Showing 33001 words to 36000 words out of 85703 words
take taji zuciyarta ta dau zafi Kamar tayi kuka dama tunda taga wankan ta firgita,Affan yace Hajiya Aunty ya Kika ce nayi? Kina ganin zata Yaba? Raudat kokari tayi ta danne tayi Murmushi dole tace sosai ma ai yau sai ta kusa Suma Ina tabbatar maka sai tace tana sonka,Affan ya daga Mata babban yatsa ya Bude motarsa wacce ta Sha wanki kal kal tare da shigewa ya bar gidan,Yana barin gidan Raudat kasa tafiya tayi daga wajen bakin ciki da bacin rai yasa ta zauna ragwaf a bakin kofarta ta zuba uban tagumi abin duniya ya Mata zafi tana tunanin bata San Sanda ta Fara hawaye ba har ta koma kuka sosai wiwi,a haka Sayyeed yazo ya samu Raudat yace baiwar Allah lafiya? Raudat da sauri ta tsaida kukanta tare da goge hawayenta tace rasuwa aka min tayi karya,yace Allah yaji Kan rai Dan Allah wace Raudat a gidan Nan?tace nice,yace ashe ma yarinya ce budurwa na zaci Babba ce,Murmushin karfin hali tayi tare da bashi key ta mike ta Shige cikin palonta,tana zuwa ta shiga kitchen ta shirya abinci lafiyayye ta window Sayyeed yaji ana cewa bakon Affan ga abinci,mamaki ya kamashi ganin windows har biyu ta cikin dakunanta suke labile ta janye tare da zuge glass ta Mika Masa tire Kato ya karba Yana kallonta, chocolate ce amma me haske haka Kalar Raudat take kyakyawa ce harda Yar karamar wushiryarta me Yar karamar Fuska jikinta Kuma Kato domin doguwa ce Kuma akwai uban mazaunai da boobs kana ganinta kasan ba karya akwai kudi Hutu da Jin dadin ya ratsata kalarta Kalar yaran Madara ne,Sayyeed dama yunwa yake ji ya zauna Yana ci yana Jin Dadi lallai Raudat tayi yace a ransa gaskiya Ina sonta Indai zata so ni Zan aureta bai San Sabo da Affan ake Masa tarbar ba,window ta sake budewa ta Miko Masa fruits cikin wani bowl ya amsa yace thanks,ta rufe window din,kitchen ta koma ta Fara tunani me Zan bashi ne ya Kara ta shiga tunani sai Kuwa ta bude fridge ta zaro kaza me kankara tayi melting kankarar sannan ta dora farfesu ta shirya shi me Rai da lafiya me dadi kadan ta ragewa kanta ta zuba Masa a flask me kyau da tsada ta sake komawa ta bude window tun kafin ma tayi magana Sayyeed ya Miko Hannu tuni Yana dariya,itama dariyar tayi ta bashi ya karba Yana godiya,yaci ya bar wani ya rufe cikinsa sai da ya cika dam sannan Raudat ta tafi ta gyara gidanta tayi wanka tare da chakarewa cikin Riga da skert na wata sabuwar Atamfa me tsada shape ya fito komai cas da ita Kamar a saceta abinka da Yan gayu wayayyu compound ta fito tana jiran dawowar Affan itama Wai yaga wankanta,Wajen Landlady taje Suka fito compound suna Hira abinsu amma hankalin Raudat yana Hanya.
