Showing 39001 words to 42000 words out of 74955 words

Chapter 14 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

kan cinyarta ta ruggume tare da sakin kuka.

Hakan ne yasa Aunty Hauwa zubda hawayen domin tasan tarihin maraicin Laylah.
A tare suka fita ita da Hajja Umma.
Yayinda Adam dasu Khadijah ke biye dasu a baya.

Ya rage daga shi sai Ishmah da Laylah.

Shiru yayi ya rumtse idanunsa yana jin sautin kukanta na ratsa kunnuwansa da zuciyarsa, wani irin tsuma jikinsa keyi tamkar wanda zazzaɓi zai rufe da ƙarfi ya taune lip inshi na ƙasa domin jin yana gab da gaza yin control ɗin jikinsa da zuciyarsa dan ji yake zaifa jawota jikinsa.

A hankali ya buɗe idanunsa jin Laylah na cewa.
“Aunty Ishmah kiyi haƙuri, in sha Allah Dadeey na cikin dausayin aljanna, ki daina mata kuka, Uncle Taj yace min ba kyau nayiwa mamaci kuka, Aunty Ishmah kinga na dena yiwa Mimina da Abba na da Yah irfan kuka, dan Uncle Taj yace min wannan shine jarrabawata in bayi butulciba Allah ya bani ladan yarda da ƙaddara. Kema kada ki butulcewa kaddararki kiyi haƙuri ki daina kuka, ke gashi ma Abbanki yana raye gasu Mahmud ga kuma Uncle Taj yana sonki”.
Cikin zubda hawayen tare da kiciniyar danne shesh-sheƙan kukanta ta ɗan ɗago kanta tare da zira mishi rikitattun idanunta.
Sai kuma duk suka kalli Laylah jin ta kamo hannun Taj ɗin tare da jawoshi ta nufi fuskar Ishmah tana magana cikin rawan murya tace.
“Uncle Taj ka share mata hawayenta kace ta daina kuka, kace mata kana sonta ina sonta Addawa na sonta Bama son tayi kuka”.
Ta dire mgnar idonta na zubda hawayen kana murya na rawa.
Sassayan numfashi ya fesar tare da jingina bayan shi da kujera sai kuma ya ɗan janye hannunsa daga riƙon da Laylah tayi mishi sai kuma ya ɗan gyara zamansa a hankali ya ɗan sa babbar yatsarsa kan lips inta da take ta ciccijewa dan ta samu ta tsaida kukanta yatsarsa yasa kan lips in tare da ɗan janye su sai kuma yasa yatsar tsakanin haƙoranta.
Sai kuma duk suka kalli juna jin Laylah na cewa.
“Uncle Taj kace muna sonta kaima kana sonta ka ɗauke mana ita mu tafi da ita, Ummeey zatace tana sonta kuma kaima kana sonta ko”.
Kanshi ya ɗan jinjina mata.
murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Duk da ban san ya akeji ba in an rasa makusanta, Amman ina jin ciwo cikin zuciyata irin ciwon da ban taɓa jin irinsa ba, inajin zuciyata tayi min ƙunci irin ƙuncin da bazan iya kamantashi ba, kukanki yana sa inji tamkar raina ake zarewa, na hana Hajja Umma ta hanaki kuka ne saboda nasan zai rage Miki raɗaɗin zuciya.
Amman kukan yayi yawa yana azabtar da zuciyata Please dan Allah Ishmah kiyi haƙuri ki daina kuka, ki gafa Laylah yarinya ƙarama Allah yayi mata Jarrabawar data ninka taki ciwo, an kashe mata, Uwa, Uba, ɗan uwa, ƴar uwa, maƙotansu, kai duk dangintafa yanzu bata da kowa a duniya sai ni dake da nake son mu zame mata uwa da uba da ƴan uwanmu da nake so su zame mata ƴan uwa.
Kiji me take ce miki ke ai kinji daɗi ga Abbanki, kuma Uncle Taj yana sonku, ki buɗe ido ki ki kalleta fa. Just 11 years ne da ita.”
Cikin sanyi ta buɗe idanunta tare da fara sauƙe tagwayen ajiyan zuciya.
Dai-dai lokacin Hafsah ta shigo da tray a hannunta wanda ke ɗauke da plate ɗin fruits sai goran ruwa da kwalin Juice.
Bisa stoll ɗin dake gabansa ta ajiye trayn kana ta juya ta fita.

