Showing 6001 words to 9000 words out of 74786 words

Chapter 3 - Nawaf Book 1 Hausa Novel Complete

13 Dec 2024

351

yaseer.
Yasmeen da yaseer k'yawawane, dan sunada kala irinta asalin buzaye.
Yasmeen tun tana yarinya takeda farin jini, kowa sonta yake, dan haka dangin babanta suka tsaneta laifin babanta ya shafeta.
Lokacin da yasmeen takai shekara 12 sai dangi suka matsa akan ayi mata aure, zuwa sannan yasmeen tanada wanda takeso wani sule, tana sonsa sosai shima haka, dan haka lokacin da'akace za'ayimata aure saitayi murna.
Amma saidai kash, dangin mahaifinta sunce sun za'ba mata miji, d'an wan babanta wato Tanimu, yasmeen sam bata son Tanimu dan d'an iskane kowa yasani kuma, amma babu yanda zatayi.
Aka saka biki wata hud'u, amma amarya bata so, dahaka biki yarage saura sati d'aya.
Ana saura kwana hud'u d'aurin aure Tanimu yazo gun yasmeen, abin yabata mamaki dan bai ta'ba zuwa wajentaba tunda aka saka musu rana.
Da'kyar umma ta lalla'bata ta fita, ko sallama bata yimasaba bare gaisuwa, yasaki baki yana zuba mata surutan banza, wai idan sunyi aure randa aka kaita zaiyi kaza zaiyi kaza.
Yasmeen taji yana d'akko mata zancen daya fi karfin tunaninta, dan haka takama hanyar gida zata tafi, da sauri Tanimu ya dam'ko yasmeen, ya matse abango.
Yasmeen tafara ihu dan ganin abubuwan daya ke mata, kafin mutane su kawo mata d'auki ya turmushe ta ak'asa, lokacin da mutane suka zo yana saman yasmeen amma baiyi mata komai ba, sai rigarta daya yaga, nanfa mutane suka shiga jibgarsa dan dama haushinsa akeji.
Kafin safiya labari ya baje garin kwangwalan wai Tanimu yayima yasmeen fad'e a daren jiya.
Duk gari ya d'auka cewa an lalata yasmeen, dan hakama fita ta gagareta, dan babu wanda zai yarda da ba haka bane, aranar kuma dangin mahaifinta sukace sun warware maganar auren, wai yasmeen 'yar iskace tana neman maza.
Abu kullum k'ara gaba yake, harta kai umma da baba basuda ikon fita sai ayita zind'ensu, harda yaseer dabai san komai ba, idan yafita sai ayita tsan gwamarsa, itako yasmeen ma aibatada ikon fita ko k'ofar gida.
Ahaka aka kulla wata 7 amma komai bai canja ba, kuma babu mai zuwa wajen yasmeen, sule ma iyayensa sun hanashi.
Bak'in ciki da damuwa suka ishi baba, dama akwai wani Alhaji dayake zuwa sayen dabbobi a wajensa, shi d'an Najeria ne a jihar kano.
Baba baiyi k'asa aguywa ba wajan sanarma Alhaji halin dasuke ciki,, Alhaji buba ya tausaya musu sosai, dan haka ya ce, "su baba su shirya yatafi dasu Najeria.
Babu musu suka yarda, batareda kowa yasaniba suka baro kwangwalan, koda Alhaji buba yakawo su gidansa sai hajiya jummai ta nuna musu tsangwama, ta ce, "saidai baba yarink'a musu gadi dama mai gadinsu yagudu saboda wahala.
Baba bai musaba yakar'bi tayinta, baba yana gadi umma tana taya hajiyar wasu 'yan ayyukan gida.
