fuska tana hararar yasmeen, "k yasmeen kiji tsoron ALLAH wai da baki so faisal ba sai yanzu dakike agidan mijinki, karfa ki manta mijinki yafi faisal komai wlhy 'kyau aji ilimi wayewa, dan iskanci da shaye2 bashi bane wayewa.
Yasmeen ta kamo hannun Ameena ta matse anata, Ameena ki saurareni nakai 'karahen zancena mana, kema kinsan bazan ta6a son faisal ba arayuwata, baki bari nafaďi abinda ke raina bane.
Abinda yasa kikaji na ce, "miki faisal ne damuwata shine, yau tsawon kwana uku kenan kulum sai faisal ya kirani, gashi yay ta turomin sakwanni, shiyyasa ma kwana biyu na daina chatting kwata2.
Ameena ina tsoron mugun nan ya gane, na tabbata bazai ta6a fahimtata ba.
Ameena ta ce, "tofa, ba ance tun randa faisal yazo gidanku da safennanba washe gari yabar 'kasar??, nimadai haka naji, amma fa number dayake kirana da ita ta 9ja ce.
Ameena taja numfashi, ta buďe baki da nufin yin magana.......sai Nawaf da mas'ud sukai sallama, dole suka katse hirar tasu.
Su Nawaf suka zauna, mas'ud ya ce, "tunda ku kun'ki zuwa mu gashi yau munzo mu kwashe ladan.
Yasmeen da Nawaf sukayi dariya, yasmeen ta ce, "ayi ha'kuri muma zamuzo, Nawaf ya ce, "kinga ishirunki, ranar aii saida naje gidan, shiko tunda aka gama biki bai zoba, saboda santin amarci, ranar har momcy daida ta tambayeshi.
Mas'ud ya zaro ido kai da gsk kakeyi.
Nawaf yay dariya yana faďin eh mana.
Nandai sukaita hirarsu, har la'asar, mas'ud ya ce, "Ameena ta tashi su tafi, dole tabi umarnin mijinta, amma badan tasoba, dan tanaso su 'kare maganar da suka fara da yasmeen.
To itama yasmeen ďin taso hakan amma bayanda zatayi.
Har get ta rakasu sanan ta dawo dan harda Nawaf suka fita, tunda lokacin sallah yayi.

_________________________________ haka rayuwa taci gaba da tafiya, yau da gobe sai ALLAH, Nawaf yanata shirya musu tafiya katsina, amma dan rainin hankali bai sanar da yasmeen ba, tagadai yanata sayo abubuwa yana ajiyewa, itako ko kallo bai ishetaba bare ta tambaya.
Dan yanzu ba sosai suke shiga harkar juna ba.
Yau su duka suna falo amma babu wanda yadamu da abinda ďan uwansa yakeyi, yasmeen tana zaune akasa ta shinmiďa farin hankici ta ďora 'kafarta akai tana yanke farce.
Nawaf kuma yana kwance saman doguwar kujera yana kallon kwallo.
Wayar yasmeen tashiga 6urari, takai dubanta ga wayar faisal ne, cikin rashin gsky ta kalli Nawaf, idanunsa suna kan tv amma hankalinsa yana kanta, ta gefen ido yake kallonta.
Ta kauda ido daga kallonsa alokacin wayar ta tsinke, cigaba tayi da yanke 'kumbarta.
Aka 'kara kiran wayar nanma harta tsinke bata motsaba, shikuma kuma yaci gaba da kira, saida yakira sau 6 ana bakwaine yasmeen takai hannu zata ďauka, da sauri Nawaf ya kawo hannu shima da nufin ďauka, saiya dafe hannun yasmeen.
Suka ďago lokaci ďaya suna kallon juna, har wayar ta tsinke basu saniba, kallo sukema juna mai cike da 'kauna, Nawaf yafara janye idanunsa saboda sake kiran wayar da akayi.
Yasmeen ta sake danne wayar sosai da hannunta, cikin zafin nama Nawaf ya cire hannunta, ya tsaida kallonsa ga mai kiran wayar FAISAL!!!!, ya maimaita sunan ahankali, ďaukar wayar yayi ya koma saman kujera.
