Showing 45001 words to 48000 words out of 74786 words

Chapter 16 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

362

akwai ranar ramuwa tana zuwa.
Momcy tafito daga ďaki tana faďin miya faru kuma??, Anwar yagaya mata abinda Abdallah yafaďa, ta ce, "to ya isa haka, amma Auta yanzu nan sabofa wasannan ka'ki zuwa islamiyya ko???..
ALLAH A'a momcy, yau 'kari za'a mana kuma na iya wajen shiyyasa, momcy tazauna tana faďin to shikenan aii.
Babu daďewa aka fara wasa, falon yayi tsit, kowa idonsa yana kan tv, yasmeen wani daďi takeji a zuciyarta dan ganin Nawaf, koba komai tarage raďaďin dake damun zuciyarta na son wanda bai damu da itaba.
Wasa yayi wasa, anata gwagwarmaya da juna dan kowa gwanine, har akaje hutun rabin lokaci babu wanda yaci.
Bayan andawo babu daďewa ASINAL ta zirama su Nawaf kwallo, wannan yasa suka dage suma da bada 'kaimi, to suma su Nawaf sun zurama Asinal kwallo ďaya a raga, ana gab da tashi Nawaf ya 'kara zirama Asinal kwallo araga, cikin jin haushin kwallon dasukacisu wani ďan wasan asinal ya taďe 'kafar Nawaf yafaďi.
Bisa tsautsayi wani yataka kafarsa da wannan mugun takalmin na 'yan kwallo.
Wata irin 'kara Nawaf yasaki, wadda tai daidai da wadda yasmeen tasaki afalon.
Da sauri momcy tari'ke yasmeen, su Anwar ma kuka sukeyi dan duk wanda yagani yasan Nawaf yaji takawarnan ajikinsa.
Masu taimakon gaggawa suka rufu akansa, daga bayama ďaukesa akayi daga cikin filin gaba ďaya.
Awannan lokacin hankalin duk wani masoyinsa atashe yake, musamman ma mutanen 9ja da saudia, harda sauran 'kasashen duniya, dan duk wanda yake abinda duniya zata sansa dolene yasamu ďunbin masoya aduniya dakuma ma'kiya.
Nima kaina saida nayi masa kuka, dan yana cikin jin jiki.
Arikice papa yashigo gidan dan shima yakalli wasan a office.
Wasu takardu yaďiba yafita yana mai bama iyalin nasa ha'kuri, airport yanufa wajen wani abokinsa, domin nema musu biza shida iyalinsa.
To dayake babban mutumne kuma mai alfarma, sai aka samu babu 6ata lokaci, zuwa gobe jirginsu zai ďaga.
Yadawo gida ya sanar dasu halin da'ake ciki, dan haka momcy da yasmeen suka fara shiri, sune zasu fara yin gaba, sukuma su Abdallah zasu taho abaya suma.
Ranar haka gidan aka wuni sukuku kamar anyi mutuwa.

