Showing 9001 words to 12000 words out of 74955 words

Chapter 4 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

sawunta ya fara bi, da kallon dake da ɓoyeyyen manufar da yake tuhuma da neman dalilin daya watsa mishi nitsuwarshi a darare biyu da suka shuɗe.

Ita kuwa Aysha bisa takunta mai cike da nutsuwa take tafiya.

Ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kantaba ya amsa gairsuwar da Maryam keyi mishi, kana ya gaida Garkuwa.
Dai-dai lokacin kuma Aysha ta iso gabansa. Nannauyan ajiyan zuciya ya ɓoye cikin ƙahon zuciyarsa tare da sauƙeshi a hankali, kana ya fara ware idanunsa tare da yin sama dasu, har zuwa kan 0 face ɗinta da ya fito ras cikin tarhan da tayi.
A hankali ya lumshe idanunsa kana ya buɗe su a hankali jin, tana ce mishi.
“Sunana Aysha Abdullahi Matawalle”.
Kai ya jinjina tare da maimaita sunan a ranshi a fili kuwa a hankali yace.
“Afif Muhammad Taj”. Sai kuma ya ɗan kalli gefen hagunshi da wannan ma'akacin yake, tsuke fuska yayi cike da wani irin ɓoyeyyen yanayi yayi mishi nuni da ya wuce gaba yana zuwa.
Da sauri Balaraben ya ɗan rusunar da kanshi kana ya ɗan raɓa gefen Aysha ya ɗan yi gaba kaɗan.
Garkuwa da Maryam jallabiyoyi suka fara ɗan tsitstsinta ba tare da sun matsa daga wurin ba.

A hankali murya can ƙasan maƙoshinsa tamkar mai raɗa yace.
“Yah jiki basu sake tashi ba ko?”.
Ido ta ɗan jujjuya tare da cewa.
“Nifa lafiyata Lau, kawai tsoro naji”.
Ɗan ware idanunsa yayi alamar kin tabbatar?
Da sauri tace.
“Wallahi kuwa ni fa banda aljanu”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da zira hannun sa, cikin aljuhun jallabiyar tasa.
Ita kuwa a hankali ta fara taku tare da ƙara matso inda yake, wayarsa ta miƙa kishi tare da cewa.
“Ga wayarka, bani tawa!”.
Hannunshi na dama yasa ya amshi wayar tare da zurawa a aljihunsa na dama.
Har lau kuma idanunsa na kan fuskarta,
Sai kuma ya ɗan matsa saboda wasu matasan India da suka zo wucewa ta gefensu.
Sai kuma aka fara kallon kallo, domin su matasan sun shagala da kallon Aysha musamman yadda take ta moi-moi da bakinta tana mgna ƙasa-ƙasa da fillanci.
“Haka kawai dan na tsorata a jirgi, sai ka liƙamin aljanu to ni dai Allah ya sani bani da aljanu, masu shima Allah ya rabasu dashi, ni kuma Allah ya ƙareni da wannan fatan naka”.
Sai kuma ta juya ta kalli gefentan saboda ganin yadda ya tsuke fuska yayi kici-kici, ganin samarin nanne na gefentan dake kallonta yakeyiwa wani irin hantarerren kallon da dole yasa suka wuce.
Sai kuma tayi saurin yin baya kaɗan ganin yana raɓawa gefentan zai wuce sanda yazo dai-dai da itane kuma a hankali yace.
“Ni ba fata nake mikiba”.
Ya bata amsar da fillancin Ethiopia wanda ta ɗan fahimci abinda ya faɗa, sai dai kuma ta cika da mamakin jin yana fillancin.
Shi kuwa a hankali ya tsaya
Dai-dai wurin Cart ɗin kayanshi da Balaraben nan ke tsaye, hannunshi ya sanya a ciki ya ɗauko ƴan wasu abubuwa baƙaƙe masu taushi,
Gabanta ya dawo ya ɗan tsaya, saboda ta juyo ganin kamar zai tafi kuma bai bata wayartaba.
Ɗaya daga cikin abubuwan daya ɗaukon ya miƙa mata tare da cewa.
“Kisa wannan, ki kuma kiyaye hukunci sheriya ki daina fita haka”.
Cikin rashin fahimta tasa hannun ta amshi ɗaya, ga mamakinta Niƙab ne, ganin hakane yasa ta fahimci manufarsa.

