Showing 57001 words to 60000 words out of 74786 words

Chapter 20 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

370

kunyar momy datakeji.
Momcy ta ce, "sannu kinji ďiyata, yanzu zaki iya tashi??, yasmeen tai saurin kaďa kai Alamar eh.
Okey to inazuwa, momcy tami'ke tara6a ta gefen Nawaf tashiga bayi.
Da sauri Nawaf ya 'karasa wajen wardrobe ďinsa yabuďe wani akwati riga maiďan kauri yaďakko yanufo gadon, hawowa yayi saman gadon ya ďagoda yasmeen zaune, taisaurin ri'keshi tana faďin wayyo zafi, ya rungumota zuwa jikinsa ya ce, "sorry my dear bari nasaka miki riga kinga momcy tana nanko.
Yasaka mata kayan cikin hanzari, tana rungume ajikinsa momcy tafito tana faďin yauwa yasmeen daure kitashi kinji.... yasmeen tayin'kura zata tashi daga jikinsa, tai saurin cije le6e tana fitarda huci da'kyar.
Momcy tari'keta da sauri tana faďin sannu kinji, Nawaf ya ce, "momcy konazo na ďauketane??, harararsa momcy tayi suka shige bathroom ďin.
Nawaf yasaki wani murmushi tareda faďawa saman gadon zuciyarsa fal farinciki da nishaďi,, afili yafurta yaudai an wuce wajan, yafaďa yana shafa gemunsa na gayu.
Momcy tafito fuska aďaure ta ce, "kaje ka taimaka mata tayi wankan, Nawaf yashi zaune da sauri, kansa na 'kasa ya ce, "to mom batayarda kin taimaka mataba ne??, momcy ta harareshi tana faďin ai ita tanada kunya bakamar kaiba, tana faďa tafice daga bedroom ďin.
Nawaf yami'ke zuwa bathroom ďin, yasmeen dake tsaye tana cire kaya, tayi saurin 'kudundune jikinta waje ďaya, yay ďan murmushi yana ta6e baki, ya'karasa wajenta yana faďin oh, xarah na, ai ta6oye ye ta'kare kuma, zokiga nayi miki maganin kukan nan.
Cak yaďauketa yasaka acikin rawan da momcy ta haďa, yasmeen ta ri'keshi tana kukan shagwa6a, yashiga shafa kanta yana lallashi cikin hikima da lalla6a yagasa mata jikinta, itakuma tana zuba masa shagwa6a, ya ce, "kin iya wankan tsarki ko??.
Cikin gatse ta ce, "ban iyaba,, shikam bai fahimci gatse take masaba, dan haka yashiga koya mata, yanaďota a tawul yakawo ďaki.

KIRA......hum akwai wasu mutane dasuke faďar adaren farko ba'a shan wahala,, ban 'karyatasuba bankuma yarda dasuba,, saidai inaso natuna musu cewa dukkan macen data ri'ke martabarta zuwa gidan miji tofa dolene tafuskanci wannan ranar, kuma tabbas wannan wahalar dasuke 'karyatawa saitashata.
Nibanga laifin marubutaba dasuke tsoratar damu akan daren farko, hakan abune mai'kyau, kuma waďanda basuda aure zasuso tattalin nasu budurcin harzuwa wannan rana, domin kwaďayi samun tagomashin albarka da darajar wannan rana, amma ina kira agareku kudaina ďaukar dole sai anmallaka muku wata 'kyauta a washegarin wannan ranar, suma kuma mazajenmu suzama masu daraja dukkan macen dasuka samu acikakkiyar mace.
Amma akwai dalilan dasuke sawa mace tarasa budurcinta koda bata hanyar zinaba.
☆1 ďaukar abu mainauyi yakansamu rasa budurcinmu, amma bazai hana mace taji zafiba koda kaďanne awannan rana, domin itace rana tafarko data fara sanin ďa namiji.
🙈.

