Showing 45001 words to 48000 words out of 85703 words
tace ita a nan zata kwana,Kawu yace rabu da ita bata ji ai,Aunty tace ni a daki Zan kwanta ma can cikin uwar daki,Kawu yace jeki idan baccninta yayi nisa Zan shigo,ai Kuwa Siyama Taki bacci tayi alwala ta saka hijab ta Fara Nafeela ai da tayi raka'a takwas sannan ta zauna saman Sallaya,ga dare Yana yi gashi ko yaushe Kawu ya leka tana zaune a sallaya tana lazimi, window din bedroom din Aunty Kato ne a bude yake dan tsaf mutum zai wuce Siyama tana can bata sani ba tuni Kawu ya haura ta window dama matan aure da iya sanin makamar wayo Aunty tasa kawu ya rufe Mata Baki Kam karma wani sauti ya fita suka gama abinsu ras Kawu ya sake haurawa ta Window ya dawo saman katifarsa Siyama Bata San me akeyi ba tana Palo,Aunty ta gani ta fito tace Siyama gwanar addini a dinga sawa da mu,yau zafin da akeyi yafi na jiya bari na sake sheka ruwa a jikina,Siyama a ranta tace aha yau baza ku Shana ba sai dai ku kwana a haka, Aunty kam Kawu ta zubawa ruwa yayi wanka tare da tsarkake jikinsa Aunty ma tayi Suka dawo Suka kwanta aka bar Siyama bau a Palo har bacci ya kwasheta a nan.
Washe gari Kuwa gani Suka Yi Siyama tana ta kwalimar dakinta ta Masa wani uban gyara na musamman ta kunna turaren wuta ta kulle ko Ina ya dauki kamshi, da Yamma tasan Kawu bazai bari ta fita ba abinda take so ta yiwa Aslam duk bazai siyu ba dole Wayar Aunty ta dauka a boye ta Kira kawar Aunty me yin snacks na gidan biki tana yi ma ana order,tace tayi Mata meet pie me dadin gaske da Samosa sannan ta siyo lemo juice babba ta hado da shi ta bawa yarta ta kawo mata,idan ta kawo sai ta bata kudin ta kawo Mata Suka Yi lissafi tace ana yin Sallar Isha take so a kawo matar tace to ba damuwa
Siyama sai gaf da Sallar Isha ta fesa wanka ta saka doguwar rigarta ta larabawa wata maroon taji ado kawar Aunty ce ta bata da taje aikin Hajji bara rigar tana Mata kyau shi yasa take Adana ta,ta yafa mayafinta taje ta shafa humrar Aunty ta dan zubo wata a Yar karamar kwalaba,Aunty tace ke Kuma Ina Zaki je? Siyama tace to bana fita an hanani fita Kawai sai na bar kayana su rube bana sakawa,Kawu Yana jinsu ya tashi ya tafi Sallar Isha,Aunty ta shiga daki Sallah aka kawowa Siyama order dinta ta karba a boye ta biya kudin Yarinyar Yar budurwa Siyama ta kalla tace ungo kudin kice na gode sauri ki ta tafi bana so Aunty ta sani,Yarinyar ta tafi da sauri,Siyama ta Kai ledar daki ta kwaso plate biyu ta zuba meet pie din da Samosa a plate ta rufe ragowar ta boye a abinta ta ajiye lemo da cup kusa sannan ta fice,sai ga Aunty ta fito da Hijab tace zanje gidan kawata Jamila yarta ta haihu sai 10pm Zan dawo ki kula da gidan,Siyama tace to Kawu fa? Aunty tace baki ji yace yau gidan liman zai je ba abokin babanki ya gayyace shi walima an Haifa Masa yaro ai Kawunki yau sai an ganshi, tana murna dake gidan su Jamila ma ba nisa a layin ne tace Aunty a dawo lafiya tace yawwa ta fice,tana fita Siyama ta fito tayi sauri ta karbi wayar me shago ta shigar da number Aslam ta Kira,bugu daya ya daga ta matsa gefe tace ka taho kuwa? Yace gani a layin ma Sabeer ya saukeni zai dawo ya daukeni,tace kace ya dawo tara da Rabi,yanda tace haka aka yi,tana waya sai ganin Aslam tayi a kusa da ita Yana kallonta,me shagon ta mikawa wayarsa ta Masa godiya Suka jera Suka tafi,Yana faman kallonta yace yau kin Sha kyau haka ni aka yiwa kwalliyar,Murmushi tayi tace ae Suka Shige gidan har dakinta bata kulle kofa ba tasan ba kowa ta kawo Masa pie din da lemo,yace harda tanadi tayi dariya Yana ci yace yayi Dadi kuwa suna ta zuba hirar soyayya abinsu 9:30 Sabeer yazo suka tafi Siyama harda rakashi har cikin mota Suka gaisa da Sabeer ta koma gida ta cinye Su samosarta da lemon tayi Shirin bacci tayi kwanciyarta har Aunty ta dawo.
