Showing 75001 words to 78000 words out of 85703 words
rigar baccinta pink ta Sha kyau na musamman,Shehu duk an gigice anga sabon jini,kajin da ya siya Mata sai da ya siyawa yaransa ya basu nasu na Amarya Kuma daban,Nusaiba yaushe rabon da taga nama tana Kauye sai yanzu,kannenta su Ameer sai dariya suke kyalkyala mata.
Landlady wayayya ce wacce tasan ta Kan maza ga iya shagwaba da kisisina Shehu tun a wajen kwanciyar aure yasan sai yanzu yayi aure da haukarsa Kawai yake yi,washe gari kasa Fitowa yayi ko kafar gida Yana ta soyayya, Landlady girkinta tayi Nusaiba itace tayi nasu girkin ita da kannenta,da yamma Kuwa sai ga Shehu a kitchen ya ajiye hula a gefe Yana taya amarya wanke wanke,Yana gamawa yazo Yana yanka Mata Alayyahu,yau ma Shehu kwanan farin ciki yayi sun gurji juna shi da Landlady gaba daya Shehu ya susuce ya samu mace Yar gyara wacce tasan kanta,Satin Landlady daya ta Fara girki da su Nusaiba duk da haka Nusaiba bata taba shiga gidan ba sai da ta gaji taga kannenta sai shatara ta arziki Aunty Amarya take musu amma banda ita,haka da Yamma tayi wanka ta shirya ta Shiga bangaren Amarya a ranta tace gaskiya Aslam bashi da mutunci mutumin nan ba karamin makiri bane shine yayiwa Amarya wannan mu Kuma ko oho Nusaiba harda goge kwalla ta shiga Palo ac da kamshi Kawai ke tashi,Abbansu taji a kitchen suna ta Wasa da dariya da Amarya suna girki a hankali tayi Sanda Kamar barauniya ta leka kitchen din ta hango Landlady akan cinyar Shehu suna kissing,da sauri ta dawo baya tana rufe Ido ta zauna tana mamaki tace oh duniya ashe Abba dan duniya ne haka,Amarya ce tace naji Kamar yarmu na sallama ta mike ta fito tasan Nusaiba a hoto,Nusaiba tana ganin Amarya shegu kudi ba karya sai ta Mata kwarjini har kasa ta rusuna tace Ina yini Aunty,Aunty ta amsa da fara'a tace sai yau Zaki zo min kema kishi kike taya mamanki ko banga laifinki ba,Nusaiba mayyar masu kudi tace ba haka bane tana sadda Kai Kamar ba Nusaiba ba ,Shehu ne ya fito,Nusaiba tace Sannu Abba tana Zama a kujera ya amsa da fara'a sai rawar kafa yake sabo da anzo gaida Amaryarsa,bedroom ya shige Landlady tace Nusaiba jeki kular min da abincin can bari naje,Nusaiba ta Shige kitchen Itakuma Amarya ta wuce ciki tare da Shehu suna soyewarsu aka bar Nusaiba da aiki,Wasa Wasa sai gashi Amarya bata aikin kirki a gidan nan gaba Daya kusan Nusaiba ce ta Zama Yar boyi boyi ita take Kai kanta tayi ta dirzar aiki ba tare da an sakata ba sabo da Landlady tana da kudi.
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️
96-98
Official
By
AsmaBaffa
Page naki ne
FUTURE RM
Nusaiba gajiya tayi da rashin mahaifiyarsu ta tattara kannenta suka koma gaban Abbansu tare da durkusawa,Shehu yace Yaya aka Yi ne? Nusaiba tace zuwa Muka Yi mu roke ka dan Allah Abba ka dawo da Mama gida badan halinta ba ko don mu,Amarya Landlady tana ji,Shehu yace babu ruwanku Kar na sake ji Kun min maganarta Indai maganarta Zaku kawo min to karku zo inda nake,ku tashi ku bani waje ya musu tsawa suka mike sum sum Suka bar wajen,Nusaiba babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa gaskiya halin Nusaiba da uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi.
Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata.
Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah, Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye.
Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi.
Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki ta bature Sorry Sorry.
Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty.
Washe gari da Yamma Sunday Aslam Yana gida Yana zaune a center carpet Yana shan lemo Yana aiki a system Siyama kwance take a cinyarsa tayi dai dai da dan cikinta tana ta Wasa da botin din rigarsa Suka ji door bell sai da dan cikin Siyama ya motsa sakamakon karar da yaji ba zato,Siyama tace wash dan cikina zai fasa min ciki ni bana son karar nan tsoratani take yi yace Zan cireta to tunda baki so amma idan muna sama fa taya za muji knocking? ai idan na haihu sai a maida yace to ba damuwa,tashi ki bude kofa Siyama direct tace bazan iya ba wlh na gaji kayi hakuri,dariya yayi yace wannan ciki Ina ganin ta kaina da shi,tashi to na bude Siyama tace bazan iya ba dan Allah karka tashi naji dadin kwanciyar nan Allah kace su shigo mana,Aslam yace yau baza kiji kunyar ba kenan? Tace ko Kawu ne sai dai yayi hakuri bazan tashi ba,da Kansa yace ku shigo Aunty ta bude kofa tare da shigowa bayanta Mama ce sanye da Hijab,Aslam Yana ganin Mama ya daure Fuska tam ba mutunci,Siyama kuwa bata tashin ba kamar yanda ta fada,Aunty ce ta harareta ba shiri ta mike zaune a gajiye ba dankwali ma a kanta doguwar rigace a jikinta Yar kanti tace Aunty Sannu da zuwa,ta gaishe da Aunty ta gaisar da Mama ta amsa tana washe baki harda cewa Siyama Allah ya raba lafiya,Kitchen ta shiga ta kawo musu lemo da snacks ta zauna kusa da Aunty ko minti daya bata Yi ba ta kwanta a cinyar Aunty,Aunty tace ke dagani a kanki aka Fara ciki da kinzo waje ki kwantawa mutum a jiki,Siyama kin tashi tayi har Aslam ya gaida Aunty Kawai ko kallon Mama baiyi ba ya mike zai haura sama Aunty tace Aslam wajenka nazo fa,dawowa yayi ya zauna yace Aunty gani,Aunty tace wata Alfarma nazo nema wajenka dan Allah Aslam abinda Mama da Nusaiba Suka maka ka yafe musu kayi hakuri Allah ma Yana yafe Mana bare dan Adam ka yafe Mata,Mama ta karbe harda durkusawa a kasa dan Allah Aslam ka yafe min nasan munyi maka laifi ka yafe min dan Allah,Aslam ya kalleta shekeke bai ce kala ba,bazai yafe ba,Aunty tace kayi hakuri Aslam Allah Yana son bawa me hakuri da yafiya,ganin Aunty ce take ta rokonsa Kawai yace to amma fa bai ce ya yafe ba,Aunty taci gaba tace dama Shehu ne tunda ya saketa yau wajen watanta hudu yaki ya dawo da ita babu irin hakurin da bata bashi ba yaki yarda kowa a dangi da Yan Uwa har abokai sunje wajensa akan Maganar yaki amincewa,Kuma wlh ta tuba ta gane gaskiya a matsayinta na Yar uwa musulma akace yau Allah ya shiryata ai abin farin ciki ne ga mu musulmai to dan Allah ka sa baki kayiwa Shehu magana ya maidata Kaine kadai zaka fada Masa yaji dan Allah,Aslam ya gama Jin Aunty yace ni Aunty mene hadina da iyalin Abba Shehu,Ina yaro me zai kaini shiga zancen manya in yaga dama ya dawo da ita idan bai ga da ba ta hakura ta koma Kauye inda tafi wayo ni ba ruwana da ai bata san dan Adam me daraja bane bata taba