☆2 hanya tabiyu itace yawan tsallaka abu, ko hawa bishiya, gudu, ko yawan tsalle2, dakuma horo da akebama yara amakaranta, kamarsu tsallen kwaďo, gwale2 da makaman tansu.
tokam waďan nan hanyoyin sukansa mace ta rasa yanar budurcinta.

☆3 saikuma hanya ta uku,, wa'iyazubillah, ita ce hanyar maďugo, tabas mata sukan rasa budurcinsu ta wannan hanyar, miji bazai ganki da darajaba, gakuma ďunbin zunubi awajen ubangiji,, wasuma basa sha'awar yin aure saboda sheďanci da bushewar zuciya sun kanainayesu.
Ya ALLAH ka tserar damu,, kakuma ganardamu, katsaremana kakanninmu da iyayenmu da yayyanemu da 'kawayenmu da 'kannenmu, da 'yayanmu daga faďawa halaka,, ALLAH yashirya masuyi, damasu sha'awar aikatawa ya ALLAH ka tausasa zukatansu.
Amma mata yakamata mucigaba da gane muhimmancin budurci da tasirinsa acikin rayuwar aurenmu, ALLAH yabama 'yan baya ikon kai nasu budurcin suma inda yadace, ameen🙏🏻👍🏻.

Nawaf ya canja kayansa zuwa jallabiya, sannan yafito domin ďakkoma yasmeen wata rigar danyin sallar magriba.
Afalo yay arba da momcy, tadawo hannunta ďauke da shayi da magunguna, tawuce batareda ta kalli inda Nawaf yakeba, shima baice komaiba yawuce ďakin yasmeen, saidai jikinsa asanyaye, bayaso yaga momcy ko papa suna fushi dashi, ya'karasa ďakin yaďako ma yasmeen wata doguwar rigar, sanda yadawo momcy tana bama yasmeen shayi ALLAH yasoshima da rigar wanka ajikinta.
Ya ajiye kayan saman gadon yana kallon yasmeen 'kasa2, ahankali ta ce, "mom na'koshi, lalla6ata momcy tayi taďan 'kara sannan taba magani tasha ta kwanta.
Momcy tami'ke tafice tana harar Nawaf dayake zaune bakin gado ya rabga uban tagumi.
Bayan fitarta yatashi yakoma kusada yasmeen, ya zame 'karamin tawul ďin data nannaďe kanta dashi dan sumarta ta tsane,, ya wargaza gashin akan filo yana faďin kibarsa haka yasha iska.
Ya tsuggunno ya sumbaci kumatunta sannan ya ce, "naje masallaci saina dawo.
Tana jinsa duk abinda yakeyi amma ko motsi batayiba, bayan fitarsa tayi murmushi tareda zirarar da hawaye,, tabbas batayi ba'kincin abinda Nawaf yaymataba saidai tasha wala, dan Nawaf damugunta yazo mata kokuma gaggawa, amma hakan bazai sa taji haushinsaba kota tsanesa, saima take ganin yanzune zai sota da 'kyaunarta harma da ganin girmanta, tatuna irin sambatu da addu'oin daya ringa zubo mata, yafaďa mata ita kaďaice abin sonsa, kuma yadaďe yana 'kaunarta, shin da gskne kokuwa dan baya cikin hankalinsane??.
To komadai miye lokaci zai nuna, kuma tana sauraren zuwan lokacin, amma tabbas itakam takamu da son mijinta mai tsanani, musamman ma yau daya sake kusanta kansa da ita, haka tayita zancen zuci har barci ya kwasheta.
Nawaf daya dawo daga sallah saiya wuce wajan momcy danya bata ha'kuri, Aďakinta yasameta tana lazumi, yazauna kusada ita yana wani sissinkuyar da kai.
Momcy ta shafa addu'ar tana faďin kai kuma lafiya??, Nawaf ya'kara 'kasa da kai yana faďin sorry momcy, dan ALLAH kiyi ha'kuri da duk laifin dakike ganin nayi miki, na ďauki laifina kuma insha ALLAHU zan gyara, bakuma zan sakeba, insha ALLAHU yanzu zamu zauna lafiya nida yasmeen harma mu sakaku farin ciki, dan ALLAH karkuyi fushi dani plz.
Momcy taja ajiyar zuciya, amma kasandai abbuna baka 'kyautaba ko??, kasan wannan ba halin kwarai bane, matarka tanada hakki akanka, kaima kasani, kuma ka girmeta ka fita hankali, dammi zaka biye mata ku aikata abinda bai daceba, yasmeen yarinyace mai hankali da nutsuwa, kowa ya zauna da'ita saiya sota.
Hakane momcy, nima ďin ko adaďin ina 'kaunarta sharrin shaiďanne kawai, amma insha ALLAHU baza'a sakeba.
To shikenan ALLAH yabaku zaman lafiya yakuma baku zuriya tagari.
Nawaf ya amsa akan la66ansa da ameen, nandai momcy tayi masa nasihohi, sannan yami'ke ya ce, "momcy papa fa??, yana ďakinsa momcy tafaďa, kaje ku gaisa mana,, A'a momcy barsa sai gobe idan ALLAH yakaimu, yau nasan inada laifi awajensa, gashi nabar Yasmeen ita kaďai.
Momcy tayi murmushi ta ce, "to saida safe, idan ta tashi kace inamata sannu.
To my dear mom zataji yafaďa yana fita.

