Showing 21001 words to 24000 words out of 85703 words

Chapter 8 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

601

Namiji irin Aslam hadadden mutum Kamar shi yayi kansa kice Wai kin gaji da shi,ae dan Allah ni na gaji bana son auren ya sakeni,kinfi so ki Zama bazawara ae gwara haka ke karuwai ma suna nan su da karuwanci suke Yi suna zaman su a duniya Lafiya bare ni Dan an sakeni na Zama bazawara,wlh idan Bai sakeni ba Kara Zan kaishi wajen Yan Hisba,Siyama juyawa tayi tare da komawa wajen Aslam ta fada Masa abinda Nusaiba ke so saki,yaji Matukar ciwo ya danne,Yana komawa gida tace wallahi yau ba zaman lafiya sai ka sakeni,Aslam yaki kulata rigarsa ta rike ya samu ya kwashe ta da Mari ya sake zabga Mata Mari Wanda ba shiri ta sake shi tana kuka wallahi sai ka sakeni,yace baki ji kunya ba mahaukaciya aure wata hudu na sakeki Baki da hankali,kuka Nusaiba takeyi sosai yaki sakinta haka Suka kwashe satikai kullum da masifar da zata fito da ita a saketa sabo da bai da kudin da zata karba yanzu Kuma sai takalo rashin mutunci iri iri shi Kuma yaki sakinta,harda daina kwana a dakinsa ta dawo palo a nan take kwana kullum.

Yau Mama ce tazo gidan tana zuwa ta saki ihu a palon tace a Nan yata take Zama daki nawa ne? Nusaiba dake zaune tace daya,Daya tal yanzu idan da kwana zanyi bani da wajen bacci kenan tab amma Aslam ba karamin azzalumi bane ka ajiye bawa me rai a nan, Nusaiba tace zauna Mama bari na Miki girki dama bana dafa Masa abinci,Mama tace kinyi dai dai tana zaune Nusaiba ta dafa Mata shinkafa da Miya harda kazar da ya siyo jiya Mama taci ta tauna Kashi ta sha ruwa me sanyi ta sake zuga yarta tace Kai Kai kamarki a wannan gidan daki Daya sai Palo kujerun ma ba na kasar waje bane ba Yan Dubai ba Yan nan Kano ne,Nusaiba tace kalleni Mama yanda na girma nayi kiba nayi wani fresh kowa ya ganni yaga kalar hutu amma matsiyacin ya makale yaki sakina,gida ko filin tsakar gida babu kalli tv din ma karama sai kace ta Office din principal din makarantar sikandire cewar Mama,wani takaicin Aslam ya sake rufe Nusaiba,Mama Kuwa sai sake zugata takeyi,tashi tayi ta leka kitchen ai wani ihu ta saki tace hodijam inji Dan fillo wannan kina samun balance kuwa? Sai dai manage Mama shi yasa bana shiga

Suna haka Aslam ya shigo sanye cikin wata shadda Yar ubansu grey color cikin kayansa na baya masu tsada ya saka ya shigo da takardun makarantarsa,Mama ta Bata rai tare da kallonsa shekeke ta tabe baki tace kamar gaske akwai kudin Kai karya bata Yi ba,Aslam ko kulata baiyi ba ya wuce bedroom dinsa,Mama tsabar rashin son zaman lafiya tace sai na dawo kwana zanzo na kwana biyu haka,Nusaiba tace Allah ya nuna mana Mama sannan ta fita ta tafi gida,Aslam ya fita bai dade ba ya dawo da Leda a hannu yayo cefane harda Naman rago da yawa,tun kafin yayi magana Nusaiba tace wlh sai dai ka dafa da kanka Kuma abinci daga ni sai uwata na dafawa mun cinye,bata ko rage Masa ba gashi Yana Jin yunwa Charity bata da waya bare ya Kira ta, tashi yayi ya fita bai ko saurari Nusaiba ba ya shiga Napep zuwa gidan su Charity

