Showing 18001 words to 21000 words out of 85703 words
kaina na ganka kato,yace haba,? Tace Allah da karami nake ganinka, dariya sukayi Siyama tace Kara sa key na uku a fito da mota,Aslam ya bubbuga kofa gam gam hankalin su Nusaiba ya sake tashi yace a fito da mota,abinda zai muku zakuyi mamaki idan baku fito da mota ba cewar Charity tana taya Aslam Kamar kanwarsa.
Sai zuwa Safiya Aslam ya Bude kofa zai Basu abinci Nusaiba ta kwada Masa tsinin takalmi choge Nan take ya dafe Kai ya Fadi kasa a sume ga Charity bata kusa da gudu Nusaiba da Mama Suka fice daga gidan suka tafi wurin siyar da motoci zasu karbi kudi babu Wanda ya karbi mota ba alamarsa Suka tambayar duniya akace ba a sanshi ba Ashe Dan damfara ne barawon mota Kuma ya gudu da mota,Nusaiba sai da ta Fadi har kasa sabo da kudin ta gama kasafin su,ba kunya suka tashi Suka koma gidan Aslam,lokacin Charity ta shigo ta kwala ihu ganinsa a kwance jini na zuba ta Kansa da gudu ta fita ta samo wasu maza biyu Suka taimaka Mata aka sashi a mota taxi zuwa asibiti,Allah yasa Babu matsalar kirki dressing Suka Masa bayan ya farfado suka dawo gida Kansa nade da bandage Charity tana Masa Sannu sannan tana bashi hakuri har Maman Nusaiba ta shigo da gudu tana kuka tace Nusaiba ce ta Sume,Siyama ta rude ta fita taga Nusaiba a sume tayi suman karya sun hada wayo,Aslam ya fito shima da Kansa ya dauki Nusaiba Kamar bai gano su ba ya shigar da ita bedroom ya kulle ya sake sa key yace sai ta fito min da motata,Mama da tana murna Aslam ya yarda da karyar su, yace Mama tun kafin na dakko bindiga ki bar min gida,Mama da gudu ta fice daga gidan,Charity tace dan Allah kayi hakuri haka tunda motar nan sun riga sun siyar,Nusaiba tana daga ciki a kulle ta saki kuka tace wlh dan damfara ne ya gudu da kudin,Aslam saman kujera ya zauna cike da bacin rai sai da yayi kwalla sabo da bakin ciki yanzu ya tabbatar Kuwa siyar da motar tayi,yana so ya siyar da su ya biya banki kudi yanzu ta salwantar da motar gashi tafi kowacce tsada,hawaye ne ya zubo Masa Sabo da bakin ciki wannan wacce irin kaddara ce haka,tashi yayi Kawai ya sa key ya bude Nusaiba ta fito tana kallonsa tace akan wata tsohuwar mota harda kwalla lallai ka cika me son kudi Kan bala'i,waccen irin marar Imani ce ke Nusaiba Charity ta furta ranta a jagule ashar Nusaiba ta dura Mata ta haura sama tana Jan tsaki tana cewa akan wata banzar tsohuwar mota.
Cikin kwana uku Aslam ya tattara komai na kadara ya damkawa bank gida Kawai yake jiran ranar da zasu zo,Mum ma dubu dari Uku ta turo Masa daga can kasar da take Qatar, wasu kayan girkin ma babu a gidan yau Charity ta rasa me zata dafa kwata kwata tana Jin kunya Kuma a halin da yake ciki ta tambayi wani Abu Kawai sai ta dafa wake da shinkafa da Mai da yaji,ta shiga tayi wanka ta canja cikin doguwar rigar tsohon leshi tayi kyau gata kyakyawa komai yaji,tana Fitowa ta iske Nusaiba an Sha gayu cikin wani tsadajjen material tana latsa waya,Aslam ne ya fito sanye cikin kayan Shan iska Gajeren wando da Riga me gajeren hannu sky and white yayi kyau sai dai ya dan rame sabo da matsalar da yake ciki,Siyama tace Yaya Aslam na gama abinci amma wake da shinkafa na dafa da Mai da yaji,yace oh da kin fada min ba abubuwa na manta wasu abin sun Kare da an siyo ai Allah bai hanani kudin cefane ba ai ni na manta ke kuma baki tuna min ba,Charity tace bana so na takura maka ne ban San halin da kake ciki ba,thank you ya furta,Nusaiba ko kallon su Bata Yi ba tana Danna waya sai ma tabe baki da tayi,Siyama tace amma Ina ganin da kifi zaka fi iya ci,dubu Daya ta isa? ya tambaya tace ae ta karba,Nusaiba ta ja tsaki tana kunkuni Dan karya anzo gidanmu da motocin aro ana nuna kudi an kawo Ni tankamemen gida Ashe duk na aro ne daga yin aure cikin wata uku za ace komai ya Kare bank ya cinye kudi dama ba gaskiya bane duk kayan aro ne.