Haka lokacin na tafiya Aslam duk Sanda yaga damar zuwa sai sun faki idon Aunty da Kawu suke samu su Shige su Sha Hira ya tafi basu taba Kama shi ba.
Siyama ta gaji da halin Kawu tace wlh yau Zan Bari ya kamamu,ai Kuwa Aslam yazo yana dakinta dama da shi aka shirya plan din,bai taba kwanciya a katifar ba sai yau,Suka dinga hirarsu Kamar ba matsala ko an gansu da karfi yanda kowa na gidan Yana ji har dariyarsu ana ji,Kawu Yana tsakar gida daga shi sai dogon wando da Singlet,Aunty ta mike ta zauna tsoro taji ma ko aljanune a dakin Siyama suke Hira maganarsu ta fito fili,Kawu yace Siyama ke Siyama,Siyama Suka Yi kus Kamar ruwa ya dauke can tace naam ta fito har da nuna rashin gaskiya,Kawu ya mike ta koma dakin da gudu zata turo kofa Kawu ya Danna da karfi Siyama tana dannawa amma yafita karfi ya Bude ta karfi ya shiga ya Iske Aslam a kwance sanye cikin shadda Yar ubansu,Kuma ko a jikinsa ko tsoro bai ji ba tunda Yana sani,Kawu ya Fara salati harda rufe Ido ya fito gashi Yana Jin kunyar Aslam sosai bazai iya ci Masa mutunci ba,Aunty ma ta leka ta dawo baya tana salati tace kaga abinda nake fada maka ko da alama ba yau Suka Fara ba na dade Ina zargin Siyama dan Kuwa akwai Sanda takeyin kwalliya ta musamman da dare to gashi ka gani da idonka har cikin dakinta,Siyama ta fito tana kukan karya Dan Allah Kawu kayi hakuri dama Kaine ka hanashi zuwa shine nace ya dinga zuwa Muna buya Watarana ma Sai 2am yake barin gidan nan laifinka ne Kawu,Aunty tace yanzu kaga duk abinda zai faru ma ya faru,Aslam ne ya fito Kamar gidan Ubansa ko ajikinsa Yana takunsa,Siyama tace ai Kaine Kawu.....Mari ya zubawa Siyama sabo da Takaici,Aslam ya riketa da sauri,ta juya Masa Fuska tace tayani gani fuskata Kuwa tana nan,Aslam yace tana nan sosa min wajen,yasa Hannu ya Sosa Mata,Kawu yace Aslam Ina ganin mutuncinka ka sani Allah Yana ganinka,yata ce duk abinda ya sameta Kaine wlh,Aunty ta ja tsaki tace mene ma bai faru ba kana gani dai wlh ka Amince ayi sauri ayi bikin nan tun kafin masifa ta danno Mana gida,Kawu ya tsorata matuka tunda Aslam yake iya zuwa cikin gida har dakin budurwa su raba dare to komaima zai faru,Kawu cikin bacin rai yace Dan ubanki kinwa kanki Babu ke ba kayan daki cokali bazan siya Miki ba,Kai Kuma gobe gobe ka turo manya ka sani ficika bazan kashe ba Kuma babu taro auren bazawara ma Sai yafi naku armashi in Banda Yan daurin aure kar naga uban kowa a gidana,Kuma Babu me Kai maka Amarya ana daurawa kazo ka dauketa,Aslam yafi kowa murna a ransa yace mun Zama turawa Haka ake so ai,Siyama tace Wlh Kawu ba abinda mukayi Wanda ya sabawa Allah,Kawu yace ai tun daga Kebewa da kuka Yi daki Daya Kun sabawa Allah kuci gaba da istingifari Kawai mutanen banza sakarkaru Kai ka girma Namiji ka dinga biyewa mace,Aslam harda durkusawa yace dan Allah Kawu ku yafe Mana,Itama Siyama ta durkusa baza mu sake ba,,Kawu yace kanku kuka yiwa bazan siya Miki komai ba ko tukunya baza a Dora ba,Babu shagali ba gayyata,Aslam yace hakan ma yayi mun gode,karma ku gode ku tashi ku bani waje,Suka juya Suka fice Siyama ta diinga murna,Aslam yace Ni dama ban damu da wani taron Iska ba,Siyama tace shike nan ba anko ba gayyata ta furta da tausayi,Aslam yace nan da sati za a daura kin Zama amarya yau bazan Yi bacci ba, Siyama tace Ina waye ya bani bacci ai sai addua,Aslam yace yanzu an gama yakin karshe ki Fara bawa kawu hakuri lokacin bashi hakuri yayi ai suka Yi dariya ya Mata sallama ya tafi.
