Showing 69001 words to 72000 words out of 85703 words

Chapter 24 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

778

ta ganshi da mace shine tace budurwarsa ce bata San cewar Amaryar liman bace ogan Affan Kuma Liman dinne yasa Affan ya kaita wajen wata Mata suna business tare da matar Liman,matar daga kasar waje tazo shine Affan ya kaita.

Raudah hijab ta zurma ta fito da uban gudu tare da bude motarta ta shige ta Mata key motar taki tashi tayi tayi motar taki ta fito da sauri daga gidan sai ga yaron Affan da machine yazo gidan zai karbi takardu,da sauri tace dan Allah kaini ShopRite sauri,ya zaci ma wata masifa ce ta faru ya juya machine ta hau da sauri tana cewa kayi gudu Yi sauri Salahu dan Allah Yana tambaya lafiya Hajiya? Kayi sauri please duk ta gigita me machine suna ta fyalla gudu a titi tana kayi sauri ka Kara wuta Yana tsinka gudun gaske a rude yaje ya daki mota Suka watse a gefen kwalta Raudah ko motsi bata Yi kanta ya fashe daga gefe Yana jini,me machine din Kuwa Suma yayi Yana farfadowa yasan inda yake sai raunuka da yaji,mutane sun taru akansu aka kwashi Raudah da Salahu yaron Affan zuwa asibiti,lokacin Affan ma ya koma Office Kawai yaji Kira Yana dagawa ya mike Zumbur a gigice Yana tambaya a wanne asibitin ya tafi da sauri figi motarsa sai asibitin,matarsa Kawai yake cewa dakin da Raudah take aka kaishi Yana Shiga ya iske ta farfado amma ta karye baras a kafa sai kanta an nade daga gefen da bandage,tana ta kuka a kwance Affan bai ma tambayi me ta fito Yi ba Kawai ta lafiyarta yake Yi,ganin tana ta kuka ya Fara lallashinta,a gefenta ya zauna tare da maida kanta jikinsa Yana lallashinta tana hawaye yace Inshaallah Zaki warke kinji,anjima kadan za ayi aiki a dora min ke,ya Isa haka kukan Affan ko aiki sai mataimakinsa yayiwa magana ya kula da komai ya tafi jinyar matarsa sai ta warke zai dawo ya sanarwa liman gaba Daya family Suka Zo dubiya har Liman,a ranar aka dora Raudah ana ta zuwa dubiya har Yusuf da matarsa sunzo,shi kuwa yaron Affan tuni ma an sallame shi sai da Raudah ta kwashe sati biyu a asibiti Affan shike jinyarta shike Mata komai bai bari ma yan uwan Raudah sun zauna ba tunda suka zo dubiya,mamanta ce ma ta dage sai da tayi sati guda a asibitin sannan ta koma.

Wheelchair aka bawa Rauda da sandunan koya tafiya lokacin da aka sallameta,Raudah tana tuna dalilin fitarta daga gida sai hawaye da kukan takaicin halinta tana nadama da Dana sani,gashi Affan din yand a yasan bata tambaye shi ba ta fito amma ko zancen bai Mata ba ta lafiyarta yake Yi ya daina zuwa aiki sai jinyarta shike Mata komai ita Kuwa me zata ce da wannan bawan Allah tayi dacen miji da wani ne sai dai a kaita gidansu in ta warke a dawo da ita, motar Affan ce ta shigo gidansa ya fito ya Bude dayan bangaren sannan ya bude booth ya dakko wheelchair ya dakko Raudah tare da dora ta a Kai tare da rufe motar ya turata a hankali zuwa ciki,Raudah tana ta zagin kanta a zuciyarta abinda ta aikata,Affan gwani ne wajen gyara da tsafta sai da ya gyara gidan nan tsaf sannan ya yiwa Raudah wanka shima yayi ya dorata saman kujerarta suka fito,ya shiryata cikin gown gajera marar nauyi,abinci yayi order aka kawo musu har gida suka ci sannan ya fita masallaci ita Kuma tayi sallah a zaune saman kujerarta.

