Showing 15001 words to 18000 words out of 74955 words

Chapter 6 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

jikin filar masallacin ya saki maraitaccen kuka, wanda aka kira da Ma'aruf ɗinma kuka yaleyi.

Tajj kuwa lip inshi na kasa ya jiza da ƙarfi, sai yake misalta da ace Yah Abananshi ne ke kuka hakan ya zaiji a cikin ransa,
Yasan ji zaiyi kamar zai suma, ya kuma tabbatar sai yayi duk yadda zai yi ya tsaida mishi hawayen nan.

Sai kuma ya maida hankalishi kan Ishmah dake mgna cikin tausayawa.
“Dan Allah Taj ka taimakawa tsohon nan, Please ka tsayar mai da zuban hawayensa”.
Cikin sanyi murya yace.
“Please Ishmah kada kiyi kuka, kin san cewa kukanki na ƙona min zuciya ko, gaya min wanne irin taimako zan mishi”.
Da sauri tace.
“Ka tayashi basu haƙuri ayi auren!”.
Cikin jin kukanta na hautsuna mishi lissafi yace.
“Ai har sun riga da sun tafi”.
Da sauri ya zazzaro idanunsa jin abinda tace, murya a kaɗe yace.
“eyeh hello mai kikace”.
Cikin rauni da kuma iya gskyarta kana da shesh-sheƙan kuka mai cike da rauni tace.
“Tajj ka aureta!!!”.
Da ƙarfi ya koma ya jingina da jikin gini, sai kuma ya kalli Dottijon nan da yake kuka harda majina yana bin.
mutane yana kama hannunsu yana cewa.
“Dan Allah ka auri ƴata Adaya na baka ita.”
Mafi akasari sai su kauda kai.
A haka har ya iso gaba Taj.
Riƙe hannayensa yayi duka biyu, murya na rawa yace.
“Dan Allah dan soyayyarka da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, dan tsarkin Alkur'ani da yake kanka a haddace, da kimar iyayenka Afif ka auri ƴata Adaya na baka ita duniya da ƙiyima ka aureta ka amintar da ita domin irin kane mijin daya dace da ita.”
Jin kalamansa ne yasa jikinsa wani irin saƙewa yayi luƙus sai kawai ya zauna dirshan.
Kana a sashin Ishmah kuwa cikin taya dottijon nan magiya tace.
“Taj! Taj!! Taj!!!”. Sai a kira na ukun ne ya iya furta.
“Uhmmmmm”.
Cikin tausasa lafazi murya na rawa tace.
“Dan Allah dan Annabi da darajar Yah Abana da kuma ƙaunarka da Ummey da Amincinmu, da gskyar abotarmu, da mutuntakarmu, ka aureta ka tsaida hawayen dottijon nan”.
Ya ilahi ya mujibat da'awati, yah hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, innalillahi wa innalillahi rajiun”. Sune iya ababen da yake iya furtawa a bakinsa sai kuma yayi saurin cewa.
“Shiru Ishmah na amince zanyi wannan taimakon saboda Allah da Manzonsa da ke”.
Yayi mgnar da Yaren Hausa da zama shi da itane yasa ya fara iyawa kaɗan kaɗan.
Kana yayi Hausanne saboda yasan da wuya a samu wanda zai gane a cikin mutanen wurin, Amman in fillancin Ethiopia yayi wasu zasu iya ganewa.

Sai kuma ya saki wani irin sassayan numfashi tare da kallon kamilin dottijon nan mai cike da kima kamala da rauni da yake ta zubda hawayen da magiya.
“Ka taimakeni ka auri Adaya Afif kayi min wannan taimakon, in kayi min haka ka gama min komai a aduniya, Dan Allah ka auri Adaya”.

Wayarshi ya zaro tare da rubutawa Abu Hashim text message ya tura mishi.
Da sauri Abu Hashim ya zaro wareshi jin alamun saƙo ya shigo.