Alhaji buba yanada wani yaro mara jin magana, sunansa Fasal, shikad'ai ya haifa dan haka ake nuna masa gata na tsiya, tunda faisal ya 'kayalla idanu yaga Yasmeen ya kafa mata k'ahon zuk'a.
Yasmeen bata manta da abinda yafaruba a garinsu dan haka take baya2 da faisal, duk abinda yake faruwa hajiya jummai tana kula, tasan kuma halin d'anta yanzu saiya 'bata yarinyar mutane, dan haka ta tsawatar masa.
Alhaji buba yasaka su yasmeen makaranta , ahankali k'yawun yasmeen yafara fitowa, zawa sannan faisal yakai 'kololuwar sha'awar yasmeen, awata ranar lahadine, yad'auki hanyar cimma burinsa, yasaka yasmeen ta gyara masa d'aki, daga haka ya rutseta a d'aki, ihu takwala wanda yasa hajiya jummai isowa da gudu d'akin faisal, saita tarar yana shirin aikata ta'asa, ta daka masa tsawa sanna ta 'ban'bare yasmeen dak'yar.
Babu wani mataki da 'aka d'auka, dan ko fad'a basuyima faisal ba, dan haka hankalin umma da baba yatashi, suka fara tsanar zaman gidan, dan indai aka cigaba da tafiya haka wataran faisal saiya lalata musu yarinya.
Da alhaji buba yaga hankalinsu yatashi saiya ce, "yana nemawa faisal auren yasmeen idan yadawo daga karatu america za'ayi biki, inko har basu aminceba to zasu barmasa gida, indan suka amince to zai siya musu gidan dazasu zauna ya nemawa baba aikinyi yabar gadi, zaikuma d'auki nauyin karatun yasmeen da faisal harzuwa inda suke buk'ata.
Da farko basu aminceba dan sunsan faisal bashida tarbiya, amma dasukaga babu sarki sai ALLAH saisuka amince.
Aka saka rana da komai, faisal yatafi america karo karatu, badan yasoba, dan yaso saiya mallaki yasmeen kafin yatafi, bawani so yake mataba sha'awarta kawai yakeyi, daya sami biyan buk'ata zai watsar da banxa😔.
Bayan komai ya kankama alhaji buba yacika al'kawarin duk daya d'auka yasiyama baba gida madaidaici, yakuma d'auki nauyin karatun su yasmeen, yanzu haka yasmeen tana karatu a (FCE KANO ) yaseer yana shekararsa ta k'arshe a secondary, idan yasmeen zata makaranta ko anguwa kaita akeyi, dan an d'akko mata direba na musamman wato balarabe, duk motar dayaso yake d'aukowa a gidan su faisal yakai yasmeen makaran ta daduk inda take buk'ata.
Sutura kuwa mai tsadar gsk su alhaji suke sayama yasmeen, haka kayan kwalliya, hajiya jummai tana k'ok'ari wajen sayama yasmeen, waya mai tsada yasmeen take ri'kewa, wata sa'in agidan take weekend, sunayin waya da faisal, saidai hirar tasa duk takan kasance batsa, abun yana damun yasmeen amma babu yanda zatayi.
Yanzu haka saura wata 5 faisal ya kammala karatunsa, yana dawowa kuma za'asha biki, saidai yasmeen da iyayenta duk basa son wannan aure, kullum addu'arsu ALLAH yakawo sanadin da auren zai rushe, wannan shine tarihin yasmeen....................✍🏻