A6angaren Nawaf kuwa karaya yasamu a'kafa, yanacan kwance rijif cikin ciwo, amma zuwa yanzu an gyara karayar, harma yasamu barci.
Washe gari suka lula zuwa Spain domin ganin halin da Nawaf yake ciki.
Momcy da papa da yasmeen kenan.
Abdallah da Anwar da mas'ud zasuzo daga baya sukuma.
Bayan sun sauka a masauki sun huta, dukda bawani hutawama sukayi sosaiba saboda hankalinsu yana wajensa.
Wani abokinsa ne yazo yay musu jagora zuwa asibitin, yasmeen sai zare ido akeyi ana kalle2 tun ajirgi, sun isa haďaďďen asibitin na alfarma kuma 'kayatacce, wanda 'yan kwallone kawai sukeda dangantaka dashi.
Bayan kamar minti shabiyar aka basu izinin shiga wajen Nawaf.
Tunda akace sushiga jikin yasmeen yay sanyi, papa ne yafara shiga sannan momcy, Nawaf dake kwance yafara murmushin 'karfin hali dan ganin iyayensa, yasmeen ma tashigo jiki asanyaye, saidai ta la6e abayan momcy.
Ya yun'kura zai tashi amma saiya kasa, ya ďan runtse idanu tareda cije le6e danjin zafi, da sauri papa yamaida shi kwance yana faďin A'a modebbo yi kwanciyarka kaji.
Nawaf yakuma murmusawa yana faďin momcy sannunku dazuwa, momcy tayi murmushi itama ta ce, "yauwa abbuna kaine da sannu yajikin??, ya ce, "Alhmdllh momcy, ina sauran 'kanni na suke??,
Momcy ta ce, "suna gida amma zasuzo nan gaba suma insha ALLAHU, tajuya dan bataji motsin yasmeen ba, saita ganta abayanta ta raku6e, momcy takamo hannunta tana faďin ďiyata 6oyewa kikayi??, da sauri Nawaf yaďago idanu suka haďa ido da yasmeen, tai saurin yin 'kasa da kai.
Taďan rissaina tana gaisheshi da tambayar jikinsa??, ya ce, "da sau'ki, jiyake ciwon nasa ya warke tunda yaga TAURARUWARSA, ya lumshe manyan idanunsa wani sanyi yana kwarar azuciyarsa, shikam saiyace gara da yaji ciwonnan, koba komai tasanadin ciwon yaga yasmeen.
Momcy da papa suka zauna saman kujeru biyu dake ďakin, papa ya ce, "fatima zauna kema, yanuna ma yasmeen gefen gadaon da Nawaf yake kwance.
Cikin jin kunya ta zauna kaďan kamar tana kusada wuta.
Hira suka shiga yi da tambayar yanda akayi abin yafaru, dukda duk sun gani, amma yasmeen bata cewa komai, sai wasa datakeyi da yatsun hannunta.
Sun daďe suna hira daga baya papa da momcy suka mi'ke sukace yasmeen tazauna anan suna zuwa yanzu zasu dawo.
Bayan fitarsu ďankin yay tsit babu wanda yake motsi acikinsu, sai Nawaf daya tsirama yasmeen idanu kamar zai cinyeta ďanya, ahankali yasmeen ta yun'kura zata tashi, da sauri Nawaf ya dam'ke hannunta, ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo, kallon ido cikin ido sukema juna, yasmeen tafara janye nata idanu.
Ahankali Nawaf yafirta 'yammata babu maganane??, yasmeen ta ce, "bana gaishekaba.
Ya ďan murmusa to ina zakije dakike 'ko'karin tashi??, taďan motsa hannunta daya ri'ke, murya 'kasa2 ta ce, "zan koma kan kujerane.
Hummm to idan su papa suka dawofa?, shiru tayi bata amsaba, ya matsa hannunta yana murzawa ahankali, gaba ďaya tsigar jikinta tashi takeyi, tana mamakin wannan wane irin kuma sabon salone Nawaf yazo dashi, cikin rawar murya ta ce, "plz kasakar min hannu karsu mom su dawo su gammu ahaka.