Gorar ruwan ya ɗauka tare da ɓalle marfin kana ya zuba mata a cup ɗin tare da miƙa mata.
“Amshi kisha”.
Cikin sakin wani nannauyan ajiyan zuciya ta tsuke lips inta tare da marairaitar da kwayar idanunta cikin sakin sassayan kuka murya cike da rauni da yake bayyana shogwaɓarta tace.
“Taj shike nan yanzu bani da uwa a duniya na zama marainiya ba uwa ba miji”.
Haka nan yake jin bazai iya janye idanunsa cikin nataba yadda tayi da fuskantar kai kace ƴar 8 yaers ce.
Ƙara miƙo mata cup ɗin yayi tare da lumshe rikitattun idanunsa murya a sarƙafe da tausayi da zazzafan yanayi a kanta cikin sanyi yace.
“Ishmah duk biyu Taj ɗinki zai cike miki gurminsu dan bazai bari ki zubda hawayen kiba, amshi ruwa kisha”.
Cikin sanyi ta amshi cup ɗin tare da tsaida idanunta da suka sauya launi saboda rashin bacci da kukan data tayi yanzu,
manyan idanunsa da tausayinta ya sauya musu launi ya lunshe matare da mata alam sha.

Cup ɗin ta kai bakinta, tare da zuƙan sassayan ruwa, idanutan ta lumshe lokacin da taji sanyin ruwan yana ratsa maƙoshinta tare da dira kan zuciyarta.
“Hhyyymmm”. Ta ajiye wani numfashin dai-dai lokacin kuma Hafsat ta shigo da wani tray ɗin, wanda ke ɗauke da ƴar madaidaiciyar kwarya mai masifar kyau, sai kuma ludeyin duba, da kuma wata ƴar roba, ajiyewa tayi gefen na forkon tare da cewa.
“Bismillah Yah Taj kasha ruwa, kafin in kawo ma abinci”.
Da sauri ya kalli trayn duka biyu, kana ya kalleta cikin mamaki yace.
“Wani abincin kuma, a'a karma ki kawo wani abu, wannan ma ai ya isa”.
Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
“A'a Yah Taj ai wannan duk ba abinci a ciki ɗan abubuwan shane kawai”.
Yana mai kallon Laylah dake ƙwaƙume da Ishmah yace.
“Eh ya isa, ki huta”.
Kai kawai Hafsat ta gyaɗa dan ta rabu dashi, tana fita ta wuce, part ɗin Yah Muhammad, kai tsaye kitchen ta wuce nan ta samu Aunty Nana sukaci gaba da aikinsu.

Ita kuwa Ishmah cikin sanyi murya a disashe harce raunace tace.
“Taj kasha ruwa!”.
Kai ya jujjuya mata, cikin sanyi hawaye na zuba tace.
“Meyasa zakace bazaka sha ruwan ba?”.
Fuskarta ya nuna tare da cewa.
“In dai har ina ganin hawayenki na kwaranya na gaza tsaidasu, to me amfanin zuwana, kuma ya zanyi in iya shan wani abu a bakina daya gaza tausar zuciyarki Ishmah”.
Ya ƙare maganar da iya gskyar zuciyarsa.

Da sauri ta fara sharce hawayenta da bayan hannunta tare da karkata tana ɗan gyara zamanta ta fuskanceshi da kyau tana mai ɗan ture Laylah kaɗan ta zauna a tsakiyarsu cikin muryar da tafi kama data sakalallu da yarinya tace.
“Ka gani na share hawaye na, kuma yi shiru, Please kasha ruwa”.
Idanunsa ya ɗan siranta tare da cewa.
“Ki fara ci!”.
Da sauri ta jawo, stoll ɗin gabanta, plate ɗin dake ɗauke da fruits ta ɗauka, tare da ɗan matsowa kana ta ajiye shi kan sawun Laylah dake miƙe a tsakiyarsu, fork ɗin ta ɗauka tare da miƙa mishi, shiru yayi yana lallonta ta tsakankanin gashin idonsa yayinda zuciyarsa da ruhinsa ke haƙaito mishi wani irin amintaccen alaƙa a tsakaninsu duk duniya banda Ummeey da Addawa ko yayunshi baya irin wannan kusanci dasu gwarama Aunty Rashida.

