Showing 78001 words to 81000 words out of 85703 words

Chapter 27 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

779

da Shehu,Zabura Mama tayi gwanin tausayi tace yazo ne? Yace ae yazo ya koma ma yace idan kin shirya ko yaushe zaki iya tarewa a dakinki,Mama tace yau Zan koma ai tsofaffin gidan Mata Suka ce ai Kya tsaya dai ki gyara jikinki,Suka hana Mama Sai lokacin suke bata abinci ishashe sabo da sunji taci gaba zata koma birni lokacin abinci sai ta ture,har kyautar Sabulai da su Omo suke bata Kuma ta daina taya su aiki amma abinci sai ta ture,kowacce sai ta bata kyautar magungunan Mata na gyara jiki,Mama sabo da an Mata kishiya ta dage da Sha tana ta gyara kanta bata aiki kaushin Hannu duk ya gudu babu tayi Yar kibarta da haske,sai da tayi gyaran sosai sannan ta shirya wasu dattijai su biyu Suka rakota gidan mijinta,Yaranta sai rungumeta da murna Kamar me,Su dai dattijai suna kawota Suka koma Kauye abinsu,Yaran Mama sun zagayeta suna ta murna yau sun rasa inda zasu saka kansu,Nusaiba ce ta kawo Mata abinci a plate da cokali harda siyo Mata lemo, Mama ta bude abincin ta ga shinkafa da Miya da nama harda salat,Mama yaushe rabo tace haka kuka ci gaba a rayuwa? Nusaiba tayi dariya tace Mama ai yanzu Abba abinda muke so muke dafawa,haka yake cewa mu zabi abinda muke so,Ameer yace kinga shagon Abba da kasuwancinsa ya bunkasa sosai, Mashaallah cewar Mama ta Fara antaya loma sai da taga bayan abincin nan tas,Nusaiba tace a Karo miki? tace na koshi Alhmdllh,duk da haka Nusaiba sai da ta tsamo Mata nama a tukunya kusan guda goma tace Mama cinye nasan yanzu kina yiwa mutum baki ko tsinuwa zata Kama mutum sabo da rashin cin nama akwai dafi me zafi yanzu a yawunki,Mama tayi dariya tace sai ku kuka da kanku amma ai kullum Albarka nake saka muku ko laifi kuka min naji haushi a bayan idon ku sai nace na yafe muku Allah ya muku albarka,Nusaiba tace badan Aslam ba shike nan Mama baza ki dawo ba,Mama tace ke dai bari Naga rayuwa yanzu fatana ki samu miji ko talaka ne, ameen cewar Nusaiba zanje Nima na nemi gafarar Aslam da Sufyan.

Shehu dai a ranar ma Mama bata ganshi ba haka ta kwana ita kadai,washe gari da Yamma Nusaiba ta shirya ita da Ihsan kanwarta ta rakata Suka Fara zuwa gidan Sufyan sun ci sa'a Yana gida dake weekend ne,shima matarsa tana da ciki,matar bata San su waye ba ta sauke su cikin mutuntuwa Nusaiba sai kallon gidan takeyi komai an zuba sabo,Sufyan ne ya fito ya ga Nusaiba abinka da so,Sufyan gangariyar so yayiwa Nusaiba tsakani da Allah bai wani bata Fuska ba tunda yasan shima Yana da laifi tana da aure ya dinga soyayya da ita,gaisawa Suka yi tace zuwa nayi na baka hakuri ka yafe min abinda nayi maka,Yace oh ba damuwa na yafe Miki Nima ki yafe min munyi kuskure Allah ya yafe mana,tace na gode ta mike zasu tafi ya bata 5k taki karba sai Ihsan ya bawa ita Kuwa ta karbe Suka wuce gidan Aslam

