Showing 30001 words to 33000 words out of 85703 words

Chapter 11 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

605

butulu ashe kadan kike jira dama kaga maciya amana,Nusaiba Kuwa dariya ta hau shekawa tace Siyama kice da gaske kina ciki yanzu wannan gidan Zaki shiga hhhhhhh ta sake kecewa da dariya tace asha talauci lafiya karki ji kunya Ni Kam na bar miki wlh bana Yi,Siyama ce ta kalle su tace mahaukata Jahilai an fada Miki tsoronki zanji ko bai sakeki ba kina jin Zan kasa aurensa idan nayi niyya,Kuma wallahi da Sannu sai kunyi kuka Watarana,Aslam Yana jinsu yace Kinga let's go Siyama kina saurarar Wanda basu San me suke ba a duniya magana da su ai bata lokaci ne,Mama tace iyye wato Aslam yanzu na zama waccen ban San me nake ba ka manta Sanda kake zuwa kana roko a aura maka Nusaiba,Aslam hannun Siyama ya rike tare da janta Suka tafi,Mama tace yau Naga dan iskan karshen zamani Kinga harda rike hannunta wato mu gani Yana sonta,Nusaiba tace Mama ke Kika damu dashi ga sabon me kudi nan new Money Sufyan muje Kawai Suka tafi gida tare da Mama ko a jikinsu.
Aslam kuwa Kuwa a kofar gidan su Siyama ya tsaya Suka ci gaba da hirar su cike da nishadi da farin ciki.





Waye Aslam








AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️

41-45


Official


By
AsmaBaffa






Page naki ne

Fateemah Farouk
Ameerah Abdussalam
Hanana Smart









Aslam Shareef Alhassan cikakken Fulanin Mambila ne gaf da Cameron fulanine usil,babansa Shareef Alhassan me tarin arziki ne na shanu da kadarori sannan Kuma Yana da ilimin addini Dana zamani Alhaji ne sosai a Mambila,auren zumunci aka Masa da Yar uwarsa Zuwaira wato Maman Aslam Mum,sai da Aslam ya girma bayan an haife shi yana secondary Suka dawo Kano da Zama lokacin kasuwancin Shareef ya shahara ga siyasa Yana yi Katsam Allah ya Masa rasuwa sanadin hatsarin jirgin sama zuwa India,Bayan komai ya lafa Juwairiyya mum wacce suke cewa Zuwaira itace taci gaba da kasuwancin Kamar Namiji tana daukan nauyin danta Aslam yayi ilimi har ta kaishi kasar waje America karatu lokacin Mum arziki yaci gaba sosai ta bunkasa komai Dake Allah yayita da kwazo da fasaha Kuma itama tayi ilimi har matakin Diploma a hannun mijinta tayi Diploma sannan komai nasa Yana shawara da ita da taimakonta ake komai sabo da Haka Yana rasuwa ta Haye karagarsa taci gaba da juya Dukiyar Aslam Allah Kuma yasa shi kadai Suka Haifa dama dangin su Mum kusan basa haihuwa da yawa daga me haihuwa Daya sai me haihuwa biyu haka suke,tunda iyayensu Suka rasu gashi Basu da yawan dangi sosai tunda basa haihuwa da yawa wannan yasa zumuncin ma Sai lokaci lokaci suke zuwa can,Sai Kuma Yan Uwa Wanda suke aure a Kano ko Kaduna.

Aslam a haka ya Zama saurayi kyakyawan Matashin hadadden gaske ga iya daukan wanka ga saka sutura duk inda ya wuce kamshi yake zubawa Kamar me,gashi da addini ga hakuri ga hankali gaba Daya iyayensa ya gado a kyakyawan hali ya samu tarbiya da ilimin boko Dana addini,Yana yin masters sannan Mum ta kyaleshi ta damka Masa dukiyarsa a hannunsa ya koma juya abinsa,Aslam sai da ya Zama hamshakin Mai mudi Kai da gani ba karya bai fuskanci wani Jarabta ba ba ko daya kullum a huce yake,Mum gaba daya sabo da Yana damunta da aiki ya Masa yawa sai ta gudu Qatar inda kanwar Babarta ke aure a can suke zaune abinsu ,duk haka Aslam sai Sanda yaga dama yake zuwa Office Sai wasu kamfanunuwan nasa da yake lekawa Yana kula da ma'aikata tsabar son hutunsa idan yaga dama Sai yayi sati biyu a iya samansa ba tare da ya sakko ko kasa ba,har Allah ya hada shi da su Nusaiba ya sota Kuma ya aure ta a Nan jarabtarsa take shi kam.