Wareshi tayi tare da kaishi kan fuskarta, kana tasa hannun ta ta baya ta ɗaurashi.
Shi kuwa hannunsa ya harɗe a ƙirji tare da jingina da jikin kantar yayi irin tsayuwar nan ta gefe ɗaya, ya zura mata idanunsu.
Kasancewar bata iya ɗaurawa ba yasa ya ɗan karkace, hakanne yasashi, ɗagowa daga jinginar da yayi tare da matsota kana yasa hannun dai-dai saman hancinta, ƴan tsunsa biyu yasa ya ɗan kamo ɗan saman niƙab ɗin, bai bari ko farcensa ya taba fatartaba.
Dai-dai lokacin kuma Maryam da Garkuwa suka juyo kansu a tare.
Cikin nazartar yanayin Garkuwa ta zuba musu ido tana nazartan su.
Maryam kuwa cikin sauri tace.
“Aunty Aysha Yah Barrister nefa, ya kira wai in baki, waya zai tambayeki wacce iriyar waya kikeso ya saya Miki.
Toh Amman nace, mishi ai mun gane wacce ta ɓatanma, gashi har munzo amsarta”.
Ta ƙarashe mgnar tana kallon Taj da yake miƙa wa Aysha sauran niƙab ɗin.
Sai kuma ya kauda kanshi gefe ganin, kallon da Maryam ɗin keyi masa.

Ita kuwa Aysha numfashi ta fesar tare da cewa.
“Nifa abunan ɗauke min numfashi yakeyi”.
Yana mai miƙo mata wayarta yace.
“Idan kin saba zaki daina ji”.
kai ta gyaɗa mishi tare da amsar wayar.
Sai kuma ya juyo da sauri jin muryar Addawa na cewa.
“Tajuddeen!”.
Sai kuma ta zuba mishi ido dake nuna mgnar zuci da takeyi.
Ikon Allah Tajuddeen yau kuma, kaine a gaban mace, har kana gyara mata niƙab.
A zahiri kuwa sai cewa tayi.
“Wannan ƴar wacce ƙasace? Kuma me sunanki?”.
Cikin Murmushin Aysha tace.
“Suna Aysha Nigeria ce ƙasata”.
Kai ta jinjina tare da amsa gaisuwar su Maryam.
Shi kuwa Taj ido ya ɗan tsurawa Aysha jin tana cewa.
“Dan Allah ya akayi kake iya buɗe wayata”.

Kanshi ya ɗan kauda daga kallon ƙwayar idanunta kana yace.
“Da fingerprints nake buɗeshi”.
Fuska cike da mamaki tace.
“Toh ya za'ayi finger ɗinka ta iya buɗe wayar tunda dai da iya finger ɗina kawai na sai tashi”.
Cike da kamala da kwarjini da sanyinsa na nutsuwa yace.
“Toh nima ban san ya akayi hakaba”.
Da sauri ta jujjuya wayar tata, tare da matsa gefe, haskenta ya ɗauke, ta kuma shiga key, miƙa kishi tayi tare da cewa.
“Dan Allah sa mu gani.”
Kai ya ɗan juya tare da danna kan babbar yatsarsa.
Ga mamakinta sai gashi ya buɗu.
Da sauri tace.
“Ikon Allah ya buɗufa”.
Sai kuma tayi sauri ta shiga Settings, ta sake dubawa da kyau yatsa ɗaya ce, sake canza yatsar tayi tasa ta hagu, kana ta miƙa mishi tare da cewa.
“Please sa mu gani dan Allah”.
Manna yatsar yayi amman sai bai buɗuba.
da sauri ta kalleshi lokacin da taga yasa yatsarsa ta hagu saiga waya kam ta buɗu.
“Ikon Allah kenan zanen yatsunku iri ɗaya ne?”.
Cewar Garkuwa.
Maryam kuwa da sauri tace.
“Haka dai na fahimta, Amman abinda bada mamaki kam.
Kanshi ya ɗan jinjina tare da miƙa mata wayar sabodo Addawa datasa hannun ta kamo hannunsa tana tafiya.
Ba musu ya bita saboda ganin ma'aikatan wurin nata firfita dan lokaci salla ya ƙarato.
Sauri-sauri gudu-gudu suka zo wurin biya.