Siyama Kawunta ne ya kirata yace Siyama zo,har dakinsa ta shiga tare da durkusawa tace Kawu gani yace Siyama Kar kiga Kamar na takura miki,Babanki mahaifi Yana da babban Amini Mai suna Mallam Arifullah,amininsa ne na gaske duk duniya bai da aboki sama da shi tun ainihi liman ne me tarin ilimi Yana da matan sa biyu da yaransa Tara,Bayan babanki ya rasu duk wata sai ya kawo Mana Kayan abinci har Kika girma Kuma tun kina karama duk shekara sai ya Miki dinkin Sallah kala biyu nasan kin sanshi ma Zaki ganeshi domin Yana zuwa gidan nan sosai mutumin kirki ne,Siyama tace na ganeshi Kawu har nake ce Masa Liman amma me kudi,yace yawwa kin gano shi Yana da arziki sosai to shine dai yace Yana da wani yaronsa Wanda ya yaba da nutsuwarsa da tarbiyyarsa me zai hana idan Kun dai daita kuyi aure Kar kice na takura Miki,Siyama tace kawu ya kake Abu Kamar ba Kawuna ba nasan ai baza ka cuceni ba ko,Kuma baza a min auren dole ba sai idan na Amince yace hakane Siyama tace to ba matsala yazo,Kawu yace dan Allah karki watsawa Mallam kasa a Ido Yana kaunarki Yana kaunar mahaifinki,Siyama tace to ita Kam duk duniya bata ga Kamar Aslam ba,duk shi bai nuna Yana sonta ba ya zata yi gwara idan ta samu mijinta Kawai ta aure shi ta huta.
Wanka tayi da kwalliya cikin leshinta me kyau na bikin Nusaiba da tasa Aslam ya dinka mata da shi taci kwalliya ta Sha kyau ta zauna tana jiran Wanda aka ce zai zo.
Affan ne yazo har kofar gidan da motarsa cikin wankansa shi duk gidansu bai dame shi ba yasan shima a baya talakan ne sosai shi yaga ma gidansu da kyansa ba laifi ba ruwansa da wani talaka da Mai kudi duk Daya suke a wajensa,Wayar Kawu ya Kira Suka gaisa yace ya karaso,Kawu yace Siyama yazo Yana kofar gida shigar da shi dakin zaure tace to ta mike ta yafa mayafinta sannan ta fita cikin takunta me kyau,Yana cikin mota ya hangota ta fito ba karya tana da kyau ta hadu ta Kai a so ta amma shi Kam gaskiya wankan Raudat yafi Masa kyau gwara ya kalli Raudat sau dubu,Dake Affan yasan mutunci Fitowa yayi daga motar da gayunsa ya amsa sallamarta,tayi Murmushi tace ka shigo ya bita Suka shiga palon Wanda ba komai sai red carpet dake malale a kasa, Affan baya son Zama a kasa Kar kayansa su yamutse haka ya hakura ya dan dosana duwawunsa,Ruwa da lemon da Kawu ya siyo taje ta kawo Masa sannan Itama ta zauna can gefe,Ina yini tace,ya amsa lafiya Alhmdllh ya mutan gida tace lafiya lau,yanda taga Yana kwalisa bata zaci mutunci haka daga gare shi ba, Affan bai son wulakanta dan Adam shi Kam,baiyi zancen soyayya ba bare zancen aure,bai ma Yi zancen Liman ba Kawai Yana duba wayarsa ya dago Suka hada Ido da Siyama wayarsa aka Kira ya daga Wanda yake siyen shadda a wajensa ne yace ka duba WhatsApp na turo maka da latest,Affan a waya Suka dinga labarin wanka da gayu ita dai Siyama tana ji har ya gama ya duba chat ya gansu zuka zuka,ya nunawa Siyama yace Kinga colors tayani zaba,Siyama ta leka Wayar ta nuna Kalar ta Mata pink tace wannan color yayi,Affan yace ke baki San Kalar maza ba na Mata Kika sani matsa can gefe
Siyama tayi Murmushi ya Gama zabensa pink din data dauka a ciki ya sake nuna Mata yace sai wacce color Kuma? ta sake zaben dark blue,yace sai kace Dan fulani sukayi dariya bai dade ba ya mike yace zai tafi har sun Dan Saba ta rakoshi jikin mota kenan yace me color din Mata sai Watarana kuma,tace to ka gaida gida na gode tana Murmushi dai dai lokacin Aslam ya karaso kofar gidan a motar Sabeer ganin ya fito Gaban Siyama ya Fadi Haka Kawai taji kunyarsa da tsoronsa ya kamata tana zance,kallon Affan yayi Kawai Aslam ya bata rai ya daure Fuska tam juyawa yayi ya koma cikin mota yace Sabeer muje kawai,Affan bai sani ba ya zaro kudi dubu biyar yace gashi ki sa Kati bai San ko waya Bata da ita ba,Aslam ya kura musu Ido gashi Yana yiwa Sabeer masifa muje dalla malam
Siyama kin karbar kudin tayi Affan yace mene haka Kuma bana so nayi kyauta a maida min,Siyama juyawa tayi Kawai ta Shige gida duk ta firgice ta tsorata, Affan baki ya tabe yaja motarsa ya wuce,Aslam tuni sun tafi.