Aslam fari tas kyakyawa ne ajin farko,dogo ne amma ba can ba haka ba ramamme ba baza Kuma ace me kiba ba,sumarsa baka wuluk ce me yawan gaske taji gyara style style yake Mata Kamar dan turai,hancinsa dogo ne ba can ba bakinsa karami me dauke da jajayen lips,idanuwansa matsagaita masu kyau,sannan fuskarsa ba me Fadi ba Kuma ba sirirya ba komai nasa chas dai dai kowacce mace ta ganshi sai ta kyasa.

Siyama
Siyama Ahmad Sani Yan Niger ne asalinsu buzaye ne amma tun iyaye da kakanni a Kano Suka taso a Kano Suka gansu daga zuwa Neman kudi Suka dinga hayayyafa har Suka tara dangi a Nan Kano Kuma sun watsu gari daban daban wasu a kauyen Kano wasu a birni,Baban Siyama Ahmad Wanda suke cewa Amadou kanin Dauda ne kawun Siyama bayan Dauda yayi aure Allah bai bashi haihuwa ba gashi su biyu ne rak a wajen iyayensu,Dauda Yana ta aure aure amma ko wacce mace rashin haihuwa yasa take ficewa har ya gaji da aure ya hakura,shi kuwa Ahmad Yana aure shekara daya Matarsa Maryam ta Haifi yarta kyakyawar gaske fara,ai Maryam tana haihuwa abinka da zumunci irin na da Amadou ya kira yayansa yace yayi 'ya matata ta Haifi mace amma na bar maka ita halak malak sabo da haka Suna ma Kai zaka zaba Mata,Dauda harda kukan farin ciki yace na zabi Siyama a saka mata,ai Kuwa yarinya taci suna Siyama,Dauda dalilin kyautar yarsa Siyama ya nemi Hajara wato Aunty wacce bazawara ce itama bata haihuwa Kawai ya aureta tunda lalurarsu iri daya ce.

Ranar da aka yaye Siyama Amadou ya dakko Siyama da kayanta kaf ya kawowa Dauda har gidansa Dake rijiyar lemo Kano yace Yaya ga yarka na kawo maka ta damemu da fitina,Dauda yace a bani a bata dama duk kewarta ta dameni ya karbe Siyama,Amadou akan hanyarsa ta komawa gida mota ta bige shi Nan take ya rasu,Dauda Kamar zaiyi hauka har gobe idan ya tuna Amadou sai ya zubar da hawaye,Siyama ta taso cikin gata so da kulawa sai abinda take so duk duniya ba Wanda Dauda yake so sama da Siyama,itama Aunty ta dauki son duniya ta dorawa Siyama sakamakon bata taba haihuwa ba,macece me iya Zama da mutane ga iya raino da kula haka ta tsaya akan Siyama har ta Isa zuwa makaranta Suka sata a makarantar boko da Islamiyya,data Kara girma har makarantar dare take zuwa shi yasa Siyama take da kokari primary ma private aka saka ta shi yasa take Jin turanci sosai,..