Koda aka haɗa lissafi Garkuwa na saurin kiran Yah Usman.
Ɗaya daga cikin ma'aikatan yace musu.
Taj ya biya musu ai.
Ya ƙare fadar hakan da miƙawa Aysha wata jaka mai kyau, tare da ce mata Taj ne yace a bata.
Ikon Allah gashi tuni shi ya fita, basuma sameshi a wurinba, bare suyi mishi godiya.

Suna cikin haka Yah Usman ya iso, da mota da driver nan suka kwashi duk kayan da suka saya.

Da gudu-gudu suka shiga gida ruwa suka ɗan watsa tare da yin al'wala hakama Yah Usman da driver.
Daga nan kuma suka taho harami ya Usman na bin Aysha da kallon da yasa ƙanwarsa fahimtar ya ƙyasa ne.

Alhamdulillah anyi arfa lfy, aikin mahajjatan ya cika, sai waɗanda suka fara sauƙa Makka ne suke da sauran ziyara Madina birnin ma'aiki. (S.A.W) haka dai akayi ta gudanar da aikin wanda zuwa yanzu har mahajjatan ko wacce ƙasa da suka fara zuwa sun fara komawa.

Alhamdulillah su Aysha ma duk sun gama ziyar bankwana.
A hankali suke fitowa cikin Rauda, cike da bege da son Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
Da jin ƙunar barin inda yake kwance shi da sahabbansa.

A hankali Aysha ke sharche hawayenta da fingers ɗinta, da suka sha jan lalle, dan yau zasu koma Makka, kuma jibi laraba jirginsu zai tashi in sun koma Laraba kuma, al'hamis jumma'a za'a ɗaura aurenta da Barrister Kamal Mubi yayan Maryam kenan.
Haka nan take jin tsananin so da ƙaunar Madina, duk da wani sashi na zuciyarta na cike da kewar ƙasarta Nigeria.

Ji take kamar ta ɓuya, katta koma Nigeria.

Jiki a mace suka fito, kamar ko yaushe, da sauri, ta tsaya jin Garkuwa na gaisawa da muryar Taj.
Ido ya zuba mata cike da tarin tambayoyi ganin tana zubda hawaye, ganin kamar bazata yi mgna bane yasa yace.
“Lfy kuwa ko dai jikin ne?”.
Cikin sanyi murya na rawa alamun kuka na iya kwabce mata tace.
“Ji nakeyi bana son inyi nesa da Rauda, ji nakeyi Madina tafi min ko wanne wurin daɗi a duniya”.
Sai kuma tayi shiru saboda sassayan kukan daya kwabce mata.
Zuwa yanzu ya fahimci cewa.
Ita macece mai rauni, da saurin kuka, ga kuma shagwaɓa da gwaurayen sakalci-sakalci.
Garkuwa kuwa, tuni itama idonta ke zubda hawaye, shi kuwa Taj a hankali ya kalli.
Side ɗin da su Ummeynshi suke bisa alamu Zam-zam suke sha.
Cikin sanyi yace.
“Ayyah toh kuyi addu'a Allah ya lamunce Miki duk shekara ki samu zuwa mana”.
Da sauri tace.
“Inayi kuma, in sha Allah zan ƙara gobe ma a ɗawafin ban kwana.”
Kiran da Ummeynshi tayi mushine yasa ya sallamesu, ya nufi inda su Ummeyn suke su kuma suka tafi suka shiga motocin su, zuwa makka.


