Showing 6001 words to 9000 words out of 85703 words

Chapter 3 - Auren Mu Book 1 Hausa Novel Complete

25 Jan 2025

598

dadi take ji dama ta gaji da kiransa Baba,yace Fadi sunan Auntynki Fadi muji, Charity tace Hajara Musa Aunty tace to hankalinta ya fara dawowa jikinta,daga Nan Charity ta Fara magana sai me ma'ana wacce ta Zama dole sai tayi magana a Haka a haka ta dawo normal itama Nusaiba haka ba Wanda ya Musu fada ko Daya da aka tambaye su ma Suka ce wani ne ya fesa musu wani Abu a Fuska Basu sake sanin inda suke ba sai a daji Suka tsinci kansu,Nusaiba tace yan Yankan Kai Suka ce a dawo da wannan matan sunfi karfin mu matan manya ne shike nan daga nan basu sake ganinsu ba sai a bolar unguwarsu,Mama tace Addua ce tayi maganin tsafinsu, Haka aka dinga zuwa tayasu murna har suka dawo bakin tallan su.

Raudat ce ta dawo daga Office ta fito da ledar kayan makulashenta Affan ya fito zai tafi Neman kudi ko zai samu,Tsaki ta Masa tace kullum mutum sai fita kullum amma kudin haya ya kasa biya,kallonta yayi yace you are very lucky yanzu fita zanyi Ina da aikin yi da yau sai kin gane kurenki ya juya ya tafi abinsa,Yana fita wani kamfani yaje hadadde ya tambaya Oga yazo Kuwa? Manager yace bai Zo ba yayi tafiya jiya yace Dubu dari biyar zaka bani ka fada Masa,Manager jiki na rawa ya bawa Affan dubu dari Uku ya tafi,Affan kudin haya ya biya ya siyo kayan abinci da sababbin Kaya kala kala kanana da shaddoji da yadika harda takalma,Sai ganin Affan suke Yi Yana shiga ya fita cikin Kaya masu kyau,Raudat tace Amma Dan fashi ne Kai ba a sani ba da alama sana'a tayi kyau an kwaci kudin wani,Affan yace ke da kike karuwanci budurwa me zaman kanta kowa ya ji labari ai yasan karuwanci kikeyi motar ma mun San waye ya siya Sugar Daddy ne ya Gama tabeki Ina tausayawa Wanda zai aureki Yana nan zai ta wahala akanki sai ya aura yaji ya Sha wata mahaukaciyar corner kinji kunya,baza ki iya hakura da talaucinku ba,Raudat taji cin mutuncin yayi yawa ta fashe da kuka yace ai baki ga komai ba ma Sai an Miki dukan tsiya an zagi iyayenki a bariki sannan Zaki San kin Shiga duniya am warning you ki koma gida yafi Miki mutunci,ga inda larabawa ya kamata su sakawa suna Shari,ai ke titin maza ce kowa bi yake abi ta Shari sittin a fito ta Shari Mansir ko mai kin bayar a waje,Raudat tace kaima ai kwarto ne,gidan wa Kika ji na taba haurawa? Allah ya Isa ta furta tare da shigewa part dinta ya dinga dariya yace ki fito muyi mana matsoraciya yaja Tsaki ya shige bangarensa shima.

Aisha matsawa tayi sai Farooq ya saketa sabo da haihuwa,Farooq yace wlh Indai akan laifin da nake Miki ne na daina Aisha na tuba bazan sake bata Miki rai ba yanzu zamu zauna lafiya Ina sonki dan Allah kiyi Hakuri, Aisha tace ba akan fada bane ko wanne ma'aurata Haka suke fada kullum Kawai ka sakeni haihuwa nake so na gaji da Zama da Kai, Farooq ya dafe Kai yace Aisha bakya tausayina? tace Kawai ka sakeni,kuka wiwi yakeyi ya buga ya raya taki yarda yaje ya sanar da iyayensa sunce tunda ta bukata ai ya halatta haihuwa take so ya barta ta tafi,Maman Aisha Kuwa har gida ta aikawa Iyayen Farooq Kan su sa a sakar Mata yarta haihuwa suke so,dole Farooq ya rubuta saki daya ya bawa Aisha tana kuka shima Yana kuka domin itama bata son barin gidan tana son mijinta amma son haihuwa ya rufe Mata Ido Haka ta hada kayanta Yana kallo tayi tafiyarta.

