Showing 1 words to 3000 words out of 74955 words
Chapter 1 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
***
[1/1, 12:35 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
23/10/2023 Monday. 2:18 PM.
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 1*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai, tare da salati ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama.* Alhamdulillah yau Yau 23 ga watan 10 shekara ta 2023, Allah ya nufeni da kafa alƙa'amina na fara rubuta sabon littafina mai suna INDA RAI, Ya Allah ina tawassali da kyawawan sunayenka, Allah ka bani ikon rubuta alkhairi a cikin wannan littafin nawa, kayi riƙo da hannayena da rubuta sharri duk ƙanƙantarsa, ka bani hikima da basirar rubuta abinda zai amfanin al'ummar musulmi baki ɗaya, Alhamdulillah Yah Allah ngd maka dama ka nuna min forkon littafin nan Lfy. Ya hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, ka nuna min ƙarshe littafin nan Lfy dani da masu karatun baki ɗaya,Yah Allah ka nuna mana forkon littafin da tsakiyarsa da ƙarshensa dama duk wani sashi da layi da ɗigo na cikin littafin nan Lfy. Yah Allah kayi riƙo da hannayena da tunani da yatsuna da rubuta abinda zai zame min masifa ko wahala ko tozarta na nan gidan duniya da ƙiyama. Yah Allah gamu gareka kaine mai rawaya, mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, Yah Allah ka rayamu bisa imani kan tafarkin Muslunci da bin dokokin shariya, Rabbi ka azurtamu da lfya, da imani, da wadata, da kwanciyar hankali, da zaman lafiya, kasa muyi kekkyawar rayuwa, ka bamu kekyawan karshe, kasa mucika da imani, da kalmar shahada, ka sadamu da mala'ikun rahama yayin fita ranmu, ka sauƙaƙa mana amsa tambayoyin Qabari, ka yalwanta mana makwancinmu ka faɗaɗamana, ka haskaka mana, ka ni'imta mana, ka ƙamsashamana, ka sayan ƙaburburanmu su kasance dausayin Jannatul Firdausi, damu da iyayenmu da ƴaƴanmu da yayunmu da kannemu, da kullum musulmi. Ya rabbil izzati ka samu ƙarƙashin inawur al'arshinka a ranar da babu wata inuwa sa ita, badan mu ba, badan ayyukan muba, Yah Allah sai dan rahamarka da ƙaunarka garemu, Allah ka sauƙaƙa mana tsallake siraɗi,😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻. Yah Allah kasamu cikin al'ummar Annabi amintacciya. Yah Allah mu bayinkane masu yawan zunubai, sai dai hasken gafararka da rahamar ka ya rinjayi duhun zunubanmu, Yah kayi mana gafara da rahama ka shafe zunubanmu. Ka shiryemu bisa tafarkin gaski ka ɗaurar mana da imaninmu a zukatan mu, Yah Allah kada ka jarabcemu da ƙaddarar Jarrabawar da zata raunata mana imaninmu bare ya rabaku dashi.
Ya Allah ka azurtamu da halal, ka nesanta haram daga garemu. Yah Rabbi mu ma buƙatane a gareka kai kuma mai badawane da baya yankewa. Yah Allah masu lafiya, ka ƙara mana Lfy da imani, marasa lafiya ka basu lfya da imani, masu ciki Allah ka sauƙesu lafiya, masu son haihuwa ya Allah ka azurtasu da nagartattun yara. Yan Allah mu masu Yara Allah badan halinmuba Allah ka shirya manasu ka tsaresu da sharrin akiruzzaman, Yah Allah masu neman mazan Aure Allah ka azurtasu da maza na gari, maza masu neman aure ka azurtasu da mata na gari. Yah Allah masu son zuwa aikin hajji da niya, Allah ka kawo mana sauƙin rayuwa da rogomin farashin komai na rayuwa ka bamu ikon zuwa Hajji kasa muyi Hajji Mabrooq, Yah Allah yan uwanmu musulmai dake Palastine Yah wahidulqaharu, ka shigar musu faɗanan ka tozarta waɗanan baƙaƙen kafuran Yahudawa da basa son ci gaban addininmu. Yah Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu. Yah Allah ka kawo mana sauƙi da ƙarshen yan ta'adda dake addabar ƙasarmu Nigeria, Yah Allah ka karemu damu da maƙotanmu, musamman Niger, dama duk Afirka baki daya da duk inda musulmai suke a faɗin duniyar nan. Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati.