Sun taso a unguwar tare da Nusaiba dake layinsu daya ita Nusaiba ma har primary ta gomnati tayi sabo da talauci,Sanda Shehu yayi Dan kudin nasa basu taso ba,Kuma ba kudi bane rufin asiri ne Kawai, ana Kai Siyama Secondary school Suka hadu da Nusaiba a can,ko a class Nusaiba dama bata da mutunci idan ta Raina kurar mutum zaiga wulakanci,Bata kawa da mutum sai tasan kun fita arziki shine zata Shige maka abinda ya hadata kawance da Siyama kenan idan taje gidan su Siyama zata ci shinkafa da Miya su kuwa gidansu sai a kwashe wata guda ba ayi shinkafa da Miya ba,suna Ss2 Nusaiba ta daina zuwa makaranta sai tallan kosai kannenta ke zuwa sabo da talauci gwara ta Nemo musu ko zasu samu abincin ci,Siyama Kuwa ita da sauran sun Gama secondary school suna da shekaru 19 tana zaune sai dai tallan su har ta Kara shekara hudu Wanda da akwai kudi da tuni sun Gama degree,yanzu sun Kai 23yrs, Yan Mata ne sosai .
Siyama doguwa ce Fara me round face me dauke da dogon hancinta zarkadede,idanuwanta manya dasu masu kyau kamar tana Jin bacci haka take sai ka rantse bacci take ji kullum a Haka take,gashi ne da ita sosai gata da dan jikinta mul mul ba Kashi sai dai ba me kiba za a ce ba,komai mashaallah.

Nusaiba Kuwa Yan asalin Rogo ne wajen jahar Kano Shehu dan dangi ne Yana da Yan Uwa da yawa sai dai Basu da Hali duk talakawa ne a kauyen Rogo,itama Mama tana da nata Dangin da yawa a Rogo amma guda Daya ce wacce suke uwa Daya uba daya sauran duk dangi ne, Amma duk cikinsu babu me iyaye duk sun mutu tunda Suma sun tsufa bare iyayensu sai dangi,Mama me Suna Bara'atu Yar asalin kauyen kayau ce a Rogo ma a wani mugun Kauye take Wanda basu karatu Babu ilimin Addink bare boko,a haka Shehu ya nace sai ita shi yaga fetsarariya dama sai da aka fada kaf gidan su Mama basu da mutunci a kauyen basu da Kara Basu da kunya su kamar a jininsu yake Imaninsu kudi Kawai,Shehu yace ba komai zai sata a makaranta,Bayan ya aureta tun Yana zuwa cikin birni cirani har ya mallaki filinsa ya Gina ya dakko Mama daga Kauye ya dawo da ita birni,ya sata a makarantar yaki da jahilci ta matan aure inda ake koya musu ilimin addini da karatun hausa

Mama ita ko a makarantar ma dakikiya ce sam bata ganewa sai ta dade a aya Daya,aya daya sai ta kwashe satikai bata iya ba,a Haka ma dan Shehu Yana koya Mata a gida,idan Suka Zo karatu ta dinga kunkuni da masifa kenan Shehu har rankwashinta yasha Yi sabo da jahilci da kin karatu,Fatiha ma Sai da ya tsaya a kanta sosai ta iya,ya koya Mata wankan haila da komai,Sallah ma Shehu ya koya Mata,a hankali Mama ta Fara Zama tsagera a unguwar,duk Sanda Shehu ya siyo kayan abinci kwana kadan sai yaji tace ya kare, sai da masu shagunan unguwar Suka fada Masa cewar matarsa fa tana kawo musu su shinkafa,taliya etc suna siya ya sa ido Ashe siyarwa takeyi ta soke kudin,Shehu ya Kai kararta gidansu yafi a irga karshe ma Dangin Mama suci ubansa ya dawo bashi da bakin fadawa Yan Uwansa tunda dama tun farko sun hanashi yaki ji,ana Haka Mama ta haifo yarta mace,Shehu yace zai maida sunan uwarsa Mama tace bai Isa ba ita tun tana yarinya take mafarkin yarta ana fada Mata a mafarki sunan yarki Nusaiba,Shehu yace sai kace wata manzo ko waliyiya to baki Isa ba,Suka dinga fada karshe dole ya hakura ya saka suna Nusaiba ta Haifi Danta na biyu Nan ma ta kafa ta tsare tace Ameer ake yayi shi za a sawa danta,Shehu ya saka,ta haifo Ihsan

