Showing 42001 words to 45000 words out of 85703 words

Chapter 15 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

609

sai ki ta min abu da kudinki karfa Watarana a min gori ni bana so nasan halin Mata bana Jin Dadi ki dinga kyaleni Ina biya Mana please bana so idan ba Haka ba Zan koma gida Kawai kin maidani yaro,Dariya tayi tace afwan to ka huta ,yace karki kawo min abinci nifa ba yaro bane ba Kuma duhun Kaine dani ba sannan Ina Jin turanci,tace to sorry na daina tace zanzo da dare muje yawo ta Kai hannu zata ja Masa gemu ya goce yace wannan fa raini ne ke ba matata ba sannan ba budurwata ba Zaki lalatani ya juya tare da rufe kofarsa,ta tafi tana Murmushi dama tsokanarsa tayi tasan fadin ransa.

Yau Kawu yana dawowa Siyama ta masa Sannu da zuwa ya amsa ta karbi kayansa ta Kai daki sai tsarabar Kauye lafiyayyen nonon shanu kindirmo cikin katon wani bowl,Kwan zabi,etc Aunty tace Sannu da zuwa Suka shiga daki Siyama kuma ta Kira Aslam,kashewa yayi tare da kiranta back sallama tayi ya lumshe Ido yanda muryarta ke tafiya da Imaninsa,inyini yaya ya aikin,lfy Alhmdllh ya furta Yana gyara kwanciyarsa saman kujera tace Kawu ya dawo yanzu,yace Allah mun gode maka tunda ya dawo lafiya daga nan Suka fada hirarsu ta masoya har Kawu ya fito yayi wanka tare da gabatar da Sallar Isha Yana Jin Siyama ta makale murya tana ta yiwa bawan Allah shagwaba,bata San yana jinta ba,tana kwance a tsakar gida suna Palo shi da Aunty ita Aunty ma bata ji me take cewa ba amma Kawu hankalinsa na kanta,karaf yaji tana cewa kasan Ina sonka nima amma sai kayi ta cewa Kai kadai kake so na gobe zaka Zo da Yamma,yace bayan kin daina zuwa layin mu ma,tace zanzo ne ,Kawu ya zaci Siyama gidan Farooq take shiga bai san ko taje unguwar ba a waje suke Zama Kuma tunda Nusaiba ta bar gidan sau daya taje,Kawu a ransa yace wato Siyama ba Wasa take ba zuwa zatayi ya Mata cikin shegen amma gobe zai gani idan zata fita, gajiya yayi da ji ya fito,Siyama tana ganin ya fito da Fushi tace Zan kiraka Yaya ta kashe wayar amma sai tayi kamar bata kashe ba taci ga da cewa ka jirani gobe zanzo gidanka da Yamma,Dariya tayi tace hmmm sai dai na zo,kawu yace Siyama zo magana tayi Aslam Kawu na kirana ka kirani anjima
Kawu ne ya daka Mata tsawa Allah yasa dama ta kashe wayar, yazo ya fisge Wayar tunaninsa wayar suke da Aslam ya Kara Wayar a kunne Yana masifa yace duk abinda ya samu yata Kaine wallahi Matukar aka lalata min yarinya Kaine ya Danna wajen red ya kashe bai kula ba dama a kashe take,yace ke Kuma Siyama duk abinda zaku yi kuyi bazan bashi ke ba ya juya ya koma daki.

Siyama ta fashe da kuka kasa kasa karshe ma ta koma dakinta ta kwanta,washe gari Kawu ya kafa ya tsare Yana jira yaga ta Ina Siyama zata fita,4pm yaga tayi wanka ta shirya ta saka hijab tace Aunty zanje karbo Miki Humrar, Kawu yace gidan ubanwa Zaki je,Ashe da gaske kike Siyama gidan Namiji Zaki je,tace nife ba can Zan je ba jiya ma kawai fada nayi amma na kashe wayar,Ni kike tsokana sabo da ni sa'anki ne ya taso zai sharara Mata Mari tace a'a bada Kai nake ba da Kaina nake tsokana,yace to daga yau ba inda Zaki je na hanaki fita ko kofar gida Kuma ki fadawa Aslam din Kar ya sake zuwa min gida tunda ba alheri kuke shukawa ba,ke Zaki iya sani inyi abinda banyi niyya ba.