Sai kuma ya jinjina kanshi tare da zaro kuɗin daga aljihunsa, kana ya irgasu, dubu 1,22000 ne kuɗinsu na can.

Da sauri ya miƙe ya nufi mall da ke cikin harabar masallacin.
Dabino da sweets ya seyo katon bibbiyu
Kana ya dawo da sassarfa ya zauna gefen. Dottijon da har yanzu yake riƙe da Tajj yanayi mishi magiya hawaye na ɗiga bisa tafukan hannun Taj ɗin.

Gyara zama Abu Hashim yayi tare fuskar Dottijon nan da yake gab da sumewa, cikin yarensu Aromo yace.
“Ni Oumar Ibarahim ina nemawa, ɗana Tajuddeen auren yarka Adaya ga sadaki mu, naira dubu 100”.

Wani irin dogon numfashi Dottijon yaja tare da juyawa ya fuskanci alƙibla yayi sujudushukur kana ya juyo ya kalli Taj tare da cewa.
“Alhamdulillah kayi haƙuri kaga na takuraka duk da na fahimci baka so. Toh Alhamdulillah gashi mun samu wani zai aurawa ɗansa ita”.
Yayi mgnar tare da juyowa ya fuskanci Abu Hashim da ba wanda ya sanshi a cikin masallacin.

Ma'aruf ne ya kalleshi cike da son gano wani aibu ko naƙasu tare dashi.
Amma. Ina babu saboda Abu Hashim yana samu albashi mai gwaɓi a hannun Taj Shiyasa in kan ganshi bazaka gane sana'arsa ba, to driving ɗinma da sai Taj na garine haka yasa a wadace yace gashi mutun ne shi kamili mai haiba.
Kuma in kaga yanayisa dole yana da ɗa kamar Tajj.
Nan take kuwa a wurin aka ɗaurin auren.
Adaya da T.....


*Shi wannan littafin salon sa na dabanne ni kaina yana tsumani, ki biya koyi karatu cikin aminci 1k ne kacal fa 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276, ku kuma mutane Niger 1000fc ne jaka ɗaya kacal kenan +22790899076 Zaku biya ta wurin Mommy*

By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/4, 12:58 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 4*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Littafin INDA RAI na kiɗine yanzu free pages ne mukeyi ku biya in saku a group, ku karanta cikin aminci ba haƙƙin kowa bisa kanku, 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Gareku mutanen Niger 1000fc ne zaku biya jaka ɗaya kenan ga number wacce zakuyiwa magana +22790899076 Please a mutunta shekarunta babbar macece.*

*Haɗin amarya budurwa mai ƙarancin shekaru da mai matsakaicin shekaru da kuma mai ɗan yawan shekaru, kana haɗin amarya bazawarar da take da ragowar ƙuruciya, da mai matsakaicin shekaru da wacce shekaru sun ɗan ja, hadi dai-dai da halittarki ƴar uwata, ƙawata, ƙanwata, ƴata, ƴaƴata, kai harma da ke kakata, akwaisu masu maida tsohuwa yarinya, duk mutuwa da sakewar fatar nan zata tattare da tsuke ta katse ta rayu da ni'imtaccen yayyafin gyaran zaman aure. To wai ke mai jego ina kike akwaisu fa naku haɗin, in ma yawan* *haihuwa yasa wurin ya sake ya kuma ƙafe, barden goyo ko ɗanyen goyo, akwai haɗinku Zaki min bayanin me matsalarki! Sakewa ne? Rashin ni'ima ne? Rashin feeling ne, ko rashin kuzari ne Duk fa akwai haɗinshi haɗin uwar gida ko tsakar gida duk akwai, set ɗin na hawa hawane, duk ƙanƙantar kuɗin Customers na baya zuwa ya koma baya, ƙananan set ɗin daga 40k ne zuwa ƙasa 35k 30k 25k 20k 15k ƙaramin haɗina ɗan autan 12k sai haɗin robor ƙasaitacciyar macen 5k. akwai manyan set ɗin daga 50k 60k 70k 80k 90k sai sha kunɗum ɗin 100k. Sai maganin infection set 10k rabin 5k Maliƙi 5k daɗi har maɗiga 5k akwai haɗin kazar 12k akwai zabuwar 20k in dai a shirye kike ga 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, ta wannan number zaki turo min shaidar biyanki 08069423567 itace ta Customers ɗina na kayan ɗa'a*