Charity ta kalleta Kawai ta yafa mayafi ta fice ta siyo salat da tumatir da kudinya ta siyo kifi manya soyayyu ta dawo ta iske Nusaiba inda ta barta ta samu Aslam a dining Yana jira,a gurguje ta yanka salat da tumatir da cucumber ta wanke ta kawo Dining,tana zuwa Nusaiba ta taso ta zuba abinci tasa Mai da yaji ta barbada Maggi zata kwashi salat Charity ta rike hannunta tace kinyi kadan yarinya wannan ba kudinki bane sai ki bari sai na zuba Miki,Nusaiba tayi zuciya ta mike tace bazan ci ba na fasa cin abincin gaba daya,Wacce Nusaiba ta zuba Charity ta ja gabanta ta saka kifi da Salat sannan ta zubawa Aslam shima da kifi da Salat ya fara ci,Nusaiba Kuwa ta WhatsApp tace anjima Sufyan saurayinta yazo ya kaita zata ci Dinner a restaurant da rawar jiki yace an gama.
Aslam Yana fita Sufyan yazo da Yamma likis Nusaiba ta dauki wanka har bakin gate ya dauke ta ya kaita hadadden wurin cin abinci,Suka ci Suka Sha harda ciko Mata Leda da snacks Suka dawo har bakin gate ya sauketa Suka Yi sallama,lokacin Aslam bai dawo ba a taxi ya fita Charity tana kallonta basu kula juna ba.
Bayan kwana biyu Aslam Yana gudun Kar azo a musu wulakanci Nusaiba tana gyara kayanta yace Baby ki shirya gobe zamu tashi daga wannan gidan zamu koma gidan Dana Kama Mana haya,Wani Takaici ya kama Nusaiba,Aslam yace kaddara ce kiyi hakuri kinji,Kuka Nusaiba ta rushe Masa da shi tace ka cuceni da ka min karya na aureka,me yasa baka da Imani burinka ka jefani a wahala,Aslam yace kiyi hakuri,ranar kwana Nusaiba tayi tana kuka dama yanzu bata bashi hakkinsa ta daina tunda taji ba kudi ta daina yarda da shi Watarana sai yayi Kamar zai Mata kuka take yarda da kyar.
Washe gari taxi ya Nemo Siyama ta fito da kayanta itama ta sa a Bayan mota,Dukkan kayan sawarsa da na Nusaiba mota guda aka Yi aka Kai gidan,kayan abinci da komai aka kwashe da abin bukata sauran duk a gidan aka bari,kayan kitchen na amfani duk ya tattara komai ankai,Nusaiba tana hawaye ta fito ta Shiga taxi ya zauna a gefenta Charity tana gaban mota,mota na tafiya Nusaiba tana hawaye tana cewa babu ac ne tana fifita da hannu,Siyama ta furta Aslam Wanda ya Saba da ac baiyi complain ba sai ke sama ta Kai da can kin San ac din ne, ki min Shuru munafuka cewar Nusaiba.