Yayinda yasmeen tayi mutuwar zaune, kiran faisal yayi, jikin faisal yana 6ari ya ďaga azatonsa yasmeen ce, NAWAF yay shiru batareda yayi maganaba.
Faisal ya ce, "my luv plz kizo gareni, idan ba hakaba zan iya mutuwa, ina nan kwance tsawon satu uku babu lafiya, ki taimaka kizo na ganki my luv!!!.... Nawaf ya rintse idanunsa, danjin 'katon banza yana kiran matarsa my luv!!, wata razananniyar tsawa ya dakawa faisal.
Kaiiiiiiiiiii!!!, wawa jaki jahili, wlhy ka sake kiran matata my luv saina kasheka dan ubanka, kai wane irin jakine zaka rin'ka kiran matar aure jahilin banza!!!!, wlhy daga yau yazama na 'karshe dazaka sake kiranta, inko ba hakaba zakayi dana sani kaida jahilan iyayen ka, yana gama faďa ya yanke wayar.
Kwala wayar yayi da bango aiko ta ta rarratse, yatashi yanufi wayar kamar wani mayun wacin zaki, yasmeen ta rintse idanunta azotonta wajenta yanufo saitaga ya wuceta.
Yasa 'kafa ya take waya ya 'kara takata, sannan ya buďe ya cire sim cart ďin ya karya shi, itadai yasmeen sai jikinta yake 6ari.
Yana gamawa ya dawo kanta ta rungume jikinta tana kuka, gashin kanta ya dam'ke ahannunsa ya fisga da 'karfi, tari'ke hannunsa tana kuka, idanunsa sunyi jajur saboda 6acin rai.
Cikin muryarsa tamakar zaiyi kuka ya ce, "ya ce, "kin cuceni kina gidana kina soyayya da wani, ke wacce iri jahila ce???.
Cikin 6acin rai yasmeen ta ce, "ka daina ce mini jahila, danni ban aikata abinda kake zargina dashiba???, dan haka ka sakar mini gashi.
Yakuma murďe gashin tareda wanka mata mari, cikin 'karaji ya ce, "idan ba haka bane uban mi yasa yake kiranki, ubanmiye a tsakaninki dashi, wlhy zan iya kasheki shima na kasheki, sannan na kashe kaina.
Yasmeen ta fashe da kuka, tana faďin ka kasheni ALLAH yasani gsky na faďa maka.
Ahankali ya saki gashinta yana cije baki, yakoma 'kasa ya zauna da6as kamar ďan bori, kai ya dafe yana jujjuyawa, yashiga hargitsa sumar kansa tamkar mai ciwon hauka.
Yasmeen ta tsura masa idanu tana hawaye, ga tsoro fal cikinta dan ganin yanda Nawaf keta jujjuya kai kamar ďan kwaya.
Sunkai awa biyu ahaka kowa yana jinyar kansa, daga baya Nawaf ya shige bedroom, kaitsaye bathroom ya wuce, shawa ya sakarma kansa, batareda yacire kayan jikinsaba, yakai minti30 ahaka, saidaga baya yay wanka ya fito, shiryawa yay cikin 'kananun kaya, ya fito.
Har yanzu yasmeen tana gurin daya barta tana kuka, ko kallon inda take baiyiba ya fice.
Ahankali ta tashi taje tayi wanka itama, tayi sallah ta kwanta, wani wahalallen zazza6i ya rufeta, gado ta haye ta kwanta tana rawar sanyi.
Har dare Nawaf bai dawoba zuwa sanan yasmeen ta gama gala baita, duk abunnan da yake faruwa Nawaf yana 6an garen momcy yana hirarsa, dan yarage 6acin rai.
Momcy ta ce, "wai ina ďiyata??? modebbo, Nawaf ya ce, "tanaca karatu takeyi shiyyasa kikaga bata zoba.
Okey aii nazata ko batada lafiya, A'a lafiyarta 'kalau.
Sai 'karfe tara yakoma 6angarensu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login