Tunda tazo bakin gate ta Fara hawaye ta tuna haukar da tayi da wannan gidanta ne ta cuci kanta,Ihsan tace Aunty kiyi hakuri haka kin Riga kin cuci kanki Siyama ta Shige gidan kunyi change kawa da kawa Kun auri miji daya haka Allah ya rubuta sai kin Fara Shiga gidan itama gashi tazo ta Shige ta fiki wayo da Imani Aurenku Aunty kawaye ko wacce ta dandani zumar Mijin Daya shike nan 50-50,Nusaiba tace yau na shiga Uku ubanki Ihsan wato har kinyi girman da Kika San mene zumar maza zanci Ubanki wallahi sai na fadawa Abba yaci ubanki wato Yar iska kike so ki dawo,Nima fa Aunty na Isa auren nan wlh 18yrs fa komai na hada wlh ina samun miji aure zanyi ni dai,gashi nan a novel nake Jin soyayya idan Muna karantawa a makaranta a Wayar wasu friends, writers da basa tsaftace alkalaminsu wani ka rantse Bf kake kallo,Nusaiba tace ai wasu na daya daga cikin Wanda suke gurbatawa Yara tarbiyya komai fada akeyi gatsal batsa tun farko har karshen novel yawanci ma yaran Mata sunfi manyan matan karatun novels,Allah ya shirya yasa su gane su gyara alkalaminsu wajen rubutu sabo da tarbiyyar yaranmu masu tasowa gaba,Ihsan tace to Aunty da dadi auren? Baki Nusaiba ta bude tace ke in kina da saurayi ki fito da shi gwara a Miki auren nan, Ihsan tace Ina da abina,dariya ta bawa Nusaiba suna rike da hannun juna tace waye? tace Mahmoud wani yayan kawata ne manager ne a bank baki ganshi ba Aunty ya hadu mugun sona yake kin San na fiki haske duk gidanmu nice ziza haka yake ce min Zizata,Nusaiba tace ba karya Ihsan na yarda to kice ya dinga zuwa zance,tace dama ce Masa nayi Kar yazo Abba zai dukeni,kice yazo kina yin candy sai a daura mu Sha biki,Murna Ihsan take yi writers sun ruda yarinya da soyayya.