Bayan wata daya Oga Aslam in Banda tunanin Nusaiba ba abinda yakeyi ya tambayi Mum dinsa ko Zata Gane su Sam Bata gane ba har can Taraba yaje ya zaga danginsa amma baiga ko masu Kama da su Nusaiba ba,ya shiga damuwa ba abinda yake tunawa sai Nusaiba amma bai gansu ba,yau ya fita gidan Abokinsa Yana driving yazo dai dai layin su Nusaiba sai ga Nusaiba ta dawo daga wani shago ta siyo garin kwaki,a gigice yayi parking a saitin Nusaiba tare da sauke Glass yace Hey,Nusaiba ta ganshi tabbas shine karyarsu ta Kare jikinta ya hau rawa Kar Kar, yace Kinga get in the car let's talk,shiga muyi magana,Nusaiba bata da zabi haka ta Bude gaban mota ta Shige tuni ta Fara kuka asirinsu ya tonu,kafin ma yayi magana tace dan Allah ka yafe Mana wlh dama ba Yan uwanku bane yunwa ce ta kaimu,dama haka mukeyi duk randa bamu Dora tukunya ba sai mu samu unguwa me kyau mu dinga shiga gidan mutane Watarana ma Yan polio muke cewa sai a bamu abinci mu ci mu koshi mu tafi wannan karon shine Muka fada gidanka ka kulle mu,Aslam yace oh my God da tun farko Kun fada min ai bazan sa a kulle ku ba Kun min karya kunwa kanku ya kuka Yi da iyayenku?Nusaiba ta bashi labari yayi dariya sosai a nan ta nuna Masa gidansu da gidan su Charity sannan ya tafi Yana ta farin ciki.

Tun daga ranar yake zuwa gidan su Nusaiba Mama sai Murna takeyi Allah yasa ya auri Nusaibanta,gidansu ya samu aka sake Gina musu dakuna guda biyu ya Zama suna da dakuna Uku ya budewa Mama katon shago a layin Danta Ameer Yana Zama a ciki duk kannen Nusaiba ya canja musu school Mama ta koma bata da matsala suna babbar Sana'a idan Ameer ya tafi makaranta Mama ke Zama a shagon idan ya dawo sai ya karbeta,Har Nusaiba ta daina talla ya maidata school Allah Allah suke Aslam yace Yana son Nusaiba, Charity dai tana tallanta duk tasan taimakon da yayiwa su Nusaiba itama ya bawa Dauda kudi ya ja jari,Nusaiba an samu suturu masu tsada wanka take dauka sosai ta Zama Yar gayu yanzu sai ji da Kai takeyi ana haka Aslam ya sanar da Mum dinsa ya samu matar Aure, tace a satin Nan zata Zo Nigeria,Aslam yau driver ya kawo shi ya Sha wanka na daban Yana zuba kamshi cikin wani shadajjen yadi milk,Nusaiba ta fito suna tsaye a jikin motarsa yace kin San me yake tafe dani Kuwa Nusaiba,tace Ina jinka Allah Allah take ya furta,yace tunda na ganki naji Ina sonki a Raina Kuma Ina so na aureki da gaske nakeyi,Nusaiba tana ji tace ka turo manya ko gobe ma ba damuwa,mamaki yayi amma yaji dadi yace Inshaallah gobe Mum zata Zo idan tayi bincike Zan turo Manya ki fadawa Abba yayi nasa binciken,Nusaiba tace kyale Abba Indai Mama ta yarda ba matsala ba sai anyi bincike ba,ka Sanni na sanka mene a ciki,Aslam Yana ta mamaki dai haka,shi kuwa Shehu ana fada Masa ya shiga bincike Kuma ya samu Aslam mutumin kirki ne Dan manya Dan asali.

