Showing 6001 words to 9000 words out of 74955 words

Chapter 3 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

amarya Budurwa ko Bazawarara duk ku taho kowa da zazzafan haɗinsa, ina araha kam duk ɗan karen tsadan da kayan suka ƙara Amman fa ina hana bashi. Idan kayan ɗa'a kikeso ga number da zakuyi min min da ita 08069423567.


*Littafin INDA RAI na kiɗine, yanzu munayin free pages ne, ki biya ki karanta cikin aminci, 1k ne kacal, 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki kuma ta wannan number 09097853276. Ku ma mutan Niger 1000fc ne zaku biya wato jaka ɗaya rak. Ta wurin Mommy zaku biya.+22790899076*


Kiran ne ya ƙara shigowa da sauri Maryam ta miƙa mata wayar.
Atake hoton fuskar wani kekkyawan dattijo fari ƙal dake zaune a tsakiyar zaratan maza manya da ƴan saffa-saffa wanda sun kai takwas zagaye dashi sai kuma Taj dake gabashin zaune ya ɗaura kanshi bisa guiwowin Dottijon,ya bayyana wanda aka rubuta. Yah Abana.
Bisa alamu duk mutanen Ethiopia ne, domin su kalar fatarsu da farinsu ke nunasu a duk inda suke a faɗin duniya wanda kalar ƴan Sudan na ɗan ɗibi da suɗin.

Kasake tayi har kiran ya tsinke.
Sai kuma ta kalli fuskar wayar ganin babu matakan tsarone yasa ta sauƙe numfashi tare da kutsa kai ta shiga.
Wurin Contacts ɗinsa sabida tabbatarwa, da sauri ta fara bin sunayen mutanen da yafi mata kama da sunayen larabawa da rubutun da yafi kama da na larabawa da akayi amfanin dashi wurin rubuta sunayen.
Cikin sauri tace.
“Tabbas ba wayata bace gashi komai ba nawa bane”.
Kai Maryam da Garkuwa suka jinjina tare da cewa bai lura bane ya dauƙi taki wayar ya bar Miki tashi.”
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“Ok bari in kira layin nawa in gaya mishi ya mana canjin waya”.
Ta ƙare maganar tana sa number ta.
Kana ta danna kiran.
Dai dai lokacin kuma Afif Taj yayi wani gajiyeyyen miƙa, tare da gyara kwanciyarsa bisa tattausan katifar gadonsa na masauƙinsa mai alfarma, wani irin mayataccen bacci mai gauraye da gajiya yakeji, ji yakeyi tamkar kanshi zai rabe gida biyu, so yake ya watsa ruwa ya sauƙa ƙasa ya tafi Harami, Amman ina bazai iya saboda tarin gajiyar dake tattare dashi.
Sassayan numfashi mai sanyi ya fesar tare da miƙa, hannunshi ya jawo ɗaya daga cikin woyoyinsa biyu daya aje akan bedside drower, ya sani Ummenshi bazata yi bacciba har sai taji ya isa Lfy.
Haka kuma Yah Abananshi sai yaji sauƙansa Lfy yake samun nutsuwa.
Yana mai ware idanunsa da bacci ya fara cin ƙarfinsu ya ɗan shafa fuskar wayar.

A kuma dai-dai lokacin Aysha ta kalli Garkuwa tare da cewa.
“Wayarfa switch off”.
Tana zama bakin gadon ta, tace.
“Toh ko ya kashe wayar ne”.
Numfashi ta ɗan fesar tare da lumshe idanunta kana tace.
“No dama nasa wayar a Airplane mode. Wata ƙil shi baima lura ba wayarsa bane”.
Sai kuma tayi saurin jiyowa ta kalli Maryam tare da cewa.
“Ni Allah ma ya rufan asiri yasa ba'a jirgin nabar wayata ba”.
Sai kuma tayi saurin kallon fuskar wayar jin tana ringing ga mamakinta layinta ne.

Shi kuwa Afif Taj, manna wayar yayi a kunnensa yana mgnar zuciya mai haɗe da nazari.
“Yah Salam na ɗauki wayar mai aljanun nan kenan na bar nawa a wurinta.
Ayyah Ummeei na tayi ta kira kenan bata sameni ba”.
Sai kuma yasa hannunsa ɗaya ya jawo ɗaya wayartashi.
Yess yasamu kiran iyayen nasa kuma, sai dai kasancewar wayar na silent kasancewar itace, wacce yake yawan amfani da ita, waccar ta wurin Aysha iya Family inshi kaɗai yake kira da ita, a Family inma mafi kusanci dashi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta amsa kiran, saboda jin Garkuwa na cewa.
“Ki amsa mana”.
A kunneta ta liƙa wayar, cikin sanyi murya tayi cikekken sallama.