To miye idansun gammu, kinsan babu abinda zasuce aii,, eh, amma da kunya dai,, babu wani kunya malama yafaďa Yana yun'kurawa zai tashi saikuma yay sauri dafe gado yana faďin wash ALLAHNA!!.
da sauri yasmeen ta ce, "yayadai??", ya yatsine fuska yana faďin wlhy mantawa nakeyi inada ciwo, ga 'kafar zafi idan na motsata.
Yasmeen ta ce, "ayya sannu, cikin muryar tausayi take maganar.
Kai ya girgiza mata alamar yauwa, ya ce, "zansha ruwa.
Tajuyo tana kallonsa, ta ce, "ruwa kuma??, ya ce, "eh",.
ruwan dake gefen gadon ta ďakko ta buďe murfin tami'ka masa, ya harareta to dawane hannun kikeso nasha kenan??, ta turo baki gaba ta ce, "toda wayake baka?, kuma aii hannunka lafiya lau yake ko?.
Ya ce, "Ahmad ne yake bani mana, shima ďan kwallone abokinsane ďan kasar saudiyyane, haifaffen amerika, ta ce, "to kakirashi mana yacigaba da aikinsa.
Nawaf ya haďe fuska yana kallonta, ya ce, "mikike nufi?, "k bazaki iya yimini ba??.
Tayi shiru, ya ce, "okey bari momcy tadawo ita saitayi mini aii, kinsan babu yanda za'ayi uwa tabar ďanta ayashe.
Yasmeen tai kwalkwal da idanu kamar zatayi kuka, ta ce, "ainidai ban faďaba ko??, ya ta6e baki yana faďin ai basai kin faďaba malama, yanayinki ya nuna.
Bayanda zatayi dole ta mi'ke taunifi saitin kansa, tami'ka masa ruwan, ya ce, "kinsandai babu yanda za'ayi nasha ruwa akwance ko? Saikin taimaka mini na tashi, koki ďago kaina, yasmeen ta ce, "azuciyarta kaikam kacika matsala wlhy.
Dole ta tallafo kansa, tasaka masa ruwan yasha kaďan yajanye baki, ta ce, "dama shan ruwan gulmane.
Ya ce, "nine magulmacin kenan??, yafaďa yana hararta.
Ta ce, "nidai aiibance kaiba.
Haba yarinya duk wanda yay zagi akasuwa aii yasan dawanda yake barganina akwance ina dai2 dake wlhy .
Kafin tayi magana su momcy suka dawo.
Nawaf ya ce, "papa ina kukaje??.
Munje wajen manyankune kozasu bamu kai mu koma Najeria tare, to papa misukace maku??, hummm basu aminceba, wai baikamata su ďora mana nauyiba, dansuke da alhakin kulawa dakai, kuma anna zakafi saurin warkewa tunda sunada isasun kayan aiki, ingantattu kuma.
To papa kubarsu suyi aikinsu dama nasan dawuya su amince gsky.
Papa ya ce, "babu damuwa ai muna nan tareda kai insha ALLAHU, dama maman kace tadage akan mutafi dakai.
Nawaf yamaida kallonsa ga momcy, ya ce, "sorry my momcy karki damu insha ALLAHU anan ma suna bani kulawa sosai, kuma zan koma daidai insha ALLAH.
to shikenan modebbo ALLAH ya amince mana.
Amin suka amsa harda yasmeen.
Papa ya ce, "to bari mu koma masuki dan suna nuna mana lokacin ziyarku ya 'kare saikuma gobe, ALLAH ya'kara lafiya.
Amin suka amsa gaba ďaya, kafin su momcy su mi'ke tuni yasmeen tafice abinta.
Nawaf ya bita da kallo yana cije le6e, azuciyarsa ya ce, "yarinya dole ki soni!!!.
Tunda suka tafi saiyaji ďakin babu daďi, baigaji da kallon 'kya'ky'kyawar fuskar yasmeen ba, amma babu yanda zaiyi.
Likita yashigo ya dubashi, saima yaymasa allurar barci danya samu hutawa.