Hanky Aslam ya mikawa Nusaiba ta dauka da bala'i ta jefar,wata unguwa Suka Isa wacce ta masu rufin asiri ce da talakawa a Kano,wani dan karamin gida ne Wanda na bulon siminti ne gidan hayane Wanda ke dauke da Palo da one room kacal sai toilet da kitchen shikenan gidajen haka suke a jere iri Daya sun Kai guda goma wani me kudi ya Gina yake zuba Yan haya,Yan makaranta ma sunfi yawa a wajen Sabo da irin kankantar gidajen,Nusaiba taki Fitowa daga taxi tana kuka sai da me Taxi ya daka Mata tsawa,dama an diga an kawo kayansu duka, Ciki Suka shiga kujeru ne a palon matsagaita amma masu kyau ne sai karamar plasma tv,dama duk tiles ne har dan tsakar gidan,bedroom din Kuma gado ne shima Kalar kujerun da labile Kalar komai kala Daya Kamar wani gidan Yar maryar talaka,kitchen Dan kut da shi,Yace ki daina kuka ki shirya kitchen,Nusaiba ko kulashi bata Yi ba Siyama ce ta shirya Kaya ta gyara komai har bedroom din ta shirya sannan ta dauki jakar kayanta tace Yaya Aslam na tafi sai na sake leko ku,Yace dan Allah ki dinga dan zagayowa, Inshaallah cewar Siyama,Ya bata dubu biyar da kyar ta karba Dan Kawai bata da ko sisi ne,a nan ta bar Nusaiba a zaune tana shirga kuka.
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️
31-35
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne
BK
MMN MUNIBA
HAFSA ABDULLAHI
Kallonta yayi tana ta kuka shima yayi shuru ya gaji yace kaddara ce ta afka min ba haka naso ba ki daina wannan kukan daga karshe ya tashi ya fita abinda Babu na ci ya siyo musu ya sake zubawa a kitchen amma Nusaiba ko kallonsa bata yi ba har azahar tayi lokacin yace kin San dai lokacin Sallah yayi ko,kanta ta dago idonta jajir ta watsa shi a saman fuskarta,tashi yayi tare da daura alawala ya fice ya barta nan tana zaune sai da aka idar da Sallah sannan ta iya tashi ta shiga bedroom din ta jefa hand bag dinta saman bed din ta shiga toilet tana Jan ajiyar zuciya kamar wacce aka nadawa duka.
Siyama Kuwa tana komawa gida ta shiga da sallama Aunty tace ba dai an koroki ba? Siyama bata boye musu ba ta Basu labarin komai Aunty tace amma Nusaiba ta bata wayonta ka samu miji haka irin mijin Novel zukeke ga kudi amma ta dinga irin wannan rayuwar gaskiya na tausaya Masa shike nan zauna mu koma siyar da alalar mu inda Muka fi wayo amma Nusaiba ta bani mamaki samun miji haka,Dauda yace to anji kin damu mutane da miji kyakyawa ne ni bani da kyan ne?kina ta wani yabon mijin wata ga naki amma baza ki yabe shi ba,Siyama tace to ai Kaine Kawu lebe Kamar sakatar kofa,zanci Ubanki Dan ubanki lebena ne kamar sakatar kofa? Siyama ta sake cewa ba lebeba hakora kamar goslow a hanyar Lagos wasu sun taho ta nan wasu ta can,Dauda yace Zaki ci ubanki ni ba ubanki bane Zaki dinga maida Ni kakanki ki kiyayeni wlh,Aunty tayi dariya tace gwara da yarka ce ta fada da nice cewa zaka Yi sai kaci mutunci na