ɗaya fork ɗin ta sake ɗauka tare da ɗan sokashi saman water millo, sai kuma ta bawa Laylah tare da cewa.
“Hah Laylah buɗe baki”.

Ciki Laylah ta shafa tare da cewa.
“Alhamdulillah Aunty Khadijah ta bani Labal, da wani abu mai daɗi a ciki nasha cikina ya cika. Uncle Taj ne baici komaiba tunda muka taso”.
Ta ƙare maganar da alamun fura da nonon da tasha ya fara sakar mata kasalan bacci.

“Ki ƙara da fruits ɗin mana“.
Kai ta jujjuya tare da ɗan lumshe idanunta kana ta ɗan raɓa jikin Ishmah ta mannu da ita.

Ganin haka ne yasa ta ɗan tallabeta ta gefe, sai kuma ta tsaida idonta kan fuskar Taj ɗin tare da bashi fork ɗin kana ta kwaɓe fuska tare da cewa.
“Dan Allah kaci”.
Ta ƙare maganar hawaye na taruwar mata, ganin haka ne yasashi amsar fork ɗin.
Yanka uku yaci na kankanan, sai kuma ya ɗan soki Apple yaci kusan rabinsa kana ya ɗan ture plate ɗin tare da cewa.
“Alhamdulillah”.
Kai ta ɗan jinjina kana ta ɗan sunkuyo ta buɗe ƴar kwaryar nan, damemmen fura da nono ne, mai ɗan karen sanyi ya damu yayi luƙui.
Sai kuma ta buɗe ƴar robar nan, gogeggiyar kwakwace sai kuma ƴan yanka-yanka inabi.
Numfashi ta ɗan fesar tare da juyesu cikin nonon.
tare da ɗan sa ludeyin nan ta motsashi ya haɗe da juna.
Sai kuma ta daukeshi daga ƙasansa wanda fayfayne da zagayyen abin aje ƙoren, bisa cinyarta ta ɗaurashi tare da matsoshi sosai, tana ajiye ludeyin ta gabansa tace.
“Bismillah.”
Rau-rau tayi da ido alamun zatayi kuka ganin ya kafeta da ido yaƙi cewa komai.
Ganin yadda tayin ne ya sashi ɗaukar ludeyen tare da ɗan ɗiba.
Sai kuma ya kaishi bakinta yana faɗin.
“Ce Bismillah”.
Rau-rau tayi da idonta tare da cewa.
“Bana jin yunwa”.
Ta ida mgnar hawayenta na silalowa.
Lumshe idanunsa yayi kana ya buɗesu tare da tsareta dasu yana mai ƙara yarda da zuciyarsa cewa halittartace shagwaɓarta dake kashe mushi zuciya da sashi cin ruwan ƙanshi na ƙafwa cikin sanyi tamkar raɗa yace.
“In baki shaba bazan shaba”.
Ya ida mgnar yana manna mata ludayin bisa lips inta.
Tare da mata alamun sha.
Cikin jin bata sha'awar cin komai na duniya ta ɗan buɗe bakin, a hankali ya juye mata furar a baki kana ya ɗan janye ludayin.
ita kuwa Ishmah hankali ta maida lips inta ta rufe ba tare da ta haɗiye samunba.
Da sauri ta ɗan fiddo idanunta ganin ya ronƙofo ya matso da kanshi saitin fuskantar.
Wani irin tsuma jikinta ya fara na kusancinsu.

Shi kuwa Taj a hankali ya haɗe laɓɓansa ya ɗan hura mata iskar bakinsa kan fuskar wanda yasata jan numfashi da yafi kama da ajiyar zuciya kuma dole ta haɗiye damun furar.