Yana Fitowa daga Napep Suka hadu da Shehu Baban Nusaiba,Shehu da fara'a da murna yace surukina gobe nake so nazo gidan naka jaje wlh ashe haka Abu ya faru marar Dadi,Aslam ya duka zai gaida shi yace tashi tashi Aslam ubangiji ya maida alkhairi,yace ameen,Shehu yace ya Nusaiban iceko lafiya kuke? Aslam baiyi kasa a gwiwa ba ya zayyanewa Shehu komai,Shehu Baki ya rike yace wallahi ban San me ake ciki ba abin wato har ya Kai haka,duk uba bazai so a saki yarsa ba amma tunda Nusaiba take maka haka na baka dama ko nine iyaka abinda Zan iya kenan na saketa,Dan Allah kayi hakuri Kai mutumin kirki ne,har gobe Ina ganin mutuncinka Kuma bazan fasa zumunci da Kai ba ko da ace baka tare da yata,Aslam yaji dadi da farin ciki,Shehu yace ka kyale Maman Yarinyar tunaninsu daya taho muje gidan Yar uwata ka huta a can,Shehu yaja Aslam zuwa gidan Yar uwarsa Alawiyya ba nisa da gidansa ita me rufin asiri take aure komai nasu me kyau ne,kana ganin Aslam zaka Yi tunanin da kudinsa tunda Yana da sutura,palon Alawiyya Suka shiga babbar dattijuwa yace mijin Nusaiba ne,Alawiyya tace Shehu ai na gane shi,Aslam ya gaishe da ita ta fita ta kawo musu lafiyayyen girki Aslam dama yunwa kamar zai mutu baiyi Kara ba ya zage yaci ya koshi shi da Shehu Kamar ba surukai ba suna yin Sallar la'asar Aslam yace zai tafi Shehu ya rakoshi har kofar gida Suka Yi sallama shi ya koma cikin gidan wajen Yar uwarsa,Aslam Kuma ya karasa kofar gidan su Charity,Yana tura yaro ciki sai gata ta fito zata siyo manja,taga Aslam ba zato,Murmushi ta saki kayatacce tace Ina yini ya amsa da fara'a tace Ina kaje haka? Yace cefane nayi tace baza ta dafa ba nama ne zai lalace shi yasa nace Bari na kiraki ko ki dafa min ko kizo ki dauka ki kawo gidanku kuci Kar ya lalace,Charity tace nama guda wa yaki dadi har kasa yawuna ya tsinke,ya saki Murmushi ba shiri,ciki ta koma tace Aunty ga kudin ki aiki yaro Aslam yazo nema na,Aunty tace Kuma dan Iskanci sai ki dawo da kudin,Bata tsaya ji ba tace ki fadawa Kawu matsala ce a gidan zanje wajen Nusaiba,Aunty tace to a kula dai tace to,ta fito tare da cewa muje Suka fito tare Suka Mike suna tafiya suna Hira har yaji sanyi a ransa

Titin kwalta zasu tsallaka Yana ta tunani ya tafi bai kula da mota ta kusa zuwa inda yake ba Siyama ce ta taho da gudu ta fisgi hannunsa tace mota da sauri suka tsallaka suna tsallakawa motar ta wuce da mugun gudu,ta kalleshi tace tunanin me kake Yi haka ta furta tana kokarin zare hannunta a nasa Wanda ya damke hannun nata cikin nasa Yana Jin wani shock da bai taba jinsa a jikin wata ya mace ba,Napep Suka shiga zuwa gidansa Siyama ce ta biya kudin ta hanashi ya biya kudin,suna zuwa Nusaiba chatting take abinta ga ledar kayan nan a gefe,Siyama tana zuwa tace ke ballagazar matar aure shashashar matar Aslam, kallon Charity Nusaiba tayi Kawai ta ja tsaki,Siyama ta zari ledar Aslam ya zauna tace Ogana me za a dafa Murmushi ya saki yace kiyi farfesu Kawai sai Dan abincin dare,an gama ta furta tana kallon Nusaiba tayi fatali da kafar Nusaiba dake mike a hanya tace matsa can Yar banza Yar wofi,wawiyar banza,Dariya Aslam ya shiga yi Nusaiba ta galla Masa harara tace dan uwarki ba Charity kike ba ko Ngozi kike nafi karfinki wahalalliya me bauta a banza, Siyama ta yiwa Nusaiba dakuwa ta shiga kitchen tare da kunna gas ta Fara aikin girkin sai wurin magriba ta gama farfesun ta ebi dan kadan a roba me murfi ta rufe,Ta fuskanci yana son tuwon danyar shinkafa shi tayi Masa da miyar danyar kubewa ta Gama komai yayi Alwala zai fita masallaci tace na gama, yace Banga kinci ba tace gashi na eba ta nuna Masa robar, tare Suka fita ta shiga napep shi Kuma ya wuce masallaci.