Mum tana zuwa washe gari taje gidan su Nusaiba Kuma ta yaba da hankalinsu ba a dauki lokaci ba aka kawo kudin aure sannan aka saka rana wata Daya kacal,Mama harka ta bude itama kullum Shar zaka ganta da yaranta Shehu ya samu jari Babba sai harkarsa take dama baya iya ciyarwa, Charity tuni an Fara shirye shirye Charity gidansu na bulon siminti ko Ina a sumulmule su dan fi su Nusaiba danshi danshi,Nusaiba tana tashi fitar da anko ko shawarar Charity bata nema ba ta fito da leshi Dan dubu goma Sha biyar, Charity tace Haba Nusaiba kamar kin manta inda Muka taso ya rayuwarmu take kaf kawayenmu talakawa ne Yan talla ko ni da nake babbar kawarki a Ina Zan samo wannan kudin haka,Nusaiba ta yatsina fuska tace ke karki damu zansa my Love ya dinka Miki haka na fitar da anko biki ne na masu kudi wacce taga zata iya tayi wacce baza ta iya ba fine dama Mum dinsa Bata Jin dadi ba wata Dinner za ayi ba,dalla share zancen nan na baki labari nasan fa ana daura aure zamu tafi honey moon irin su Paris da Dubai ya Kika ce,Charity ta kalli Nusaiba tace tsakani da Allah Nusaiba kin canja kina bani mamaki Wai kudin Aslam Zaki aura ko kuwa aure zakiyi tsakani da Allah na fa kasa gane miki,Nusaiba tace Kinga nifa bana son irin wannan ke ana neman harkar ci gaba kina shirme yanzu kudi ake aure ki tashi ki nemi naki kema idan saurayi bai shirya kashe kudi ba yaje ya huta yaci gaba da Adana gwaurantakarsa Ni da uwata Alhmdllh yanzu mun samu daula,Siyama ta tsaya kawai tana kallon Nusaiba da mamaki.

Nusaiba tana komawa gida ta bawa Mama labarin Kawarta Siyama,Mama tace Yarinyar nan data maida sunanta na arna shine zata koya Miki tarbiyya,Yarinyar da kullum cikin Riga da wando take Kamar Yar arna ni haushi ma kike bani da kike Bari Yana taimaka musu da kudi har jari ya bawa Dauda idan tayi zuciya ta samo nata mijin shashashar yarinya kodaddiya idan kin shiga karki zauna haka sakaka duk abinda Kika samo ki kawo gida a hankali mu tara kadara yanzu ba a Zama haka,Nusaiba tace haba Mama Ina da wayo fa Kuma nononki na tsotsa,ai kinfi kowa Shan Nono na Sanda kina yarinya baki girma da wuri ba shi yasa ban yayeki da wuri ba sai da Kika Sha nono da yawa Suka Yi dariya,Mama tace Kinga yanzu ke ba sa'ar Siyama bace Allah ya Baki miji me kudi kin girmi kawa da ita ki tabbatar ta koma boyi boyinki a gidan mijinki kizo ki dauketa a matsayin Yar aiki ta nan zata tabbatar ke ba sa'arta bace yanzu,Nusaiba tace kin kawo Shawara Mama dole ta koyi darasi bari Kawai ayi auren










AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢️AUREN MU🛢️


11-15


Official

By
AsmaBaffa




Page naki ne
UMMU DEEJAT







Raudat ta ja tsaki,cikin masifa ya hayayyako ya tsani Tsaki botikin wankin nata ya dauka ya juye Mata ruwan kumfar a jikinta, tace mugu azzalumi sai na rama talaka baka da sisi kudin haya ma ka kasa biya ta dauki ruwansa na dauraya ya rike botikin tana ja yana ja yace kin San Allah Indan Kika bari na zani ki sai kin koma ja,sai kalarki ta koma ja ki kiyayeni kin San Ni waye,an ja tsakin ta sake jan dogon tsaki tace an ja tsmmmmm ta sake jan dogon tsaki tace kayi abinda zaka Yi sai gayu ba ko kwandala,Affan Kansa ya kalla yace kalleni kalli kalata kyakyawan guy,Dariya Raudat tayi tace na banza ba ai gwara mummuna me kudi koma mene yafi irinku,Takaici ya Kama Affan ya dauki bra dinta yaje ya cillata ta saman katanga tace Kaine talaka an fada maka biyu ne kacal dani,Guda biyu rak gareki haka zaki fita ragajeje kowa ya gani abinda kike iyayi da shi,abu ya zube zubabbe sai kace pillow Gwauro,yanzu da Zan baka da gudu zaka fara kaunarsa,can ya matse Miki..