A tare suka sauƙe numfashi kana yasa hannun da niya ɗibo wani sai kuma yayi saurin ɗago kanshi jin ta cewa.
“Dan Allah ka sha, ai na sha kuma wlh bana jin yunwa”.
Ta ƙare maganar tare da amsar ludeyen ta ɗebo ta miƙa mishi.
Amsar ludeyen yayi tare da yin Bismillah.
Wani irin sassayan numfashi ya fesar haɗi da lunshe idanunsa lokacin da yakai samun bakinsa yaji ɗan-ɗanon nonon gami da garɗin fura, kana ga garɗin kwakwa da inabi, ga zakin zuma a madadin sugar.
Tongue ɗinsa ya ɗan zaro tare da ɗan lasar gefen lip inshi na sama da nonon ya ɗan taɓa.

Ido ta ɗan zubawa sajenshi dake zuba ƙelli da sheƙi.

Shi kuma Taj cikin jin daɗi damun, yaci gaba da shan.
Sosai ya sha kusan rabinsa, kana a hankali yasa hannunsa ya ɗauki fefeyin da aka rufe dashi, tare da rufewa tare da cewa.
“Alhamdulillah Ishmah yanzu dai na ƙoshi, ki ajiye minshi a fridge gobe zan sha”.
Tana mai ɗan tallabo Laylah sosai a jikinta tace.
“Yayi ma daɗi”.
Kai ya ɗan jinjina mata tare da miƙewa tsaye jin an kira sallan la'asar.

“Zaka tafi masallaci ko?”.
Yana mai gyara tsayuwarsa yace.
“Eh ki tada Laylah ma kuyi salla”.

Tana mai gyarawa Laylah kwanciya tace.
“Toh”.
Sai kuma tabi bayan shi suka fito.
“Ishmah kin fito”.
Hajja Umma dake zaune da Khadijah tace.
Cikin sanyi murya tace.
“Eh”.
Da sauri duk suka juyo suna kallonta dai-dai lokacin kuma Abba da Barrister Kamal, da Dr Nafi'u, suka shigo Mukhtar na baya.
“Wa alaikissalam”. ta amsa
Cikin jin daɗi Abba da Yayunta suka haɗa baki wurin cewa.
“Ikon Allah Aisha baki ya buɗu”.
Suka ƙare maganar suna shigowa tare da yiwa sauran iso.
Ido ta zubawa Mukhtar Bappa Kawu kenan kamar yadda ƴaƴan yayunsa da ƙannensa ke kiransa.
Shima ido yan zuba mata cikin so da tausayin maraicin daya cimmata a gida batayi aureba.
“Bappa Kawu kazone”.
Kai ya ɗan sunkuyar domin tunda batun soyayyarsu ta watse ta koma kiransa da Bappa Kawu.
Sai kuma ta kalli Barrister Kamal dake cewa.
“Hajia ta, ya ƙarin haƙurinmu?”.
Kai ta ɗan sunkuyar hawaye na silalomata tace.
“Alhamdulillah Barrister haƙuri ya zama dole”.
Dr Nafi'u kuwa gefentan ya matso sosai tare da cewa.
“My wife ya jikin da sauƙi ko”.
Kai ta gyaɗa mishi alamun eh saboda yadda ya matsota har kamar zai manne kafaɗarsa da tata.