Nusaiba tunda tana zuwa restaurant bata damu da abincin Aslam ba Sufyan Yana mugun kashe Mata kudi yanzu burinta Aslam ya sake ta,washe gari Mama Shehu ta tambaya tace zata je kauyensu ya barta tana tafiya sai gidan Nusaiba da Yar Jakarta wai tazo zata kwana biyu a gidan yarta,Nusaiba ta dauki Jakarta ta Kai bedroom ta hau girke girke Aslam Yana zuwa yaji kamshin girki na tashi yasan da dalili shigarsa bedroom kenan ya iske Mama a ciki yaga Kuma jakar tata tabbas kwana zata yi, mamakin suke mugun bashi,Mama ganin ya shiga ta fito,a gabansa a palo Suka zubo abincinsu Suka ci Suka koshi ko tayi basu Masa ba Yana Jin yunwa sai fita yayi yaci a resturant bai dawo ba sai 10pm lokacin Mama da Nusaiba sunyi Shirin bacci sun kwanta a saman gadon me gidan sun shige bargo tare,Aslam ya dan leka ya girgiza Kai yace idan baki da kunya Mama kin hadu da Dan zamani,bedroom din ya Shiga Mama ta bude baki,toilet ya Shiga suna ji Yana wanka Mama tace yau na shiga Uku da fitsararre,sai da yayi wanka ya fito daure da guntun towel,Mama Hannu ta dora a Kai tare rufe Ido tana yau na shiga Uku yau Naga jaraba,cikin bargon ta Danna kanta,turaruka ya fesa ya zura Jallabiya arsh,Kawai Saman bed din ya nufa yace Mama Dan matsa gefe kadan gadon zai iya daukar mu mu uku ba damuwa,Mama taga da gaske hawa zaiyi ya kwanta ta dirga kasa harda faduwa tace amma Kai ba dan arziki bane ban taba ganin suruki marar tarbiyya ba sai kai ta fice Palo tana cewa Nusaiba Miko min jakata a Daren nan Zan koma gida,Nusaiba ta mike tana hararar Aslam ta dauki jakar Mama da tarkacenta ta fito,Aslam ya kwanta a saman bed dinsa tare da Jan tsaki yace iskancin banza tunaninku ku kadai ne Yan iska uwar banza ya lulluba da bargonsa,Ita Kuwa Nusaiba a daren ta fita ta samawa Mama Napep ta koma gida,Shehu sai ganinta yayi ta dawo,yace ya na ganki ke da Kika ce Zaki kwana a kauye,Mama tace Wlh mutan gidan da naje domin su sunyi tafiya basa gida shi yasa na dawo,Shehu yace ke Kika sani kuma.
Washe gari da wuri Nusaiba ta Kai karara Aslam Office din Yan Hisba tace so take a fadawa mijinta ya saketa bashi da lafiya baya iya biya Mata bukatar Aure sannan ma ita ta daina sonsa ya Fadi abinda ya kashe zata biya shi ya saketa,Aslam yana gida ya fito zai fita Kawai yayi arba da jamian hisba mutum biyu suka Mika Masa takarda ana nemansa a Office din Hisba yasan Nusaiba ce kawai Sabo da haka Kawai sai ya nufi can a Napep.