*Littafin INDA RAI, na kuɗine, kuma nawa ne ni AYSHA ALIYU GARKUWA, hakkin makalarsa nawa ne, ban yardaba ban amince ba, ban lamunceba, a juya min labarin littafina ta ko wacce sigar, har sai an nemi sahalewata da yardana... idan na amince na bada dama sai ayi. Zama Lafiya yafi Zama ɗan sarki barin haƙƙin wani shine zaman lfyar tauye haƙƙin wani kuwa ko ka zauna Lfy a duniya tofa kasan/kinsa/kunsan gida biyu Allah yayi mana.....!*
*Yah Allah ka jiƙan mahaifinta, Faɗimatuzzahara, Rabbi kayiwa (Dedde na) Rahama da gafara alfarmar Annabi da Alqur'ani, Yah Allah kasa mutuwa hutuce a gare ta. Da ita da Yah Abubakar na da Kakata Ayshae, Innayi na, da kakana M Muhammad Babayo Maiturare da kuma Muhammadu Daniya. Da ma dukkan yan uwana Amin Ya Allah*
_Wannan littafin sadaukarwane, ga ɗaukacin ƴan uwanmu musulman ƙasar Palastine da aka kashe Yah Allah ka jiƙansu kayi musu rahama ya hayyu ya ƙayyum ka ɗaukaka Musulunci da Musulmai ka ƙasƙantar da Kafirci da Kafirai._
*Littafin INDA RAI na kiɗine 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 mutan Niger ku kuma 1000fc ne wato kaka ɗaya kacal ta wurin Mommy zaku biya +22790899076. Please mommy babbar macece dan Allah mu girmama shekarunta.*
Adamawa Yola. Yau garin an tashi da tsananin sanyi mai ratsa jiki da ɓargon ɗan adam, sanyine kuma irin na damuna, wanda aka kwana zuga ruwan saman kamar da bakin ƙwarya, kana aka wayi gari dashi, domin har yanzu karfe 5:00 pm. Ana sassayan yayyafin da ya tsananta sanyi a garin wanda ya tilastawa mafi akasarin, mazauna garin sanya rigunan da zasuyi musu Garkuwa Da sanyin...
Yola international airport.
Cike yaƙe maƙil, da tarin dan-danzo Mahajatan jirgin ƙarshe da zai tashi daga Nigeria zuwa Saudi Arabia.
Gaba ɗaya taron matafiyan, duk wanda ka gani, fuskarsa cike da tarin Alihini, ɗimuwa,gami da matsanancin bugawar zuciya mai cike da Fargana kana da taraddadin mai tsananin gaske, irin fargabar da ɗan takarar shugaban ƙasa da ya binne miliyoyin kuɗaɗe a campaign, yake riskar kansa a lokacin da ake faɗin sakamakon zaben, to irin wannan fargabar maniyatan suke ciki baki ɗayansu.
Saboda hukumar amsar jiragen baƙin mahajjata na duniya baki ɗaya, ta fitar da sanarwar cewa, da ƙarfe sha biyun daren yau ɗin ne, za'a rufe KING FAHD international Airport, Saudi Arabia, wanda dama shine ƙarshen rufewa, duk sauran Airports ɗin a rufe su, saboda dafifi da ƙurewar lokacin.