Washe gari tana Palo tare da Affan suna kallo Landlady ta shigo bayan sun gaisa Affan ya koma bedroom ya basu waje,Rauda ta kalli Landlady tana hawaye tace kin cuceni ke ba matar kwarai bace Kuma ba abokiyar zama bace,sam bakya Dora mutum a hanyar gaskiya gashi nan abinda Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala,Ina zamana da mijina lafiya ke kin kasa aure kinzo kina zugani bakya taba yabon maza sai dai ki Fadi sharrinsu shi yasa da yawa wasu matan idan Suka taru basu da aiki sai fadan sharrin maza basu fadan alkhairinsu a haka wasu Wanda suke zaune lafiya da mazajensu shike nan an gurbata musu zuciya sai su Fara zargin nasu in ba a yi sa'a ba rashin zaman lafiya ya Fara kenan,Mata in Suka taru basu da aiki sai zagin maza da halayensu ki sani wata idan bata dauka ba wata dauka zata Yi karshe auren ya mutu ma,ba kowa ce take auren miji me kule kulen mata ba Kamar mijinki da Kika taba aure Bmbai yuwuwa kiwa maza kudin goro,na Zama sakarai da ilimina da hankalina na zauna Ina daukan shawararki landlady kiji tsoron Allah kije kiyi aure ki daina lalata Mana namu,kuma Indai zugace zata kawoki gidana karki sake zuwa inda nake bani ba bake har abada,kin girmeni babbar mace ce ke amma baki da tunani, Landlady tasan itama bata kyauta ba tace kiyi hakuri Raudah wlh aurena dana Yi na fuskanci halin mijina kenan sai nake tunanin kowa ma haka yake wannan yasa na kasa kara yin aure amma Inshaallah nima na gane gaskiya,Raudah tace oho Miki ni dai in bada alheri Zaki Zo ba karki sake zuwa gidana yanzu ma ki tashi ki tafi, Landlady ta mike jiki ba kwari ta tafi,Raudah tana hawaye Affan ya fito yace Wai me yasa kullum sai kinyi kuka ne kina Jin sauki fa kin kusa fara tafiya da kafafunki Inshaallah.

