Showing 72001 words to 75000 words out of 85703 words
ku? Yace sai next week akwai abinda Zan karasa,tace to shike nan Allah ya nuna mana,tace Ina Siyaman ne? Yace Wai kunya take ji,kirata Mana mene abin kunya yarinya taki sakewa dani,a waya ya kira Siyama tana dagawa yace kizo inji Mum,Fitowa tayi Aslam Yana kokarin jawo hannunta tayi maza ta matsa bangaren Mum tare da Zama a kasa Mum tana sama,Mum tace ki zauna a kujerar Mana Siyama ai an Zama daya ki daina wani kunya Nima na Zama mamanki ai tashi ki zauna kema,Siyama sai lokacin ta samu kujerarta daban ta zauna,Aslam sai kashe Mata Ido daya yake ta dauke kallonta daga garesa,Suna ta hira da Mum kadan kadan take saka musu baki,Mum bata dade ba tace tafiya zata yi driver da ya kawota shine ya maida Mum,Yana dawowa daga rakiyar Mum ya Mika hannu zai Kama Siyama sabo da ta Harare shi dazu,zillewa tayi tana dariya,wayo ya Mata kamar ya fasa kamata yace kawo min lemo,taje ta kawo Yana kwance a 3seater tana Miko Masa ya hada da hannunta ya rike,Lemon ya ajiye a gefe ya jawota jikinsa,tana shagwaba tace dan Allah ban dade da yin wanka ba yau tunda ka yini a gida sai wanka kake sani wankana sau uku kenan,tana zamewa zata gudu ya Mata rikon tsauri ya Kama bakinta Yana tsotsa sosai tare da murzata bata Sanda ma ta biye Masa ba ta shiga tayashi daga nan Suka lula duniyar ma'aurata cike da so da kauna.
Nusaiba ce zaune a gida ta zuba tagumi gabanta tuwon masara ne miyar kuka da rana tsaka domin kudin abincin da Shehu ya bawa Mama na cefane ta kwashe ta kashe wasu Kuma tayi zubin adashi sai wahala yaransa suke sha,Mama ce ta kalli Nusaiba ta tabe baki tace idan Zaki ci ma kici wa ya hanaki duk inda Kika Yi aure ki bari ki haihu ai da yanzu kina da yaro da Aslam ko Sufyan a ciki dole Wanda Kika Haihu da shi ya dinga kawo Miki kudi na ciyar da dansa amma Kika ki yarda da shawarata ke baza ki haihu ba sabo da idan wannan ya talauce ki kashe aure ki auri wani ke baza ki tsufa ba Kika dinga Shan kwayoyin hana daukan ciki babu Wanda kika samu ciki da shi gashi nan ai kin koma marar amfani baki da wani amfani.
Nusaiba ta kalli Mama tace yanzu Mama nice na koma marar amfani sabo da bani da kudi bana samo Miki kudi yanzu nice marar amfani sabo da kin gama cinye kudin Mazajen Dana aura? Mama tace ae baki da wani amfani an fada dan ubanki kuma idan ke Kika haifeni naji labari,amma wlh Mama Zaki gani Inshaallah Abba sai ya Miki kishiya Kuma Inshaallah sai an sake ki kema kiji in da dadi, ruwan mari Nusaiba taji ta ko Ina a fuskarta Mama tace dan ubanki sa'arki ce ni oh sabo da Ina Zama inyi zance dake shine Kika rainani,Nusaiba tace ae din na fada tana kuka tace wallahi Kuma ko Zaki kashe ni sai na fada Inshaallah sai an sakeki kema Kamar inda Kika kashe min aure Kika dorani a hanyar banza,Baki min tarbiyya ba baki ma cancanta ki Zama uwa ba ma,Mama ta mike ta rufe Nusaiba da duka ta ko Ina amma Nusaiba bata fasa fadar abinda taga dama ba.