Tajuddeen Muhammad Tajuddeen, (Afif)
kenan saboda sunan kankanshine yaci.
Tajuddeen Shiyasa akayi masa laƙani da Afif.
Sai Afif ɗin kuma ya danne Tajuddeen ɗin.

Shiya sai na kusa da shine kaɗai suka san hakan.
Hakan yasa ko mutum ɗaya bai gane cewa dashi Afif aka ɗaura aren Adaya ba.

Shi kuwa Taj ana gama ɗaura auren bisa sunan da ƙa'idar addinin musulunci.
Yaja wani ɗimautaccen numfashi tare da zurawa, Abu Hashim idanu, ganin Dottijon nan ya jawo hannunshi tare da cewa.
“Bismillah ko Malam Ousman muje, kaga gidana, yana nan gefen masallacin, muje in danƙa maka hannun Adaya ka kaiwa ɗanka.”
Da sauri Abu Hashim ya juyo ya kalli Taj domin kalaman dottijon sun zo musu a bazata.
Shi kuwa Taj wayarshi da yayi mishi text message dashi ɗazu, ya kumayi mishi wani text ɗin.

Da sauri Abu Hashim ya zaro wayatarshi daga aljihu, tare da duba saƙon.
Murmushi ya ɗanyi tare da miƙewa tsaye tare da fara gaisawa da mutanen dake ta miƙa mishi hannun daga bisani suka fita.

Taj kuwa yunƙura yayi tare da tattaro ragwar ɗan kuzarinsa ya miƙe tsaye tare da binsu a baya, tafiya yake yi tamkar babu laka a jikinsu, tarin ƙalubalen dake gabansa a lamarin yake hasasowa yadda zai fuskanci mahaifinsa yayi mishi wannan bayani mai kama da tatsuniya ko mafarki, ko hikayar cikakkun marubuta mai cike da sarƙaƙiya.

Numfashi mai nauyi ya sauƙe tare da rumtse idanunsa, ya sani ko Ummeynshi bazai iya fuskanta ido da ido wai yace mata, yayiwa kanshi aure ba, bare kuma Yah Abananshi da ya san halinshi farin sani, baya ɗaukan wargi,
yatsunsa biyu yasa ya sharce zufan dake tsatstsapa mishi bisa goshinsa.
A hankali ya jingina jikin motarsu, tare da rumtse idanunsa, ya sani Ko babban yayansu, Hafiz bai isa yayi aure mahaifinsu bai saniba, wanda shima yana da yaran da sun kusa aurema bare shi, ya Salam shine abinda ya furta a tsakanin lips inshi, runtse idanunsa yayi tare daci gaba da mgnar zuci dake tabbatar mai da cewa Ishmah na juya tunaninshi da kwanyarsa ta yadda baya iya ƙin yin duk wani abinda zai sata farin ciki, Allah ya sani ji yake rayuwarsa bazata samu cikakkiyar nasarar in har bai sata farin ciki ba.

Ido ya zubawa Abu Hashim da Dottijon nan da wasu mutane da basasu, gaza huduba, sunka nufi wani gate, da yake fuskantar harabar masallacin.

Lunshe idanun yayi kana ya buɗesu, ganin sun shiga wannan gidan, wanda bisa dukkan alamun nanne gidansu Adaya.