Tace yanzu an waye sunayen larabawa ake yayi Ihsan kawai,Shehu ya kyaleta ya saka sai da kyar da ta sake haihuwa ta yarda aka sa sunan Babar Shehu Asmau ai Kuwa tace Husna Kawai ita fa ta waye Kuma baza ta boye ba ai ba uwarta bace haka ta Haifi yaranta karshe ma Shehu Yana son haihuwa tace ta gama tayi planing shike nan ta tsaya da haihuwa abinta, gaba Daya tafi karfin Shehu ya rasa inda zaiyi da ita,wulakanci iri iri,da kudinsa Shehu zai siyi abinci amma idan ta dafa ta hanashi sannan yaranta kadai zata bawa Kuma Suma kadan sai ta siyar da sauran taci tsire da kudin, idan taga dama zagin Shehu ma takeyi shi Kuma Shehu hakuri yake da ita Kawai Sabo da yaranta,duk sabo da yaran data tara yake kyaleta sabo da idan ya koreta ma ya zaiyi da yaransa sannan rashin uwa a zamanin nan ba karamin matsala bane ga Yara shi yasa Kawai yake hakuri,akwai Sanda ma idan Suka Yi fada to da wuri zata rufe gidan idan Shehu ya fita masallaci Sallar Isha ya Sha kwana a masallaci
Ita Kuma bata ganin hakurinsa haka tunaninta Kawai Dan ta Isa ne ko masifarta ce tasa,ya rasa ya zaiyi da ita Kawai ya daina bata ficika Kuma ya daina bata abinci Wai ko zata Yi hankali,wannan talaucin yasa Mama tayi laushi ita da Nusaiba Kawai ta ya zasu ci su koshi suke yi amma gashi Aslam Yana zuwa Suka samu kudi sai wulakanci Kuma Wanda yafi na baya ma,gidanta Kuma da Shehu yace ya siyar ba siyarwa yayi ba gani yayi akan Addua yarta ta bace zata siyar da gidanta yaji tsoro ne Kar ta koma bin bokaye abin bazai Yi da kyau ba shi yasa yayi Mata wayo ya nuna ya siyar da shi,duk wani zalunci sau tari ba zakuntarta yake Yi ba Yana yi ne sabo da nemawa Kansa sauki sai gashi dai karshe sai da ta kaishi ga zaluntar yaransa da matar ma tunda ya hanasu abinci Wanda hakkinsa ne,ita Kuma
Nusaiba tun tana karama zuwa tasha talla da yawan rike kudi shi ya jawo idonta ya bude da kudi da shegen son kudi Idan kaci kayan me talla ka hanata kudi zaka ga rashin mutunci shi yasa takewa Aslam haka ta Saba fada da maza a wajen talla dama mafadaciya ce Kawai dai ita ba Yar iska bace bata bari a kawo Mata iskanci amma talla Yana daya daga cikin abinda ya jawo Nusaiba tafi karfin kowa bata tsoron kowa komai girman mutum ga Kuma gadon su na uwa wajen rashin mutunci da rashin sanin ya kamata,Mama sabo da rashin karatunta shi yasa Bata damu da ilimin yaranta ba.

Nusaiba wankan tarwada ce Kuma ba laifi tana da kyanta dai dai gwargwado baza ace Mata mummuna ba,itama doguwa ce sai dai siririya ce amma ba can ba sannan tana da shape dinta dai dai ita Kuma dama Indai ta samu Kayan kwalliya to Yar kwalliya ce sabanin Siyama da tun tana karama bata kwalliya ita sai dai ta sa Riga da wando Bata taba saka skert ko zani kullum da Riga da wando har ta girma take zuwa wajen gwanjo ta zabo kala kala masu Fadi manya manya hakan yasa aka sa Mata suna Charity tace Begins at home taji ta karba shike Nan sunan ya bita Indai baka ce Siyama Charity ba Babu me ganeta ko kace Siyama sai ance wacce? Sai kace Charity sannan za a gane.
Charity saka Riga da wandonta ya jawo Mata bata samari da yawa sai dai dai kadan amma Nusaiba Kuwa Allah ya bata kowa sonta yake sabo da Yar kwalliyarta,Kuma Charity gata kyakyawa Fara amma Riga da wando yasa ba a zuwa ma wasu ma zaton su Yar Igbo ce in ka ganta haka,Nusaiba Kuwa iyayinta kadai da gwalli Yana jawo Mata samari amma bata taba samun me kudi ba sai Aslam shi yasa Kawai ta aure shi Dan kudin ita Indai Namiji me kyau ne baya birgeta tafi son kudi duk kyansa bata bukata
Siyama Kuwa Samarinta Basu da yawa amma duk na kirki ne masu sonta tsakani da Allah Kuma masu rufin asiri ne kowanne ba na banza lokacin bata son zancen ma aure harkarta takeyi tunda Dangin Hunaif Suka Mata sharrin Yar lesbian ce ta daina kula kowanne Namiji harkarta Kawai takeyi,kowa kallon wata Yar duniya yakewa Siyama ana yiwa Nusaiba kallon mutuniyar kirki,Haka Kawai ma Siyama bata Yi komai ba za a dinga Mata kazafi a layin ana gulmarta musamman samarin layin sun sata a gaba. wannan kenan