Siyama bata ce komai ba tace kayi hakuri kawu ta koma ta zauna a dakinta,Aunty ta fito tace wallahi abinda kakeyi ba tsari gaskiya duk abinda yaron nan yayi maka idan yaji ka hanashi zuwa gidan nan ai mutuncinka zai zube dan Allah karka Yi haka ai da kunya,Siyama baza ta aikata ba wlh ba abinda zai faru me yasa kake haka wai,Kawu ne ya mike ya fice,Yana fita ya hadu da Maman Nusaiba ta dawo daga unguwa ta Masa kallon banza tace oh Mallam Dauda sai muka ji Kuma wannan matsiyacin zaka aurawa Yar rikon ka sabo da ba yarka bace za a zalunci yarinya a bata me karayar arziki,da yarka ce ai da baka yarda ba,Kai Kam juya marar amfani,ai Kai hoto ne a duniya mutum mutumi tunda baka haihuwa mene amfaninka baka San ciwon haihuwa ba baka San zafin da ba,in Banda Kai kwangiri ne kana gani 'yata ta fito sai da muka sa ya saketa sabo da bakin talauci shine Kai zaka Kai Yar wani sabo da zalunci me za aci da Aslam,ka duba Nusaiba yanzu ta shiga daula fantamawa takeyi yanda take so, tsohon banza ta juya ta wuce,Mamaki ya Kama Dauda ya bude baki haka Kawai shi ba kulata yake Yi ba ta bude baki taci mutuncinsa haka ta tafi,yace irin wannan annoba ne ga al'ummar duniya wannan matar Shehu Yana fama ai fasa fitar yayi ya koma gida,Yana zuwa ya fara bawa Aunty labari kaf har gwadawa yake yanda Mama tayi Masa,Siyama ta kyalkyale da dariya ta dinga dariya tace hakkin marainiya ne,hakkina ne wlh a guji batawa maraya rai gashi Allah ya saukar da aya,wlh Kawu Ina jiye maka Kar rabo ya kasheka lokacinka baiyi ba,rabo kisa yake watakil sai baka raye za ayi,gwara ka hakura Kar lokacin zuwan 'ya'yana duniya ya matso kazo ka hana zaka iya mutuwa,Kawu tunawa yayi yanda akace rabo na kisa tsoro ya kamashi Kar ya mutu,Shuru yayi tare da lulawa tunanin duniya,Siyama ta dinga dariya ta mike ta ebo kindirmo ta zuba sugar tana juyawa tana cewa rai ,Kawu yayi Shuru Aunty tace ayi bawa da kafiya haba Dauda.










AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


56-60



Official



By
AsmaBaffa







Page naku ne

UMMY M
MARYAM BASHIR
MBELLO








Dauda Yana zaune bai ce komai ba,Siyama tana kallonsa ko zata ji zai ce ya yarda amma sai ji tayi yace idan na mutu ma kwana na ne ya kare dama Allah yayi kwanana ya kare sabo da haka Ina Kan bakana Kuma karki sake yazo min gida,kwana uku Kawu ya hanata fita Kuma ya hana Aslam zuwa zance,Siyama duk ta Shiga duwa,Aslam ma Sai dai suyi waya a boye kasancewar yace sai ya kwace Wayar in ya sake ji suna waya,ai Kuwa Watarana Kawu ya Kama Siyama tana waya da Aslam,tana tsaka da waya sai ga Kawu Katsam ya Miko Hannu yace bani Wayar,Siyama tace Yaya Aslam karka kirani idan kaji Shuru Kawu yazo zai kwace Wayar,Aslam yace alright bashi I love you karki yarda a raba mu please,tace Inshaallah Muna tare har abada,Wayar Kawu ya fisge ya kashe ta gaba Daya ya juya ya tafi da wayar, Kawu Yana Fitowa ya fice daga gidan,Siyama ya bari tana kuka Aunty ce ta shigo ta zauna a gefen katifar Siyama tace kiyi hakuri Siyama,duk aure da Kika gani idan aka Yi sak ba wani kalubale to bai ma fiye Danko ba ko Mene zaka Nema idan da nasara sai an samu matsaltsalu sai an Sha wahala,abinda nake so dake kici gaba da addua idan Aslam ne Alkhairi Allah ya baki shi idan Kuma ba Alkhairi ne bane Allah ya zaba miki mafi Alkha....ba wani mafi Alkhairi Aslam ne Alkhairi na Kawai idan ana son zaman lafiya a bashi ni tun kafin na kangare na daina Jin magana gwara ma ki fadawa mijinki tun kafin na Fara fetsara a gidan nan,Aunty tace to fa ku Yara idan kuka tsunduma bakwa Jin Kira ai sai kiyi tunda bakya Jin magana..

