Showing 63001 words to 66000 words out of 85703 words
Affan Ido akan Shige da ficensa
Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa, Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa.
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️
81-85
Official
By
AsmaBaffa
Page naki ne
FUTURE RM
Kuka Raudah ke yi yaki daga Wayarta Yana can wajen abokansa sai kusan 12 na dare ya dawo Yana bude kofarsa ya ganta a palonsa,tana ganinsa ta mike tsaye yazo zai wuce ransa a bace ta zube har kasa ta durkusa tana hawaye tace dan Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba,Affan ya kalleta shi mamaki take bashi yanda taci kuka,kamar bazai hakura ba yace tashi na hakura ni ki daina durkusa min haka,na hakura ya zanyi Dake tunda Ina sonki na fada Miki bana son kishin zargi idan kishi yayi yawa zargi yake sawa idan nayi niyyar kula wata har zan bari ma ki gane kin San maza kuwa,bana son zargi a rayuwata bana so karki sake min irin haka,Raudah da tana ganin Affan Kamar sai yanda tayi da shi sai taga ashe ba haka yake ba baya takuwa ko kadan Namiji ne bai son raini,tuni ta Shiga hankalinta,yace kije kiyi bacci,ta mike sum sum har ta fita ta dawo tace baka ce kana so na ba,bazan fada ba yau Banga dama ba ya furta Yana hararta,tace to ni Ina sonka yace can da yawarki,tafiya tayi dai zuciyarta ba dadi da safe bata je aiki ba Monday guda Affan bai ce Yana sonta ba tana nan tana bacin rai, Tuesday ma kin zuwa tayi tace bata da lafiya sai ta warke,Affan yaga motarta kwana biyu ba inda ta fita ko a compound basu hadu ba Kuma ko ta window bai leka ba bata leko ba zai shiga mota ya fasa yazo yayi knocking door nata ta bude ya ganta ras da ita taci kwalliya,tace Ina kwana lfy Alhmdllh kwana biyu bakya fita lafiya? Kai nake jira kace kana so na sai na fita,Affan Ido ya zaro yace kina da abin mamaki Raudah....kuka ta saki kaji ko kaji ko Beb dinma ka daina fada sai Raudah,Murmushi yayi Yana kallon ikon Allah,yace sai ance ana sonki dole shine Kika San ana sonki? tace ae ni Indai ana so na Kuma ana son zaman lafiya kullum sai ance min I love you morning, afternoon and night,I love you ya furta tace naji na yanzu Saura bashin na jiya sai da ya fada yafi sau biyar sannan tace yayi haka a dawo lafiya,ya tafi Yana dariyar Raudah.
Siyama ce ta zuba wani abinci zata ci Aslam yace yayi kadan ki Karo a gidanku ba haka kike ci ba,tana shagwaba tace ai tunkafin ayi min aure Sam bana iya cin abinci bana son ci ma dole nake yiwa kaina Aslam a ransa yace to ga Kawu yace idan yaga ta rame akwai matsa dole na samo Mata multivitamin,tashi yayi yace da kin fada min tuntuni ai da na samo Miki maganin cin abinci ki dawo normal haka akeyi,Bari naje chemist tace to,yaje chemist din layin yace Multivitamin zaka bani maganin cin abinci babba,me chemist yace Kaine baka iya cin abinci? Yace ae me chemist shi ba likita bane Yar makarantar ma school of health technology ya Fara aka kore shi ai Kuwa ya dauki me karfi maganin boosting din apetite da Kuma multivitamin ya bashi me kyau me karfi yazo ya ebo ruwa ya balla ya bata ta Sha ashe muguwar yunwa yake sawa tare da shegen bacci,Minti talatin ta shafa cikinta tace ji nake Kamar an sace min kayan cikina Honey wayam ba komai,abincinsa da bai ci ba yace sai anjima ta dauke ta cinye tas,tana ci wani mugun bacci ya kamata ta mike tsam ta tafi bedroom dinsa ta kwanta bacci take ba ji ba gani har dare bata tashi ba,zuwa yayi Yana tashinta yace