Afalonsa ya isake Abdallah da Anwar wai sunzo dubashi, ya zauna suka gaisa, da tambayarsa ya jiki??, ya ce, "da sau'ki sosai, Anwar ya ce, "abi wai ina abla??.
Tana ďaki tana barci, barci kuma yaya?, tun yanzu ko itama batada lafiyarne??, Nawaf ya girgiza kai yana hararar Abdallah, sai ba'ada lafiya ake kwanciyar wuri, kunga saida safe kutashi ku tafi..
Anwar ya shagwa6e fuska kai abi hirafa mukazo muku, kuma saika koremu.
A'a niba kirarku nakeba, kuje gobe idan ALLAH yakaimu kwazo hirar nima zuwa zanyi na kwanta, badan sunsoba suka mi'ke kowa yana zum'bura baki.
Nawaf yarufe 'kofar yakashe komai yanufi ďakinsa,, wani irin farincikine ke ďawainiya dashi, ya 'karasa kangadon ya zauna kusada fuskar yasmeen, ya tsura mata fararen idanunsa tanata barcinta hankali kwance, ahankali numfashinta yake fita, ta cure waje ďaya kamar ďa acikin uwarsa.
Nawaf yay murmushi yana shafa sumar kanta, data bazu akan filo har saman fuskarta, yasaka ďanyatsa ďaya ya janye wasu gashi dasuka rufe mata fuska, ahankali yafurta ALLAH yay miki albarka yabarmu tare har abada, ALLAH yabamu 'ya'ya masu 'kyawawan halayenki, yadu'ka ya sumbaci goshinta, tasaki wani lallausan murmushi tamkar idonta biyu.
Shima murmushin yasaki, yami'ke yacanja kayansa zuwa nabarci bayan yagama zuba sambatunsa, da zazzagawa yasmeen kalamn 'kauna batareda tasaniba.
Gadon yahawo ya cire mata bargon sannan ya canja mata rigar wankan zuwa ta barci, yay musu addu'a tareda rungume matarsa suka lula duniyar barci.

Da asuba tarigashi tashi, dan haka ta sulale zuwa ďakinta, acan tayi sallah takoma barci harda kulle 'kofa.
Fitarta babu daďewa Nawaf yatashi, ya laluba bata nan, saiya mi'ke yana murmushi, shima alwala yayi yafice masallaci, koda yadawo saiya nufi ďakin yasmeen, amma 'kofar arufe, ďakainsa ya wuce yakwanta shima...............✍🏻






Kuyi ha'kuri yaudai babu yawa ina busy ne.