Me gidan da suke cewa Landlady itace ta fito tace Kai Wai ku baku Zama lafiya ne sai kace karnuka kullum fada me yasa bakwa ji ne? Affan bai biya kudi ba har yau Landlady tace Kai bana ta taka ba dan gidana bane kaki biyana kudi kullum bana ganinka ko ka biya kudi ko ka bar min gidana in kawo Wanda zasu iya biya,Raudat tace a biya kudi a zauna lafiya tsaki yaja yayi sauri ya shanya kayansa ya gudu part dinsa yasan bai biya ba

Kwanan Affa shida ba a ganinsa a gidan dukkan yan gidan Basu ganinsa an rasa Ina ya tafi ashe yana gidan da asuba yake ficewa sai dare yake dawowa sabo da Kar ma Landlady ta ganshi,yau sai da asuba kafin ya tashi a bacci ta fada bangarensa ta sameshi ya tashi kenan ya idar da Sallah zaiyi shiri ya bar gidan,yace lafiya? Me ya faru haba landlady dakin Namiji ne fa Kika fado min ciki irin wannan lokaci power namaji tana tashi yanzu ne dai dai lokacin da Namiji yake mikewa Zan iya raping dinki, yanzu idan nayi Raping naki yaya kenan kina mace Kuma baki wuce 40yrs ba har yanzu zamu iya sha'awarki ni har na fara Jin ma sha'awarki, Landlady tsoro ya kamata Kar fa da gaske Affan yake tasan bata kyauta ba tace Yi hakuri to kudi nazo karba ka shirya anjima ina jiranka tana Gama fada ta fice,da sauri Affan ya shirya ya Sha tea ya fice ya bar gidan bai dawo ba sai tsakar dare,Raudat tayi zaton ma ya bar gidan ba kudi amma sai taji kamshin girkinsa na tashi a nan ta tabbatar Yana nan akwai sheka girki wajen Affan

Nusaiba sun buga sun raya me gadi yaki Bude musu yace Kun zo daga Kauye Ina kuka sani a birni da har zaku fita yawon gantali Salon ku bace Oga ya koreni,gashi karya sukayi ba damar suce ba daga Kauye suke ba,cikin palon suka koma Charity tace muna cewa bada Kauye muke ba Masu kudi kamamu zasu Yi suce munzo bincike,Nusaiba tace mun shiga Uku gidanmu,mamata ni ke Mata tallan kosai,Abbanmu ma na shiga Uku na gama yawo,Charity Kuwa duk ac dake palon gumi take faman hadawa tace a hannun Kanin Babana nake kin San Halinsa shi da Anty matarsa na shiga Uku duk aikin gidan nan ni nake Yi ga tallan Alala da nake fita mu roki Yar aiki ta fada musu ba kwana zamuyi ba dama biki muka zo mun leko mu gaisa,haka Nusaiba tace kin iya dabara Suka samu me aikin ta shigo tana mopping, Charity tace Dan Allah kice musu su Begin at home ne ma'ana Charity zuwa mukayi mu gaisa daga gidan biki muka dan karaso yau zamu koma,Yar aiki tace to ta koma sama tayi knocking Oga Yana ta aiki a computer yece come in,Me aiki ta shiga ta sanar masa da Sakon su Nusaiba,tana cewa begin at home wai Charity yace cikin yan uwan Mum ne wannan maguzawan da suke Mambila baza a bari su tafi ba yau su nufi hanyar Taraba da Yamma haka ai kamata yayi su huta har na sati daya Mambila fa ke kinsan nisan wajen kuwa yanda Mum ke son Yan uwan ta ya kamata su huta kin San Ina son abinda Mum ke so Kar a barsu su tafi Kuma karki sake dawowa I'm busy Right now bana son fita idan kika sake dawowa na koreki daga aiki.