wannan wanne irin bacci ne magriba ta wuce fa har na dawo daga masallaci Daukanta yayi tare da direta a kasa tana tangadi ta shiga toilet da kyar tayi Alwala da Sallah a wajen ta kwanta sai bacci Aslam yaji gidan ba dadi abokiyar tasa tana ta bacci Sallar Isha ma da kyar ta iya tashi ga jikinta ya mutu,Har 11pm tana bacci Aslam sai me aiki ya sa ta Masa girki, yayi wanka tare da Shirin bacci yazo Kawai ya dakko rigar bacci wata sabuwa ya cire Mata kayan jikinta garin cire kayan bacci sha'awarsa ta motsa ya fasa sa Mata kayan yaja ta suka Shige bargo tare zaiyi shagali tana ta faman bacci jiki a mace Yana Fara taba ta sai dai ta bige hannunsa tace ni bana so wlh ka kyaleni bacci,Aslam takaicin magani yasa ya kwashe su tare da watsa su a dustbin yace baza a sake shansa ba haka Kawai ya jawo min tsiya
Magani dai sai da safe ya saki Siyama da safen ma ba sosai ba,zata tafi kitchen ya riketa yace kalli hannuna yanda ya dawo red sabo da dukanki,dariya tayi tace maganin nan ne gaskiya,Nima Naga alama tace baccin Dadi a Kara min,yace na zubar da dan Iska jiya ya hanani Jin dadi sai hakura nayi amma yanzu ba fashi Siyama tace ai banci abinci ba yunwa nakeji yace to gama aikin ,ta fita ya koma baccinsa,tana kitchen din amma ciye ciyenta takeyi tun kafin ta gama Kamar zata cinye abincin gidan,tana gama soye soyenta ta zauna ta karya ko jiransa baza ta iya ba sai data gama ta koma bedroom dinta wanka tayi ta shirya cikin Dan Bum short black sai wata rigarsa silk white da digo digon baki me dogon hannu ce da kwala,pcap ta saka me black da adon fari,gashinta kwance a baya tayi bala'in kyau,ta fito daga room dinta sai gashi ya fito sanye cikin Jallabiya arsh Yana kamshi, ka tashi har kayi wanka ashe,Yana can Yana aikin kallonta bai ji me tace ba sai da tace hello sannan ya dawo hayyacinsa,tace ka tsaya kana ta kallona,kinyi kyau da yawa ne shi yasa,jawota yayi jikinsa Yana shakar kamshinta
Bayan ya karya ya dauketa sai dakinsa domin bazai iya hakuri ba a matse yake,Haka ya soye ya barta da jinya.
Amarci suke Sha Kamar ba gobe zuwa wata uku Siyama ta murza kiba tayi wani kyau da haske kana ganinta kasan tana hutawa hankalinta a kwance yake,lokacin tace zata je gida ta gaida su Kawu,Ranar wata Sunday Suka shirya cikin sutura me tsada sunyi kyau matuka Suka fito Yana kallonta yace dole Kawu yace na iya kiwo ya bude Mata mota ta shiga sannan ya zaga ya Shiga yayi driving din su zuwa gidan su Siyama,Yana yin parking ya fito kenan ya Bude mata kofa ta fito sai ga Nusaiba ta dawo daga shago hannunta rike da leda ta siyo manja bai fi na dari ba,ta rame tayi baki sai kallon Siyama takeyi da Aslam tana zare Ido,Aslam ko kallonta baiyi ba,Nusaiba kishin Siyama take yi Bata kulata ba,Siyama ce tace Yar budurwar bazawara daga Ina,Nusaiba Tsaki ta ja tayi gaba fuuu,dariya ta bawa Siyama tace Nusaiba kawarki ce Charity fa Nusaiba ko kulasu bata Yi ba ta fada gidansu tana kuka a gaban Mama,Mama tace wanne Iskanci ne wannan wallahi Kika fasa manjan nan sai dai kuci shinkafa da waken nan babu mai wallahi kudin cefanen da ubanku ya bayar na dauke dari biyar na zuba a dashi dama da irin wannan Yar cuwa cuwar muke yin dan adashin nan namu,Nusaiba tana hawaye tace ni gwara Ina gidan mijina ko gidan Sufyan ne ya fiye min,Mama tace ki Bari kiyi idda Inshaallah hannun Aslam ma zaki koma,ai na kusa iddar Ina sane dake akwai abinda zanyi karki damu yarinya,Nusaiba sai lokacin ta danyi murmushi.