Affan kuwa Yana Office ya fara tunanen matarsa irin farin cikin da yake kwasa a wajenta tun kafin 5pm ya tattara sai gida,shi da yace sai 5pm Raudah tana kitchen sai ganinsa tayi ya shigo bayan ya Mata sallama ta amsa ya Rungume abarsa a jikinsa,Allah yasa ta gama kwai Kawai take dafawa shima ya dahu tana jira ne ta sauke ya shigo,Gas din ya kashe tare da Daukanta cak Kamar jaririya sai bedroom dinsa,burin Raudah ya cika ya dawo da wuri tace kasan me na tuna? Yace sai kin fada Yana ajiyeta saman gadonsa tana dariya kasa kasa tace fadan mu da kullum bamu da aiki sai fada Murmushi yayi yace sabo da yawan appointment dina ne,dariya Suka yi yace ai kin rainani da yawa ne,tace ai kuwa Watarana da na maka Tsaki ka mareni gaskiya na maru sai da na kwana kumatuna suna zafi tun daga ranar ban Kuma ba,me yasa Kika sa min Ido ne a lokacin? Maybe so ne,a'a ba wani so yanda Kika tsaneni,dariya suke yana shafa cikinta Yana Kare Mata kallo tayi kyau sosai sanye take cikin kana nan kaya wani dan short wando da Yar rigarsa yace halina da ke iya wanka kina birgeni ga tsafta ko Ina kamshi duk wani lungu da sako kamshi yake zubawa har can head of Service clean Yana kamshi tv dinsu dake kunne a bedroom din tana ta wakoki iri iri na Nija,Raudah tace Baby ka iya rawa? Yace rawa ban taba gwadawa ba a rayuwata ba wannan ba girma rawa sai Mata ai amma Namiji me class baya rawa bata cikin swag dina, Murmushi tayi tana shafa sajensa da gemunsa tace Yan gayu, Ido ya zuba Mata itama shi take kallo cike da shauki yace Allah sarki Hussain yayi asara,dariya tayi tace ba ruwana ni da ni na fada sai ka Fara Jin haushi kace Ina zancen tsohon mijina,yace ki daina cewa Hussain mutanen kirki su ake kira da Hussain amma shi Usaini yake su Usaini anyi asara,Raudah ta Masa Shuru sabo da tana magana zai ce tana Masa maganar wani,tashi ki kawo min milk before na fara servicing dinki,tace alright ta mike tana cewa kayi timbidi da yawa,dariya yayi yace dan Allah karki sa na tuno timbidin Yara me karni na kasa Shan madarar,Ni timbidin mazan aure nake nufi,lips dinsa ya lashe tace Allah ya shiryeka suna dariya yace ameen taje ta kawo Masa madarar tare suka shanye tace ka Dade kayi karko duk nasan ba rago bane,kissing dinta ya Fara Yana sarrafata Kamar zai cinye ta danya itama haka har Suka lula duniyar su ta Dadi.
Aslam tunda Siyama ta samu ciki kullum Kansa Yana saman cikin tun cikin ma bai fito ba,ya dinga Tambayarta me take son ci,in Banda gyada me gishiri ba abinda take ci kullum sai abinci Wanda ya Zama dole tana ci ta koshi ga gyadarta a kusa,bayan Mum ta tafi da sati daya Aslam da Siyama Suka tattara Suka tafi yawon shakatawarsu kasashen duniya,Nusaiba sai labari ta ji,ta zauna tana ta faman bala'i ita Daya a tsakar gida tace Siyama baza ta taba ganin dai dai a rayuwarta ba,tsawa kwarantsa sai ta fado Mata a kai ta mutu kowa ya huta,shima Aslam sai ya talauce ya tsiyace da izinin Allah sai yayi bara a gefen kwalta sai yazo wajena ya nemi taimakon Naira hamsim,Mama tace Ameen Inshaallah basu babu ganin dai dai Siyama sai ta dawo tallan goro,Siyama tace Kuma baza ta taba haihuwa ba, Inshaallah cewar Mama bari zata dinga yi jini ya barkewa shegiya sai ta shekara tana zubar da jini mijin bai samu damar saduwa da ita ba suna ta fama su kadai.