Wacece Raudat

Raudat Ibrahim Waku 'yace ga Ibrahim Waku hamshakin me kudi ne dan asalin jahar Gombe Wanda ke zaune a Oyo state,tunda kasuwanci ya kaishi can ya shahara ya Zama hamshakin me kudi na gaske ya tattara da yaransa su Raudat gaba daya ya koma Oyo da Zama,matarsa daya tal Hajiya Rahmatu itama Yar Gombe ce, yaransu biyar Raudat ce babba sai kannenta biyu maza biyu mata,Raudat tana gama secondary ta samu Saurayinta Hussain dan Kaduna state,Hussain talakawa ne a zahiri ba son Raudat yake ba irin masu auren Mata ne dan kudinsu dan ace Kawai ya auri Yar me kudi,Baban Raudat tunda yaga Hussain da Kuma cewar baya sana'a ko kadan yace ta hakura amma taki ji Sam dole aka Yi Mata auren wuri

Bayan anyi auren Raudat da Hussain Baban Raudat shine ya Kama musu gida haya a Kaduna sannan gara ma kayan abinci mota guda aka ajiye da komai sannan baya Bari yarsa Raudat da talauci,Raudat komai ita ke Yi a gidan ta koma itace mijin ba karya akwaita da hankali ga hakuri duk wani kyan haki Raudat tana da shi dai dai gwargwado,Hussain Kawai sai dai ya kwanta an bashi jari ya cinye an sake bashi har Karo na uku amma sai ya kashe,tunda Raudat ta aure shi bai taba kwanciyar aure da ita ba Basu taba sex ba sabo da bashi da lafiya amma yaki yarda fada bashi da lafiya,abinka da yarinya itama sai ta kasa fadawa kowa suna zaune haka har kusan shekara Hussain ga mugun son Mata bai da aiki sai kula Mata duk kudinsa Yan Mata ke cinyewa shi Kuma dayar ma da ya aura ya kasa biya Mata bukata amma Yana hangen na waje,a Haka ko Raudat bata bashi kudi ba sai wulakanci da cin mutunci iri iri Indai tana son zaman lafiya to ta bashi kudi,abinda yake batawa Raudat rai Shan giyarsa sai ya Sha giya yazo ya Mata dukan taiya,duk ta rame sam bata San mene dadin miji ba,ana haka ya fara Mata sharri sai ya shirya zance na karya ya fadawa dan ginsa da abokansa,akwai Sanda ma yace bata bashi abinci Kuma har zaginsa takeyi,Watarana ma ya dinga fadawa abokansa ai maza take bi da Aurenta har kunnen Danginsa zance.

Su Kuma dangi ba bincike ba komai suka saka Raudat a gaba Babar Hussain da kanta ta sa Hussain ya saki Raudat dama bai damu da ita ba itace take sonsa kawai a hakan ma da ya saketa sai da ta Sha kuka auren shekararsa Daya da Dan watanni ta koma gidansu,tayi jinyar zuciyarta sosai kafin ta hakura da son Hussain shi kuwa Hussain baya ta tata Sam,Babanta ne ya maida ta school tayi degree tana gamawa ya samo Mata aiki Babba da NGO su Kuma duk inda aka turaka aiki dole sai ka je,Kano Suka kawota supervisor ce sune suka rabawa irinsu sababbin motoci masu tsada,dama Kuma a can Oyo tana da tata motar da Babanta ya siya Mata,shi yasa tazo kano ta Kama gidan haya har Suka hadu da Affan suke fada Kuma kusan a tare Suka zo Kama gidan ta Sha Matukar wahala a hannun Hussain kafin Allah ya yanke mata.