Siyama tana komawa gida tace kawu ya tafi Aunty na dawo Suka ce to sai bayan Isha Kya bamu labari tace to tare da fadawa dakinta ta kwanta akan katifarta ta fashe da kuka Wai Aslam ya ganta tana zance har da cewa na shiga Uku na shiga dubu tana rusa uban kuka Kamar wacce aka Mata mugun duka,Aunty ce taji kukanta ta fado dakin da gudu tana cewa me Zan gani Siyama lafiya? Saurayin ne yaci Miki mutunci ko me? Marinki yayi? Siyama tace shike nan tawa ta Kare na gama yawo ta sake sakin kuka tana shesheka tace Aslam ne Aslam,Aunty tace mutuwa yayi? Siyama tace Aunty Aslam Aunty wash...shike nan Aunty Aslam ya kamani ya ganni Ina zance Innalillahi, Subhannallahi,Ashahdu Allah ilaha illallah ta Dora Hannu aka tace Aslam kuru kuru ya ganni,Aunty Tsaki ta ja tace ke dalla rufe Mana baki mahaukaciya amma dai sonsa kike dama ko? Charity tace Mijin Nusaiban haba Aunty mijin kawata kuma abin kunya ne ai,Aunty tace to rufe Mana baki sakarya, Kawai ki Fara Mana kuka sabo da rashin aikin yi,Siyama tagumi ta zuba tana goge hawaye ta kasa tashi Sam sabo da jimami.
Aslam kuwa suna tafiya Sabeer yace zamuje park din? da masifa ya furta ka kaini gida Malam Babu Maganar park din banza kaini gida gwara nayi tunani me kyau na huta,ka fasa zuw...bazan je ba karka dameni ya furta da masifa,Sabeer yace kaga nifa bani naje zance wajen Yarinyar Nan ba bare kace,to ni nace maka naji haushinta ne Ina ruwana ta kula maza dubu ma Ina ruwana,Sabeer dariya kawai yayi Yana tukinsa yace tana da saurayinta kana ganinsa dai sharr da shi gwara ka auri Nabeela, Allah ya kiyaye na auri sakin wawa Nima fa sakin wawan nayiwa wata nasan me tayiwa mijinta ya saketa ba duk bazawara ce ta kirki ba gwara wacce ma mijinta ya mutu amma Wanda ake sakowa na tsorata da su wa yasan me Suka aikata aka sake su,Sabeer yace wallahi akwai Wanda laifin mazajensu ne,Aslam yace ae naji naji bana so bata min ba ni da wata kafarta a gwame,nufinka idan ta sa min riga da wando haka Zan na ganin Ball leg dinta sun kantare,Sabeer dariya Kamar me yace yaushe kaga kafafunta maye yanzu har ka San tana da Ball leg? Kwarai kuwa ko zaka ce karya ne? Sabeer yace tabbas wlh ba musu lallai mutumin auren Nusaiba ya sake gogar dakai da ko kallon Mata baka yi,Aslam yace dan Allah ka kyaleni bana son surutun me gwamammiyar kafa dai bana Yi karka sake min zancenta ana Neman macen kirki kana kawo min bage,Sabeer yace sorry na Siyama yana dariya,ance maka son Siyama nake Yi wai nifa ban shirya aure ba ku sani ma ya furta Yana turo jajayen lips dinsa yace kaini wajen Mum ma gwara na ga uwata na huta da duk wata ya mace.