Me aiki da sauri ta dawo ta fadawa su charity abinda yace tace yace Kar na sake komawa inda yake baza ku min asarar aiki ba idan zaku kwanta ga daki nan ta nuna musu wani bedroom, Nusaiba ta fashe da kuka tace muje sama da kanmu suka mike tare da haurawa,lokacin daure yake da towel zai shiga wanka kowacce kofa Suka kwankwasa ba kowa har suka kwankwasa tasa cikin masifa yace idan na fito sai na balla ko waye da gudu suka sauka kasa suka sake Zama a Palo ko zai fito Shuru Shuru ba kowa har dare yayi suka fashe da kuka, dakin da aka ce su shiga shi suka shige tap din ma kasa kunnawa suka Yi sai da kyar suka kunna Alwala sukayi tare da gabatar da Sallah,har isha tayi basu ji motsin kowa ba suka sake fashewa da kuka gashi Basu da waya ko lambar wani babu a kansu bare ma su roki me gadi ya basu aro.
Mun jawa kanmu mun Sha kokonmu amma Muka ki godewa Allah cewar Charity a haka me aiki ta sake kawo musu lafiyayyen abinci haka suka sake cika cikinsu amma idan suka tuna gida sai kuka har bacci ya kwashe su.

Washe Gari Suka Yi Sallah suka fito suna tunanin ganin wani ba kowa sai me aiki tana girki sunyi sunyi akan ta fadawa oga zasu tafi Amma tace ya Mata warning baza ta je ba,Wasa Wasa har Suka kwashe kwana uku a gidan basu ga ko Kare ba tun suna cin abinci suna murna har bacin rai da tsoro ya hanasu ci,ga abincin suna gani amma sun kasa ci ba kwanciyar hankali.

Gidan su Nusaiba tun suna tunanin yawan banza ta tafi har Suka dawo kuka da addua,Shehu sabo da Yana cikin bacin rai har da basu kudin cefane,Mama ta dafa shinkafa da wake da Mai da yaji,Ihsan tace ga shinkafa yau zamu ci amma abin haushin Aunty bata nan suna bakin ciki suna murna ta wani bangaren zasu ci shinkafa,mutanen layin sai jaje ake musu ana tayasu da addua Allah ya bayyana su Nusaiba,Shehu akan baya so ya kashe kudinsa yace ba inda Zan Kai Sadaka a tayani da addua da kaina Zan roki Allah watakil ma nafi malaman matsayi a wajen Allah muyi addua da kanmu,Mama tana hawaye komai na sana'arta ya tsaya yarta ta bace tace ai ba malamai aka ce ka bi ba cewa akayi ka bada a masallaci a tayamu da addua sai kayiwa Almajirai Sadaka,Shehu yace ai ke baki San Allah ba tunaninku mata kullum a bi malamai idan baza kiyi Addua da kanki ba ki barshi,Mama cikin jarinta ta dauki dari biyar ta bawa Ameer danta tace ungo kaje masallacin juma'a kaga yau Juma'a ka siyi ruwa na du kudin ka rabawa Alummar annabi Allah ya bayyana Mana su Nusaiba,Ameer ya karba da sauri ya tafi zai siyi ruwa ya rabawa Alummar annabi Sadaqa,Mama tana da filinta na gado ta ajiye abinta,sabo da tayi Sadaka Allah ya bayyana Mata yarta tace zata siyar da filin,Shehu Sadakar dari biyu ya kasa Amma tana daga filinta zata siyar yace zai siya ya lallaba Mama zai siyi fili,filin a Kauye yake Bai wuce dubu dari biyu ba amma Shehu yace filin Bai wuce dubu dari da talatin ba Mama bata San Kan komai ba yace ya siya zai bada kudi ya lallaba ya karbe takardu tayi signing da komai shima haka ba shedu bata fadawa kowa ba Shehu ya hana kudi tana ta binsa karshe ma Sai labari taji ya siyar da filin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login