©2017


💗bilyn Abdul💗
💓Mrs Abdus'salam💓
💗luv u oll my fan's😘💗
[1/12, 9:00 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF 🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💓



Page👉🏻47 & 48

.....Sai wajen shaďaya suka tashi, dan zan iya cewa kusan lokaci ďaya suka tashi, yasmeen jinta take wani fayau kamar isaka zata ďauketa, yanzuma saida ta'kara shiga ruwan zafi, tagasa jikinta tayi wanka, bawata kwalliya tayiba fauda kawai tashafa sama2 sai kwalli, tasaka siket da riga na atanfa, tana son fita gaidasu momcy amma tanajin kunya, bakuma taso ta haďu da Nawaf, takoma bakin gado ta zauna shiru, maganganu takeji 'kasa2 afalo, tami'ke ahankali tafito, dai dai nan Nawaf shima yafito sanye cikin farar shadda ďinkin zamani, kallo ďaya tayi masa ta ďauke kai, su ladidi suka rissana suna gaishesu, kusan atare suka amsa.
Yasmeen ta ce, "sannunku da 'ko'kari ladidi harkun gyara waje haka??, talatu ta ce, "ai tun ďazuma mukayi hajiya yanzuma abincine momy tasamu mu kawo muku.
ayya to sannunku da 'ko'kari kunji, ALLAH yabiyaku ya baku miji nagari.
Sukace ameen suna dariya, dan sunajin daďin addu'arta.
Bayan fitarsu tawuce kichin batareda ta kalli ko'inda Nawaf yake zauneba, binta yayi da kallo harta shige, tafiyarta ta canja, gsky tabashi tausayi, shima saidaga baya yagane yayi 6arna baikuma tausayamata ba, to asannan idanunsa yarufe baya tana komai, harta fito yana zancen zuci.
Shayi tahaďa masa da sauran kayan break ďin, tazo gabansa ta ajiye saman tebirďin tsakkiyar falon, dan tasan baya cin abinci a dinning, tagama jerewa takoma gefe tazauna da kofin shayi ahannunta batareda tayi masa maganaba.
Shikuma sai binta yake da kallo kamar yau ya fara ganinta, ahankali ya furta xarah!, wani zuuuuuuu yasmeen taji acikin kanta, bakowa yake kiranta da ainahin sunantaba fateema barema xarah, saitaji sunan wani iri kamar banataba kokuma wani (SABON AL'AMARI) sabon littafina mai zuwa insha ALLAHU.
Jin tayi shiru yakuma faďin xarah!!, wannan karon har tsigar jikinta saida ta tashi, dan saida yaja sunan, ta ďago manyan idanunta tana kallonsa, shima kallonta yakeyi, ta kauda idonta daga kallonsa ta ce, "ina saurarenka.
Ya gyara zamansa har yanzu idonsa yana kanta, ya ce, "zonan kiji mana, batareda ta kalleshiba ta ce, "kafaďa ahaka mana aii inajinka, yakai hannu yana shafa gemunsa tareda kwantar da bayansa jikin kujera, ya ce, "plz kizo kici abinci".
Saida ta kalli kofin shayin dake hannunta sannan ta ce, "bagashi ina shaba.
Shayi aiba abinci bane xarah, ana shanshine kawai dan hanji ya warware, saida taďan ta6e baki sannan ta ce, "karka damu nikam ya isheni, tasowa yayi yanufo inda take danyaga magana bazata yimasaba, ya zauna kusada ita sosai, saita matsa, ya ce, "tofa fancy face guduna kikeyi kuma??.