Da daddere bayan sunyi wanka sun ɗan huta gajiyar hanya daga Madina zuwa Makka, ne suka ɗan fita shopping Malls dake kusa dasu, suka ɗan tsitstsinto ƴan ƙananan abubuwan da ba'a rasaba.

Bayan sun dawo sun gama harharda kayansu, Yah Usman yazo ya kwashi, dan za'a sasu a tawaga ta musamman ne dan jirginsu gobe da Magrib zai tashi.

Nan suka zauna suna ɗan hira.
wayar da Maryam keyi da Ruƙayya matar Barrister Kamal ne yasa duk sukayi shiru, saboda suna ɗan iya juyo me take cewa cike da tsananin fusata da ƙunan rai da makantar zuciya da kishi yake dirar wanda ke maida wasu mata tamkar zautattu tace.
“Dan.....!


By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/3, 5:15 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 3*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Littafin INDA RAI na kiɗine, yanzu free pages ne mukeyi, ki biya kafin a gama, 1k ne kacal zaki turo ta 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Gareku mutan Niger 1000fc zaku biya wato jaka ɗaya kacal kenan ga number da zakuyiwa magana ku biya ta wurin Mommy +22790899076*


Yauwa matan alkhairi ku matso kuji, wani sabon haɗi na musamman mai huce mana haushinmu, ya magance mana matsalarmu. Mata da yawa na koka min matsalar Basir da sanyi ya kashe musu mazanjensu, har basu iya bya msu bƙtrsu bare aje ga gamsar dasu a tarayya, wasu kan ce abin ya ƙanƙance.
To kuzo da kekkyawan yaƙinin Ubangijin ya sauƙar da maganin wannan ciwon tun kafin ya sauƙi cutar.
Inada haɗin na musamman na mazane ras. Hajia matsalarki tazo ƙarshe da izinin Ubangiji in kina buƙatar ƙarin bayini, kin kuma tabbatar zaki saya ne to kiyi min PC haɗin Rabin set 5k set ɗin kuma 10k akwai kuma mgni infection sadidinan shima haɗin rabi 5k set 10k..

“Dangin miji dangin shaiɗan, su Maryam manyan munafukai dangin shaidan, ashe da karuwar Yayan naki, kuka taho Makkan ban saniba?, da yake ke makirace, munafuka, baki gaya min cewa da karuwar shi ya biya manaba, ke kan ki kin sani wallahi da nasan da wata macce karuwa a cikin jerin waɗanda ya biya wa hajjin bana, wlh da bazan zoba, domin itace baƙuwar zuwa Makka, ki gaya mata cewa, ni wannan karon zuwa na bakwai kenan ina zuwa da mijina.
Dan haka tun wuri kice mata ta nemi nata mijin Barrister mijin Ruƙayya ce ita ɗaya, domin Ruƙayya aka halicci Barrister ita kaɗai saboda haka ki faɗa wa wannan Karuwar banza karuwar wofi Ni Ruƙayya nafi ƙarfin haɗa miji da ita”.
Ta dasa ayar mgnar cikin tsananin zafin kishin da kansa wasu mahauka tan mata iya yin komai a kan mazansu.
Ita kam Aysha rumtse idanunta tayi, tare da sunkuyar da kanta ƙasa zuciyarta na wani irin suya...