Cikin son yakice nannauyan baccin dake danneshi ya amsa sallamar tare da cewa.
“Kina ina!?”.
Cikin sauƙe numfashi ta lumshe manyan Idanunta masu masifar haske da ƙyalli tare da faɗa mishi sunan masauƙinsu da room number insu, ta ɗaura da faɗin.
“Ka ɗauki wayata ka bar, min taka”.
Ta ƙare maganar cike da tsananin mamakin to ya akayi ya samu ya cire pin ɗin wayar tata har ya kirata, nazarin nata ya katsene jin yana cewa.
“Yah Abana, da Ummeei na sun kira ko?”.
Da sauri tace.
“Eh Yah Abana da Fist Love ne, suka kira Ummei bata kiraba”.
Ɗan gudun numfashi ya fesar kana yace.
“Ok kada ki amsa kiran kowa idan an sake kira.”
Da sauri tace.
“Ton ni kuma waye da waye suka Kirani!?”.
Cikin lumshe idanunsa yace.
“I don't know”.
Cikin fahimtar shi mutum ne mai taƙaitattun kalamai ta ɗan yamutsa fuska tare da cewa.
“Please idan Barrister ya kira kada ka ɗaga, in kuma Dadeey na ta kira ka ɗaga, ko Abba na kace musu munyi canji wayene.
Kuma kace musu ina lfy”.
Cikin ƙosawa da surutun nata yace.
“Bazan iyaba”.
Yana faɗin haka ya katse kiran, tare da cilla wayar gefe,
Kana ya kira Ummei shi da ɗaya wayar tasa.
Bugu ɗaya ana biyu ta amsa bisa dukkan alamu tana cikin haramine dan yaji sowan dubban jama'a, wacce tafi ta kullum saboda ƙaratowar ranar arfa yasa gaba ɗaya mahajjata sunata hallara cikin Makka.
“Afifff”.
Ta ƙira sunansa cikin mabayyaniyar so irin ta uwa da ɗanta.
Cike da gajiya kana da magagin baccin yace.
“Ummeey na mun sauƙa Lfy”.
Cikin jin daɗi tayi hamdala tare da cewa.
“Alhamdulillah tun ɗazu na kiraka baka ɗauka ba,
Malam ma ya kiraka duk bakayi picking calls inmu ba, kana lfy dai kam ko?”.

Tamkar yana gabanta ya gyaɗa kai kana ya ɗaura da cewa.
“Alhamdulillah Ummeey”.

“Zaka shigo Harami yanzu ne?”.
Cewar Ummeey.
Yana gyara kwanciyarsa yace.
“Sai asuba”. Kai ta gyaɗa tare, da miƙawa Malam Muhammad wayar, amsa yayi tare da kaiwa kunne cikin tattausan lafazi da irin soyayyar nan da bata ɓuya a kan fuska dottijon yayi sallama tare da ɗaurawa da cewa
“Abana”. Dan haka yake kiransa, kasan cewar sunan mahaifinsa garesa shi kuwa Afif yana juyawa gefen damanshi yace.
“Yah Abana”. Murmushin mai sauti dottijon yayi, kana suka gaisa tare dayi mishi sannu da gaji.

Jin yadda muryar ɗan nashi yayi ƙasa sosai alamun bacci ne, yasa ya sallameshi, daga nan sukaci gaba da ibadunsu.

Su Aysha kuwa bayan sunyi wanka sun ɗan ci abinci.
Suka sauƙo ƙasa kasan cewar masauƙinsu ba nisa da Harami.
Daga nan suka fara gabatar da aikinsu.

Shi kuwa pilot Afif Taj, lumshe idanunsa yayi tare da karanto addu'ar kwanciya bacci yayi, saboda yana da al'walansa. Yana gamawa ya shafe jikinsa kana ya kwanta tare da fuskantar alƙibla, yana mai tasbihi, cikin second nin da bazasu gaza 23 ba bacci yayi awon gaba da shi.


Gaba ɗaya Mahajjata, basu da wani tunanin ko, nutsuwa da ya wuce gabatar da aikinsu.