Ta haďiye shayin data kur6a sannan ta ce, "ai mugu abin gudune, yaďan zaro ido nine mugun??, tami'ke tsaye tana faďin kaima shaidane aii, nikam saidai nabawa wasu labarin muguntarka, tana gama faďa tashige bedroom tarufe.
Yabita da kallo yana murmushi lallai yarinya kina nufin ba'azo 'karsheba kenan?? Aii dolene kiyi ha'kuri dan nariga nayi winning game ďin, kekuma kinada game over, result kaiwai nake jira, kujerar daya taso yakoma yahau cin abincinsa.
Bayan ya kammla ya gyara wajen, yanason zuwa gaida su momcy yana tsoron haďuwarsa da papa, yasan momcy tanada saurin fushi amma tanada saurin sauka, amma papa sai a hankali, yanzu yana zuwa zai hau kansa da faďa ALLAH ne kawai zai kwacesa, kamar daga sama yaji sallamar mas'ud, ya amsa yana faďin bismillah dama gunka zani ďan haďi, mas'ud dake shigowa ya ce, "ďan haďi ko ďan faďar gsky, Ameena ma ta shigo, Nawaf ya ce, "ALLAH yasoka harda Ameena dasai ka yabawa aya za'kinta.
Mas'ud da ameena suka zauna suna dariya, mas'ud ya ce, "malam mika isa kamin nidai gsky nafaďa aii, babu wani gsky malam kazo kawai kayimin haďi awajen su momcy, yanzu haka tsoron zuwa gaida papa nakeyi.
Hhhhh gay kace kotu zaka shiga babu lauya kawai,, Nawaf suka gama gaisawa da ameena sannan ya ce, "aiko maga takaddama babu, suka tuntsire da dariya su duka.
Yasmeen tabuďe ďaki tafito danjin an ambaci sunan Ameena, cikin farin ciki ta rungume Ameena saidai fuskarta tana nuna kamar batajin daďi, Ameena ta ce, "yar uwa ykk, lfy lou 'yar uwa ya 'karfin jikinki??, Alhmdllh, aini sainaga kema kamar bakida lafiya?, saida ta kalli Nawaf sannan ta ce, " 'kalau nake sister mikika ganine??, ba komai nagankine fayau.
Mas'ud yakali Nawaf kallon tuhuma, da ido yay masa magana wai lafiya, Nawaf ya datsa hannunsa saman ďayan tafin hannunsa Alamar yagama aiki, ido mas'ud yazaro ya ce, "kai haba??.
Nawaf yay wata 'yar dariya yana faďin angaya maka nina wasane, am winning wlhy.
Yasmeen duk tana kallon zancen kurman dasukeyi, dan haka suna haďa ido da Nawaf ta harareshi, yay ďan murmushi yana shafa sumar kansa, tami'ke takawo musu ruwa da lemu, saida tagama basu sannan takama hannun Ameena suka shige bedroom, mas'ud ya ce, "za'ayi gulmarmu ne??, Ameena tajuyo tana faďin idan kunsan kunyi abin gulmar ba.
Nawaf yaďago daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, mutumina kaima kasani zata gumtsa matane kawai, mas'ud yay dariya amma kaimafa ďan iskane, tokaida bakada lafiyama ina kaga 'karfi.
To sarkin 'yanson gulma ina ruwanka, nida wajenkama zani samo mata magani saikuma naga momcy tabata wani, amma kamarfa bai mata aikiba, naga tana tafiya bayanda tasaba ba.
Kai ďan duniya kana nufin har momcy tasani?,, kabari kawai nima wlhy banso hakanba, amma tazo ta ritsani..
Hhhhh lallai kacika mara kunya kuwa Alhaji,, Nawaf ya harareshi, nida kai a tantance mara kunya, jiyafa inajinka sama2 kana koro rashin kunya,, hhhh aini akan aikina nake ehe.
Ummmm lallai kam su aiki manya....

