Showing 57001 words to 60000 words out of 85703 words

Chapter 20 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

616

taci gaba da cewa ga amaryarka me kayan aiki ya sake fashewa da dariya,ta nuna kirjinta da hannu biyu tace Kai kake da nan, a taba can a latsa nan sai na Siyama ikon Allah ta furta tana nuna Boobs dinta ,Affan Yana dariya ya rungumeta tare da dagata sama,tace ban gama kirarin ba fa,a lafiya dai....Baki ya rufe Mata da nasa yana sha

Tace yau fa mu fita zamuyi yawo ba batun wani amarya duk inda zaka je sai na bika, yace to duk abinda kike so,Siyama ta Fara murna zata fita ba kulle,bayan sun karya a Palo Suka zauna yana zaune a doguwar kujera ya bude kafafunsa daya kafar a mike a saman kujera Daya kafar tana kasa Siyama ta kwanta a tsakiyarsa gadon bayanta Yana saman kirjinsa Yana koya Mata game a waya sun rike Wayar tare da hannayensu duka tana gwadawa suna ta fama suna nishadi.
Zuwa Yamma Suka dau wanka kamar zasu je party tasa wata arniyar Arabian gown black taji ado silver color, takalmita da jaka Silver shi Kuma shadda ya Sha Silver me tsadar gaske kana gani kasan ba karya ya rike hannunta Suka fita wata rantsatsiyar Jeep dinsa,wani katafaren Joint Suka je duk Wanda ka gani a wajen to ya Isa,suna shiga rike da Hannu Suka iske Nusaiba a wajen mijinta ya kaita amma Abokinsa ya kirashi ya fita yace ta jirashi nan da 30mnt Yana fita su Aslam Suka shigo,sun ga Nusaiba amma kamar Basu ganta ba Suka zauna a kujera Aslam ya jawo Siyama ta zauna a saman cinyarsa yana sani yayi hakan,Siyama ta kasa Zama sabo da kunya ta koma saman kujerarta ta zauna,Nusaiba ta firgita taga Aslam Kamar a wata hadaddiyar mota Suka fito amma bata kula ba sosai lokacin,Siyama ce tace Honey bani key din motarka na ajiye maka a handbag dina,Nusaiba mikewa tayi ta kalli motar duk wajen babu me irinta tunani tayi tace maybe arowa ma yayi karya ne talakane har yanzu wai ni za a yiwa burga ta ja tsaki ta zauna tare da gallawa Siyama Harara,Siyama ko kallon Nusaiba bata Yi ba,ganin Nusaiba tana ta kallon Aslma tace please Ni ka canja mana joint muje Cenema kallon film yace alright ya riko hannunta yace sai abinda Kika ce ai shi za ayi Baby yaja hannunta Suka fita,Nusaiba tace karyar banza bibiyata sukeyi shi yasa Suka zo za a min burga ni Ina mamaki ma da har yanzu yake kamshi me dadi haka sutura me tsada ya kamata na Fara ganin wuyan rigarsa ya kode ya yage Yana wari amma kullum mutum kamshi Kamar namijin karuwa,harda aro mota azo za a rude ni Yan Iska Yan karya Yan Yan yan...ita Kuma Wai sa car key din a jakata sabo da naji suna da mota fake....ta ja tsaki,tashi tayi ta leka bata ga kowa ba motar da take tunani a ita Suka Zo bata ganta ba tace sun shiga taxi matsiyata Yan karya me motar ya dauki abarsa ta juya ciki.

Siyama kuwa zasu shiga Cenema Kawai Aslam yaji sha'awa shi bazai iya jira ba,matarsa yake so ya murza,order ya musu na take away kaji da su ice cream da sauransu tana rike a hannunsa yace muje gida an fasa kallon Watarana sai mu zo bazan iya barin sabuwar Amaryata ta huta na hours ba ace bana taba komai ke muje bazan iya ba na fasa yaja hannunta Suka Shiga mota,Siyama tace mun fasa? Yace ae Nima ai ganganci nayi da na fito da Amaryata bazan yarda ba gaskiya wayo zaki min muje gida haka Kawai kowa idan yayi aure Yana hutawa ni shike nan na zauna a kallon film zaki min wayo,dariya ya bawa Siyama yace haka Kawai sai kalle min matata akeyi a banza...