Kawu da Shehu watansu kusan biyu a kasar waje ana kaisu yawan bude Ido Suka koma Saudiya a karshe Suka sauke farali can suka hadu da Aslam da Siyama, daga nan gida Suka dawo Suka bar su Aslam a can,Shehu yayi bulbul yayi kyan gani gashi suna ta waya da Landlady ita ta Dade da dawowa Nigeria sun gama shirya aurensu ,sai daga baya yaji ma ashe tana da kudi
Shehu bayan sun huta da sati biyu ya samu Mama cikin dare suna kwance ya tashe ta yace tashi zamuyi wata magana,Mama ta mike tana Jan tsaki wacce magana ce wannan sai cikin dare mutum yana baccinsa Fadi ni naji mene? yace dama fada Miki zanyi Zan Kara aure wani watan idan Allah ya kaimu za a daura min aure,ban gane ba wanne aure? Wanda Kika sani dai shi Zan Kara ma'ana Zan Kara Mata ku Zama ku biyu,banyi dan naci zarafinki ba,ahayye eheheheeeeee heeeeeeyy Mama tayi shewa tace dama ka dade kana cin amanata ban sani ba kwarto a wanne dakin zaka sakata daki uku ne daki daya namu daki daya na Mata daki daya na maza to Ina waje? Shehu yace Aslam ne zai min auren nan fa kwandala bazan kashe ba shine zai min komai yace, yace idan so nake ma zai bani gida na saka Amarya,nace a'a gwara na hada Kan Yara na gida na Zan kawo ta tunda gidan zaiyi part guda yace zai gina min part daban a cikin gidan nan a wancen part din dana katange ban gina ba,Mama ta fashe da kuka da ihu cikin dare tace amma Allah ya tsinewa Aslam Albarka bazai ga annabi ba,Su Nusaiba sunji ihun Mama Suka firfito,Mama cikin tsakar daren ta fito tsakiyar unguwa tana zunduma ihu da kuruwa sai da makwafta suka fito Shehu yace kowa ya koma gidansa akan Zan Kara aure take wannan haukan,aka dinga tir da halin Mama,da kyar su Nusaiba Suka lallabo ta ta dawo gida tace wallahi yau bazan kwana a daki ba a tsakar gida Zan kwana tun suna lallashi har Suka gaji Suka koma daki ita Kuma Mama a tsaye gari ya waye Mata tana faman zunduma ihu,Shehu bakin ciki Kamar ya kashe shi ta gama tozarta shi,Kamar Wasa da safe sai ga motar yashi tana ta saukewa a kofar gidan Shehu aikin Aslam ne,Mama tace Nusaiba ku fita ku barbaje yashin nan a kasa duk ku tirje shi,sauran yaran Suka ki zuwa Nusaiba ce take taya uwarta kishi ta fito Kamar sabon kamu tana eban yashin tana watsarwa a cikin kwata,Allah ya kawo Shehu ya kamata ya nada Mata shegen duka Kamar zata mutu,Shehu Yana shiga gida Mama taci kwalar Shehu tace idan kayi min kishiya shegiya nake algungumi azzalumi Allah ya isa shine ka samo me kudi zaka auro bazan yafe ba sabo da mu talakawa ne wallahi sai ka sake ni ka sakeni,a gaban yaranta tayiwa Shehu haka Shehu hannunta ya cire daga jikinsa ta karfi yace ki tafi gidan ubanki na sake ki saki daya,Mama Hannu ta daura a Kai tana ihu shine ka sakeni Allah ya Isa kuka take ta tattara nata ya nata cikin fushi ta tasa keyar Nusaiba kadai Suka tafi Kauye garin su Mama su biyu,shi kuwa Shehu yace Allah raka taki gona aka ci gaba da gini.