Siyama ranar haka ta yini sukuku ko aiki bata taya Aunty ba,Aslam kuwa gidan da Mum take yaje ya sameta a Palo ita Daya,bayan ya gaida ta,Mum tace Aslam kamar kana cikin damuwa kwana biyu Naga Kuma kamar ka Dan rame lafiya? Marairaicewa yayi sannan ya Fara bawa Mum labarin komai,ita Mum Murna takeyi danta ya samu mace,yace Mum kina murna baki ji me nace ba Kawunta yace bazai bani ita ba Kuma ya kwace Wayarta sannan yace Kar na sake zuwar Masa gida,Mum ta kalli Aslam tace Inshaallah zai hakura karka damu ka kwantar da hankalinka,Mum taya hankalina zai kwanta idan ban sameta ba fa ya zanyi,Ni ban taba son wata haka ba,ka kwantar da hankalinka nace Inshaallah zai hakura Kuma ko waye haka zaiyi a matsayinsa na uba babbar kawar yarsa dole ya hana,Addua zaka Yi sosai,Aslam yace yanzu Mum baza kije min ba? Wannan yakin naka ne Aslam ka dage kawai,Shuru yayi Kawai ya zuba tagumi ya tsinci muryar Mum tana cewa Amma na maka sha'awar Siyama,Ki daina sha'awar min Mata Ni kadai nake son abata Wai yaji haushi tace baza taje Masa ba, Mum ta dinga dariya tace to aci gaba da sonta lafiya,tashi ma yayi ya bar gidan.
Bayan kwana uku Aslam duk ya wani fututtuke ya tashi hankalinsa ya rasa inda zai sa Kansa rashin Jin Siyama,itama bangaren Siyama haka.

Zuwa Yamma Siyama da Aunty Suna tsakar gida saman katuwar tabarma suna Jin radio Kawu Yana zaune saman kujera aka sako wakar soyayya Siyama ta mike zaune tana saurar wakar
Mawakiyar tace kaine tunanina,Siyama tana bada amsa uhmmm Aslam ne wannan wakar sak tamu, mawakiyar ta sake furta Kaine ruwan Sha na,Siyama tace me gardi ma ruwan, kaunarka tayi girma a zuciya tace tabbas haka ne Aslam dina,Zo ka kula Dani me so na inji me wakar, Siyama harda hawaye tana Jin wakar Kawu ya tsaya kawai Yana kallon ikon Allah shi da Aunty, kuka ta saki sosai tasa tafukan hannayenta tare da rufe fuskarta,Aunty tausayin Siyama ya kamata,tana shesheka tace amma Aunty ke da Kawu ba auren soyayya kuka Yi ba da alama baku San mene so ba,Kawu ta kalla tace Kawu kasan Kuwa me nake ji a raina ka tausayawa yarka Kawu ,shi kuwa ko kulata baiyi ba.

Zuwa dare Aslam ya kasa daurewa yazo da Kansa gidan ya Samu Kawu ya tafi wajen abokansa Bayan Sallar Isha,Aunty tana daki sai Siyama a tsakar gidan zaune ta hada Kai da gwiwa,Aslam da Kansa ya shigo gidan ba Sako ba,tana Jin taku da kamshi ta dago da sauri,Siyama ta mike Zumbur tana kallonsa,tsoro take ji Kar Kawu ya shigo ya samu Aslam hannunsa ta ja da sauri tayi maza ta turashi dakinta,tana turashi ciki Kawu ya shigo gidan Aunty ma ta fito tayiwa Kawu shimfida a tsakar gidan Sabo da ana zafi a waje suke kwana,Siyama ta dora Hannu a Kai tana kallo Kawu ya kwanta,Aunty ma tayi nata shimfidar gefen Kawu ta kwanta,Siyama ta Fara tunani ta ya Aslam zai bar gidan oho,Aunty tace kin tsaya Mana a kai ke baza kiyi shimfidar ba? tace sai can anjima,Kawu yace bar algunguma ita ga Yar soyayya,Siyama dakinta ta Shige ta kulle kofa harda sa key sun zaci duk fushin soyayyar ne.