Suma su yasmeen masauki suka koma, yasmeen ďakinta ita kaďai, papa da momcy kuma ďaya suma.
Tagama komai na al'adar rayuwarta ta kwanta, amma sai tunanin Nawaf yadawo mata, ta tuna yanda yau yake mata magana cikin taushin murya, babu faďa bare nuna jin haushi, ta kalli hannunta daya ri'ke, hannun ta sumbata tana murmushi, talumshe idanu tareda furta i luv u my Nawaf...., tai saurin rufe bakinta🙊tana girgiza kai.
Na ce, "yasmeen ina saura kuma, sirrin 6oye yafito fili.
Haka tayita juye juye dan takasa barci, daga 'karshema saita mi'ke tashiga bayi tayo alwala, tazo tayita nafil fili, tana ro'kon ALLAH yabama mijinta lafiya da dukkan muslmi al'umar ANNABI......................✍🏻










Asalamu alaikum
'Yan uwa kuyita ha'kuri danifa,karku ďauka ina muku jan raine, A'a kunsan ance lafiya uwar jiki babu mai fushi dake, ina bu'kar addu'arku...
Luv u oll😘😘😍😍










© 2016







💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞luv u oll my fan's😘💞
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻39 & 40
....da 'kyar ta tashi tai sallah da asuba, ta kuma komawa barci, sai 'karfe goma ta tashi na safe, shima saida momcy ta tada ita, ta tashi tayi wanka tayi shirinta cikin doguwa riga ba'ka, ta naďe kanta da farin gyale, tayi 'kyau sosai, ko abincin da'aka kawo mata bata tsaya ciba tafito dan su momcy suna jiranta.
Ta tsugunna har 'kasa ta gaishesu, cikin fara'a suka amsa, har papa na tsokanarta da faďin, gara muje da wuri kafin mijinki yafa kiran wayoyinmu, yasmeen tayi ďan murmushi cikin jin kunya.
Momcy takama hannunta ta mi'kar da ita.
Ahmad ne yazo ya ďaukesu, momcy da papa suna baya yasmeen kuma agaba kusada Ahmad.
Asibitin cike yake da 'yan kwallo, Ahmad ya ce, "sunzo duba marasa lafiyane, su papa suka nemi guri suka zauna, Ahmad ya ce, "yasmeen mushiga ke saiki gaisa da abokanmu, suma suga matar modebbo ko??, momcy ta ce, "eh yakamata hakan, tashi kuje yasmeen.
Yasmeen tami'ke tana faďin to momy, Ahmad da yasmeen suka nufi ďakin da Nawaf yake kwance, cike yake da abokansu, wasu azaune wasu atsaye, yasmeen tayi tsaye takasa shiga saboda kunya, Ahmad ya ce, "shigo mana.
Yasmeen tashigo kanta a'kasa, sukam sai kallonta sukeyi, yau dai Nawaf azaune yake, yajingina da filo a bayansa, kuma kumburin 'kafar da sau'ki, ya mi'kama yasmeen hannu alamar wai tazo, ta no'ke kafaďa, alamar A'a.
Yay murmushi yana faďin to zoki zauna nan, dan kinga nan duk abokainane, karsu ďauka 'kanwatace ba matataba.
Yasmeen ta'karasa ta zauna kusada 'kafafunsa, yakamo hannunta ya rumtse anasa, sannan ya maida kansa ga abokan nasa dasuketa kallon yasmeen, ya ce, "friend ga matana, sunanta fateema xarah.
Cikin harshen turanci yake maganar, sukace wow!! Beautiful Sannu dazuwa.
Itama cikin harshen turancin ta gaidasu, suka shiga mi'ka mata hannu wai su gaisa, Nawaf ya girgiza kai tareda sake ru'ko đanyan hannun nata, ya ce, "koda wasa karma ki fara, amma da hausa yafaďa.
Wani bature acikinsu ya ce, modebbo miyasa zaka hanata, aii gaisuwa zamuyi ko??, ya girgiza kai yana faďin no ita bata gaisuwa da maza, saidai zaku iya gaisawa da baki.
Sai koďata sukeyi, wani harda faďin wai zaizo 9ja abashi mata.
Na ce, "aiko yazo yaza6a a group ďina duk wadda tayi masa nabasa, kai ni harma na za6ar masa, ku kawo kunnanku nagaya muku,, nabashi kai🙊............baridai nayi shiru, kar wasu suce ban za6esuba😜.
Bayan sun gama gaisawa suka fice, har yanzu Nawaf yana ri'ke da hannun yasmeen yana murzawa ahankali, ta ce, "plz ka sakeni su momcy suna zuwafa, yaja numfashi, to sarkin tsoro, kedai ba'a ta6a jikinki ko?, kodayake ba'kya bu'katar hakanne?, tazare hannunta ďaya daga nasa tana ta6e baki.
Ahankali ya ce, "kina nandai baki canjaba ko?, ta ce, "kaima ai baka canjaba,.
Ya ce, "ko??, taďan murguďa baki, tana faďin kaima kasani aii.
Ya ce, "nasan mi??
Ta gyara zamanta tana faďin kasan baka canjaba ďinba.
Fatar hannunta yakama yamirďe.
Tari'ke hannunsa kam, wayyo ALLAH da zafi fa??.