Aslam tsabar muguntarsa ya samu part din Amarya aka kera shi Kamar gidan wani hamshakin me kudi 3room and Palo aka Mata sai kitchen dinta da komai,babu inda za ayi gate wani makwafcin Shehu zai tashi daga unguwar yayi sabon gida Aslam ya siyawa Shehu gidan aka bajeshi tare da hade shi a bangaren Amarya aka mata gate me cin mota biyu abinta ko Ina yasha tiles da Interlock kyau Kam ba a magana gidan ya keru,ita Kuwa bangaren Mama Yana nan sai paint aka mata Kawai shi ma me paint ne yaji kansu ya musu komai siminti ne,Mama Kuwa da Nusaiba tunda Suka koma Kauye garau garau ma da kyar suke samu ga kazanta,daga dankali sai kunu sai tuwo,dambu,danwake shima kadan ake basu,Basu taba sanin da a Rahma suke ba sai da Suka zo Kauye ashe a gidan Shehu ba karamin dadi suke ji ba,sun rame sunyi baki,tsakanin Nusaiba da Mama sai fada suke Yi babu mutunci a tsakaninsu
Yau suna zaune a wani dakin kasa Wanda shine makwancinsu sai tabarma wata yarinya ce ta shigo ta ajiye musu kunu a wani dan karamin kofi Wai shine abincin ranansu ai Nusaiba tace wallahi duk da bani da kudin mota gida zan koma wajen mahaifina,Mama ashariya ta dannawa Nusaiba tace sai kin dawo marar mutunci marar biyayya ga uwarta,tace ae naji tafiya zanyi wallahi yau bazan kwana a garin nan ba,Fitowa tayi ta shiga dakin wata tsohuwa a gidan me siyar da daddawar miya,Nusaiba tasan inda matar ke Adana kudinta sai ta dinga Jan Me daddawa da surutu suna ta hira har lokacin Sallah yayi tsohuwar ta mike ta fice zata Yi Alwala tana shiga bandaki Nusaiba ta bude wajen ajiyar ta kwashe dubu uku tasan zai isheta kudin mota har da rara,ranar kuma an daura auren Shehu da Amaryarsa Landlady
kayan daki na gayu da tsada Landlady ta zuba a gidan kana gani kasan ba karya,a ranar da yamma Kuma ta tare ba kowa a gidan sai Raudah Wanda ma har Affan yazo Daukanta zasu tafi gida sai ga Nusaiba da Kaya niki niki a Ghana must go ta dawo.
Affan ya dau wankan sugar yana tsaye a jikin mota yana jiran Raudansa Nusaiba sai kallonsa takeyi har da goge Fuska ko zai kyasa yace Yana sonta,Jakarta ta rike a hannu a Dan gayence Wai Kar ta kwafsa,zata wuce ta gaban Affan tace sannu lokacin Rauda ta fito taji Nusaiba tana cewa bawan Allah wani gidan kake nema ne? Affan ya kalleta sama da kasa yace ke lafiya Ina ruwanki dani karki jawo min matata yau ta hanani bacci mijin tace ne ni nan da kika ganni bani da amfani wajen Yan matan waje gwara kija tsummar ratuwarki ki Kara gaba gwandala ta baza kici ba,Nusaiba dariya tayi irin ta samu Hanya tace hmm amma matar taka ta birgeni haka ake son mace,Affan yace ae ai ta Isa ne kin san wasu ai basu Kai su mallaki miji ba sabo da Basu iya allonsu ba basu da hali na gari shi yasa ake yawan sakin Mata basu iya Zama da miji ba,Nusaiba sai taji Kamar da ita yake,yace Amaryar Shehu Muka kawo ai Shehu yayi dacen mace yanzu zai samu kwanciyar hankali ance uwar gidansa ballagaza ce ita da yarta Basu San me suke ba ance ma ko a unguwa an tsane su,Nusaiba Kamar ta fashe da kuka bawan Allah ya tsaya sai caba Mata magana yake,ita bata San ma Affan bai San ko Shehun ba sai dazu ya ganshi Suka gaisa labari Suka ji a layin ana fada, Raudah ce ta karaso tana hararar Nusaiba ko kunya Raudah babu akan kishi ganin layin ba kowa sai iya su harda shafa gemun Affan ana Masa shagwaba tace muje ta juyo ta kalli Nusaiba tana Mata up and down,Affan yace baiwar Allah ko Zaki Mana wanke wanke da shara a dauke