Aslam kuwa gidan Kawu Suka shiga Aunty sai Murna Siyama tayi kiba an Kara kyau alamar kana gani kasan tana cikin kwanciyar hankali,Kawu ne ya fito Yana kallon Siyama yace fatan dai Jin dadi ne ya sa Kika canja haka ba Sha ka fashe kike Sha ba da Kuma wannan kwayoyin na Karin hasken fata,Siyama tace ni da nake Fara Kawu Jin dadi mana,yace to madalla Allah yayi albarka ya Kara muku zaman lafiya yaro ka iya kiwo gata nan ta canja haka ake so to ke Kuma Kar naji Kar na gani na fada Miki karki sake a kawo min kararki na fada Miki,Aunty tace to ai taji dan Allah,a gida ya barta ta yini ranar sai magriba ya dawo Suka tafi gida ya kaita wajen Mum ta kwashi gaisuwa a nan taji Mum zata tafi Qatar ta koma can ta huta Wai ta fasa auren Indai Shehu ne bata sonsa,daga Nan ya kaita gidan su Sabeer Wanda shima gaf yake da aure.
Raudah biki ya matso ta koma gidansu can tana Shan gyaran jiki iri iri iri,Affan ma bangarensa ya gama gina gidansa me kyan gaske dama tunda ya samu aiki fili ya Fara siya ya Fara gininsa a hankali gidane flat me shegen kyau,Raudah Kuwa Babanta me kudin gaske ne Furniture dinta da duk wani kayan da za a zuba Mata a gidan daga kasar waje aka kawo su na musamman,ana Saura kwana uku daurin aure duk wani gyara an gama anzo an shirya Mata kayan gidanta a Kano unguwa ce me kyau ta masu hali dama shi Affan sarkin gayu da son wanka komai sai me kyau,sun gama gayyatar mutane ranar Alhamis duk Dangin Affan maza Suka tafi daurin aure da da abokansa duk acan zasu kwana a daura aure su taho da Amarya,Yan uwansu na zamfara duk sun tafi,an musu masauki a hotel duk mutum biyu daki daya haka Suka kwana washe gari ana yin Sallar Juma'a aka daura Auren Affan da Raudah Kan sadaki Naira dubu Hamsim,Affan Yana gaisawa da mutane Zo kuga wanka wajen ango kowa sai kallonsa yake sabo da gayu,ya juyo kenan Suka hada Ido da Yusuf Yayansa ya saka Dan Yadinsa da gani kasan wahala yake Sha,Cin Amana ba kyau,Affan ya karasa wajensa suna mugun Kama yace yaushe kazo Yaya? Baka gayyace ni ba naji labari nazo ai, Affan gefe ya ja shi yace a Ina kaji labari? Yace Nabeela ce ta fada min komai naka har IV ta tura min a waya,Na dade Ina Neman Ina zan ganka na roki gafararka Affan ban ganka ba sai da Allah ya hadani da Nabeela ta fada min inda kake da aikinka da kake da aurenka,Affan kayi hakuri ka yafe min,nasan naci amanarka a matsayinka na dan uwana,ka sadaukar da komai naka a kaina dan na samu ilimi nayi kudi na dawo na dauki nauyinka amma ban saka maka da komai ba sai jefaka cikin kunci nasan na zalunceka Affan na jefaka cikin kunci ka yafe min Affan na gane kuskurena Kuma Inshaallah Zan gyara ka karbeni a matsayin dan uwanka Karo na biyu,ka bani dama na gyara kuskurena,Yusuf Yana hawaye Yana magana yace I missed you Affan,Affan yace ba komai Yaya na yafe maka da Kai da Nabeela na yafe muku,tazo wajena naji abinda ya faru da Kai Allah ya kiyaye gaba,Yusuf yace Ameen yanzu da kyar na samu Offer teaching a secondary school kasan aiki a kasar nan,Affan yace karka damu Yaya Inshaallah Zan sa uban gidana ya baka jari ko da milliyan uku ce ka Fara kasuwanci ko ya yake kaga kana aikinka kana kasuwancin ko yaya ai yafi,Godiya Yusuf ya dinga zubawa yace ba komai ai kai dan uwana ne jinina bani da kamarka Yaya,muje ku gaisa da Liman shine uban gidana ya jashi Suka gaisa,ya kaishi wajen surukinsa Baban Raudah suka gaisa daga nan mutane duk sun tafi kowa ya hada karensa daga Sayyeed sai Ango sai Yusuf.