Raudah tana kujerarta ta miko hannu tare da rike hannun Affan tana hawayenta tace dan Allah ka yafe min na tuba bazan sake ba,ta bashi labarin komai zugata da Landlady keyi tace karshe gashi ta kaini ta baro na karye ta fashe da kuka,Affan yace ai Raudah tunda naji kinyi hatsari nasan kishi ne ya fito dake shi yasa ma ban tambayeki ba nasan baki da wata matsala face kishi,abinda yasa Kuma bana damuwa so ne a kaina akeyi Kar wata ta kwace ni to ni ai na Zama dan gata gashi kin jawa kanki kin karye Allah ya takaita ma,haba wifey babu izinina Kika fito haba Raudah kishi fa idan yayi yawa zargi yake kawowa,da sauri tace wlh bana zarginka Kawai in ta zugani ne sai naga kamar haka ka yafe min kayi hakuri bazan sake ba babu ruwana yanzu gashi na karye a banza,Affan ya kyalkyale da dariya tana hawaye ta duke shi a kafada,yace ai Ni Kika jawa aikin,ki sani bazan taba cin Amanarki ba na Sha fada miki,to yanzu idan ta kasance Zan Kara kishiya yaya kenan Raudah? tace ai ma Inshaallah baza ta faru b,to idan ta faru fa? Mutuwa zanyi Kawai,yace kin gani wannan halin naki sai ke Kika ce kin tuba kuma? Baki ta turo tace ae na tuba bazanyi fada ba bazan ce komai ba Kuma bazan bibiyeka ba sai dai Kawai aga na mutu,Affan yayi dariya sosai tace ai kana da kyau ko wacce sonka zata dinga yi ni Kuma bana sooooo....ta karasa da kuka,To yanzu Raudah nifa ba ni nayi kaina ba Nima tashi nayi na ganni haka,Raudah tace ka kakalo shi Mana tunda kana ta gyara jikinka kana daukan wanka kullum kayi ta matso kyawunka kana fita gashi nan sai kafi 1h a toilet kana wanka duk ka goge fatarka kullum fari kake sake Yi kullum gashi nan bature kake Zama,Affan dariya Kamar me yace to na daina wankan sai na zauna miki a kazami gobe kice Nima Ina warin hammata,yanzu sai kince kin tuba kin daina ko? Raudah tace Zan dinga yiwa kaina Addua kaima ka tayani,Affan ya sake sakin dariya tace wannan ba abin dariya bane kaje kullum kayi ta gyara Suma ba ji ba gani ko wacce Yar iskar budurwa tana zare Ido gashi nan gaf ake da yaye dalibai daga Yan secondary zasuyi candy gashi Yan University sun kusa gamawa naji a labarai ance final exam zasu zana Kuma Yan Service sun gama miji suke jira wallahi ta Allah ba tasu ba, Affan har wani dadi yake ji ana kishinsa yace to ya Isa me Miji,Raudah tace kayi hakuri na tuba Allah kishi irin na baya da nayi bazan sake ba amma zan dinga dan yin kadan kadan shi yasa nake baka hakuri kayi hakuri dani Dan Allah har Allah ya yaye min,Affan yace to an gama Raudah,no your love zaka ce ta gyara masa Yace Okay My love,My one and only, My Heart,My soul my life Kuma Queen dita,Raudah Murmushi tayi tana Jin dadi tace ga mijina me jinyata me so na wata tazo itama Watarana ayi jinyarta haka dole naji haushi,kwana nawa baka Yi komai dani ba lafiya iceko? Affan yace Baby rigima baki da lafiya a karyen zanyi wani xxx dake,Raudah tace a'a in kana so kayi Zan maka komai Zan daure ai na Fara Jin sauki kafar basai a lallabata a gefe daya ba,Wai wayo take wa Affan Kar ma yaji Yana so ya Karo aure tunda bata da lafiya ko yayi sha'awar wata ita bata da lafiya baza ta iya Masa komai ba akan haka gwara ta daure tunda tana gani idan Yana Mata wanka Yana shiga yanayin bukatar mace daurewa Kawai yake yi shi yasa gwara ta tari abin.
Affan da wuri ya amshi tayin Raudah yana murna yau zai gagije,ai Kuwa da dare haka kafa aka sata a gefe Suka jiyar da juna dadi.

Washe gari Raudah tana kallon labarai a tashar hausa suna zaune da Affan taji ance gomnati ta dage jarabawar waec da dalibai zasu zana Yan secondary school an Kara wata uku nan gaba,Raudah tace Alhmdllh Yan banzan Yara aci gaba da shiga aji,Me labarai tace kungiyar Asu jibi Monday zasu Kara tafiya yajin aiki na Sai baba ta gani,Raudah ta kyalkyale da dariya tace maga karyar gama degree dan ubanku,Affan Yana jinta waya yake dannawa amma sai da ya tsaya kallon Raudah tana bashi dariya matuka.

Bayan kwanaki ya Fara koyawa Raudah tafiya har ta iya ta Fara takawa da kanta har ta dawo tana tafiya normal Kamar bata taba karyewa ba,likita yace ta dinga Dan zaga unguwa tana tafiya a kafa me dan nisa,tare da Affan Suka fito sunyi gayu sosai Affan sanye da 3qrt da t-shirt komai fari,ita Kuwa Abaya ta sa silver color me shegen kyau tayi rolling suna tafiya a layin suna zancen soyayya suna nishadi kamar saurayi da budurwa ka gansu gwanin birgewa,Suna ta nishadi yana tsokanarta,wata Yar budurwa ce tazo wucewa Raudah da sauri ta koma ta bayansa tare da rufe Masa idanu da tafukan hannayenta dariya sukeyi musamman Affan, sai wurin magriba Suka dawo gida.