Siyama ta shiga gidan harda durkusawa Kawu tace Mahaifina ka yafe min,sai yau Wai zata mahaifinta ta bawa Aunty dariya, tace Kawuna ka yafe min na tuba bazan sake ba dan Allah Kar kayi Fushi dani sai Allah ya tsine min na tuba,tashi ki bani waje Yar banza fitsararriya tunda nace zan bashi ke Kuma mene na damuna,Siyama tace Kawu ka sa min Albarka to,duka ya Kai Mata ta tashi da gudu tana dariya ta koma dakinta sai tsalle da murna harda cewa Babana dake lahira yayanka Amadou Yana rike yarka Amana yanzu,su Kawu suna jinta tana ta hauka iri iri.
Raudat bayan taje gida ta huta suna ta hira da kannenta kanana su biyar da Mamansu,haka Babansu ya dawo daga Office tana murna yace a'a Raudat zuwa haka ba sanarwa tace Papa nayi missing naku shi yasa nazo ranar Monday Zan koma,yace Alright ya aikin naki? tace Alhmdllh Papa na iskeku lafiya yace lafiya lau,ciki ya shiga ita Kuma taje tayi bacci ta huta da Yamma lis tayi wanka ta fito cikin hadaddun kayanta English fited gown ta Sha me dogon hannu,kyau Kam ta Sha shi tayi rolling da mayafinta,hand bag ta dakko ta fito tare da yiwa Umminsu Sallama tace Zan dan zaga gari,Ummi tace to a dawo lafiya ta koma part din Papa tace papa Zan Dan zaga gari bani mukullin farar motarka please yace duba kasan pillow, ta duba ta zaba a ciki sannan ta Masa sallama ta fita abinta kannenta suna Aunty zamu je tace ba Zan je da kowa ba
Affan ta Kira a waya ya Gama bacci ya tashi yayi wanka Yana shiri ta Kira ya daga tace fito mu tafi,kana nan Kaya ya Sha wani wando pencil creazy da shi me kyan gaske sai riga me Fadi Yar sarau sarau bata da kauri daga baya ta zobe baya yafi gaba tsayi Suma Tasha gyara sai da Raudat ta gaji da jira daga cewa Kaya Kawai zai sa ya gama komai Yana ta kalailaitar jikinsa ya gama ya fito Yana kamshi ana taku dai dai da wayarsa me tsada,tun daga nesa take kallonsa yanda ya Sha kyau Kamar a turai,Raudat harda kwantar da kanta a saman sitiyari tana tunaninsa horn tayi kadan sannan taci gaba da kallonsa har ya bude Gaban mota ya shigo,duk kamshin da takeyi nasa sai da ya doke nata,yace Hajiya Aunty,tace dan Allah ka daina ce min Aunty ni bana so ka girmeni sosai ka dinga ce min Aunty,yace alright Yana dariya an gama Hajjaju ta,ta sake kallonsa kamar zata Yi kuka sai kace tsohuwa,yace to Raudat shike nan, tace haka gatsal kuma,yace to me zance? Ina laifin ma kace min Queen,Queen dina my Queen ya furta tayi Murmushi tace naam Affan International yanda taji Sayyeed Abokinsa Yana fada Masa,Dukkan abokansa sai kace Affan International ake ganewa,dariya yayi yace wannan fa Yan school ne suka saka min,Affan International.