zaton ma Zan Mata rana ba a rayuwa,Aunty tace bana son taurin Kai Aslam ya Ina rokar ka kana botsewa,yace Aunty shike nan taci darajarki albarkacinki Zan Masa magana amma bata da matsayin da Zan taka har can wajensa Zan dai kirashi a waya kawai in ya yarda tayi murna idan bai yarda ba ruwanta mutum dai abinda ya shuka shi zai girba Kuma Alhmdllh ko yanzu tun a duniya ba ayi nisa ba sun Fara girban nasu hukuncin,bazai yuwu ka shuka gero kace zaka girbi shinkafa ba bazai yuwu ba kowa yayi yanda yake so to bazai ga yanda yake so ba, idan Kuwa kayi abinda baka so to kuwa zaka ga abinda kake so haka rayuwa take,basai Yar taki ta auri me kudin ba jarinku kuci gaba da cin duniya gashi nan talaka ma ta rasa yanzu sai ku nema Mata hatimin annabi Yusuf ta sha ko ta samu ko talaka ne abinda bakwa so din dai...Aunty ce tace ya Isa haka Aslam idan baza kayi ba ka Mana Shuru ni ban ma San haka kake da mugun riko ba,Aunty baki San me aka Masa bane har uwarsa sun zageta babu wulakancin da basuyi Masa ba cewar Siyama,Aunty tace bana so Siyama gyara nazo bana son tone tone ke me Miji Zaki zake ki tare masa Maman Nusaiba ai uwarki ce kema,Mama tace Siyama kiyi hakuri ki yafe min,Siyama tace ni baki min komai ba zagina nane da tsine min da kuka yi Kuma kanku ta koma to haushin me zanji,Aslam yace ko ma dai mene dan kanku Kuma ko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba Zan Masa magana,Aunty tace yawwa ko Kai fa Basu dade ba Mama tana Jin tsoro ta damu sai an tafi Aslam tsoro yake bata,ai Kuwa Suka tafi Suna tafiya Aslam yace lallai Aunty ai Kawai lallaba su nayi ba inda zanje ko waya bazan Masa ba ta shekara dari bata koma gidan Miji ba,Siyama tace a'a fa ka riga ka fadawa Aunty yanzu jiranka zata yi kayi hakuri dai kayi Masa waya sabo da Aunty idan baka yi ba ka raina min Iyayena fa Kuma ni nasan mijina ba haka yake ba Wanda na aura me yafiya ne da hakuri yace naji Mrs Aslam zanyi ku kyaleni na Sha ruwa please,Jikinsa ta koma ta kwanta.
Yaran Mama Kuwa tunda Suka ji tana gidan Kawu kullum suna gidan Wajen uwarsu Yara da mahaifiyarsu akwai shakuwa ta musamman sabo da yaran Aunty da Kawu Suka dage Shehu yayi hakuri ya maida Mama sai Nusaiba itama duk da Shehu Yana Mata fada haka take bashi hakuri bata gajiya amma Shehu ya kafe yaki abinka da me hakuri bai iya Fushi ba, Landlady ce ta siyowa su Nusaiba kayan sawa harda takalma da kudinta ganin Basu da suturar arziki Musamman Nusaiba da Sufyan ya kwace Mata sutura gaba daya ya hanata shi yasa bata da kayan sawa,Aunty har Raudah ta bugawa waya tace dan Allah ta hado Mata kayan da zata bayar kwance ta Aiko Mata zata bawa Yar mijinta bata da kayan sawa,haka Raudah ta ciko Leda da Kaya masu kyau kusan ma sababbi ne Landlady ta bawa Nusaiba kala bakwai a ciki sai Ihsan da take Yar budurwa itama aka bata wasu a ciki kala hudu, har takalma kala hudu Raudah ta bada da mayafai duk aka bawa Nusaiba,Nusaiba tana murna sosai wani bangaren Kuma idan ta tuna tsiyar data shuka da daular da ta shiga ita da sutura ma Sai dai ta bawa wani yau ta dawo gidan jiya ita ake bawa kwance a rayuwarta ta baya talla ne Kawai bata dauka ba,Watarana cikin dare sai kuka take tilka ta koshi.