Hotel Suka koma Affan cikin kayan da yazo dasu akwai shaddar da bai saka ba sabo da tela Wai ya Masa Katon dinki me Fadi Yusuf ya Fishi kiba kadan sai ya bashi yace yayi wanka ya saka suje yaga Raudah yawa ne aga Yayana guda da local yadi,Dariya Yusuf yayi yace kana nan dai Affan Kai da wanka Amana ne haka yayi wanka yasa shaddar dai dai shi yayi kyau Kuwa ya fito Suka tafi,Raudah anci gayu Yarabawa sun cika gidan suna ta kade kadensu na yarabawa suna tikar rawa,Raudah ma tana cikinsu sabo da abokan arziki ne Kawai, Affan ya kirata a waya tazo su gaisa da Yayansa,Raudah ta fito harda Jin kunya ta rusuna harda durkusawa ta gaida Yusuf ya amsa Yana cewa tashi tashi Raudah na gode Allah ya baku zaman lafiya,kin ganni feel free duk abinda ya Miki ba daidai ba just call me,dariya sukayi Sayyeed yace mu wuce dare da nayi,Affan a gurguje ya sa Mata number Yusuf ya bawa Yusuf Number Raudah Suka taho gaba dayasu Uku a jirgi Affan shi ya biya Yusuf.
Suna zuwa Kano sai da ya kaishi gidan Amarya da ya gida ya gani,Yusuf yace gidana da ka sani da fa sun kwace amma dana dage da addua sun dawo min da gidana motocin Suka rike Kawai, Affan yace Allah zai baka wata Inshaallah
Zuwa dare aka kawo Amarya a jirgi daga Yan Uwa sai wasu yarabawa Mata su Uku abokan arziki,a gidan Liman ake shagali can aka sauki bakin Amarya da amaryar gaba daya tana can gidan Liman,Yusuf a wajen Su Affan zai kwana gidan hayar Affan inda suke zaune da Raudah can aka sauki baki maza,Suna kwance a bed daya Affan da Yusuf sai hira suke Affan yace muyi bacci ni gaskiya bacci zanyi gobe Ina wajen Amarya bani ba bacci gobe gwara nayi nawa yau,Yusuf yace zumudi Affan ko kunya babu, ya kamata idan anyi nisa da amarci kazo kaduna gidana kaga matata da yaro na,Affan yace zanzo amma ya kamata ka maida Nabeela tunda gaba dayanku Kun gane kuskuren ku,Nabeela Bata so na Affan sabo da kudina ta aureni lokacin amma a gaskiya Kai ta ke so ni yanzu na samu me so na tsakani da Allah Waheeda matar arziki ta isheni idan ta samu miji tayi aure, Affan yace to shike nan Allah ya bata na gari ni dai gobe i yanzu Ina can ana min shagwaba da kuka,dariya Yusuf yayi yace wlh karka daga kafa ranar farko ta wuce ka tafi ko wacce rana dadi,Affan yace ahaf ai sai dai in Suma naga tayi Suka Yi dariya suna hira har bacci ya kwashe su.
Washe gari da Yamma Amarya Raudah tayi wanka ta hade cikin wani material pink ya hadu ta zuba kyau dinkin fitted gown kamar readymade ta sha mayafi me daukan Ido shima pink komai pink takalmi da jaka pink lady in pink,Wanda Suka kawota ne Suka kaita gidan Miji ko digon hawaye Raudah bata Yi ba sabanin ta taba aure sannan Kuma ba a gida take zaune ba idonta Kar a cikin Mayafi.
Abokan ango duk sun ware Yusuf Kuwa Affan Dubu talatin ya bashi cash cikin gudunmuwar da ya samu ya tafi gida abinsa Yana farin ciki.
Yan Kai Amarya suna kaita Suka bi jirgi Suka koma tun yamma aka bar amarya ita kadai sai Landlady data Kara gyara Mata gidan ta kunna turarukan wuta ta fesa room freshner a ko Ina bedroom uku ne a gidan ko wanne room da toilet Palo guda biyu sai kitchen sai wata toilet din kofarta daga wajen Compound,akwai tsakar gida yaji interlock da flowers,ga parking space zai ci mota hudu suna zaune da Amarya da landlady,Landlady tace ki sa Ido akan mijinki Kinga kyakyawa Kika aura mazan yanzu sai ka sa Ido in ba Haka ba zai barki a nan gida yaje Yana kula wasu a waje,motsi idan yayi ki dinga kula da shi sannan ki Masa biyayya ki rike mijinki Hannu bibiyu amma karki barshi haka sakaka maza mayaudara ne mazalunta ne,Kinga Raudah Namiji ba dan goyo bane ki kula da Shige da ficensa,Raudah tace na gode ya zama dole na sa Ido akan mijina,Affan da Yamma rana Kiri Kiri 4pm ya shigo gidan yazo ya tsallake Landlady ya ajiye hularsa a saman bed kusa da