Masu sharhi Ina godiya






AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️ AUREN MU🛢️


76-80



Official

By
AsmaBaffa







Page naki ne

AUTARESS









Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da ledar a gabanta tare da cewa gashi inji Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya musu sallama ya tafi

Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba ya koma gida abinsa.

Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya zubo Masa Yana rokonsa yace tashi ka bar min gida cikin tsawa ba shiri ya tashi ya fice,ran Aslam yayi mugun baci sai da Siyama ta fito ta zauna a gefensa tace lafiya yace Wai ashe Wanda ya auri Nusaiba tun tana da aurena yake bibiyar min Mata Yana fita da ita,Siyama nan take kishi ya motsa tace to sai me tunda Kun rabu shi ka kore shi mene na wani cewa Yana bibiyar maka Mata,au dama matarka ce shine harda tashin hankalinka haka da damuwa akan wata banzar Nusaiba,okay na gano son abarka kakeyi sai ya saketa ka dawo da ita,Aslam yace Allah ya baki hakuri ni ba haka nake nufi ba nufina a lokacin ai tana matata ba Wai yanzu ba,Juyawa tayi tace ba komai,fisgota yayi ta fado jikinsa yace ban yarda ba ai Indai kaji bahaushe anyi Masa laifi yace ba komai to wlh da komai dawo nan, dariya ya bata amma ta maze tace ka sakeni nace ba damuwa,yace akwai fa ayita ta Kare a nan baki Isa ba,baki ta turo yayi kissing dinta tare da furta to kiyi hakuri bazan sake ba Ni dai magana ta wuce ya mutu,tace amma kasan.....kafin ta karasa yace dan Allah da annabi kiyi shuru Allah ya baki hakuri ni dai Indai akan wannan ne,Siyama tayi Shuru tana zaune a cinyarsa,yace to ki min magana Mana kiyi murmushi,tace cewa fa kayi dan Allah nayi shuru to nayi shuru,Aslam yace kai Ina Shan wahala dake ai dai nace kiyi hakuri, tace na hakura karka sake min zancen Nusaiba wallahi idan ba Haka ba zaka ga danyen kai,dariya yayi yace to naji bazan sake ba yanzu ma kuskure ne ke kika fassara ni daban,cike da shagwaba tace mutum Kawai ka kawo zancen wata ballagazar banza bazara iskar damuna,Boobs dinta ya cafka ya shiga sarrafata ba shiri tayi shuru duk da cewa ba wani abu zaiyi ba face rage zafi sai ta warke tukun.

Washe gari Sufyan Ya sake zuwa gidan Aslam bai same shi ba ya fita yayi murna dama Siyama yake so ya gani Yana compound me aiki tace Wai tazo inji Mijin Nusaiba,Siyama Hijab ta saka ta fito bayan sun gaisa rokarta ya dinga Yi dan Allah madam kisa baki me gidanki ya maidani bakin aikina,Siyama tace kasan kayi kuskure Babba kaima Wanda gaskiya ko ni bazan iya Masa magana ba a kanka kayi hakuri tunda yace a'a to fa sai hakuri kayi hakuri Allah ya baka wani aikin,Yace dan Allah Siyama ki taimaka min,Siyama tace Ina ma Zan iya taimakonka da nayi amma bazan iya ba kayi hakuri Kawai ta juya ta tafi abinta haka Sufyan ya fita jiki ba kwari,washe gari Aslam ya Kira Sufyan ya bashi takardarsa ta sallama daga aiki Yana ta rokonsa amma Ina baya Jin Kira.
Sufyan Yana komawa gida ya iske Nusaiba ta dawo daga gidan iyayenta Wanda ko tambayarsa bata Yi ba,takardar ya wulla Mata ransa a bace yace Kinga abinda Kika jawo min ko,kin gani ko Yar iska dabba wacce bata San me take ba jahila,Yar talla, kin Sa na bakantawa Iyayena kin jawo an koreni daga aiki Allah ya Isa tsakanina dake kuma ki koma inda Kika fito gidan ubanki na sake ki saki daya,Nusaiba tace ka sakeni ? Yace ae zata Masa rashin kunya ya hau jibgarta ya Mata jina jina sannan yace wallahi ko hankici baza ki dauka a gidan nan ba baki zo da uwar komai ba duk ni na siya Miki sabo da Haka ki koma gidan ubanki haka,Nusaiba tana kuka jiki duk kulun duka tafi karfin ta taba komai Dan kuwa shi ya siya mata,Haka ta mike tana dingishi zata tafi,Hannunta Sufyan ya fisga ta Fadi a kasa ya dinga janta tana ihu Kamar wani buhun gishiri haka ya bude gate ya jefata waje ya kulle gidansa ya barta a nan tana ta uban kuka har ta gaji ta mike da kyar ta shiga Napep sai gida,tana shiga da kyar take tafiya tana kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi.

Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera tana kallon hadadden Office din tace Sannu da aiki yace yawwa suna haka sai ga wata arniya ta shigo da wasu takardu sanye da gown ko gwiwa bata Kai ba komin surarta a waje ta Sha kitson attach tayi kyau gata da hips,Raudah baki ta bude tana kallo shi bai kula bama Signing ya Mata tare da Mika Mata ta karba ta dauki Hanya zata fita tabi ta gefen Raudah,da yatsa Raudah ta dan taba Duwawun matar, Affan yace mene Haka beb? Tace wannan wace? Yace Secretariat ta ce,tace kana nufin kullum sai kaga wannan? Yace mene ne Wai? Baza ka kawo Namiji ba sai mace to duwawunta kake kallo ko me,kalli fa duwawunta kullum da safe sai ka ganta Ina can na saki baki hai a bude Saurayina yana nan yana kallon duwawun Chinaza,wlh Affan idan ka kalli duwawunta bazan yafe ba,Affan yace Wai in tambayeki baki yarda dani ba,haba Raudah kishin nan naki yayi sau nawa zan fada Miki ke kadai nake da ita,bazan iya cin amanarki ba,I will never ever cheat on you Karki bari muyi auren zargi so kike kishi ya halakar dake,Ni wlh Kawai ka canja sakatariya zuwa sakatare Namiji gaskiya ban yarda ba,yace ba laifin data min baki Isa kisa na sallameta ba Kuma bani na kawota ba Liman ne ai kin san gidansa tunda munje tare kin gaishe shi je ki fada Masa ya canja ta Indai kin San haka zaki to karki sake zuwa Office Dina ya mike tare da dukan table sai data tsorata yace tashi ki tafi gida bana son zargi bana taba ko hannun mace akan kishin banza kizo ki sani gaba ki hanani sakewa ba ke kadai kike da saurayi ba sannan idan niyyar cutarki nayi ta ya Zan Bari ki gane, tashi ki tafi bazan cuceki ba Ina sonki babu wacce nake so sai ke bana ko budurwa bare neman Mata bana son zargi,Raudah mikewa tayi ta Fara hawaye yace oh my God me na miki? tace ni dai karka kalli duwawunta,yace to naji bazan kalla ba idona ma Zan rufe muje na rakaki mota a haka ya lallaba Raudah ta koma gida.

Tunda ta koma gida part din Landlady ta shiga suna Hira tace karki yarda da Maza Yar uwa maciya amana ne duk yanda kike da kyau sai sun kula Mata,ki kula da Affan sosai yanda yake da kyau Mata bibiyarsa suke kisa Ido akansa idan ba Haka ba wata ta kwace Miki shi,Landlady ta dinga zuga Raudah,Raudah har da bata labarin sakatariya,tace to ki shiga ki fita a sallameta a canja masa Namiji ko mace me addini, Raudah ta Fara tunanin ya zata yi ai da yamma ta shirya sai gidan Liman
Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana ta godiya.

Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi, Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama.
Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta dakko Masa file sai da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login