Cikin tsananin shiga ruɗu, wani farin Dottijo da bazai gaza shekaru 52 da biyu ba, ya shiga cikin asalin taron Maniyatan, gyaran murya yayi tare da fuskantar su, da kyau a matsayinsa na Amirul Hajj, na Adamawa wanda kuma a shekarar ne aka ɗorashi, yayin da tuni tsagin adawar sa suke farin cikin, ganin a shekararsa ta farko Maniyata sama da ɗari bakwai da hamsin ne bazasu samu damar zuwa Hajji ba.
Fuskantar taron ɗaruruwan Mutanen maza da mata, yayi cikin Muryarsa dake cike da rauni, tashin hankali da Karaye yace.
“Da forko ina mai baku haƙuri, bisa jinkirin da aka samu na isowar jirgin ƙarshe da zai kwashi mahajjatanmu, zuwa ƙasa mai tsarki.
Kuyi haƙuri ku kwantar da hankalinku, kun sani na sani alƙawarin Allah tabbaceccene, in dai Allah ya ƙaddara bana zamuje Saudi Arabia kuma muyi aikin hajji to in sha Allah, sai munje, in kuma Allah yayi bamu da rabon zuwa bana, tofa duk nacinmu da ƙoƙarina wurin ganin hakan ya tabbata bazai yuwuba, so mu maida lamarinmu ga Allah domin shine kaɗai mai iya mana...”
Sai kuma yayi shiru tare da zurawa P.A ɗin tsohon Amirul Hajj ido, wanda aka sauƙe, kafin a ɗorashi.
Cikin haƙilo,hargowa gami da ɗaga sautin murya mai tattare da kishi ya kalli taron jama'ar tare da cewa.
“Na nawa kuma, ai kunga banbancin aikinsa da wanda ya gabata ina tunawa last year, tun saura kwana biyar a rufe Jidda Airport, aka gama kwashe mahajjatanmu, bana kuma gashi duk, Nigeria mune kuran baya, kai Bama Nigeria kaɗaiba duk duniya mune kuran baya, yanzu fa ku duba karfe 5:00 pm. Jirgin namu ma bai isoba bare aje ga batun scaring bare akai ga tashinmu.
Gashi a ƙalla mun kai mutum 700 to jirgin da yake dashi da muke tsammanin zuwanshi ma mutum 500 kacal zai ɗauka.
Kunga kenan duk yadda za'ayi ma sai mutum ɗari biyu da burbushi sun rasa damar zuwa aikin hajji da kuɗinsu, Amman za'a hanasu zuwa.
Annabi yayi gaskiya da yace. Muje tun kafin a fara hanamu zuwa”.
Gaba ɗaya al'ummar wurin mgnar sa tayi tasiri a zukatansu, saboda shi maniyacin zuwa Hajji babu abinda ya tsana a duniya, kamar abinda zai katangeshi da tafiya.
Wani sashi kuma na masoyan tsohon Amirul Hajj da aka sauƙene suka fara sowar cewa.
Bamayin bamayi mai girma Gamna a canza mana shi.
Mafiya akasarin maniyatan kuma kuka suke yi sharshar da hawayensu, More especially wadanda shine zuwansu na farko
su kam kuka suke harda gunji.
Cikin gamsuwa da fusatan maniyatan farin Dottijon dake cike da kamala ya ɗaga musu hannun, cikin tsananin tuhumar kansa da laifi ganin ya gaza wadatarwa mahajjatansu ababen sufuri wasu hawaye ne masu zafi suka fara tsatsfowa cikin jijiyoyin idanunsa. Allah ya sani baya son ya zama sanadin rashin zuwar wasu domin ba mamaki wani in bai je bana ba, babu tabbacin duk zasu kai next year a raye, murya na rawa ya kallesu kana yace.
“Kuyi haƙuri mu maida lamarinmu ga Ubangiji mabuwayi gagara misali, in sha Allah, duk zamu tafi, gani nan fa nima kaina ban taf....
Da wani irin sauri duk suka ɗaɗɗaga kawunansu sama.
Saboda jin Diri da rugugin babban jirgi dake saukar angulu a cikin Airport ɗin.