Suma su yasmeen ana 'kuryar ďaki itada tata aminiyar, Ameena ta ce, "yasmeen mike damunkine wai??, yasmeen tayi kwalkwal da idanu tana shirin yin kuka, cikin rawar murya ta ce, "Ameena mugunnan yasameni abanza batareda yafara sonaba kamar yanda muka shirya dake.
Ameena tazaro idanu kai sis... garin yaya hakan tafarune?, yasmeen tafaďa mata yanda sukayi da umma jiya, taďora dafaďin dagafa bashi ha'kuri yay min faďe, dan nidai faďe zan kira wannan wlhy.
Ameena tayi dariya A'a babu wani faďe, mutum da matarsa sai ace yayi faďe, kice 'yar uwa angirma,, yasmeen ta harareta kin ganki ko zaki fara.
Ameena tadafata tana dariya yiha'kuri amarsu, haba shiyyasa naga Nawaf yanata fara'a ga 'kyallin angwanci yanayi.
Harrarta yasmeen tasakeyi, tana kaimata duka da filo, itakuma Ameena tana tuntsura dariya dabata ha'kuri, tari'ke filon tana sassauta dariyarta, kinga yi ha'kuri na daina, yanzudai ya ake cikine??.
Yasmeen ta ce, "ai saina garashi nima, dan bazai shani abanzaba, duk muguntar dayayimin saina rama,, A'a yasmeen kawai kishare, kinga ko ada kema kina masa rashin kunya, kinga kenan kowa yana ta6a kowa, kawai ki ringumi mijinki ku zauna lafiya, fatanmu yanzu kuma muga sakamako kawai, kayan harka na nan zan aiko haleematu takawo miki.
Cikin rashin fahimta yasmeen ta ce, "miye kuma kayan harka??, saida ameena tayi 'yar dariya sannan ta zayyane mata komai, tab ALLAH yakiyaye yasmeen tafaďa, ni nasha wani abu, kina ganin ba'kar wahalar danasha hannun mugunnan jiya, ke kobansha wahalaba babu abinda zansha inma gaya miki gsky, kawai saina zauna nayita ďirkar magani batareda ciwoba, 'katon banza yayta shan romo yana raina mini hankali ko,, aii badan wannan nazo duniyaba 'yammata.
Oh oh yarinya zaki shane, ina zaune zakizomin da zancen, idan ALLAH yabaki fitinannen miji irin mas'ud wlhy dole kisha, kuma ina nan dake zaki bani labarine.
Baki yasmeen ta ta6e ke nifa bazan zauna yamaidani wata kasar takawarsaba,, dan haka kima daina saran zan sakko wataran.
😂'yammata kenan mudai 'yan kallone, yasmeen ta ce, "uhmmmm keni mubar wannan zance kitso najeson yi yaza'ayine?, wake miki kitso?.
Uhmmmm wata yarinyace a 'kasan layinnan, idan kin shirya sainasa su halimatu su kawo miki ita, to shikenan amma kinsan halimatu bata zuwa gidannan saboda momcy ko??.
Hhhh ke bar 'yar iska amma ai batajin kunyar yin zancen Abdallah gaban mami ko?.
A'a shima ai hakan take, ko agaban papa labarin masoyiyarsa yake, ranar inaji modebbo yana masa masifa wai bashida kunya.
Tofa kaji manya su kunyar garesu?, 'k wai kema modebbon kike cemasane??, yasmeen ta ta6e baki keni duk sunan dayazo min nasa faďa nakeyi wlhy, A 'yammata yakama acanja masa suna.
Yasmeen ta ce, "k bayanzuba saiya jigatu sannan, dan idan nabarsa haka yaga lagona.
Hummm yarinya kidaibi ahankali, mazan nan sunada hanyoyin maganinmu kala2, danhaka atafi a slowly..
Suka tuntsure da dariya harda tafawa.
Nawaf yaturo 'kofar yashigo da sallama, Ameena ce kawai ta amsa masa, ya ce, "masu hira bari muje masallaci, kuma kutashi kuyi sallah.
Ameena ta ce, "to, saikun dawo, harya kai 'kofa saikuma yadawo, yadu'ko ya sumbaci kumatun yasmeen, dasauri taďago

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login