Barrister Kamal kuwa Taj ya kalla cikin sonshi yace.
“Kaji manyan likitocin zuciya da ƙwaƙwalwa ita da akace sai bayan kwana 20 zatayi mgana sai gashi in 20 minute ka sa bakinta buɗewa.
Anya kuwa Sheykh ba wani sirri tsakaninku”.
Kusan duk Murmushi sukeyi tare da kallon Taj ɗin da ya ɗan kalli Ishmah tare da cewa.
“Ba wani sirri Barrister haɗin Allah ne”.
Dr Nafi'u kuwa tauke fuska yayi yana dannawa Taj ɗin harara.
Ita kuwa Ishmah Taj ɗin take kallo yadda yake kauda kai baya ma son kallon Dr Nafi'u.
Sai kuma ta kalli Mukhtar dake cewa.
“Boɗɗi am, ya mukaji da hakuri?”.
Ya ƙare maganar hawaye na tsatstsapo mishi, domin sosai ya saba da Dadeey ya kuma san taso alaƙarshi da ɗiyarta, yana kiranta da Boɗɗi ne kamar yadda Dadeey ke kiranta.
A hankali ta ɗan sa hannunta share hawayenta tare da zama kusa da Hajja Umma, murya na rawa tace.
“Haƙuri ya zama dole Bappa Kawu, Dadeey na ta tafi”.
Sai kuma ta fara shesh-sheƙan kuka, cikin sanyi murya mai cike da tausasawa da kuma kulawaTaj yace.
“Ishmah kiyi haƙuri, mu bar yiwa Dadeey kuka muyi mata addu'a ko, bana son kukan nan ya isa haka”.
Ya ƙare maganar yana zama gefen Barrister Kamal.
Ita kuwa Ishmah ta ƙasan ido take kallon Barrister Kamal, Dr Nafi'u, Mukhtar, in manema ne dai da masoya Allah bai hanataba, auren nedai Allah bai sauƙo da shiba.
Shi kuwa Taj ɗan gyaran murya yayi tare da fara jawo addu'o'in newa mamaci gafara da yafiyar Allah da kuma rahamarka.
اللَّهُمَّ اغْفِرْ لَهُ وَارْحَمْهُ، وَعَافِهِ، وَاعْفُ عَنْهُ، وَأَكْرِمْ نُزُلَهُ، وَوَسِّعْ مُدْخَلَهُ، وَاغْسِلْهُ بِالْمَاءِ وَالثَّلْجِ وَالْبَرَدْ، وَنَقِّهِ مِنَ الْخَطَايَا كَما نَقَّيْتَ الثَّوْبُ الأَبْيَضَ مِنَ الدَّنَسِ، وَأَبْدِلْهُ دَاراً خَيْراً مِنْ دَارِهِ، وَأَهْلاً خَيْراً مِنْ أَهْلِهِ، وَزَوْجاً خَيْراً مِنْ زَوْجِهِ، وَأَدْخِلْهُ الْجَنَّةَ، وَأَعِذْهُ مِنْ
عَذَابِ الْقَبْرِ وَعَذَابِ النَّارِ
Kusan a tare duk suka lumshe idanunsu harda shi kanshi Dr Nafi'u.
Domin yadda yake jan sautin addu'ar da yadda muryarsa ke fitane yasa su jin tsikar jikinsu na tashi.
Kusan a tare a tare suke amsawa da Amin-Amin.

Bayan su shafane kuma, suka miƙa dan fita, har sunje bakin ƙofar Mukhtar yace.
“Baddi ni zan wuce in munyi salla, sai munyi waya”.
Cikin sanyi tace.
“Ngd ƙwarai Bappa Kawu ka gaida mutan Gombe, Allah ya maida ka lfy ka gaida min Sadik da Aliya”.
Cikin jin daɗi yadda take son ƴaranshi yace.
“In sha Allah zasuji”.
Daga nan suka fita.

Bayan an idar da sallan la'asar ɗin ne Ishmah tacewa.
Khadijah da Hafsat suje su Gyara BQ.
“Ai tun ɗazu Rahman da Minat suka gyara shi komai fes kin san Rahman gwanar gyara ce”.
Cewar Khadijah, cikin gamsuwa tace.
“To muyi salla”...


Da daddare bayan anyi sallan Isha.
Kusan duk tare suke a Parlour Dadeey a nan kuma sukaci abincin daren.

Sai shi da Rahama ta kai mishi BQ ɗin.

Washe gari da safe misalin ƙarfe 10 dai-dai Ishmah ta fito daga cikin gidan ta nufi BQ ɗin tana riƙe da hannun Laylah.
Khalid da Minat na biye dasu a baya, riƙe womers.

Ahankali ta ɗaga hannunta na dama tayi Knowking kusan sekonni talatin taji shiru sake knowking tayi har sau biyu still taji shiru ɗan jimm tayi tare da ɗan fesar da sassayan numfashi kana ta sake knowking a karo na uku, still shiru taji alamar ba motsin mutum da zai buɗe ajiyar zuciya ta sauƙe kana ta ɗan murɗa Handle ɗin ƙofar lumshe idanunta tayi tare da ɗan buɗesu jin ƙofar a abuɗe take.
Turawa tayi ta kutsa kanta ciki, bakinta na ɗauke da sallama a nitse ta sanya ƙafarta na dama acikin Falon ahankali ta saki wani sanyayyan numfashi tare da shaƙan wani ni'imantaccen ƙamshi mai daɗin shaƙa haɗi da sanyin Ac mai sauƙar da nitsuwa daya wadataci cikin Falon.
Ahankali ta ƙara sa takawa cikin Falon yayin da sanyin ke ratsa mata Jiki da zuciya.