Garkuwa kuwa cikin mamaki take sauraren kalamanta da taci gaba da faɗa tana mamakin tsananin kishin jahilcin hauka da wasu mata keyi.
Sai kuma Maryam tayi sauri katseta ta hanyar cewa.
“Aunty Ruƙayya, inafa mutuntaki,Ina ganin kimarki so dan haka ki daina kirana munafuka, yadda kike matar yayana, shine ya haɗamu dangantaka, itama yayan nawa ne zai haɗamu dangantaka, kuma Aysha ba karuwa bace, ina mai kyautata nats zaton har a wurin Allah ta fiki kima, tunda ta fiki tsoronshi da bin dokokinshi domin da itace a matsayikin ba zata wulaƙantaki ba”.
Wohoho ina wuta Ruƙayya ta Abka,Maryam cikin Tsananin hargowa da hayagaga tace.
“Ke ƙaramar alhaƙi, ke akayan miya mecece na rantse da Allah zaki gane kin zageni, nayi miki alƙawarin sai na farraƙa tsakaninki da Yayan naki.
Cikin matsanancin bugun zuciya Aysha ta runtse idanunta hawaye Masu masifar ɗumi na tsatstsafo mata.
Ruƙayya kuwa cikin hargowa tamkar zata fasa Speaker wayar ta cigaba da faɗin.
“Ita kuma wannan Mara aikinyi ki faɗa mata in dai Barrister take jira tayi aure, to in sha Allah a bazawararta zata mutu. Mijina nan gani nan bari awar mayya ga yaji ga albasa Amman ba daman ci, in kuma ta kuskura tayi taurin kan shigowa gidan mijina, duk abinda ya sameta tayi kuka da kanta.”
Cikin mamaki Garkuwa ke cigaba da sauraron ɗaɗɗatan maganar dake fitowa daga bakin Ruƙayya tabbas wasu matan haukar kishi na shirin zautar dasu...
Aysha kam tuni hawayen da take ƙoƙarin riƙe wa suka fara silalomata.
Wannan dalilin nefa, yasa take tsoron aure, Shiyasa tunda suka zo makka sau uku ta yarda suka haɗu da Barrister, tunda tasan yazo da matarsa, kuma bata son ta shiga haƙƙinta, shike nan ita kuma ƙaddararta kenan?.

Da sauri Garkuwa ta zare wayar a kunnen Maryam tare da katse kiran kana tace.
“Yin mgna a cikin fushi kuskurene,domin duk sanda mutum yayi fushi bashi ke magana ba shaiɗan ne keyi ki bari sai kin huce, kuma ai bada kema ya kamata, tayi wannan haushinba, mijinta zata tara tayi idan tana tunanin tana da ikon hanashi Aure.”

Haka dai tayi ta tausar Maryam da Aysha da tai Murmushin mai haɗe da hawaye kana tace.
“Idan har aurena da Barrister alkhairi ne to ya Allah ka tabbatar in kuma ba alkhairi bane, Yah hayyu ya ƙayyum bi rahamatika astagis, ya fito min da wani mafi alkhairi a gareni”.
Da Amin suka amsa baki ɗayan su.
Daga nan suka kwanta kowa da tunanin da yake aransa.
Barrister kuwa baima san abinda matarsa tayi ba bare yayi yunƙurin ɗaukar mataki

Ƙarfe uku dai-dai suka tashi suka tafi Harami acan suka wayi gari har zuwa ƙarfe, goma lokacin da suke ɗawafin ban bakwana.


Duk da yanzu dubban ɗaruruwan mahajjata sun ragu amman hakan bai hana ka'aba cikaba.

Cike da kuzari da yaƙini Aysha keyin ɗawafin, tana mai nanawatawa mahaliccinmu buƙatunta.
Ɗawafin takeyi tana kuma kutsawa cikin dubban al'ummar tana kara kusanto ka'aba dan so take ta jita a jikin ka'aba.
Cikin yardar Allah kuma ta samu ta ƙutsa ta gefen hajarul Aswad.
Wani irin matsa taji taro jama'a sunyi mata har numfashinta na kwabcewa Amman hakan bai hanata kutsawa ba, zuwa yanzu ji take kamar sawunta baya taka ƙasa, tana makalene a tsakanin kafaɗun manyan matan Chaina mutane masu kama da aljanu dan ƙarfi.