Suna compound na gidan Aslam sai ga motar Aslam ta shigo ya dawo, door bell Nusaiba ta danna amma Siyama tasa an hanata yin kara,knocking tayi Allah yasa tana kitchen ta fito tace Baby tare da bude kofa ai Kuwa Ihsan ta washe baki tace irin Yan Novels,dariya ta basu Siyama tace kune a gidan ku shigo suka shiga kamshi da sanyi Yana dukan su,Siyama tace yau an tuna da kawancen kenan? Nusaiba tace uhm zuwa nayi mijinki ya yafe min ko na samu hakkinsa ya daina bibiyata na samu mijin aure,Siyama tace Inshaallah ma ya yafe Miki Nusaiba,Duniya kenan Wai Nusaiba ce yau ke neman Yafiyar wani,bana son Iskanci tunda kin aure shi da shegen munafuncinki da kutungwila ai sai ki kyaleni,Dariya Siyama tayi tace kece Kika yiwa kanki fa Nusaiba babu laifina,Nusaiba tana dariya tace da laifinki Mana tunda kece kike kula da shi idan ba shishigi ba Ina ruwan Yar aiki da kula da mijin matar gida,to ita matar wa yace tayi wasarere da mijinta,Kinga mu ki kawo mana kayan dadi muci karki dame mu cewar Nusaiba,Siyama ta kawo musu abubuwan ci da sha sai lokacin Aslam ya turo kofa tare da shigowa,Siyama ta mike taje tana Masa oyoyo oyoyo harda Masa kirari ga hantsi leka gidajen kowa,me karya icen dawa sai giwa,hadarin sama zo da jido ko tsawa,angon Siyama Oga yazo, Kaine da gidan Kaine da dakin, bakaki me karya gada,ko su bi ko suki sai dai su bari, abi oga a zauna lafiya,Oga karya kafafun arna,aje gari ya jima sai kwarya,sunyi bakar tafiya ka kayar,Dan asali kuji babban suna,sai an Kai su tasha ko sunki,dariya yakeyi shi mamaki ma Aslam yake sai kace wata Yar tauri yanda ta iya kirari kamar me Waka kullum da Kalar da take Masa ba irin na baya ba Indai tana nishadi to zai Sha kirari sai dai ya tsaya Yana kallonta Kuma wani Dadi yake ji sai yaji Kansa yayi wani gingiringim, rungumeta yayi tana dariya itama hannunsa ta rike ta kaishi ya zauna ta kalli Nusaiba da Ihsan Wanda Suka zuba musu Ido suna Shan kallo Siyama tace ga Sadauki ku gaida shi,Sadauki Aslam shi Kuma an murtuke Fuska ba raini,Nusaiba tace Ina yini wani kallon banza ya Mata da kyar yace lfy,Ihsan Kuwa tana gaida shi ya amsa da fara'a yace ya school tace Alhmdllh,Siyama tace wannan ba karatu take ba na Santa har gidan kawarta take tafiya karatun Novel soyayya ta sani Kawai,Ihsan tayi dariya Nusaiba tace ta ya Kika sani? tace ni da tayi a gabana naje gidan kawata ce yayar kawar Ihsan basu San Ina wajen ba in Banda zancen aure ba abinda sukeyi wallahi ku aurar da ita da wuri Ihsan Nema take ta lalace,Ihsan Fuska ta boye tana Jin kunya a hankali tace ai Ina da saurayina,Aslam yace ae lallai da gaske ne,Siyama tace kaji ko Baby na fada muku,bakya so kiyi karatu me zurfi? Aslam ya tambaya,tace ai yace zai biya min a gidansa sai nayi a can dakin mijina,dariya ta Kama Aslam Wai dakin mijjnta,Yace to Masha Allah,Nusaiba ce ta katse hirar tace Siyama tana mintsinawa Siyama Ido Wai ta yiwa Aslam magana,Siyama tace Sadaukina Nusaiba fa zuwa tayi ka yafe mata abinda tayi maka shi Kawai take bukata,ke dan Allah saurara karki min wannan zancen bana so ya mike ya haura sama abinsa ya barsu,Siyama tace tab akwai aiki,yanzu abinda za ayi Zan ta rokar Miki shi Inshaallah zai hakura,Nusaiba jikinta yayi sanyi tace dan Allah ki taimaka Kawata,Siyama tace karki damu,Nusaiba tace Bari mu tafi Kar Mama tayi Mana fada kin San yanzu Mama an San annabi ya faku,dariya Suka yi Siyama tace Ina zuwa ta haura sama da sauri ta shiga bedroom ta samu Aslam ya tube zai shiga wanka yaga ta bude akwati tana eban turaruka da kayan make up ya kalleta yace Ina Zaki Kai su? tace Nusaiba Zan bawa,yace bada abinda na siya ba zube yaje ya kwace kayan ya maida akwati ya kulle abinsa,Siyama ta Bata rai tace to ka bani kudi na basu kudin mota,yace badai kudina ba Indai Nusaiba ce baza ta sake cin kwandala ta ba har abada,Wai mene Haka Baby ai ni zaka bawa na basu ba wai Kai ka basu ba,bazan bayar ba bana son musu,tace fine ai na tuna Ina da abubuwan da Aunty ta kawo min tsaraba ban saka ba ai wannan Nawa ne ba naka ba,ta dakko Abaya masu kyan gaske blue da black kala biyu ta zuba a Leda da turaren da aka bata tsaraba sai sabulai,Aslam yace wannan kayan da nace Zaki saka min su sunyi kyau su Zaki bayar baki Isa ba kokawa Suka Fara tace ciki ne dani maza ka zubar da cikin,yace zanyi fushi,Siyama tace ka Dade baka yi fushi ba kayi,to shikenan tunda ban Isa dake ba sai na kunyata ki,zai fito wajen su Nusaiba ya disgata tasa key ta baya ta kulleshi a dakin ta fito abinta ta basu suna ta godiya,Nusaiba tace mu dai zuba Mana snacks din nan a Leda mu tafi ya min Dadi,Siyama ta juye musu a wata ledar da lemuka sun Kai biyar suka tafi da Kaya niki niki sai da ta rakasu sannan ta dawo ta bude kofar Aslam yayi Fushi sosai bai san har snacks da lemukansa an basu ba,itama Siyama bata kulashi ba tace kuma ga kayan lefenka nan tunda dama ba ni ka mallakawa ba halak malak mene amfaninsu ban Isa nayi iko da kayana ba.