Siyama kwance suke da Aslam a makeken bed dinsu sun gama soyewa suna hutawa ta juya tare da hugging din Aslam tace My Sugar dan Allah ka biya min makaranta na koma Nima nayi karatu,marairaicewa tayi da shagwaba please ko ba degree ba ko NCE ne dan Allah kaji, Aslam yace ni bana son fitarki aje a gurbata min Mata Muna zaman mu lafiya,Siyama tace Ina da hankali fa Inshaallah babu abinda zai faru wace ma ta Isa ta zuga ni na yarda ilimi Yana da dadi kaga Zan sake wayewa sex dinnan ma Sai kaga albarkacin makaranta da gogewa nazo Ina maka style har na tintsira gudi gudi,dariya Affan yayi ba shiri yace ba wayon da Zaki min Yar nan,Siyama ta sake cewa to yaran mu fa ko Dan yaranmu da zamu haifa zai musu Rana,Yan dagwai dagwai dinmu jikokin Mum, Yan fararen yaranmu masu Yan kunnuwa Affan yace naji amma sai kin samu ciki Zaki fara yarona tun a ciki ya dinga Jin turanci,Siyama tace Indai ciki ne Ina da shi fa,watanmu biyar da aure Ina da ciki,Aslam yace haka ake cikin,da gaske fa nake idan baka yarda ba muje asibiti gobe,ta ya Kika sani? tace Sanda na dinga zazzabi rannan na siyo wannan tsinken na pt na gwada Allah ya nuna Ina da ciki,shine baki fada min ba? gobe Zan kaiki asibiti ai,gari na wayewa Suka shirya sai asibiti bayan an Mata gwaji nagartacce aka tabbatar tana da ciki na wata uku dai dai,Aslam sai Murna harda kissing dinta a kumatu Suka dawo gida murna taki karewa,Siyama tace ai mu irin jinin haihuwa ne ana taba mu muke samun ciki,dariya yayi sai Murna yake zubawa daga nan ya Fara musu Shirin barin kasar.

Su kawu,Aunty da Shehu sai Wanda Affan yasa zai rakasu ko Ina suna filin jirgi,Landlady ma tazo zata tafi Umrah tana filin jirgi a nan Suka hadu da su Shehu,Shehu yaga dai dai shi yaji Landlady ta masa harda cewa sannu,tace yawwa sannunku,sai ga Shehu ya zage Yana yiwa Landlady tambayoyi kema Makkah Zaki? tace ae Umrah zanyi yace ke Kuwa ki karasa ladanki Mana kiyi aikin hajjin gaba daya amma kiyi Umrah Kawai ki dawo sabo da rashin rabo,Landlady tayi Murmushi bai san me kudi bace,Shehu ya zake suna ta hira da Landlady,Shehu harda cewa daga nan mu Paris zamu wuce sai Dubai, Landlady ta zaro Ido ta zaci wani shegen me kudi ne Shehu ta saki jiki harda bawa Shehu labarinta kaf amma bata nuna Masa me kudi bace, tun a nan Suka kulla soyayyarsu in sun dawo zasu Yi aure, Landlady a ranta tace gwara ko talaka ne Indai na samu me so na Nima nayi auren nan na huta kullum sai dai na rungumi pillow na gaji,Shehu Yana ta murna ya samu matar aure shi kam.








AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


91-95





Official

By
AsmaBaffa







Page naki ne
Bk








Affan yau zai koma aikinsa cikin shiri ya fito tare da Raudah tana shagwaba ta rakashi har mota tana kumburo baki irin na Yan Shagwabar nan da sangarta,Affan ya zaro kudi Yan dubu dubu na dubu goma ya Mika Mata ta karba tana cewa na mene? yace baki nayi ki kashe,duk da tana da kudi bata da wata matsala sai da taji dadi yace sabo da wasu mazan tunaninsu Kawai ci da Sha zasu bawa mace basu iya bawa mace dan kudi ko Yaya ne gwargwadon samunsa Watarana haka sabo da ba iya abinci da sutura bane matsalarta,in ka bata kudi maybe a danginta akwai Wanda take so ta yiwa kyauta ko ta kyautatawa kawaye ko Yan Uwa bare uwa uba iyayenta kuma,zata kyautata muamularta da Yan Uwa da abokan arziki amma mazan da yawa basa ganewa, Raudah tana shagwaba tace to ai Ina da kudi Kuma ma Ni ka dawo da wuri yafi min muhimmanci,nasan kina da su ai amma kudinki daban nawa daban wannan naki ne kiyi abinda Kika ga dama da abinki, tace to na gode Allah ya Kara budi yasa kafi haka,karfe nawa zaka dawo? 5pm ya furta Yana kallonta,dire diren kafafu ta fara tana kukan tabara yayi nisa gaskiya ni ka rage, kina aiki fa My life kin San Kuma ka'ida kiyi hakuri tare fa muke bacci kin San da Ina gida ba aiki dole Ina gida, Alright ta furta Allah ya tsare a nemo mana halali Banda haram, Inshaallah ya furta Yana cewa am gonna miss you,me too yace come here..dan kanta ta shigar cikin motar yayi kissing dinta tace ko na zo nayi driving naka? Kina amaryar Zan bar matata ta fita, dariya Suka Yi tare da dagawa juna Hannu ta Masa bye sannan ya tashi motarsa tare da barin gidan,bayan yaje Office ya kirata yafi sau biyar, sai Yamma ta sake gyara gidan tasan bai son kazanta ko ya take, girki ta shirya Masa lafiyayye ta cakare tana zumudin ganin angonta.


Siyama Kamar bata da ciki ana gobe Mum zata tafi tazo gidan Aslam,Siyama tana sama taji door bell da sauri ta fito,sanye take cikin wasu Pakistan masu kyau Riga da wando da mayafinsu farare tas sunji adon golden,Wandon me Kama da skert ne idan baka sani ba zaka rantse skert ne,dankwalin daurawa tayi a kanta amma Jin muryar Mum sai ta Yafa mayafin sannan tazo tare da bude kofar, fara'arta ta fadada tace Sannu da zuwa Mum tana Jin kunya kunya Mum ta shigo ta zauna kujera ta zuba lace me tsada, Siyama a kasa ta durkusa tare gaida Mum cike da girgimawa ko itace ta haife ta sai haka,ta mike ta cikawa Mum gabanta da kayan ci da Sha, Mum sai Murna da farin ciki danta yayi dace tace oh bakya gajiya Yar nan da hidima Allah dai yayi muku Albarka,Siyama ta amsa da Ameen tana zubawa Mum lemon a cup ta Mika Mata sannan tace bari na Masa magana ta haura sama da sauri,Mum tana ta washe baki Sabo da farin ciki,Siyama tana Shiga ta Samu Aslam yana aiki a system daga shi sai boxers,bayansa ta zaga ta duka tare da rungume shi ta baya hannayenta ta sarkafo ta wuyansa ta Masa rada a kunne Mum tana nan fa tazo tana Palo ka tashi ko nace ta shigo Nan? Ko kince ta shigo ai baza ta shugo turakata ba,to tashi tana jira fa dan Allah,yace wannan rawar kafa da kike Yi haka ko Ni bakya min haka ni ya kamata ma na Fara kishi da Mum kinfi sonta da ni,Mikewa tayi tace to ita ta haifa min Kai ai da bata haifa ba na Samu,Jallabiya ta dakko Masa ya saka sannan yace muje,tace kaje Kai kunya nake ji ta ganmu tare,bana son gulma sau nawa Muka je wajenta tare,Ni dai kaje tace,baki ya tabe ya fice ya samu Mum tana eban gara,Mum baki ta bude ta kasa rufewa tace me Zan gani haka Aslam wato sumarka da kake tarawa me shegen yawa bata Isa ba shine kaje aka zana maka kitso a kanka kalli kitso Kamar Kan mace,Aslam yace Surukarki ce tayi min tace tafi son kitso nafi Mata kyau,Mum duka ta durma Masa a gadon baya ya saki kara Yana shafa wajen yace da zafifa Mum,lallai a tsefe kitson nan yau yau,dama dazu tayi shi da safe idan Zan fita pcap nake sawa,Mum tace ya muku kyau,yaushe zaku tafi ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login