Showing 84001 words to 85703 words out of 85703 words
Aslam a gaba da kuka sai ya bata kudi tayi gudunmuwa dan Dansa da Nusaiba ke so yace me za ayiwa Nusaiba me ya dace, Siyama tana share hawaye tace a bata jari tunda mijinta baida hali sosai sai rufin asiri idan aka bata sai ta dinga sana'a a gidanta ko irin dan siyar da su Maggi,omo etc,Nawa za a bata? dubu dari ? Yace to Zan Miki transfer ki tura Mata kice gudunmuwarki ba ruwana a ciki,Siyama tace hakan ma yayi na gode,haka ta turawa Nusaiba Suka Yi shawarar kayan da zata dinga siyarwa nan gaba,Ango Kuma yace in sun Gama amarci zai maida ta makaranta itama tayi ilimi,Nusaiba sai godewa Allah akeyi ana murna.
Siyama kuwa Private University Aslam ya sata taci gaba da karatunta tana kula da danta Wanda yayi wayo sosai.
Aisha ta Haifi yarta mace katuwa,Nabeela ma mace ta Haifa,sai matar Sabeer da ta Haifi Yan biyu duka maza manya,su Aslam sune na hannun dama a nan.
Raudah ce bata Haihu ba har sai da cikinta ya shiga wata goma,Affan yace idan ba dama Kawai suje asibiti ayi aiki a cire dan,Raudah tace bazai yuwu ka kassara min rayuwa ba in samu matsala Ina lalacewa wata zaka aura haihuwa ta Allah ce a barni Allah zaiyi ikonsa haka Kawai ayi min aiki nazo na samu akasi matsala ta afku shike nan sai naji gudar Amarya a gidana bada ni ba,Affan yayi dariya yace wannan zafin kishi Ina za a kaishi Raudah ni nace zanyi kishiya Ina nake da wannan kwarin gwiwar ni waye ni,who be me? bayan kin gama dani sai abinda Kika ce,Suna haka Kamar Wasa Raudah ta fara Nakuda,damtsen Affan ta rike tace bala'iiii ah'ah Affan....wayyo ta kwala ihu ta rike Mara tace Subhannallahi...mutuwa zanyi..Affan yace idan Wasa kike ma ki daina,tunda yaji Raudah ta hayayyako Masa da masifa da bala'i Kamar zata cinye shi karka isheni karka dameni,Malam ka saurara min bana son wulakanci...yace to da gaske ne nakuda ce muje asibiti tana masifa taya Zan iya tashi ta balla Masa harara,bata ita yake ba ya dauketa da kyar ya sata a mota,tace kayan haihuwar ko da yatsunka za a yanke cibin? Affan yace ki dinga bina a hankali Baby, tace Kar na sake Jin kalmar nan a bakinka,Affan ya koma da gudu ya dakko takarkacen data shirya,ya figi mota tana ta faman wash wash Allah na har suka je asibiti aka dauketa cikin gaggawa,Affan hankalinsa a tashe sunfi kafin 1hr sannan aka ce Masa ta haihu,Uwar gidan Liman ce a wajen Raudah itama Namiji ta santalo katon gaske da gani ya dade a ciki,Raudah ta Sha wahala ba a sallameta ba sai washe gari da Yamma sannan,Matar Yusuf har tazo,Haka Maman Raudah da kanwar mamanta sunzo Suka ce tafiya zasuyi da ita,Affan yace bai yarda ba ya dauke jariri ya Hana kowa
Da kyar ya hakura yace iya sati biyu daga Haka karta Kara ko kwana daya,suka tafi kuwa har kudin rago Affan sai da ya tura raguna guda biyu sai dai suyi waya da Rauda ko video call yaga jaririnsa,Ranar Suna yaro yaci Abdallah,su Raudah acan sun Sha shagalin suna,tana cika sati biyu Affan yaje airport ta sauka da jaririnta ya dakko matarsa Suka dawo gida,sai lokacin suka nemi yar aiki Nanny dattijuwa me Kamala,Siyama har barka taje mata itama.