Yana shafa lotion bai kulata ba Wai fushi yake,ya fito ba snacks din da tayi a kitchen gaba daya Yana so zaici babu,ta dawo Palo tana kwashe kwanika yace ke Ina snacks din? tace na hada musu da shi,yace flour tawa da na siyo da kudina,Siyama tace harda lemuka sunfi biyar idan kaga dama ka fashe sabo da fushi,kwafa yaja ya mike zai bar gidan tace wlh kana cin abinci a waje sai anyita dani zaka ga makirci idan baka sani ba ka sani makira ce ni ta karshe,dariya ta bashi yace to shike nan ki nuna min makircin naki na gani ya juya zai fita ta Sha gabansa tace hmm muje bedroom idan ka min service sai ka wuce dan tani ka cinye ma harda kujerun restaurant din,yace ai ke ba kunya ce dake ba dama can,tace ae naji a haka aka gani aka ce ana so,ke har kina da bakin magana matar data dinga kuka a kaina idan ba a baki ni ba sai kin haukace, Kai ba a sirri da Kai Siyama ta furta tayi mukus,bakya Jin magana Siyama kin rainani koshi ya Miki yawa in Kika sake sai na Miki ta Abba Shehu da Mama na hanaki abinci,Dariya Suka Yi tace ai nasan baza ka iya ba, wash ka tuna min da dadinka muje ta riga shi yin sama harda Yi Masa dan Kira sai kace karuwa dole sai da ta sashi dariyar dole ya bita ba shiri,abinci ta kawo Masa yaci ya koshi sannan Suka fara shagali.

Raudah yau ta koma aikinta ta riga Affan dawowa gidan ta gyara a gurguje tayi wanka ta cakare sannan tana girkinta tasan gaf yake da dawowa, Landlady ta dakko Shehu a dankareriyar motarta Suka zo gidan Rauda Shehu an faso gari an auri me kudi motocin Landlady ma har ya koya shi Kansa driving yake ya fita inda yaga dama da motar, Mama Kuwa sati biyu kenan Shehu ko dakinta bai kalla ba tunda ta dawo,abin Yana Mata ciwo tana gidan amma bai taba lekota ba sai da ta shafe sati biyu,tana dai ta Shan gyaran jikinta,gashi ta dawo birni tayi kiba tayi haske ta murje,sai gayu take yi.
Har landlady tazo da mijinta Suka Sha hira Affan bai dawo ba gashi wayarsa bata shiga,hankalin Raudah ya tashi,bayan sunyi Sallar magriba Suka tafi ba tare da Affan ya dawo ba,Rauda tayi Sallar Isha ta zuba tagumi taji karar motarsa,da sauri ta mike ta fito taga shine ya fito ras da shi, dama yasan shi take jira hankalinta sai ya tashi,kankame shi tayi tana murna tace Allah na gode maka daka dawo min da mijina gida lafiya,Murmushi yayi yace kiyi hakuri aikine ban gama ba munyi baki gashi wayata haka kawai naga ta dauke ta mutu duf,tace okay shi yasa naji shuru ya rike hannunta Suka Shiga ciki,wanka ya shiga ta bude toilet din ta Shiga ta dakko ribbon dinta zata fito yace zo nan My Sugar, tana zuwa ya jawota ciki ya cire Mata Kaya Suka yi wankan tare,Towel din ya daura ya jawota ya bude ya sata itama a cikin towel din nasa guda daya tal Suka daura su biyu sai rike towel din yayi bazai dauru ba tana manne a jikinsa suka fito suna tafiya Kamar masu ciwon kafafu suna dariya bayan sun shirya tace yau Ina da wani labari me dadi amma muje Dining Suka fito yaga abinci na musamman kala kala an Masa yace na mene haka tace nasan baza ka iya guessing ba,wata takarda ta Mika masa tana Murmushi tace read,karantawa yayi bakinsa yaki rufewa ya wani saki dariya ta farin ciki ya duka a wajen yayi sujjudulshukur ya mike yace My Sugar You are pregnant for 3mnths oh my God dana Yana cikin mahaifarki,tace kasan kwana biyu Ina zazzabi da tashin zuciya shine na biya asibiti daga wajen aiki aka min test gashi Ina da ciki,ka kusa Zama Daddy rungumeta yayi yace dole muyi celebration yau, kissing dinta ya shiga Yi kamar me sannan ya zauna a kujera itama taja ta zauna ya sake rungumota jikinsa Yana cewa Zan iya Kuwa cin abincin nan yanzu murna zata barni Kuwa,ai yau Zan fadawa Yaya Yusuf,Raudah tana ta kallon yanda yake murna itama haka,tun daga ranar Affan kullum kafin ya fita sai ya Dora bakinsa a cikin ya kwararawa dansa Addua sannan yace Baby Daddy zai fita a Mana addua idan ya dawo ma haka sai yayi Masa addua yace Daddy ya dawo,Raudah Kuwa yanda take ji da cikin nan nata Kamar kwai.