©2016

💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞

[1/12, 8:53 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻10

......Yau takama d'aurin aure amma yasmeen batada niyyar zuwa, umma tayi mata maga ta ce, "bazata jeba sai anjima.
Shima dai Nawaff ya halarci taron d'aurin auren daganan yakama gabansa, dan shi mutumne dabaya son yawan hayaniya, gashi da mutane sun ganshi bazasu bari ya huta ba.

3:30pm
Yasmeen kwance a falo tana kallon film, umma tafito daga d'akin abba, ta zauna kusada yasmeen.
Yasmeen ta d'ago tana kallonta, umma ta ce, "mamana yau bazaki wajen bikin asma'u d'in ba??, yasmeen ta ce, "gsky umma bazan jeba bana jin dad'i, amma idan naga zuwa anjima naji sauk'i sai naje.
To shikenan ALLAH ya sauwak'e.
Amin yasmeen tafad'a tana kallon tv, lfyr yasmeen k'alau, batason zuwa wajenne su had'u da Nawaff, tana tsoron karya aikata mugun nufinsa akanta, jadabaya ga rago 🐏kuwa aiba tsoron fad'a bane, inji masu iya magana.

Badan ALLAH Nawaff yay shirin zuwa wajen walimar ba, yajene kawai domin yasmeen, amma saidai kash ita batajeba, tunda yaje yake baza idanu, amma komai kama da ita bai ganiba.
Duk abinda yake mus'ad yana kallonsa, dukda yasan Nawaff bazai aikata abinda yafad'a akan yasmeen ba, amma yayi matuk'ar farin ciki da bata zo wajenba.
Bayan antashi daga walimar su Nawaff sukai saurin guduwa, saboda mutane, amota mas'ud ya ce, "bro's waimi kake nema d'azu kaketa lek'e2.
Nawaff yad'an ja hancinsa tareda kwantawa sosai ajikin kujera yana kallon titi, daga bisani yadawo da kallonsa wajen mas'ud dake tuk'i, ya ce, mara kunyar yarinyar nan nake nema, amma ban gantaba, inaga tsoro yahanata zuwa.
Mas'ud yay murmushi, hankalinsa na bisa titi, ya ce, "aii masu iya magana suna cewa hanyar lafiya abita da shekara, nikaina naji dad'i dabata zoba.
Nawaff ya harari mas'ud, kai malam mikake nufine?? wai ko dai son k'abar nan kakeyi??.
Mas'ud yay dariya yana fad'in A'a alhaji maida wuk'ar niba sonta nakeyiba, kada kishi yasa ka b'arar dani.
Banza Nawaff yay masa, dan yasan halin Mas'ud sarai yanzu saiyayita jan wannan maganar har momcy taji.
Dahaka suka k'arasa gida, kai tsaye b'an garen momcy suka nufa, afalo suka iskesu itada papa da Abdallah.
Nawaff yazauna kusada k'afar papa yana kwasar gaisuwa, shima mas'ud ya gaisheshi, suka gaida momcy, Abdallah ya gaishesu.
Papa ya ce, " 'yan samari daga ina haka??.
Nawaff yad'an sosa sumarsa ya ce, "papa daga wajen bikin Safwan muke.
Papa ya ce, "masha ALLAH, ALLAH yasanya alkairi, kuma aii yakamata kufito da matan auren ko??, da sauri Nawaff yad'ago yana fad'in papa aurefa kace??.
Papa ya ce, "o, ashe kajini modeebbo!!.
Nawaff ya ce, "papa 27year's fa.
Momcy ta ce, "toshi wannan dakukaje bikin ba abokinku bane, amma gashi yayi, kudai nakula daga kai har Mas'ud bakwa sonyin aure, ko sokuke saikun tsufa??.
Barsu ummul'khairi, aimun yanke magana da Alhaji, nanda k'arshen shekara idan har basu kawo matan aureba, tomu zamu nema musu.
Nawaff ya ce, "papa saikace mata.
Papa yakama kunnensa, yana fad'in toku zauna kukagani, sadaka zamu badaku.
Abdallah ya tunysure da dariya.
Nawaff ya harareshi yana mazurai, kai wa kakema dariya??, mas'ud ya ce, "bro's barshi zaizo ya samemune.
Momcy tayi dariya A'a karku huce akan d'ana, tunda bashi ya ce, "ayi sadaka dakuba.
Papa ya ce, "barshi ai shima hardashi.
Abdallah ya zaro idanu, papa nikuma asuwa wai kare da gudun layya, 'yan 27year's basuyiba, bare ni d'an 20years papa kwanan fa nashiga jami'a.
Nawaff ya daka masa tsawa, kai dallah kaima mutane shiru, kabi ka ishi mutane da shegen surutu.
Abdallah ya zunb'uro baki gaba yana gunguni, amma Nawaff bayajinsa, Dan yasan idan yajisa, hummm.
Saida sukaci abinci sanan suka tafi b'an garen Nawaff.
Mas'ud ya ce, "kai malam kahuta wlhy karigaya ka kama matarka ahannu, babu rabon ayi sadaka dakai.
Nawaff ya ce, "agidan ubanwa nasamu matar, ALLAH mas'ud kaifa d'an iskane.
Mas'ud ya tun tsure da dariya, kazauna kallon ruwa wlhy kwad'o yamaka k'afa, kanaji kana gani za'ayi sadaka dakai.
Nawaff yaja tsaki tareda kwanciya saman kujera, ya lumshe idanu.
Duk surutun da mas'ud yakeyi yana jinsa amma yay kunnen uwar shegu dashi................✍🏻





💞Bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's 💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻11

....koda daddare yasmeen k'in zuwa kai amarya tayi, ta langyare akan batada lafiya, ta kashe wayarta kuma dan kar akirata.
Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, Nawaf yagama hutunsa ya tattara ya tafi kasar Spain domin cigaba da biga kwallo.
Har ya taho bai k'ara had'uwa da yaesmeen ba, hasalima yamanta da ita, yacigaba da harkokinsa kamar yanda yasaba.
Itakam yasmeen bata manta dashiba, ko makaranta zata takan fita cikin d'ar2, kullum addu'ar ta kada ALLAH ya had'ata da Nawaff ko da amafarki.
Dahaka dai aka shere wata uku bataji d'uriyarsa ba, ahan kali tafara sakin jikinta.