Minat, Khalid .ke biye da ita kai tsaye suka nufi dining area.
Iska mai sanyi ta fesar tare da tsayawa tsakiyar falon tana mai karewa ko ina kallon tsaf-tsaf gwanin ban sha'awa komai neat-neat a ranta tace kai Masha Allah Rahamah ba dai tsafta ba komai na falon ya gyaru sai ɗaukar ido da ƙyalli yake ga wani masifeffen ƙamshi dake tashi wasu irin kujeru ledar Set ne Neavy blue sai tangamemen TV da Tv starm da Woofer dake gefe tsakiyar falon kuwa wani Turkey Carpet na Neavy blue da ratsin fari yayin da cotton ɗin ma suka kasance Neavy blue da ratsin fari sosai falon yayi kyau na fitar hankali.

Cikin lumshe Idanu ta sauƙe ajiyar zuciya mai sanyi kana ta juya gefen dining,
idanunta suka sauƙa akan, Warmers, Flaks, Mug, da sauran abubuwan buƙata wanda bisa dukkan alamu ba'a ataɓa su bama.
Ɗan ware manyan Idanunta tayi kana aranta tace.
“Kenan beyi breakfast ba har yanzu?”.
Cikin yanayin nutsuwarta da kuma sanyi data sakeyi ta juya ta kalli ƙofar bedroom ɗin dake gefen dama kasancewar BQ ɗin 2bedroom ke ɗauke dashi shiru taji ɗakin alamar ba kowa, ɗan juyawa tayi tare da maida idanunta ɗakin gefen hagu nan ma taji alamar ba kowa sake juyawa tayi zuwa ɗakin gefen dama jin kamar ana magana ahankali ta zubawa ƙofar ido.

Cike da nutsuwa daya gama ratsa sassan jiki da tsoka da jini dake bin baki ɗaya ilahirin jikinsa saboda darajar Alqur'ani mai girma da yake kansa a hankali ya murɗa Handle ɗin ƙofar ya fito.
Cikin sanyi Ishmah ta ƙyafta Idanunta sau biyu kana ta tsai dashi akansa ganin sa sanye cikin riga da wando na kafta Milk color da aka watsa masa ɗinki irin na matasan zamani masu nutsuwa da arziƙi yayin da kansa ke sanye cikin hula coffee da rastin Milk kana ƙafafunsa na sanye cikin wasu takalma coffe da ratsin milk Bertozzi mai masifar taushi da ƙyalli wanda bazai gaza kaiwa 85k ba sai wani irin ni'imtaccen ƙanshin yake zubawa.

Ahankali ta sake ɗagowa tun daga kan rumfar ƙafarsa har zuwa kan kyakkyawar fuskarsa dake ɗauke da saje dake wani irin ƙyalli da sheƙi haka nan ta kasa ɗauke idanunta akansa.

Aɓangaren.Taj kuwa hankali shima ya zuba mata manyan Idanunsa Masu masifar haske da sheƙi kana suna ɗauke da zara-zaran eyelashes sanye take cikin riga da skirt na atamfa Golden Color da ratsin light blue da ratsin Orange atamfar ta zauna ɗass ajikinta haka zalika Skirt ɗin ma ya zauna ɗass kana gyalen da ta yane kanta zuwa kafadarta shima light blue ne yayin da jikinta ke fitar da sihirtaccen ƙamshin Humra da Kwallaccar da Garkuwa ta bata tayi masifar kyau duk da cewa ta ɗan rame kana ga idanunta da suka kumbura wanda bisa duk kan alamu tayi kuka sosai duba da yanda Idanunta sukayi luhu-luhu dasu cikin nutsuwa dake ratsa sassan jikinsa ya fara takowa ahankali batare daya janye idanunsa dake cikin nata ba haka zalika itama bata janye idanunta daga nasa ba.

Ahankali Minat ta juya ta kallesa bayan ta ajiye Warmers ɗin akan dining kana ta ratsa gefensa tace.
“Uncle Taj ina kwana”.
Cikin fesar da numfashi yace.
“Lafiya lau my Daughter ya gida”.
Ya amsa batare daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login