Aisha ma da cikinta Farook murna ba a magana,haka Sabeer matarsa har ta samu ciki sai amai take fama,Nabeela ma tana fama da nata.
Yau Shehu ya sanarwa Landlady zai raba musu kwana ya gamsu da shiryuwar matarsa ya Kira Mama ya kira Landlady ya musu nasiha sosai da yaransa ma ya tarasu sun Sha nasiha sannan yau ya Fara kwana a dakin Mama yaji ta zam zam Kamar ba ita ba to ta Sha gyara,Kuma Mama haka suke gaisawa da Landlady ba gaba sai dai dan kishi na Mata Wanda baza a rasa ba dole.









AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


99-100




Official

By
AsmaBaffa





Page naku ne

Hafsa Abdullahi
Fateema Farouk










Nusaiba tana zaune yau Mama ta aiketa kasuwa zata Yi Mata cefane ta shiga Napep sai me Napep yace Zan Sha Mai Hajiya tace to,gidan man da Affan yake nan ya shiga,Yaron Affan Salahu Wanda Suka Yi hatsari da Raudah akan machine dinsa Yana gidan man Affan ya sashi aiki da machine dinsa a gefe yaga Nusaiba a Napep sai kallonta yake Yi sai ta Masa Kama da matarsa data mutu da ciki wajen Nakuda,Kawai ganin tana Kama da matarsa yaji Yana sonta,Yana ta faman kallonta Kamar maye,wajen Napep din ya karasa yace Yan Mata sannu,Nusaiba rabon da wani Namiji ya kulata a duniya har ta manta sai yau,farin ciki ya kamata amma ta danne tace yawwa,yace dan Allah ya sunanki? tace Nusaiba yaji sunan matarsa data mutu mamaki ya kamashi yace ikon Allah dan Allah Dan yi dariya na gani,dariya ya bawa Nusaiba ta murmusa yace har dariyar iri daya wlh sannu baiwar Allah wallahi birgeni Kika yi haka Kawai naji Ina sonki Sunana Salahu,Nusaiba a ranta tace ji wani suna dan Allah sai ace Nusaiban Salahu ko dadi,kallonsa tayi sama da kasa Salahu matashi ne Kamar su Affan wankan tarwada ba laifi baida makusa kuma Yana gayunsa da tsafta Dan birni ne, a ranta tace karfa kiwa kanki tace na gode a fili,Yace dan Allah Dan bani number dinki idan ba damuwa,Nusaiba harda Jan aji sai da ya dinga rokonta sannan ta bashi da kyar tana yanga,Salahu Kuwa haka yake son mace me yanga sai ta birge shi tuni ya Kara Jin sonta.

A hankali waya Suka Fara da Salahu kafin wani lokaci Salahu ya siye zuciyar Nusaiba yace shi da gaske yake daga nan ya dage da zuwa zance da machine dinsa yace yafi son bazawara yanzu sunfi hankali sunga rayuwa,Yana zuwa zance an kusa turo manya aka samu munafukan layi Suka fadawa Salahu tsiyar da Nusaiba ta shuka aka sake ta,shi yasa ake so ka shuka Alkhairi duk tsiyar me hassada bazai samu abin fada akanka ba,gashi Nusaiba ta kamu da mugun son Salahu Kawai taga ya daina zuwa Kuma ya daina kiranta a waya idan ta kirashi sai yace zai Kira bazai kirata ba,Addua taci gaba da Yi ba dare ba rana tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login