Yay 'yar dariya aii dama dankiji zafin nayi, yafaďa ahankali.
Ta ce, " mutum yana hannun ALLAH amma bai daina muguntaba, wawura yakaimata tai saurin kaucewa ta ce, "aikuma kayi na 'karshe malam.
Momcy da papa suka shigo, yasmeen ta fisge hannunta tana gyara zama, su momcy suka zauna suna mai yaba yanda jikin Nawaf yay 'kyau.
Papa ya ce, "masha ALLAHU lallai jiki yayi 'kyau modebbo, yau harda zama.
Nawaf ya ce, wlhy kuwa papa harma ji nake zan iya taka 'kafar, papa yay dariya, A'a modebbo wannan da sauran lokaci aii.
Alhmdllh momcy tafaďa, aii haka muke fata muma muga ka taka, dama su Anwar sun damemu dakira, wai ykk??,
Ayya 'yan 'kannina nayi missing nasu nima, su kwantar da hankalinsu, ina samun sau'ki, bari Ahmad yazo ya kwaso mini wayoyina, nasan mutane sunata nemana.
Papa ya ce, "yakamata ka kunna kuwa, kodan gaisawa da 'yan uwa da abokan arxi'ki, dukda muma sunata kiranmu, kaga kuma bakoda yaushe muke tare da kaiba, indan kuwa ka kunna kowa zai dunga samunka, aduk lokacin daya kira.
Nawaf ya ce, "to papa bari muga yazo saiya ďakkomin.
Nan dai sukaita 'yar hirarsu, suna yaba 'ko'karin Ahmad. Nawaf ya shagwa6e fuska wai yunwa yakeji, momcy tayi dariya itada papa, kai modebbo shagwa6a kuma??, kafa girma abbunmu.
Nawaf yay ďan murmushi yana faďin papa aini idan ina gabanku jina nake yaro 'karami wlhy.
Nanma dariya sukayi, momcy ta ce, "to matarka tabaka abincin ko?, yasmeen tai saurin kallon Nawaf saiya ďaga mata gira, ita kuma ta murguďa masa baki, ya nuna kansa alamar wai shi.
Su momcy suna kallonsu, yasmeen ta haďa abinci ta matso kusada shi tana wani zuzzun6ura baki.
Ta ďiba a cokali ta mi'ka masa, saida ya harareta sannan ya kar6a, yaďan kalli gefen dasu momcy suke yaga hankalinsu baya kansu, suma hirarsu sukeyi, yay 'kasa da murya yanda bazasujiba ya ce, "ki ajiye rashin kunuarki yarinya, dan wannan karan inada hanyoyin maganinki dayawa.
Yasmeen ta ta6e baki ta ce, "aii nasaba jin wanan, hannunta yakamo ya sumbata, saida taďan girgiza dan sumbar tashigeta, Nawaf yay saurin ri'ke filet ďin dake hannunta ya ce, " 'yammata harda wannan??.
Yasmeen tai 'kasa da idanu dan yauce rana tafarko dataji tana jin kunyar Nawaf,, cikin shagwa6a ya ce, " momcy kinga ta daina bani abincin ko??.
Yasmeen tazaro ido😳itama cikin tata shagwa6ar ta ce, "mom ALLAH ina bashi shine baya ci, dama babu wata yunwa dayakeji, su momcy dariyama suka basu, dan haka suduka sukayi murmushi, papa ya ce, "to yanzu mu yazamu gane mai gsky??.
Nawaf ya harareta ALLAH papa nine mai gsky, yasmeen ta ce, "bawani nice mai gsky, Nawaf ya ce, "to nidai yunwa nakeji dan haka kibani abinci, filet ďin hannunsa ta kar6a tana hararar sa, yasaki murmushin mugunta.
Haka Nawaf yacigaba da jinyar jikinsa, Alhmdllh kuma jikin yana 'kyau, saidai tundaga ranar yasmeen take baya2 dashi, dan takula yana neman yarin'ka bata kunya agaban su papa.
Amma soyayyarsa kullum 'kara ruruwa take azuciyarta, to shima dai hakane jiyake kamar ya haďiye matar tasa, amma jin kai yahashi faďa mata yana sonta, dan haka kullum take ganin kamar tana dakon son wanda baya sontane.
Shima Nawaf yanama soyayyar dayakema yasmeen kallon son maso wani, danshi atunaninsa har yanzu yasmeen tana son tsohon mijintane, baisan bata ta6a son faisalba ko a bayaba, bare yanzu.

A yaune su mas'ud suka iso shida Anwar da Abdallah, Nawaf yayi matu'kar farin cikin zuwansu, haka suma sunyi farincikin ganin yafara samun lafiya, dan zamu iya cewa saura kaďan, yausu anan suka wuni yasmeen ma no'kewa tayi ta'ki zuwa wai kanta yana ciwo.
Suma a hotel ďin dasu yasmeen suke anan aka musu masuki, da daddare suka haďu akasha hirar 9ja, saidai papa ya ce, "kowa yaje yakwanta sanan.
Nawaf yakira Anwar ya ce, "yakaima yasmeen wayar, tana 'ko'karin kwanciya taji an buga 'kofar, saida ta le'ka taga Anwarne sanan ta buďe, Anwar lafiya dai ko??, ya mi'ka mata wayar yana faďin yayane ya ce, "nakawo miki wayar, yana bata yajuya yana faďin mu kwana lafiya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login