Wajen Mum suka tafi can Suka zauna har dare Mum har ta Fara damun Aslam cewar ka Nemo Mata ta gari Aslam gashi ma Kai naga Kamar baka da niyya Wanda hakan hatsari ne ga duk namijin da ya taba aure bai dace ya zauna ba Mata ba ka dinga dubawa kaji,to Aslam yace kawai.
Affan kuwa akan idon Raudat ya shigo da motarsa gidan tana tsaye ta juya baya ita da Landlady suna hira ya wuce da mota abinsa Yana yin parking ya fito Raudat tana kallon inda yake fitowa,part dinsa ya Shiga da sauri,Raudat ta sauke ajiyar zuciya ta Shige part dinta ita ma,ai tana Shiga ciki taji suna tafawa da Sayyeed suna magana Affan yace Kai Kuma wannan tarkacen flask din da tire Ina ka samo su? Sayyeed yace ai baka sani ba budurwa nayi Raudat ce ta dinga Miko min ta window ashe windown ku daya, Affan yayi dariya yace Kai dalla ba sonka takeyi ba mutunci ne da ita Haka take da kirki ita tana ma da mijinta matar wani ce aiki ya kawota weekend take komawa gidanta, Sayyeed ya zaci da gaske ne yace eyya na hakura gwara da ka fada min,ai Kuwa tana da kirki kalli girki ya shiga budewa Affan Yana kallo,yace ta hutar Dani dama da tunaninka na dawo na nema maka abinci,Raudat tana jinsu suka hau Hira Sayyeed har yayi wanka Affan yace ko zamu fasa gari ne?Raudat ta Riga su fitowa ta tsaya kamar zata Shiga motarta,Affan ya fito tare da Sayyeed,Affan yace Hajiya Aunty fita zakiyi ne? Tace ae Ina son fita amma bana son driving din na gaji,Affan yace muje to Mana na kaiki ni Naga yanda Kika karrama abokina na gode fa,Hmm ba komai cewar Raudat zata Shiga Bayan motar Affan yace shigo gaba Sayyeed sai ya Shiga baya shi,Sayyeed ya Bude baki matar wani Kuma Affan yace Kawai dai Sayyeed ya Shiga Bayan mota,Affan ya tashi mota Suka wuce Raudat bata San inda zata je ba,Affan yace Ina za a kaiki? tunawa tayi da wata kawarta da suke aiki waje daya wata Hafsat ta nuna Masa gidan har ya kaita kofar gidan Hafsa yace yaushe za a zo a daukeki? Raudat tace sai 10pm,Affan ya zaro Ido yace haka Kawai ki zauna a gidan wata matar tana da aure fa har goman dare ki takura musu idan mijinta Yana son yayi Yar harka fa gaskiya bai dace ba,Raudat tana dariya tace to karfe nawa Zaka dawo? Yace gaskiya 8pm Haba kina mace a dinga sakaki dake bazai yuwu ba,To sai ka dawo cewar Raudat yace yawwa 8pm ki shirya har ta juya yace Aunty ta juyo da sauri yace ba ruwanki da mijinta sawunki a likkafa ki dauke idonki dan mazan yanzu ba mutunci gare su ba wlh sai yace Yana sonki ato ki kula Kar azo kawa ta nada Miki duka a gidanta irinku Aunty sai kusa mijin wata ya kifa yaci ta ka,Dariya Raudat keyi yace gaskiya nake fada Miki ki Kama kanki ba ruwanki da mazan wasu,Raudat tace to sai dai ka dawo ta juya ta Shige tana dariya,Affan sai da ya daina ganinta sannan yace da Sayyeed Kai katon gardi dawo gaba Kuma wallahi karka sake muna kwance ko yatsanka ya taba min fatata nasan baka iya kwanciya ba na tsani jikin Namiji ya taba Ni da ace dai macece aha wannan is okay Sayyeed ya koma gaba yace nasan halinka ni a Palo ma Zan kwana Kuma kaji tsoron Allah kana kula matar wani,Affan yace ai mun Saba da ita, Sayyeed yace naga alama dalla karka Raina min hankali let's go,Suka tafi yawonsu.