Yau agajiye tadawo daga school ta shigo falon tana jan k'afa kamar kazarda kwai ya fashewa aciki, yaseer ne kawai afalon yana cin abinci, idanunsa nakan TV ko k'yaftawa bayayi.
Yasmeen tadaki kujerar dayake zaune dan taga alama baisan tashigoba, yajuyo da sauri yana kallonta.
Yasmeen ta harareshi kaidai ALLAH ya shiryaka, shikenan indai kana kallon kwallo sai a rasa hankalinka gaba d'aya.
Yaseer yay dariya, sorry my aunty ALLAH bansan kin shigoba, kinsan yau mutumina yake buga kwallo bana son komai ya katseni wlhy.
Yasmeen ta tab'e baki, waye kuma mutuminka??, ata k'aice ya ce, "modeebbo mana, gaban yasmeen yafad'i ras danjin sunan wanda yazame mata baraxana arayuwarta ta yanzu, ta ce, "waye kuma modeebbo??.
Idonsa na kan tv ya ce, "kalli tv zan nuna miki shi, shine number 10.
Yasmeen taja flet d'in abincin dayakeci gabanta, ta hauci, saidai itama hankalinta yana kan tv d'in, wani uban ihu yaseer yatashi ya kwala tareda fad'in 🗣goooooooooooooo⚽!!!!!!!!!.
Yasmeen tai saurin rufe kunnenta danjin zai fashe saboda k'arar da yaseer ya kwala🙉, cikin kara ta ce, "dalla malam karka fasamini dodon kunne.
Ya zauna yana dariya tareda 👍🏻,yana fad'in sai modeebbo, kana wuta my gay.
Sai asannan idanun yasmeen suka kai kan Nawaff tamik'e da sauri tana fad'in yaseer kana nufin wannan gay d'in, ta nuna Nawaf da aka nuno ya durkusa akasa yad'aga hannunsa samma yawani wage baki da alama shima ihun yakeyi dan murna, wasu 'yan kwallo sukazo suka rungumeshi suna ihu.
Yaseer ya ce, "shine sistona, tauraro kenan mai haskawa a duniyar kwallo, yanzu su duniya take yayi dason gani, hala kin sanshine kika mik'e zumbur.
Yasmeen taja ajiyar zuciya ta ce, "natab'a ganinsa dai, da sauri yaseer ya ce, "dan ALLAH dgsk kikeyi??.
Yasmeen ta tab'e baki, ta ce, "kaji yaro natab'a yimaka k'aryane??, awajen bikin Asma'u natab'a ganinsa, dama d'an kwallone??.
Yaseer yagyara zama Taf sisto idan kinji ana fad'in mai laya kiyayi mai zamani to modeebbo kenan!!, ai duk ranar dana had'u da bawan ALLAH nan to sainayi sadaka.
Yasmeen ta tunysure da dariya, amma kaidai d'an wahalane wlhy, tafad'a tana mik'ewa.
Yaseer ya ce, "kedai tafi dan bazaki tab'a ganewaba.

Nawaff zaune ad'akinsa akasar Spain, yana zaune bisa kujera mai zaman mutum d'aya, hannunsa rik'e da remote, yana neman tasha, wayarsa dake gefensa tayi wringing yakai hannu yad'auka.
Saida yad'an murmusa sannan ya ce, "Hello my gay ykk?
Daga can mas'ud ya ce, "ina lafiya my bro's, naga wasa d'azu yayi k'yau, ammafa kayi k'ok'ari, acinkin minti biyu na farko fa ka jefa mana kwallo a raga, ina alfahari dakai my bro's.
Nawaf yay sassanyan murmushi tamkar yana gaban mas'ud, ya ce, "nagode d'an uwana, kana k'ara mini karfin gwuywa a rayuwa.
Karka damu bro's, dama Anwar ne ya ce, "nakira masa kai, tun d'azu yake nemanka bai samuba, yanaso yayi maka murnar nasarar dakuka samu.
Nawaf ya ce, "ayya my little bro's banishi.
Anwar yakarb'a wayan cikin 'yar muryarsa ya ce, "yaya congratulation!!,
Tnx my boy, ykk??.
Ina lafiya yaya, momcy ma ta kalli wasanka na d'azu.
Woow nice, kace ina gaisheta kajiko??.
To yaya bye🖐🏻.
Okey bye autan momcy.
Mas'ud yakarb'i wayan suka cigaba da tattaunawa, mas'ud ya ce, "to shikenan bari nabarka haka, amma gsky kayi k'ok'ari nanda 2month d'in kazo, indai kanada dama, ko kwana uku kayi ma ya isa.
Okey I will try, my bro's
Okey ALLAH yakaimu lokacin.
Sukayi sallama kowa ya kashe wayar.
Nawaf ya kwantar da kansa ajikin kujerar tareda lumshe idanu..................✍🏻