Yau Affan yayi Niyyar zuwa gidan su Siyama,Liman ya bashi number Dauda kawun Siyama yace idan yaje ya Kira shine kawun Yarinyar, Affan wata sabuwar Shadda ya bare gal dinki me kyau na manyan samari masu tashe da ji da kansu, Yana furta Siyama...Wai Siyama yo ai naga Sima ma karewa, shiri ya Fara ya sa wani short tight ya matse shi sosai ya kalli Kansa yace yawwa Yana kallon Sandar girma wacce ya matse ta da wando yace ke sarkin rashin hakuri baza ki kunyatani ba ke sarkin son aiki ke dai ayi aiki ko to Kuwa baza ki samu ba kije kisa naji kunya a wajen yarinya yanzu kuwa da na matse ki ai ko motsi bakya Yi ba sarkin aiki lokaci baiyi ba ki Kara hakuri,Boxers ya sake dorawa a Kai sannan yasa wandon shaddarsa ya shafa turaruka kala kala sannan ya saka rigar shaddar wata ita ba milk ba ita arsh ba haka take,hula ya dakko a ledarta sabuwa Kalar shaddar ya feshe hular da turare me kamshi sannan ya sake taje sumarsa tare da wani dan dasa hular a gaban goshi yanda samarin zamani ke yi, Suma gata Nan a baya da yawa tari guda,sajensa zuwa gemunsa ya gyara ya shafa musu Mai me kamshi da spray dinsu ya feshe ya fesawa shaddar Kalar na kaya,sabon takalmi ya dakko shima jaraba kalar shaddar sabo da shi ya zura a kafarsa na Yan gayu yayi bala'in kyau abinka da me kyau da haske domin shi Affan Kalar skin dinsa Kalar ta Yan Latin ce Kamar irin Dan Brazil haka skin dinsa take,hancinsa dogo ne babu wacce zata ganshi ace bai birge ta ba, Fitowa yayi tare da kulle part dinsa ya juyo Yana waya da Abokinsa Sayyeed dan kd yace Ina Kano na kusa karasowa gidanka nan da 30mnt,Affan yace Zan bar maka key a wajen wata idan kazo gidan kace wace Raudat zata baka key sai ka bude ka shiga kafin na dawo,Sayyeed ya amsa da to an gama Yana kashe wayar ya dago Suka Yi Ido biyu da Raudat ta dawo daga wajen aiki ta gaji sosai yau sunyi meeting ogansu yaci mutuncinsu ya bata Mata rai,Amma tana ganin Affan komai ya canja ta manta da bacin ranta gaba Daya farin ciki ya kamata

Bata taba ganin ya Mata kyau ba irin yau kallonta yake yi bata sani ba botin din rigarta ya bude daga kirji ana hango shatin boobs dinta,tana aikin kallonsa shi Kuma Yana kallon kirjinta sai kace maye har sai da ta lura tayi maza ta gyara mayafinta da sauri ya dauke Kai kamar bai gani ba ya basar yace Hajiya Aunty Sannu dan Allah ga key dina ki ajiye a wajenki abokina zaizo zai karba a wajenki karki Yi nisa ai kina gida ko? Raudat ta karba da sauri tace to Inshaallah,yace zaizo ne bazan jira shi ba zance zanje nafi so na dawo da wuri Kar ta gaji da jirana ta ce ta fasa ko ya Kika ce? Raudat nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login