Wani nannauyan ajiyan zuciya mai tafe da raunataccen kuka ta saki lokacin da taji ta jikin ka'aba.
Fuskar ta ta manna da jikin Ka'aba murya na rawa ta fara jero tarin addu'o'inta da buƙatunta cikin raunatacciyar Muryar da tasa makusantatan juyowa suna kallonta.
Wanda gefen damanta Ummeyn Tajj ne, gefen hagunta kuma Addawa ne sai Tajj ɗin dake tsakanin kafaɗarta data kakar tashi domin itace ta kutsa ta shiga tsakanin nasu, jin yadda ta kutsone yasa ya ɗan janye jikinshi duk da bai ga waye bane.
Jin sautin kukanta da muryarta ne yasa ya juyo ya kalleta cike da mamaki.

Ita kuwa Aysha cikin raunatacciyar murya da sassayan kuka take addu'o'in da yaruka uku Larabci, Hausa, fillancin. Kusan duk take haɗesu waje ɗaya.
”Yah Allah ka sauƙaƙamin ƙaddarata, ka juya min ita izuwa kekkyawa mai daɗi, Alhamdulillah Allah na gode maka ka bani rai da lfy, da damar zuwa wannan tsarkakekken wuri, Yah Allah kaine kace mu roƙeka.
Ya Allah ka tabbatar min da alkhairi tsakanina da wannan bawa naka Barrister Kamal, idan har aurena dashi alkhairi ne ya Allah ka tabbatar mana dashi, ka tausashi zuciyar matarsa, ka bamu zaman lfya, ka hanani samun damar cutar da ita, itama ka hanata samun damar cutar dani.
Yah Allah idan har ba alkhairi tsakanina da Barrister Allah ka sauya mana da abinda yafi alkhairi a garemu. Ka fito min da mijin aurena na alkhairi ka bayyana minshi akan alkhairi kasa mana dangana tsakanin zuƙatanmu ya Allah in dai Barrister ba alkhairi bane a gareni, ka alaƙanta wanda yake alkhairi a gareni ka kuma nuna min ranar aurena.
Ka kuma sa mana haƙuri nida Barrister.
Ya Allah kayi min kekkyawar rayuwa ka bani kekkyawar ƙarshe ka shafe zunubaina.
Ka haskaka duhun zunubaina da hasken gafararka. Yah Allah ka raya min yarana kayi musu al'barka, ka shirya minsu bisa tafarkin gsky.
Yah Allah ka bawa Mahaifiyata lfya mai ɗorewa.”
Sai kuma ta kakare saboda kukan da ya taso mata daga can ƙasan zuciyarta, wanda yake son fizge numfashinta ta, da kyar ta iya jawo numfashi kana taci gaba, da jero bukatar ta, na nan gidan duniya da ƙiyama.

Yayin da Ummey da Addawa da Yah Abana, duk suka zame daga wurin dan bawa wasu damar samun kusantar ka'aba, ita kuwa Aysha ji take yi tamkar wahayin buƙatunta akeyi mata Shiyasa suka ƙi ƙarewa.

Tajj kuwa, tsintar kansa yayi, da shiga lamurran addu'o'inta, more especially yadda take yawan, mai-maita Allah ya bawa mahaifiyarta Dadey ta lfya ya yaye mata cutan dake damun, kawai ji yayi yana mai kwaranyowa Dadeey addu'o'in samun, lfya tare da ambaton babban sunanta Fatima kamar yadda yaji Aysha nayi.
Sai kuma ya ɗaura da tayata, Addu'ar shirya ga ƴaƴanta, da take kira.
Mahmood, Minat, da Khalid.
Ya tsinci zuciyarsa da tayata, Addu'ar.
Kana ya ɗaura dayi mata addu'ar da ta buwayi kunuwansa da ita.
Samun miji na gari, da fatan in dai tsakaninta da Barrister ba alkhairi to Allah ya sauya mata.
A ƙarshe suka shagala da neman rabauta na duniya da ƙiyama, da neman tsari da azabar ƙabari, da wutar jahannama, suka cike gurbin du'anin da neman jannatul Firdausi.
Yayin da gaba ɗaya kwayar idanunsa ke kan ƴan yatsunta da Maryam ta watsa mata mashahurin lallen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login