Cikin sauri wannan Dottijon ya faɗi ƙasa tare da yin sujudushukur kana hawayen farin ciki na kwanta Ya daga idanunsa.
Maniyatan kuwa hamdala suka fara yi, wasu na ruggumar juna wasu na sujudushukur ɗin, Aysha ma tana cikin masuyi sujudushukur ɗin.
Sai da tayi sujjadar ta godewa Allah, kana ta miƙe tsaye, tare da shiga sahun cikin masu ruggumar juna.
Cikin tsananin jin daɗi ta ruggume.
Maryam ƙanwar Masoyinta, abin alfahari ta wato.
Barrister Kamal Mubi.
Itama Maryam ruggume Ayshan tayi cikin jin daɗi tace Alhamdulillah, Aunty Aysha.
Allah ya amsa addu'armu”.
Cikin jin daɗin Aysha ta sharce hawayenta domin tanaji a jikinta in sha Allah, zataje aikin hajj.
Haɗaɗɗiyar wayarta ƙiran Iphone 13 pro ta zaro kana ta dannawa Barrister Kamal kira, bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga cikin tsananin so kulawa yace.
“Hallo My dear ya akayi”.
Wani amintaccen murmushin da yasa dimples ɗin ta duka biyu lotsawa tayi, tare da lumshe manyan idanunta masu yalwataccen gashin idanun dake jiƙe da ruwan hawaye cikin murya mai cike da haiba kamala da girmama kai tace.
“Alhamdulillah Barrister, jirgi ya iso”.
Da sauri yace.
“Masha Allah, Alhamdulillah Dear sarkin kuka, yanzu dai kuka ya ƙare ko shogoɓatuna?”.
Murmushi mai cike da kamala tayi, ta buɗe idanun nata cikin muryar ta da kan rikita kwanya mazaje tace.
“Eh Barrister”.
Kanshi ya jinjina cike da jin daɗi yadda take mgna dashi cike da biyayya mai gauraye da so, numfashi mai sanyi ya fesar yana mai imagine irin zaman auren da zasuyi yace.
“Amman wanne jirgine, badai Arik bakam bane ko?”.
Da sauri ta juyo gefen damanta inda farfajiyar sauƙa da tashin jiragen yake, idanunta ta zuba akan tambarin jikin jirgin da aka rubuta Saudi Arabia da manyan baƙake, kana gefe firko an rubuta da harshen larabci.
“A'a ba Arik bane!”.
“Max Air ne? Ko Kabo? Ko Mangal?".
Ya kuma tambayar ta, cike da tsoron kar karamin jirgi aka samu ya gaza ɗiban mutunen duka ya zama tana cikin waɗanda basu samu shigaba.
Cikin sauri tabi bayan Maryam da ta kamo hannun tana ja da alamun har an fara Screening.
Cike da jin daɗi tace.
“A'a Barrister duk basu bane, duk mun girmesu ai, mu a abun masu abun zamu zo, Saudi Arabia Airline ne, da kanshi yazo ɗaukarmu, wani abun saimu ƴan baiwa.”
Cikin Murmushin ta ƙare maganar tare da miƙa, ƴar takardar visa inta, aka buga mata tambari, a kai kana ta naɗeshi cikin E passport ɗinta.
Haka akaci gaba da tantancewa da yi musu duk abinda ya dace, sauri-sauri gudu-gudu.
Domin su samu su tashi karfe shida dai-dai.
Dan in sun tashi shida dai-dai ɗinne zasu isa ƙarfe goma dai-dai namu na agogon Nigeria Niger Cemaroon da Chadi wanda kuma zaiyi dai-dai da ƙarfe sha biyu na daren agogon Saudi Arabia, wanda kuma suka bada dakekkiyar sanarwar mai cikekkiyar ikon cewa sha biyu dare dai-dai zasu rufe Airport ɗinsu, sunyi gargaɗin cewa koda one minute wasu suka makara tofa dole sai dai su juya inda suka fito.