A wani matsakaicin Falo suka zauna,
Cikin hikima Abu Hashim ya gyara zama da bin mgnar da Taj ya rubuta mushi, ya kalli Dottijon tare da cewa.
“Toh Alhamdulillah yanzu dai naga gidan, zan koma nawa gidan kuma in shaidawa mahaifiyar yaron da shi kanshi yaron, dan a kimtsa inda zata zauna a kuma shirya mata, tarbar da ta dace.”
Cikin jin daɗi Dottijon yace.
“Kai Alhamdulillah naji daɗin jin haka kuwa, amman yaushe za'azo ɗaukarta”.
Cikin sauri yace.
“In sha Allah nan kusa, mijinta da kanshi zai zo ya ɗauke, tunda naga gida ai komai yazo da sauƙi”.
Cikin gamsuwa dottijon da sauran duk suke gyaɗa kai domin haka nan, sukeji sun aminta dashi”.
Shi kuwa dottijon gyara zama yayi tare da cewa.
“Toh muna nan muna tsumayinku”.
Daga nan suka ɗan tattauna.
Daga bisani suka fito.
Taj dake zaune cikin motar tasu, yana mai ƙara tsare gidan su Adayan da idanun yana kallon lungu da saƙo na sashin wurin,

Rakiya sukayi wa Abu Hashim har gindin motar, wanda basu ga Taj a cikiba kasancewar glass ɗin motar tintek ce.

Ma'aruf ne da kanshi ya buɗe mushi marfin gaba, da sauri ya shiga tare da cewa.
“Toh sai kunjini”.
Fatan sauƙa lfy sukayi mushi.
Tare da raka motar tashi da idanun, har ya ɓacewa ganinsu kana suka koma cikin gida.

Taj kuwa har yanzu wayarsa, na maƙele a kafaɗarsa, domin bai katse kiransa da Ishmah ba.
“Uhmmmmm”. Ya sauƙe numfashi, jin tana cewa.
“Taj kayi mgna mana, Please kayi mgna menene matsalarka?”.
Cikin ƙarfin hali ya buɗa lips inshi a hankali, kana ya haɗesu tare da rumtse idanunsa murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ishmah! Meke faruwa dani ne? Wai me nayi ne? Me zan cewa Ummeyna, Ishmah Yah Abana bazai ɗauki wannan wargin bafa”.
Cikin ɗaurewar kai ita kanta take nazartar kalamansa.
Wanda kamata yayi suyi wannan tunanin kafin mai abkuwa ta abku, domin wannan ya zama tamkar hikaya, ko mafarki mara tushe cike da kullewan kai tace.
“In sha Allah, komai zai zo da sauki Malam zai fahumceka, Ummeey zata zame maka hasken da zai gamsar da malam, Please ka kwantar da hankalin ka kaji Bestie”.
Ta kiranshi da sunan da tasan, in ta gaya mishi yake rufeta da faɗa dan ya tsami sunan, ita kuwa so take yayi faɗan ko zaiji sassaucin damuwar da ta fahimci tayi silar shigarsa ciki, domin tafi kowa sanin zurfin cikinsa.
Shi kuwa Taj cikin rumtse idanunsa yace.
“Sai anji ma”.
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Ido ta zubawa wayar kamar ta samu, abin kallo a jiki.

Shi kuwa Taj murya a ɗimauce yace.
“Abu Hashim gida zamu wuce”.
Yayi mgnar da yaƙinin yasan zuwa yanzu Mahaifinsa da yayunsa maza, duk sun koma gida.

Cikin girmamawa Abu Hashim ya amsa mishi, kana ya ɗauki hanyar gida.

Cikin kulawa Abu Hashim yayi parking a farfarjiyar wani, ƙaton gida da yafi kama da fada,
Sai dai ba fadan bane, kawai tsarin gininne alfarmar wanda kallo ɗaya zakayiwa gidan ka gane cewa.
Babban gidane na babban mutum mai tarin zuriya, ƴaƴa da jikoki.