Mama ce a zaune tana waya da Nusaiba tace me nake ji Haka gida daki daya chab dama karyar tasa ta Kai haka,Bari dai sai nazo ta furta lokacin Shehu Yana gida kusa da Mama a zaune,yace Wai ke me kike nufi ne? Nusaiba kin hanata sakewa naji labari jiya Ameer ya fada min komai yanzu tsakani da Allah ki kalli gidan nan da a kuntace muke amma yazo ya Kara Mana dakuna ya Bude Miki shago bafa ni ba ke ya budewa shago ya bani jari Kuma na koma kasuwa sosai ya auri yarki yanzu tsakani da Allah dan karya zai iya yin wannan taimakon,a tunanina ke me yiwa Nusaiba fada ce ashe ke kike zugata, Babu abinda zaka fadamin Shehu dakata kana ciyar damu?, Tunda na taso a gidanka wahala nake Sha Ni da yarana,Sanda Ina da hali ba kece kika cinye kudin ba suka Kare Kika tsaneni komai nayi Miki ban birge ba ya Zan Miki face na zura Miki Ido ke da yaranki tunda kince ba abinda nake tsinana muku,Hakkin Yara a kanka yake kwarai kuwa na sani amma idan na baki kudin cefane kina bari ki basu abincin ba kadan kike dafa musu ba ki siyar da sauran komai na baki siyarwa kike yi,Mama tace to ka kyale min yata ba ruwanka yace Ina da hakki na fada Mata gaskiya,yanzu bazan magana ba tunda bai kawo kararta ba amma duk Sanda ya kawo Kara Nusaiba zata Gane kurenta auren me kudi hauka ne da arziki da talauci duk na Allah ne Kuma wlh kuji tsoron Allah ya mike tare da sa takalminsa ya fice.
Mama Kuwa Ameer ta samu ta balbale shi da fada akan me zai fadawa Shehu.
Charity Alalarta taci gaba da yi amma yanzu tallan ma bata fita ake zuwa a siye a gida,Nusaiba tunda Suka koma gidan haya bata girki ficewarta takeyi su hadu da Sufyan saurayinta a restaurant in taci ta koshi ta dawo gida,Aslam da Kansa yake dafa ma Kansa abinci bai iya ba amma haka zaiyi jagwalgwalonsa ya ci,yau da Yamma Siyama sai gata a gidan sanye da hijab har kasa da Leda a hannunta tayi sallama ta shigo Murmushi ya saki shi ta iske a palo yace manyan kasa ne yau a gidan, Charity dariya tayi ta rusuna tare da gaida shi ya amsa,Ina matar fa? Ta fita ta tafi gidansu yace,Siyama tace okay dama abinci na kawo maka ban sani ba ko tana girkin,yace wow na gode Kamar kin San yunwa nake ji,ledar ta Bude ta dakko abinci a robobin take away har kala biyu tace kaga wannan Fried rice ce dazu Muka Yi da Aunty wannan Kuma tuwon shinkafa ne miyar Egusi,Kawuna nane ya samu kudi shine yau Muka ce bari muji Dadi kaci kaji da Dadi harda nama,mikewa tayi ta dakko spoon a kitchen tace gashi ya karba Yana kallonta cike da mamakinta tafi matarsa sau dubu,Fara cin abincin yayi gaskiya yayi Dadi ya furta Yana ci Siyama tana Kare Masa kallo,kallon fuskarsa takeyi Yana ci har ya cinye daya ya Sha ruwa pure water yace dayan sai dare tace to,Charity ta tura dayan kasan kujera tace gashi a nan na boye maka Kar marar Imani tazo ta dauke,dariya yayi yace na gode ta hada ledarta da roba tace tafiya zanyi tunda bata nan, yace da wuri haka kiyi zamanki ki tayani hira dama na gaji da kallon film,tace to ta zauna tare da tambayarsa har yanzu baka samu aiki ba ka fara?