Tun kafin 8pm Suka koma gida da kayan ciye ciyensu ya bar Sayyeed ya sake zuba wankan 3qtr da riga me gajeren hannu farare ya tafi dakko Raudat,8pm dot yayi horn dit dit Raudat taji ta shirya tare da yiwa Hafsat Sallama,Hafsat ta rakota tare da mijinta har mota ta Mika Mata turarukan wuta masu kyau a Leda,Affan ya kalli Raudat kadan ya juya da mota Suka hau kwalta sannan yace mijinta har da rakiya Ina ruwansa dake Kai wasu mazan ma Sai a barsu gaba Daya wasu rako Suka yo,Raudat ana ta Jin dadi har da narkewa a jikin mota taki magana ta rasa yanda zata Yi sabo da murna,yace naji kinyi shuru? Raudat ana wani tararrabewa an samu waje tace kaina ke min ciwo a ranta tana istingifari da karyar da ta shararo, Sannu ya furta tace yawwa,yace a tsaya a siya Miki paracetamol? No ta furta Ina da shi a gida yace sai a kyaleki kina cuta Kuma, yayi parking bakin wani chemist ya shiga ya siyo Mata paracetamol da ruwan roba ya dawo dauke da Leda a hannu daya hannun a aljihu Yana taku dai dai yana zuwa ya Mika Mata yace Sha,ai Raudat tabara ta fara tace bana son magani Allah,yace ashe Kuwa baza mu koma gida ba a nan zamu zauna harda gyara parking,farin ciki yasa Raudat ta Kara narkewa tace please kayi hakuri,Affan tsigar jikinsa tashi takeyi idan tana Masa Shagwabar nan tana tuna Masa da Nabeela,Murfin robar ruwan ya balle ya balli paracetamol biyu ya zuba a cikin murfin ya dan zuba ruwa ya wani narka maganin sai kace zai bawa dan yaye yace tsaya na baki to Yana kallonta,sabo da shine zai bata kalau take amma tace to tayi wani kasa da kai lagaf, Hannu yasa tare da dago kanta a hankali harda cewa haa ta bude ya zuba Mata ta shanye ji tayi kamar ta Sha alawa sabo da shi ya bata, ruwa ya bata a baki ta shanye abinta ta wani kwanta a saman kujera Yana cewa sannu yaki tashin mota sai data kwashe 30mnt tace naji sauki har na daina ji sannan ya yiwa motarsa key
yace me kike son ci? tace Ice cream ai Kuwa ya tsaya ya siya Mata wata katuwar roba guda biyu da su yogourt me sanyi ya dawo ya leko ta windown ta yace abinci fa ranki ya dade Hajiya Aunty? tace naci a wajen Hafsat,duk da haka sai da ya siyo Mata tsire lafiyayye sannan ya shiga mota Suka tafi, ana tafiya tana Shan ice cream dinta Yana driving yace ni bazan Sha ba? tace Sorry gashi yace tuki nake ai tace to sai munje gida,yace ki bani a Baki ,Ido Raudat ta zaro taji kunya tace bazan iya ba,yace kaji locality me nake ji ba dadi haka sai kace wani suna Siyama,dariya tayi taki bashi bai ce komai ba har ya kawota gida tayi godiya ta wuce part dinta shima ya shige wajen Sayyeed,tana zuwa tayi sufa akan gadonta tana tsalle da murna.
Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan bana