Da sauri Abu Hashim ɗin ya fito tare da buɗewa Taj marfin motar.
Cikin mutuwar jiki ya ziro ƙafarsa waje, ba tare da ya miƙe tsayeba, ya kamo hannun Abu Hashim, wanda hakan yasa ya sunkuyo, cikin sanyi murya yace.
“Afwan Abu Hashim, duk da nasan kai mutum ne mai amana da riƙe sirri. Amman zan kuma roƙonka da girman zatin Allah wannan al'amari ya zama sirri dagani sai kai, sai Allah, Please kada ka gayawa kowa, har sai na samu mafita”.
Cikin bayyana cikar amana da sirrantaka Abu Hashim yace.
“Nayi maka al'ƙwarin duk duniya babu maijin wannan mgnar a bakina, in sha Allah”.
Cikin gamsuwa ya miƙe tsaye, tare da nufar asalin cikin gidan.

Cike da girmamawa Mai aikata gidan duk suka nufo garesu.
Driver Malam ne ya amshi jakar dake hannun Abu Hashim tare da cewa Taj.
“Barka da isowa Abban Abba”.
Cikin ƙirƙiro murmushi dole ya kallesu tare da amsa gaisuwar da suke masa.

Tafiya mai ɗan tsawo sukayi kana suka, isa tsakiyar gidan,
Da gefen hagu da dama suke ɗauke da tsala-tsalan part guda bibbiyu komai nasu, iri ɗaya wanda 3-3 bedroom ne sai 2 Parlour, and dinning area, sai kitchen, kana da sito,

Sai kuma wani babban part da yake tsakiyarsu yana fuskantar alƙibla wanda shima 3 bedroom ne, sai kuma Parlour manya guda uku, sai ta bayan shi dake shimfi da wani ni'imtaccen gardin wanda yake ɗauke da nau'wukan itatuwan kala daban da ban, sai kuma wani ƙaton Parlour da yafi kama da holl wanda aka ƙawatashi da kayan ƙawa na alfarmar kuma shine falon forko.

Sai kuma can bakin gate da ɗauke da BQ babba 2 bedroom sai babban falo, sai kuma sashin ma'aikata.

Suna isa tsakiyar harabar cikin gidan wasu ƴan dugui-dugui ɗin yara suka fito daga part ɗin dake kusa dashi wanda, suke gab da bakin ƙofar sai, cikin tsananin jin daɗi babbar cikinsu da bazata gaza shekaru takwas ba, ta buɗe murya da iyakar ƙarfinta tare da faɗin.
“Oyoyo Uncle Afif”.
Ta ƙarashe kiran sunansa da masifar ƙarfi tare da nufarsa da gudu.

Cikin abinda bai gaza one minute ba, sai ga yara na fitowa ta ko wanne part a ƙalla sun kusan goma, gaba ɗaya sun ruɗa gidan da kiraye-karayen sunan.
“Oyoyo Uncle Afif.”

Cikin jin farin cikin ganin yaran ya ɗan rusuna ƙasa, tare da ware hannayensa.
Kamar tattabaru haka duk sukazo sukayi mushi zobe,
Yarane masu shiga rai da samar da farin ciki.

Murmushi Ummeey dake cikin kitchen dinta ita da babbar ƴarta Maryam.
Cikin tsananin jin daɗi tace.
“Alhamdulillah Babana ya iso”.
Cikin Murmushin Maryam tace.
“Bari in tafi nasan wurin Malam zai wuce.
Rashida ce wacce ita ke bin maryam ta shigo yayin da Halima ke biye da ita a baya, wacce ita Taj ke bi.
Cikin murmushi da bayyanenne jin daɗi tace.
“Ummeyy albishir.
Cikin murmushi tace.
“Naji ai yadda ƴaƴanku suka cika gidan da ihun Uncle Afif ya iso”.
Da sauri Zakeeya ƙanwar Taj mai binshi duk da tsakaninsu kusan shekaru goma ne, kana itace ƴar autar Ummeey, shigo kitchen ɗin fridge ta buɗe tare da ɗaukan Apple, Grapes, cherry, strawberry. ta ɗaurayesu tare da goran ruwa mai sanyi tana fita tace.
“Ummeey Uncle Afif fa ya iso”.
Da yake itama haka take kiranshi.
Kusan a tare ita dasu Rashida duk suka fito.