Alhamdulillah tuni sunyi nisa a komai har Passingers sun fara shiga jirgi.
A ɗaya sashin kuwa wanda ake bincikar lafiyar.
Pilots and Hostess tuni an gama bincikar lafiyar hostess ɗin kab, an kuma basu duk kulawar data dace dasu domin.
Yanzu zasu juya duk da su an sauwaya wasune.
Cikin ƙwarewa likitan dake sashi na musamman ya fara bincikar lfyar pilot ɗin da zai juya da jirgin. Sheykh Afif Muhammad Taj. ɗin da abokin aikinsa Pilot Irfan Imran ya sauƙo da jirgin kana kuma zasu juya dashi.
Cikin ƙwarewa da iyawa, Doctor ya gama dubasu ciki da waje.
A hankali ya jinjina kanshi tare da kallon Sheykh Afif Muhammad Taj yace.
“BP ɗinka Nomarl kai komai ma Normal ne sai dai Heart ɗinki na beating so fass yayi yawa, over yana bugawa sosai.
Menene matsalar?”.
Cikin sauƙe nannauyan numfashi tare da lumshe sexy eyes inshi da tarin gajiya ya ƙara rikitasu tare da ciwon kai daya buwaye shi, saboda rashin bacci, domin tunda watan Zul hajj ya tsaya bai samu cikekkiyar nitsuwaba kasancewar, yana aiki a ƙarƙashin Company Saudi Arabia Airline.
Wanda hakan kan sa duk ƙarshen shekara aikinsu kan ruɓanya.
Cikin tattausan lafazi da sassayan murya yace.
“Hmmm”.
Cikin kulawa Dr ya kalli pilot Irfan Imran dake cewa.
“Amma ai wannan ba wata matsala bace da zata hanashi aiki, sai dai kanshi na mishi ciwo”.
Ya ƙare maganar cikin alamun sanin halin Sheykh Afif Muhammad Taj ɗin, mutum ne shi mai tsananin zurfin ciki ga juriyar ciwo, ya tabbatar bazai buɗi bakinsa yace ga wani abu na mai ciwoba, ko shi sai dai ya gane, da ganin jijiyar goshinsa ya tashi, kana na gefe da gefen kanshi suna harbawa, ga kuma idanunsa da suka sauya launi zuwa ja.
Afif Taj. kenan damo Sarkin haƙuri ya kasance Mutum mai tsananin haƙuri kawaici Uwa uba zurfin ciki yana da wasu irin nutsatstsun halayya masu cike da Alkunya sai dai yana da tarin kwarji.
Kai Doctor ya jujjuya tare da cewa.
“Tun yaushe yake fama da matsalar bugun zuciyar, da ciwon kan?”.
Yana mai miƙewa tsaye yace.
“Almos 2 weeks yana fama da matsalar”.
Da sauri Dr yace.
“Ok yanzu kafin kazo, suma can Saudi Arabia sun san da wannan matsalar taka kenan?”.
Kai ya jinjina tare da fara tafiya, yana mai kallon time a haɗeɗɗen agogon Diamond na company Gucci dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Ganin ƙarfe shida saura kwata ne yasa ya ƙara saurinsa bisa gefen wani ɗan madaidacin gado ya zauna.
Pilot Irfan Imran kuma cikin yaƙini yacewa Dr.
“Yess Saudi Arabia sun sani, kuma Jordan ma sun sani, hakama Qatar dan, da haka aka bashi izinin tashi a Qatar”.
Kai Dr ya jinjina kana yayi saurin bin bayan Taj ɗin.
Wani ɗan maganin ya ɓalla tare da miƙa, mishi amsa yayi, ya afa a baki tare da amsar goran ruwan Faron, ya kora maganin dashi, sai kuma ya sauƙe numfashi mai nauyi, tare da buɗe bakinshi, kana ya ɗan ɗaga tounge ɗinshi sama kaɗan, saboda ganin Dr na son saka mishi maganin wanda ya fahimci na ciwon kaine, a ƙasan harshen nasa ya manna mishi ƙwayar magani, in 5 seconds maganin ya narke ya fara bin jijiyoyin kanshi, a hankali ya lumshe idanunsa tare da ɗan gyara kwanciyarsa.