International na wanka ko? Yace yes tana driving tace ni Kuma Affan Appointment,dariya ya saki suka je wani hadadden wajen cin abinci acan Suka ci Suka Sha sannan ta Kai shi wuraren shakatawa suna ta yawo cikin nishadi,Affan wani Kara son Raudat yake ji Kamar ya hadiyeta, sai wurin goma ta kaishi masauki baya so su rabu itama haka, Suka zauna a motar juyowa tayi kadan tana kallonsa shima ita yake kallo, hannunta ya rike a hankali tsigar jikinsu ta tashi kasa hakuri yayi tana mazaunin Driver a haka ya rungumeta yace Ina sonki Raudat ya sake kankameta Yana shakar kamshinta,jikinta ta janye yace please ina kaunarki na Dade Ina sonki na kasa fada miki dan Allah muyi aure,Raudat tace kana saurayi Ina bazawara ai bazai yuwu ba Affan International,yace ni ba komai ina sonki haka ba ruwana da wani bazawara Annabi ma ya auri Zawarawa bare ni,Raudat tace ku da samarin zamani ne sai budurwa,dan Allah ki daina fadar haka mene a virgin Ni ke nake so,Raudat tace ka bani lokaci to,zuwa yaushe? Koma yaushe ne in Naga ka cancanta shike nan, Affan yace au yanzu ban cancanta ba sai ma kinyi tunani,ya kalli Kansa yace mene Nawa bakya so ko bani da kyau ko dirina bai Miki ba? Raudat tace wane mutum akwai wacce ta Isa ma tace baka Yi ba,Zan baka amsa ai yace Allah yasa naji Alkhairi tace ameen ya bude mota ya fita tace sai gobe karfe nawa zanzo? 11am lokacin na tashi a bacci,tace gobe zamu je ka gaida su Ummi da safe sai kace ranar zaka koma kaga washe gari sai mu tafi,Affan yace ban gaji ba mu Kara kwana biyu tunda kullum zamu dinga yini tare tace no Monday da aiki yace ni na sanarwa Oga ai farko sati Daya Kika ce,kasan aikinmu ko yaushe za a iya Neman mu,Aslam yace gaskiya gwara aikin gomnati bazan iya barinki ki dinga fita haka yanda Kika ga dama ba,a Haka suka rabu Raudat ana ta murna Kamar zata kashe kanta.
Washe gari Affan harda saka wani yadi me tsada me karamin dinki ya Sha kyau sosai cikin fararen kaya za aje gaida suruki,Raudat tazo a wata kalar motar har room dinsa ta shiga tana shiga ya mike,ya ganta da ledan kayan abinci na take away yace ai na karya Ni naci abinci,a Ina? Yace fita nayi na samu waje tace nace kaje ne da zaka tafi kaci abinci a wani waje Yan garin nan fa Mata mayun maza ne so kake wata ta nace mak..tunawa tayi ta dauke wuta duf harda fuskewa tace hmm to ba komai fito muje gidan namu,Aslam ya fito Yana Murmushi ana kishinsa,katafaren gidan su Raudat suka je dama ta fada a gida wani da suke compound daya zai zo ya gaishe su yazo garin,Raudat har ciki ta Masa iso,Ummi ta fito ya durkusa tare da gaidata tana fara'a ta amsa shima Papa yazo Suka gaisa Yana cewa na gode na gode fa shi Kam Affan ya Masa ya kwanta Masa a rai, Ummi harda Zama ta saki jiki suna ta hira da Affan,shi Kuma an wani nutsu Kamar ba shi ba,kannen Raudat Suka zo Suka gaida shi,last born Dan yaro Affan yace boy zo Nan ya dauke shi yace ya sunanka? yace Irfan,Yana tsokanarsa ya Dan dade har yace zai tafi ya rabawa yaran kudade ya fito Raudat ta rakashi,tace zata maida shi masauki yace da Kansa zai koma shi zai Gane.