Shi kuwa Taj tuni ya ya shiga Parlour Malam tare da zugan ƴaƴan yayunshi da kuma ƙannensa.

Suna shiga Parlour, Malam ya saki wani irin murmushin dake bayyana tsananin so da ƙaunar da yake yiwa Taj ɗin.

Shi kuwa Taj cikin sauri ya dire wata yar kekkyawar baby da bazata gaza shara ɗaya ba, ɗiyar Yah Hafiz ce.

Yana ajiyeta, kuwa ta saki ihu, haka yasa yayi saurin ɗaukarta,
Tare da ruggume Yah Hafiz ɗin.
Wanda shine babban ƙab gidan nasu, sai Kuma Yah Sulaiman da Yah Yusuf suka ruggumeshi a tare.

Suna mai ɗan bubbuga kafa ɗarsa, tare da sumbatar gefen kuncinsa.
Shi kuwa murmushi dake bayyana irin tsananin yadda yake son ƴan uwan nasa yayi tare, da juyowa ya nufi Malam.

Hannun Mahaifin nasu ya buɗe mishi alamun yazo.
Da sassarfa ya ƙarasa gabanshi tare da durƙusawa bisa guiwowinshi.
Haka ya basu damar ruggume juna, hannunshi yasa ya tallabo fuskantar Taj da farin cikin ganinsu yasa ya fara mance kitimurmurar daya haɗawa kanshi.

Sassayan sumbata ya direwa Taj ɗin a tsakiyar goshinsa, kana ya daura hannunta tsakiyar kansa tare da cewa.
“Marhababuka Yah Abana Barka da isowa lfy Allah ya Ubangijin yayi maka albarka”.
Cikin tsananin jin daɗi ya ɗaura hannunsa bisa hannun mahaifin nasu tare da cewa.
“Amin ya Allah.
Yah Abana ya ƙafa?”.
Ya ƙare maganar yana kallon Yah Abduraham dake ta murmushi, sai kuma ya maida kallonsa kan Yah Aryan dake yiwa mahaifin nasu masaj.

Sai kuma ya juyo ya kalli Yah Aryan ɗin dake zaune gefe, yanayi mishi wani kallon dake cike da kishin irin tsananin son da mahaifinsu ke nunawa Taj ɗin.
Sai kuma ya kalli Kabber wanda shine yaro na miji ƙarami a gidan nasu baki ɗaya.
Shi kuwa Kabbir janye jikinsa ya ɗan tare da matsawa gefe.
Da sauri Malam ya rike hannunsa tare da cewa.
“A'a Kabir ina zaka je zauna nan kusa dani”.
Ya ƙare maganar dayi musu murmushi dake nuna sonsu a ranshi dan baya ƙaunar su zargi cewa, yafi son wani a cikinsu.
Hakan kuma yasa Kabir ɗin jin daɗi sai ya koma ya zauna a inda yake, shi kuwa Malam sai ya jawo hannun Taj ya ajiyeshi a gefen damansa.

Maganar zuci Aryan ya fara yi.
“Uhmmm ai dole dama shi Taj a gefen damanka zaka ajiyeshi, Kabir da shine ƙaramima kullum a gefen hagu kake ajiyeshi”.
Yayi kalam cike da kishi.

Shi kuwa Taj cike murmushi ya ɗago hannunsa tare da yafito yaran.
Ɗuuu haka duk sukazo gabansu suka zauna.
Mahira ɗiyar Yah Yusuf da kuma Iman ɗiyar Yah Hafiz ya ɗaura bisa cibiyoyinsa.
Sai kuma ya jawo Islam ɗan yayarsa Maryam gabanshi.

Yayinda saura kuma duk ya ajiyesu a ganshi.

Dai-dai lokacin kuma Zakiya ta shigo da sallama Rashida da Maryam na biye da ita a baya.
Rusunawa sukayi suka gaida mahaifin nasu da yayunsu. Kana Aryan da Kabeer suka gaida Rashida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login