Nusaiba Kuwa an Kama sana'ar Omo da su Maggi etc Hannu bibiyu har yasa ta zana waec da Neco tana Fitowa bata samu direct degree ba sai NCE ya sama mata ta Fara zuwa,Siyama kuwa anyi nisa a school,Su Nusaiba an farfado kullum Mama cewa take ta kula da mijinta ta rike shi Hannu bibiyu Kar tayi Wasa da aurenta.
Bayan wata biyar Landlady ciki ta samu dama bata taba haihuwa ba yanzu ta samu a gidan Shehu,Ihsan itama sai ciki har ta samu ciki kullum laulayi da amai,Nusaiba kuwa nata cikin ko abinci ba komai take iya ci ba sai abinda taji zuciyarta ta raya mata Haka suke fama
Siyama danta har ya fara rarrafe gwanin sha'awa gashi ta tara masa suma an daure Masa ita kamar yaron turawa kowa ya kalle shi yasan ba karya dan gidan Yan gayu ne,shi kuwa Affan Abdallansa kaishi yake ana Masa shegen aski style style har sumar tayi yawan gaske Yana zama,Babu style din da ba'a Masa yaron nan,kayansa ma in aka saka Masa kasan babansa dan wanka ne yanda ake kwalkwale yaron nan,idan Yana gida har goya shi yake yasa zani ya daure abinsa a baya Kamar mace haka Affan ke yi, yau ma Yana gida ya goya Abdallah a bayansa ya daure shi da zani harda jijjiga shi Raudah tana Masa dariya.
Bayan wasu watanni Nusaiba ta Haifi yarta mace Siyama sune na jikin gado,ranar Suna aka sa mata Jawahir, Nusaiba ana zaune cikin rufin asiri ba rashin ci ba rashin sutura Yar unguwarta idan zata je ya dauki matarsa a machine dinsu abinsu shar, Nusaiba da shegen Iyayi harda koyon machine Lifan ta iya sosai sai ta saka riga da wando ta sa Abaya da mayafi taci glass ta tuka machine taje inda taga dama,Landlady ta haifi Namiji itama. Muhammad din Siyama yayi wayo ya Fara Kiran Daddy da Mummy Yana tafiyarsa ko Ina dagwai dagwai Amma ba sosai ba, idan Aslam bazai dade a Office da shi yake tafiya yaron suje su dawo
Yau Aslam yana zaune a dakinsa a kasan dan karamin carpet dake jikin bed dinsu Yana cin abinci, Siyama tana zaune a saman bed tana bawa Muhammad Nono da yan hakoransa ya gartsa Mata cizo,bata san Sanda ta duke shi ba ji kake dim dim a bayan yaro,dariya yake yana kallonta ya dage kafa daya ya riketa da hannunsa dadi ya gama kaiwa yaro,ya zaci Wasa take Masa sai ya sake cizonta,Siyama ta fisge nononta ta cillo shi kasa aka wani dangwarar da yaro da karfi yaji zafi ya fashe da kuka tace idan ka sake cizona sai na mareka yaro marar kunya ,Aslam Fuska ya daure takaici ya kamashi yace mene haka Wai ke aljanu ne dake ne? wannan yaron me ya sani sabo da Allah dan ya cijeki baza kiyi hakuri ba,Siyama tace kaji zafin Kuwa Ina magana Yana min dariya na yaye shi daga yau yayiwa Kansa bazai sake Shan nono ba,yace ai lokaci bai Kai ba baki Isa kin yaye min yaro ba,ai Kai sai ka bashi naka nonon ya sha,dansa ya dauka da yake zaune yana kuka ya lallaba shi yace kyale Mummy taje da nononta ga abinci yaci gaba da bashi abincin Yana ci,a banza kuma ta huce tazo zata dauke shi Aslam yace kyale min yarona baza ki dinga dukansa a banza ba,Dariya tayi tace Indai