Affan

Affan Kuwa asalin Fulanin Zamfara state ne, sunansa Aliyu A. Aliyu,mahaifinsu su biyu Maza ya Haifa Yusuf shine Babba an haife shi da shekaru hudu aka samu cikin Affan,da cikin Affan Allah yayiwa babansu Aliyu rasuwa,Babar su tana haihuwa aka sakawa Affan sunan Mahaifinsa wato Aliyu shine aka boye sunan ake kiransa da Affan, su biyu Suka taso a hannun mamansu a Zamfara duk da cewar babansu bai mutu ya bar wata kadara ba face wata gona layi biyu,bayan Yusuf da Affan sun gama secondary School babu kudin ci gaba da karatu,sai Mamansu ta siyar da gonakin nasu ta hada kudin kaf ta Kira Yusuf da Affan tace kunga kudin nan nasan bazai isheku kuyi karatu ba ku biyu Kuma ina so a cikinku wani yaje yayi degree a rayuwa ya kuke gani Kai Yusuf gadon ku ne idan Kuma kowa bazai iya barwa kowa ba to sai dai mu Kama sana'a da kudin,Yusuf ya kalli Affan yace gaskiya ni bazan iya barwa Affan kudina ba,Affan Kuwa Nan take yace Yaya Yusuf ni na hakura da karatun dama kaga nine karami na bar maka kudin gado na halak malak kaje kayi karatu idan ka samu aiki daga baya ka biya min ni nayi karatun daga baya ai ba'a girma da karatu,Yusuf yayi farin ciki sosai karshe aka Nemo admission lokacin baya wahala a ABU Zaria Yusuf ya shiga ya gama degree dinsa gashi Allah ya hadashi da Abokinsa Dan gidan me kudi ya ja shi cikin Harkar kasuwancinsu na siyar da gwala gwalai har aka zo ma ana tura Yusuf kasar waje yana siyo kayan, a hankali a hankali Yusuf ya Zama me kudin gaske ya kera katafaren gida a Kaduna gida na gani na fada,ko aikin gomnati ma bai nema ba,ya manta da halaccin da Affan ya Masa ya kasa tunawa ya sashi a university,karshe da yazo zamfara da galleliyar motarsa Wai yazo daukan Mamansu zai maida ta can Kaduna kusa da shi,Mama tace Yusuf Saura Affan Yana ta Zama ba karatu burina ka biyawa Affan shima yayi karatu ya shiga University yace to zaiyi cikin ikon Allah watan mamansu Uku kacal a gidan danta ta kamu da ciwon sugar farar daya ta rasu dake Affan shima Yana gidan Yusuf din tun asali Allah yayo shi da son
Gayu da tsafta ga iya daukan wanka dama Kuma gasu kyawawan gaske.

Bayan mamansu ta rasu da watanni Yusuf ya fara wulakanta Affan kamar ba gidan dan Uwansa ba,karshe Affan har ya gaji ya fara sana'a haka Kawai sai ya saro irin Guava ya dinga siyarwa Yana samun kudinsa baya kula kayan Yayansa,ya koma sarar irin su safa da handkerchief yana bin titin kwalta a hannu Yana siyarwa,ya dawo ya koma koma siyar da su charger a gefen titi da Haka ya samu ya shiga University amma shi BUK ya samu a Kano ya dawo Kano Hostel a school ranar da ba school ya tafi siyar da kayansa a gefen hanya,har ya hadu da wani babban mutum yace yazo ya dinga zauna Masa a shago a kasuwar kofar wanbai Harkar Yan robobi,ya koma can Yana fama a Haka ya kammala degree ga Yayansa can kullum arzikinsa Kara gaba yake amma sisi baya bawa Affan bai ma San Ina yake rayuwa ba,Affan wata yarinya ya samu Yar talakawa Suka Fara soyayya Nabeela,Yana mugun kaunarta Kamar ransa a Kaduna take

Mamanta tana da ciwon zuciya kullum Affan akan taimaka musu yake duk abinda ya samo a wajen Maman budurwarsa yake karewa wajen nema Mata lafiya,Neman kudi yake Yana samu amma Maman budurwa kullum a asibiti can yake Kai kudin,magunguna shine ke siya, Basu da abincin ci shi zai siya musu a Haka jarinsa ya tarwatse babu ko sisi,Watarana Affan yaje zance Sabo da Nabeela ya koma Kaduna,ta rako shi gefen titi kenan Suka hadu da Yayansa Yusuf zai wuce a mota ya tsaya,Affan yace Yaya Suka gaisa ya nuna Masa Nabeela yace itace budurwata yace Nabeela ga yayana uwarmu Daya uban mu daya tace oh suka gaisa Yusuf sai kallonta yake gaba Daya Nabeela ta tafi da imaninsa,bayan Affan ya shiga Napep ya tafi sai ya dawo da motarsa ya Sha Gaban Nabeela yace ta shigo ya rage Mata hanya,Bata kawo komai ba ta shiga motarsa Suka tafi har gidansu har take fada Masa rashin lafiyar mamanta ya shiga gidan Suka gaisa tashi Daya ya basu dubu dari biyu,zuwa sati Yusuf ya koma gidan su Nabeela yace ta shirya zai fitar da mamanta kasar waje India nemo Mata lafiya Suka dinga murna
Affan ma tuni Suka daina ta tasa idan yazo ma bata taba fada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login