Ta samu Aslam a katifarta a zaune,a kasa ta zauna shi Yana katifar tana Murmushi wani sanyi take ji Yana ratsa ta,kallonta yake sanye take Riga da skert na Atamfa masu kyau,Ina yini tace tana Jin kunya amsawa yayi kasa kasa,ya furta ya kike kwana biyu naga ma kalau kike ai ko missing Dina baki yi kawai cin abincin ki kike Yi kina koshi Ina can hankalina a tashe,Siyama tace ka taho min da wata Wayar? yace no Kawu ya hana muyi hakuri yanzu idan na baki wata zai ce mun raina shi bai kamata ba,Siyama tace to shike nan ta turo baki tana cewa ai ba ni kadai ce na damu ba na daina damuwa ma,na daina tunani Kawai uzurina zanyi,dariya Aslam yayi Wai masifa takeyi nan bayan kasa kasa take magana a hankali Kar aji wai,da dan karfi yace haka zaki min,zaka jawo Kawu yaji kayi kasa kasa ta furta tana rufe baki da hannunta, Murmushi ya saki hankalinsa kwance ko a jikinsa yace ki daina fara'a a gidan nan yarinya karki bari a hanaki Saurayinki idan Kika yarda babu Wanda ya Isa ya aure ki,Siyama tace ai Ina ta yin tawaye yau ma kin cin abinci nayi sai 2pm,dariya ta Kama Aslam yace ai baki gwaninta ba dan 2pm kowa lokacin yake cin na rana,tsutsar cikina ta tashi kwana biyu rashin mutunci suke ji,dariya yayi ba shiri yace to kici ki koshi karki zauna da yunwa kinji,Siyama har da kuri tace gobe za aga bala'i sai 4pm zanci abinci,Aslam yasan baza ta iya ba amma yace ni dai na fada Miki karki sake a baki wani sai ni,tace af bata bakinka kake Yi ai ka lashe zaben zuciyata ta nuna kirjinta ta bangaren hagu tace Kaine a nan barin ta sake nuna hagu tace nan ma ka Sha kwana ta nan barin Kaine,tsakiya ma Kaine ka gama mamayeta,dariya yayi yace na gode haka nake so nima haka ko Ina kece you are my world,yace Ina so na tafi,tace ai kuwa Kawu basuyi bacci ba ka jira kawai,Allah yasa da motar Sabeer nazo tare muke , Alhmdllh tace suna ta hirarsu ta masoya ko bacci basa ji har Suka shiga labarin duniya,Siyama tace ta wani Yoruba malamin mu yace babu makaryaci irin bahaushe yanzu idan bashi da lafiya kana cewa ya jiki zai ce da sauki bayan 20mnt sai aji ya mutu,dariya Suka yi Aslam yace su ai idan ba sauki Kawai ba sauki mu musulmai Kuwa ba haka tsarin musulunci yake ba,Wai yasan ba sauki sai yayi karya yace da sauki amma sai aji ya mutu,suna ta nishadinsu basu sani ba sai gani suka Yi 11:30pm,Siyama tace bari na duba maka ko sunyi bacci,Fitowa tayi a hankali taje ta leka fuskar kawu har da sa Hannu ta fifita fuskarsa Shuru Yana ta baccinsa,Aunty ma haka ta sake lekata a hankali tace Aunty Aunty, tana ta bacci shuru da sauri ta koma ta fadawa Aslam sunyi bacci muje,Takalmansa ta kwashe ta rike a hannunta Suka fito Yana gaba Yana tafiyarsa normal har Suka je bakin kofa a hankali ta bude Masa kofar gidan ya fita sannan ta ajiye Masa takalman ya saka ya dawo zauren again sai kace maye tace ka tafi Kar Kawu ya tashi ya Kama ni,rungumeta yayi kamshinsa ya cika Mata hanci me dadi, tace Kai bafa kyau amma shedan yasa tayi Shuru harda lumshe ida ta zagaye shi da hannayenta dagata yayi sama a haka,dariya ta danyi ya ajiyeta a kasa sannan ya janye jikinsa tare da furta good night Yau ki kwana kina mafarkina Kuma ki ganni na aureki Muna soyayya,dariya take kasa kasa tace hmmm ai da na fika murna Zan hango mu a Palo ina zuba maka abinci,zanyi na ganmu a kitchen Muna girki,Aslam yace ban iya girki ba fa ni,dole ka dinga tayani Kuwa Indai kana gida,ki dinga Jin tausayina Baby,ai sabuwar hira Suka dasa ya manta ma Sabeer Yana jiransa a mota,yace zanzo jibi da dare yanzu na gane yanda zamuna yiwa su Kawu tace to sai kazo dare yayi fa 12am ,yace Kuma Sabeer Yana jirana ba,fita yayi ta tsaya a bakin kofar tace sai jibin Zan jiraka yace ko kiss Babu?