Kwanan su Raudat biyar a garin nan suna shakatawa kullum tare da shi suke yini kwanciyar bacci ke raba su,ranar kwana na biyar Suka dawo gida Kano,Raudat tana shiga part dinta ta hau gyara shima haka,ta Riga shi gama aikinta shi ya fita kalailaitar masifa,Yana goge kujeru ta leko ta window ya duka ta wajen saitin windown ta dan yakushi bayansa ta koma ta buya ya duba yaga ba kowa ya koma yaci gaba ta sake lekowa da cokali ta dan karci bayansa ya juyo da sauri ya kamata dariya Suka Yi yace dama naji ajikina kece ai tunda Kika yakusheni ban ji zafi ba naji wani Dadi da shock nasan kece Affan da karya yakushinta ma Wai dadi ba zafu,Raudat har yau bata bashi amsar tana sonsa ba sai aji take ja Masa tun Yana tambaya har ya gaji.
Aisha wannan karon tana hakurin dannewa basa fada da Mahaifiyarta suna zaune lafiya Sabo da sunyi nadama Matukar gaske,aikin gidan kaf kusan Aisha ke yinsa,tana son cikin nan nata duk da uban dan baya so amma ji takeyi da cikin nan,har tayi kyau ta Fara murmurewa, Farooq yayi murnar fitowar Aisha amma yaji haushi da aka ce tana da cikin wani ba nasa ba,Aisha tana ta murna zata samu danta ko ya Kawai tana wanke kayanta dana Ummanta ta Fara zubar da jini,ta tsorata sosai Suka tafi asibiti har da Baban Aisha aka je, lokacin cikin Aisha ya zube gaba Daya har ma sai da aka Mata wankin ciki,sabo da taji jiki kwanan su biyu a asibiti sannan suka dawo gida taci kuka ta koshi sai da Babanta yayi ta Mata nasiha sannan ta hakura,Ciki na zubewa mutane munafukai suka kaiwa Farooq gulmar cikin Aisha ya zube ta wani bangaren yaji Mata ciwo ta wani bangaren yaji Dadi.
Bangaren Siyama kuwa sati Daya Kawai dangi aka fadawa Suma kawu yace ba taro Yan daurin aure ne Kawai zasu Zo,Dangin uwar Babar Siyama ma haka ya fada musu,Babu Wanda aka ce yazo sai iya maza Yan Uwa,shima Aslam ya fadawa Mum, Mum tace amma nayi maka farin ciki son ai gwara ma haka ba sai da taron ba babu komai an gode amma duk da haka ayi order abinci a Kai musu su bawa danginsu Suma mu dai ta bangaren mu tunda dama wannan iftila'in ya fada maka dama bamu da Niyyar taro sai na Yan daurin aure Kawai Nan Suka Yi kulla kullarsu da Mum dinsa yanda baza suji kunya ba,Haka aka tura manya da kudin komai da komai ko Siyama bata sa rai da lefe ba,Aunty dai ta dage tana ta gyara yarta sannan tana zuwa gyaran jiki, Saura kwana uku biki aka kawo lefe sunyi mamaki akwatina goma cif Kaya na gani na fada ba abinda babu,aka dinga zuwa kallon lefen a unguwar,Maman Nusaiba taji labari ta kyalkyale da dariya tace dan karya ne haka yakeyi yanzu ana kaita zaice yaci bashin bank ba kudi sun shiga uku ta sake sakin dariya,Shehu yace kinyi asarar halinki ke dai Kam tir.
Aslam ne ya fito tare da Siyama yazo zance Suka Yi kicibus da Nusaiba mijinta ya kawota a mota ya juya,Aslam bai ma ga ko motar ba lokacin yayi nisa tuni ya bar layin,Nusaiba ansha wanka kana ganinta kasan tana hutawa ko kallonta Aslam baiyi ba ta gefenta ya wuce, har da kallon Siyama tayi dariya tace an kusa cin