Dr da kanshi yayi saurin kwantar da kanshi bisa pillow.
Lumshe idanunsa yayi kamar mai bacci, Amman ba baccin yakeba, yana sauraron bugun zuciyar tasane dake lafawa da kuma fitinenne ciwon da ya fara sauƙa.
In two minutes yaji bugun zuciyar ya lafa sosai hakama ciwon kai ɗin.
Gwaje-gwaje na musamman Dr yayi minshi dan tabbatar da lfyarsa a matsayinsa na mai jan mutum kusan dubu.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah komai yayi dai-dai zaku iya tafiya”.
Jin hakane yasa Taj miƙewa.
Tare da gyara wuyan rigarsa.
Daga nan suka fito.
Anan cikin jirgin kuwa. Alhamdulillah gaba ɗaya passingers ɗin duk sun shiga.
Yayinda tuni Hostess sun fara aikinsu, cikin iyawa da kwarewa.
Suke rurtufe durowowin jirgin, tare da gyara sakalawa passingers ɗin nasu sit belt, domin sanin pilot ɗin na shigowa zasu ɗaga ne.
Gaba ɗaya passingers ɗin kowa da irin kalar tunaninsa da muka nazarinsa da abinda yake yi.
Mafiya akasari selfee suke buga kamar ba gobe.
Wanda Maryam da Aysha ma na cikinsu.
Duk da su a first class suka, ta gaba-gaba basu da nisa da gefen matuƙan.
Sai hoto da video sukayi ita da Maryam, Murmushi Aysha dake gefen wata ƴar duma-dumar mata mai matsakaici shekaru wacce ke riƙe da wayarta bisa alamu karatun ƙur'ani takeyi cikin suratul Khaff kasan cewar yau ɗin jumma'a ne.
Ganin alamun ta dire ayar ƙarshen surar ne, tayi addu'a ta shafa a jinkinta, sai kuma ta ɗan kallesu a fakaice ganin alamun kamar dai baƙin shiga jirgine saboda yadda suke ta kabta selfee ba ƙaƙƙautawa ɗan gajeren murmushin dake nuna alamun sakin fuskantar tayi tare da ɗan jingina kanta da kujerar ta kalli gefen dama inda Aysha take, tana kallon baiwar kyau da haiba da Allah yayiwa Aysha ga tarin kwarjini, haka nan taji tana burgeta saboda Aysha mutunce mai shiga rai lokaci ɗaya, ga kwarjini tana da yanayin nan da in mutum bai san taɓa zauce tana da girman kai, sai dai bawai girman kai bane, girmama kaine in an zauna da ita kuma zaka gane nagartar halayyar masu sawa a sotane.
Cikin mutuntawa Aysha ta kalli Kamilar matar da har zuwa lokacin fuskarta ke dauke da sanyayyar murmushi kana tace.
“Hi”.
Still da murmushi afuskar matar ta ɗan gyara zaman wayar ta tace.
“Assalamu alaikum”.
Cikin lumshe ido Aysha tace.
“Afwan madadin inyi Miki sallama nace, Hi”.
Tana mai kallon Aysha tace.
“Ba komai dama nayi Miki hakane dan tunasarwa”.
Kai Aysha ta jinjina tare da gyara zamanta, kana tace.
“Sunana Aysha Abdullahi Matawalle”.
Itama matar Murmushin tayi tare da cewa.
“Ni kuma Aysha Aliyu Garkuwa”.
Cikin sauri Maryam ta ware Idanunta tace.
“Laah Aunty Garkuwa, , kai yau gani ga Garkuwa, duk da muna ƙasa ɗaya gari ɗaya Amman ban taɓa ganinki ba,