Ae yace Mata amma Ni da abokina Sabeer Muna ta fafutukar nema ko za a dace, Charity tace to Allah ya kawo tana Jin kunya tana satar kallon Aslam ba karya ya hadu gashi Kamar balarabe fari tas ita Kuwa ja ja ce, gidan ta kalla kaca kaca tace gidan naku yayi dirty yace a haka ma Ni nake sharewa,mikewa tayi ta hau shara ta gama tayi mopping ko Ina ta gyara kitchen,toilet din ma ita ta wanke musu ita kal kal ta dawo Palo ta zauna suna kallon film game yakeyi a wayarsa ps tace game kake Yi? Yace kin iya ne? Tace ae na iya wani abokina ne Hunaif yake bani wayarsa Ina Yi,yace ko dai saurayinki ne? Dariya tayi ya kalli kyawawan hakoranta reras gata kyakyawa sosai tace ya taba cewa Yana so na danginsa suka hanashi sabo da Ina saka riga da wando Wai Yar Lesbian ce ni,Dariya Aslam yayi Yana latsa waya yace ai maganinki kenan da kike saka riga da wando ke ba a kudu ba kin San wani Yana kallonki shedar da zai Miki ta banza shi yasa ake so a dinga kiyaye shiga,da shiga ake Fara gane mutumin kwarai ga sunanki Charity kowa Charity,Siyama tace ai Riga da wandon ne yasa a unguwa aka saka min suna Charity idan na nuna bana son sunan anfi kirana da shi that's why na karbi sunan Hannu bibiyu,Riga da wandon ma kana ganinsu manya manya nake sawa bana saka damammu Kuma yanzu na rage sakawa tunda nake Yana damaging Image dina,yace yawwa ko ke fa ai yafi amma dole ace Yar lesbian ce tunda barma barma kike sawa Kalar na maza,dariya ta sake Yi akwaita da fara'a,tace Allah ya tsine musu wlh masu lesbian ga maza can suna nema Mata suna musu mugunta,dariya Aslam yayi ba shiri yace Charity kenan ke kam ba ruwanki da boye boye kamar Yar kudu haka kike Charity tace idona ne ya Fara tsikewa da duniya mu fa Yan talla ne iya shege ba Wanda bama ji,sai da na Fara talla na gano illar barin ya mace tayi talla
Kaga idan mace tana talla ko wanne gara Wanda ko a Hanya Bai Isa ya Miki magana ba idan kina talla kowa zai kulaki ko wanne gaja ne Kuwa,sannan akwai Wanda a hanya bai Isa ya iya ko magana ba Amma sabo da talla zai fada maka Maganar da yaga dama,sannan me talla kowa Yana da lasisin da zai Mata magana ko a dinga tsokanarta ko wani ma yaci Mata mutunci,mace me talla Namiji zai iya janta da zancen banza ya ja mayafinta ya daketa wani ya mareta wasu Kuma duk Magana ta banza yarinya tun tana karama Matukar tana talla za a dinga Yi a gabanta,tunda waje ne na maza idan Suka taru akwai kalaman banza da bai dace taji ba amma za a dinga Yi a gabanta wasu ma su dinga janta da Harkar banza irin wannan ke sawa Yan talla suke lalacewa yau da gobe zata Saba har ta daina kunya,sannan ga gogayya da maza mutane manya daban daban zai sa idonta ya bushe ta dawo Bata da kunya Kuma bata tsoron kowa kadan daga illar talla ga ya mace,Aslam yace hakane Nima sai yanzu naga hakan, Uhm ta furta tana kallon Wayar hannunsa me tsada
Sabeer ne yayi sallama tare da shigowa shima,Sai yau Siyama taga Sabeer,gaida shi tayi Yana binta da kallo ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa ya zauna yace ko kece Siyaman? Charity tace ae yace Sannu mun gode fa,Sabeer ya dameta da kallo,Aslam Yana kallonsa,Siyama mikewa tayi tace zata tafi,sai yaushe? Aslam ya tambaya tace sai an ganni Kawai yace muje na rakaki Suka fito tare suna tafiya a hankali suna hira tana ta bashi dariya.
Nusaiba aka sauke a taxi ta tsaya tace Charity sai da Kika sake biyo mu Nan dan masifa yanzu ba kudin da za a baki to,Tsaki Siyama ta ja tare da furta banda lokacinki Nusaiba,Nusaiba ce tace zo wahalalliya Ina son magana dake,Charity ta ja gefe Nusaiba tace tunda taku tazo Daya da Aslam dan Allah kisa ya sakeni,ki fada Masa Ni takarda ta nake so ya sawwake min na gaji bazan iya rayuwa da shi ba,Siyama ta kalleta tace ki kalli