Tace sai a gidanka yace Allah yasa ta furta ameen Hannu ya Miko Mata ta kai zasu tafa ta janye,dariya ta bashi ya tafi gari duk ba mutane,sai da ya kule sannan ta maida kofa a hankali ta rufe ta dawo tana shigowa Kawu ya farka tare da hasketa da touchlight me mugun haske kamar ta Kama barayi,yace daga Ina kike? tace kofa naje rufewa na zaci ba a rufe ba Kuma ma Ina zanje babu mayafi,Kawu yace to wuce ki kwanta tace to Sum sum ta wuce dakinta ta kwaso kayan shimfidarta ta shimfida a gefen Aunty ta kwanta cike da nishadi sai Murmushi takeyi ita Daya.
Aslam kuwa Yana komawa Sabeer har yayi nisa a bacci cikin motar ya tashi Yana masifa a Ina ka zauna haka? Na fada maka fa ka shirya jirana domin Zan iya dadewa tunda gidan Zan shiga nan ya bashi labari a dakinta Suka buya,yace amma ka cika Dan Iska Aslam tab wannan ai ganganci ne,Tsaki yaja yace ba abinda bazan Yi ba akan Star dita,zaka ga star ya yiwa mota key Suka tafi gida a gidan su Sabeer ya kwana yau.

Siyama kuwa ta kwanta yau soyayya ta hanata bacci in Banda Aslam ba abinda take tunawa a ranta Katsam taji Aunty tana kiranta kasa kasa kamar munafuka,Siyama tayi Shuru a zuwan bacci takeyi,karaf a kunnen Siyama taji Kawu Yana magana kasa kasa tayi bacci? Aunty tace ae yayi nisa ma baccin,Siyama harda Jan munsharin karya,Kawu yace tashi mu tafi Aunty ta mike kamar barayi Suka Fara tafiya Sadaf Sadaf suka fada daki,Siyama tace iyye tana dariya a boye tace an shiga Uku yanzu Kawu dama bai bar Harkar nan ba ya tsufa ai wannan sai yara,can Kuma tace na tuna Aunty da kuruciyarta itama tana bukata,lallai Kawu dama haka yake Dan is....bakinta ta rufe tace amma ni ya hanani sakewa da masoyina shi ya ja tasa sun tafi duniyancinsu ba komai akwai Allah.
Washe gari da safe farkawa tayi taga Auty a shimfidarta kawu ma a tasa,Siyama tace wato da aka gama sai aka dawo dama haka ake Mana wayo,yau zanga tsiya wlh kaima baza kaji Dadi ba Allah ya kaimu dare cewar Siyama,Kawu yace ke sai Rana ta fito ne zakiyi Sallah? ta mike taje da brush tayi tare da Alwala ta koma dakinta bayan tayi sallah taci gaba da baccinta hankali kwance.

Wani Daren Yana zagayowa Siyama ta koma palon Aunty tace yau a nan Zan kwana Naga ta tsiya,Siyama tayi baccinta Aunty ba yanda bata Yi da ita ba akan ta koma dakinta taki tashi Wai ita a nan zata kwana,Aunty fita tayi inda suke kwanciya a tsakar gida ta guntsawa Kawu tace nifa yau a matse nake da wuri nake so ga Siyama ta kwanta a palon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login