shine gashi nan rigimarsa ma ta isheka,an Masa wanka? Siyama tace ae an masa,yaci gaba da lallaba shi Kamar zaiyi bacci sai yaki yi gashi Aslam ana so a Sha soyayya da Siyama yaro yaki bacci,Light ya kashe ko zaiyi bacci amma yaki yi,saman gadon ya kwanta da shi,Siyama zata Yi magana yace shiiiit Shuru Shuru...ana ta lallaba yaro har ya fara bacci Aslam ya lallaba zai tashi yaro ya fashe da kuka,Siyama ta dinga dariya tace matsa ka gani ta kwanta tare da yaron ta sa Masa nono a baki Yana Sha sai bacci Aslam yace wow tana bawa jariri nono yana cire Mata Kaya,aka dauke yaro aka maida shi bed dinsa, sai da suka kwantar dashi yayi bacci,bargonsa Dan karami aka lulluba Masa kansa a waje,tace Yana tashi wajen Nanny Zan kaishi,Aslam yace ban yarda ba babu Nannyn da Zan Bari ta dinga kwanar mim da yaro komai dattijantakarta a zamanin nan da duniya ta lalace sai an kula sosai da yara,gashi nan kyuya ta matanmu tasa suna ta jefa yaransu ga halaka ko a lalata maka rayuwa danka musamman ya mace sai an kula sosai nawa Zaki ji yaron gida yayiwa Yar wani fyade,Yar aiki ta lalata yarka tana lesbian da ita,akwai na kirki a Yan aiki Kinga ko wannan Yar aikin na yarda da ita ta dade a gidan nan I think farko ma a nan kuka taba ganinta,tun Mum tana kasar nan take Mana aiki amma komai yarda ya kamata a kiyaye,Siyama bargo ta ja musu tace to Allah ya Kare mu da yaranmu yace ameen shi yasa baza ki aiki ba karatu dai zan bari kiyi Amma kina gamawa shike nan
Tace to ka tuna min gobe Ina da test ko karatu banyi ba ta mike zata dakko littafi yace ai sai dai kici Kan jaki amma yau babu karatu sai na aure, yaron ne ya farka kadan ya kwala Kira Daddy,Aslam yace baya nan,Jin muryar Aslam sai kuka Siyama tace wannan yaron da babba ne yau sai yaci dukan tsiya,Aslam yace je ki dauki danki ni na gama bangarena bazan sake daukansa ba na gaji,ya isheni da kuka ya hanani bacci karki haifo wani da wuri wannan kadai ya ishemu nan gaba idan Muka huta da yawa sai a Karo haba Yara su dami mutum,Siyama ta tuntsire da dariya tace Kai da kace ayi sauri a Karo yace na janye magana ta yau,kaiwa Nanny shi,Siyama tana ta dariya tace kace danka bazai kwana can ba,yace Kai Mata Allah ya kiyaye kaishi,juyawa tayi zata fita yace Madam da kayan baccin Zaki fita ai tana dakin dake palon kasa,ta fita ta Kai Mata Muhammad,ta karbe shi suka kwanta sai yayi shuru ya koma baccinsa,ta dawo tace har ya koma bacci,yace dumin uwarsa yake son ji ai Kuwa bai Isa ba sai in ba da dare ba,ya jawota Suka Shige bargo
Haka rayuwar ta kasance musu cikin farin ciki da kaunar juna sai jarabawar rayuwa da Allah baya barin bawa ba jarabawa.
ALHMDLLH
Masu Sharhi Ina Matukar godiya wacce ba adadi, gaba Daya yan group din BABU KAUNA musamman masu bibiyar littafin nan Ina Matukar gode muku
Sai Watarana kuma idan da rai da lafiya cikin yardar Allah na sake muku sabon Novel Amma fa Zan dade banyi sabo ba sai an huta an huta an gaji sannan.
Copy by Zainab Butalawa
AsmaBaffa