💞bilyn Abdul💞
💞Mrs Abdus'salam💞
💞LUV U OLL MY FAN's💞
[1/12, 8:54 PM] mrs bilkisu: ☆☆☆☆☆☆☆
🎾 NAWAFF🎾
☆☆☆☆☆☆☆






NA BILKISA IBRAHIM💞




Page👉🏻12

....Zan iya cemuku biki yanata matsowa, dan shirye2 akeyi na garari agidan Alhaji buba, gidansu faisal kenan, shirin biki suke na d'an gata, dukda shi yana America abinsa, amma duk shirin da'akeyi da saninisa.
Yau tunda safe hajiya jumai tasa balarabe yakawo mata yasmeen gida.
Tunda balarabe yazo da sak'on kiran yasmeen ta had'e girar sama da k'asa😉, harga ALLAH bata son zuwa.
Umma ta ce, "wai yasmeen banaji balarabe ya ce, "hajiya na nemankiba??.
Yasmeen ta matso 😢hawayen datake matsewa tun d'azu, ta shagwab'e murya umma dan ALLAH kibarsu nikam babu inda zanje.
Dak'uwa🖐🏻 umma tayimata, kinci gidanku, hajiya ba mamarki bace ba, za kitashi kije kosaina Ci k'aniyarki, ko kin manta nanda wata d'aya kin zama surukarta.
Yasmeen tafashe dakuka, umma yanzu nan har fata kikemini nazama matar d'anta😭??.
Umma tayi murmushi mai ciwo, wanda ya nuna ainahin damuwarta, ta kamo hannun yasmeen tayi, ta zaunar da'ita gefenta tana shere mata hawaye, kinga mamana bar kuka, ba fata nake miki ba, amma yakama ta kisa a zuciyarki hajiya uwace awajenki, kuma bamusan abinda ALLAH ya shiryaba nan gaba, karki manta da irin hidima da d'awainiyar dasuke damu, komi muka zama a Najeria sune sila.
Umma aii badan ALLAH sukayi manaba, sunyine domin d'an iskan d'ansu.
Umma ta harareta banace karna sake jiba wai.
Jiki asanyaye yasmeen ta tashi, to umma na daina.
Bawata kwalliya tayiba kaya kawai ta canja ta k'ara turare ta fito.
Umma ta ce, "adawo lafiya d'iyar kwarai.
Amin kawai yasmeen ta ce, "dan idan tayi magana mai tsawo kuka zai iya zuwa mata, tasan umma ma tana cikin damuwa, tana dannewane kawai saboda ita.
A k'ofar gida suka had'u da yaseer yadawo daga islamiyya, ya ce, "sisto sai ina haka??, ta ce, "anguwa zanje.
Shiyyasa bakije islamiyyaba??, malam Dawud yanata nemanki!!.
Yasmeen ta zaro idanu da gsk kakeyi yaseer??, ALLAH karkiji wasa, dan aunty Amina ta ce, "ya karb'i hadda yau.
Yasmeen ta ce, "naga banu, bari nadawo naje wajen Aminar.
To saikin dawo, yaseer yafad'a yana nufar gida.

Tunda suka tafi take sharar kwalla, balarabe yana kallonta, harga ALLAH yana tausayama yarinyarnan, duk da bata tab'a fad'a masa damuwarta ba, amma ya fahimci bata son maigidansa, inama yanada hanyar taimaka mata wajen rushewar wannan auren K'ADDARA ko BIYAYYAR (book d'ina danafi k'yauna❤ ), amma zai gwada sa'arsa yagani.
Dahaka suka isa gidan, mai gadi ya bud'e musu get, balarabe yasamu guri yay parking.
Da sand'a yasmeen tashiga falon tamkar wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login