ki aiki kin tsaya kin zuba Mana Ido, Raudah tace ai wallahi gwara aiki ya kashe Ni idan ba namiji zaka dauka ba Indai macece bana so zanyi komai da kaina,Nusaiba juyawa tayi tana tuna rayuwarta a gidan Aslam,da kyawun Aslam da yanda yake nuna Mata so da kauna,kuka ta saki tana tafiya kasa shiga gidansu tayi ta zauna a kofar gida bakin kofar su tana ta kuka,tausayi ta bawa Raudah taje wajenta tace baiwar Allah kuyi hakuri wlh bamu fada dan mu wulakantaki ba mun San darajar dan Adam kune bakwa kau da kai ga mazajen wasu kiyi hakuri idan abinda mijina yace ya Miki zafi,Nusaiba tace ba wannan ne ya dameni ba,nadama nayi a rayuwata na tafka kuskure,to Allah ya Mana me kyau cewar Raudah tana juyawa motocin Aslam biyu Suka Yi parking daya motar securities ne daya kuma shine a bayan motar tare da Siyama,Fitowa yayi a hankali wanka iya wanka ga kyau,zagawa yayi tare da budewa Siyama mota ya riko hannunta ta fito da dan karamin cikinta a gaba ya Fara Fitowa ta Sha Abaya ta zuba kyau Kamar ba Yar kasar nan ba,sunyi kiba da kyau sun Kara wani fresh,da gani kasan sun dan huta a kasar waje, Nusaiba ta bisu da kallo kawai,Aslam Yana ganin Affan ya koma gaban Siyama ya kareta Wai Kar ya ganta tsohuwar budurwarsa Kar so ya dawo sabo,Affan dariya abin ya bashi,ke Kuma Raudah da kin ga mace sai boye Miji a tsiri nunawa lallai ita fa matarsa ce,Aslam zai wuce tsabar kishi harda nunawa bai San Affan ba,Affan ya Mika Masa Hannu da kyar ya karba Suka gaisa Siyama ta dawo gaba tace Affan kaine a unguwar tamu,yace Amarya Muka kawowa Alhaji Shehu kawar matata ce,Siyama ta kalli Raudah tace Sannu Ina yini,Aslam harda Jin haushi dan me zata gaisar da Raudah ai Raudah ce ta kamata ta gaida Siyama,Raudah ta amsa da fara'a Suka gaisa ta gaida Aslam ya amsa,Affan yace Nasha Kaye a wajenka mene abin bata rai,tunda ka lashe zabe Kai fa kace ba gaba,Murmushi Aslam yayi ba shiri ya dai tsaya sun gaisa sosai harda bawa Affan katinsa yace gashi idan kana so Watarana mu gaisa,Affan ma ya zaro katinsa yace ga nawa Wai ya nunawa Aslam shima fa babban yaro ne da aikin yinsa,Raudah sai kallon cikin Siyama takeyi dama itama ta samu nata da Affan,gidan su Siyama zasu shiga Wanda dole sai ka wuce ta kofar gidan su Nusaiba,Nusaiba tana tsaye tana ta faman kallon Aslam Kamar mayya,Aslam ya gane itace harda shafa cikin Siyama suna tafiya,Siyama tayi dariya tace dan Allah ka kyale babyn nan haka kullum hannunka na kai,Siyama tace Nusaiba kece dama ko magana haba Nusaiba,Nusaiba an sakko tace Charity sannunki tana tabe baki ,Hannun charity ya rike Suka Shiga gida me kyau Nusaiba bata gane gidan su Siyama bane yanda Kawu ya gyara gidan yayi kyau ya canja sosai,haka ta Shige gidansu ta iske kannenta duk basa nan sun tafi sashen amarya,Shehu Yana dakinsa yaji sallamarta,Fitowa yayi yaga Nusaiba a gabansa ta zube gudun Kar ya koreta ta fashe da kuka ta rike kafar Shehu tana dan Allah Abba ka yafe min na tuba wlh bazan sake biyewa Mama ba,Shehu yace Nusaiba ki ma biye Mata ni ba ruwana kece a wahale,Ka yafe min Abba yace dama ni bana Fushi dake na yafe Miki, Yar da na Haifa ai kullum Addua Zan Miki Allah ya shiryeki ,Nusaiba taji Dadi sai ta share waje ta samu wajen Zama duk da haka bata leka wajen Amarya ba abinci taci duk Yan uwan Shehu sun tafi itace ta gyara gidan tsaf tare da kannenta tayi wanka,Shehu Kuwa ana yin Sallar Isha ya wuce bangaren Amarya landlady anci gayu ta hade cikin