Tunda Aslam yace zaiyi ma Shehu magana ya manta ma da batunsu har an wuce Sati biyu Mama tana jira a gidan Kawu,Kawu ma yaji Shuru Shuru waya ya bugawa Aslam da Kansa yace bayan sun gaisa yace Aslam kaci gidanku Ina batun Maganar da kace zaka yiwa Shehu akan matarsa,Aslam sai yanzu ya tuna ma da batun Yana Office ma yace Kuyi hakuri wlh na manta,ka manta ma kace cewar Kawu,Aslam yace Bari na kirashi yanzu yanda Muka Yi zan sanar da ku,Aslam Shehu ya Kira bayan sun gaisa yace Kawu dama magana zamuyi,yace Ina jinka Aslam,yace Alfarma nake nema a wajenka Abba,Shehu da sauri yace Fadi Aslam ko Mene shi Inshaallah zanyi maka,yace akan Mama ne dan Allah kayi hakuri Allah ma muna Masa laifi Kuma Yana yafe mana bare dan Adam musamman ma Wanda yasan yayi laifi ya tuba ya gane kuskurensa,ko dan yaranta ma kayi hakuri yaran zaka duba,Shehu ko musu bai iya yiwa Aslam sai yace dama Ina sonta ai iskancinta ne yayi yawa bata da mutunci ko kadan amma zata dawo Inshaallah tunda kayi magana Inshaallah Zan dawo da ita amma ka kyaleta ta Kara Shan wahalar rayuwa tukun nima sai na gama amarci na sannan ta dawo yanzu Kam kace ta koma Kauye zan Mata magana,Aslam Yana dariyar Shehu Wai sai ya gama Amarcinsa a fili yace to Abba za a fada Mata na gode,Aslam nan take ya Kira Kawu ya fada Masa yanda sukayi da Shehu,Kawu yace Alhmdllh kaga kaima ai ka samu lada yanzu bari na sanar mata.
Kawu Mama ya samu yace ki godewa Allah Aslam yayi Miki rana Wanda duk duniya babu me miki irinta ya sa Shehu zai maida ke dakinki amma yace ki koma Kauye zai Miki magana da Kansa,Mama ta fashe da kukan farin ciki tace dan Allah ku barni a nan ku taimakeni Kauye wahala inda kasan Ina cikin wuta,Kawu yace ai yace Indai a nan kika zauna bazai dawo Dake ba ai da sauri Mama ta Fara tattara kayanta zata tafi kauyen nasu haka,Kawu yaji tausayinta amma gwara ta Sha wahala sosai yanda ko ance ta sake yin wani abin baza tayi ba,Haka ta koma Kauye taci gaba da Shan bakar wahala a gidansu tunda ba iyaye ne da ita ba a gidan Yan Uwa ne Kuma Yan uwansu kaf basu da mutunci kowa dan iskan Kansa ne kudi Kawai shine mutuncinka a idon su,Gashi idan tana so ma a San Mata abincin sai taje anyi aiki da ita a gidan surfe da daka sai tayi dole,hannun Mama yayi kanta yayi kaushi sabo da wahala,gashi Shehu Shuru har ta sake yin wata guda a kauyen su Nusaiba sai rokonsa suke Yi har kuka sai da Suka yiwa Shehu sabo da Ameer yaje yaga halin da mahaifiyarsu take ciki,Shehu sai lokacin ya nemi yan uwan Mama maza Suka Yi magana za a sake maida aure sabo da ta gama Idda tuni,bata sani bama sai Yan uwanta ne Suka sanar Mata an maida Aurenta