Alhamdulillah kuma komai na tafiya, bisa tsari na addini.
Yau kwanasu uku kenan, kuma jibine, arfa. Hankalin Majjata duk na can.

Aysha ce dake sanye cikin wani Maroon Abaya mai manyan flowers da yayi masifar yi mata kyau sai kuma Maryam dake ɗan tafiya cikin alamun, gajiya, suna ɗan sassarfan bin Garkuwa, domin, so suke su koma gida su samu su ɗan rumtsa, kasancewar a Harami suka kwana.

Cikin damuwa Aysha ta kalli Maryam tare da cewa.
“Mutumin nan fa, yauma na kira shi, bai ɗaukaba, nagaji da rashin wayata a hannuna, yau kwana ukufa kenan bai amsa kirana, ko su Dadeey na sai dai muyi waya dasu ta wayarki.”
Ta dire ayar mgnar dai-dai lokacin da suka shiga lifter da zai kai su masauƙinsu.

“Kada ki damu fa ai dole zai nemeki, dan na tabbatar wayarshi tafi taki mahimmanci, kuma Kinga tashi babbar takice, kawai collor insu ne ɗaya”.
Maryam ta faɗa mata cikin kula.
Kai ta jinjina tana ɗan lumshe Idanunta tace.
“Ni da katin nashi bai ƙareba ai ko a jikina bakiga da wayar tasa naketa kiran su Dadeey naba”.
Ɗan murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Okay Shiyasa tun jiya kika buwaye mu, ashe katine, ya ƙare, da shiru kikayi, kinata bin cike mai waya, da duba abubuwansa”.
Fuska ta ɗan ƙwaɓe wanda yasa ainihin kyawun fuskarta bayyana tare da cewa.
“Yoh shi mema a wayar tashi ba komai fa.
Ko pictures babu sai irin wanda in an kiranshi suke ɗan fitowa a fuskar wayar. Sai dai tarin Apps na Qura'an da hadisai da abubuwa su na pilot, da kuma Doctors”.
Kai Maryam ta jinjina kana tace.
“Gaskiya dai gwara ya ɗauka a samu a amshi wayar, Kinga cewa Yah Barrister mukayi wayarkin ta faɗine, kuma naji yana cewa zai saya Miki wata.”
Tayi mgnar cikin tausayawa ɗan uwanta.

Murmushin Aysha tayi tare da cewa.
“No nima bazan barshi ya sai min wata ba.”

Dai-dai lokacin kuma suka isa masauƙin.
Bayan sun shiga, ne suka nufi ɗakinsu.

Murmushin mai yelwa Barrister yayi tare da nufosu.
Cikin yanayin dake nuna yaƙinin soyayyarsa gareta, ya amshi goran Zam-zam ɗin dake hannunta.
“Baby kinyi mana addu'a ko?”.
Kai ta gyaɗa mishi tare da nuna mishi Maryam da Garkuwa, cikin mutumtaka suka gaisa kana su suka shiga ciki.
Shi kuma da ita a Corridor ɗin suka zauna bisa kujerun dake wurin.
suka ɗanyi hira kana ya miƙe suka shiga ciki.
Kuɗi ya basu baki ɗaya sun.
Kana ya fita ya tafi.

Yana fita suka ci abinci da suka shigo dashi kana, suka ɗan watsa ruwa, suka kwanta bacci.

A hankali yake kimtsa kanshi, cikin wani tattausar jallabiya fara ƙal, sai kuma hiramin daya saka sky blue daya yafa a saman kafaɗunsa, sai kuma yar tattausar hular fara mai ratsin sky blue ɗin ya murza a kanshi, turaren Hubban shadidan, ya feshe jikinsa, dashi, kana ya zira tattausan silifas, shima sky blue.
Bakin gadon ya zauna yana shafa fuskarshi da hannun dama, yana jin alamun tofowar sajen da baya barinshi ya bayyana a jikinsa, dan shi saje baya cikin, ababen da ya damu da bari, dan gani yake zai dameshi.
Numfashi ya fesar yana mai tunanin, yana gama aikin, Cheving face ɗin nashi zai fara yi.
Wayar Aysha dake kan pillow ya jawo, tare da ɗan taɓa ƙasan fuskantar wayar kaɗan da babbar yatsarsa,
Ido ya zuba wa fuskar wayar, cike da mamakin yadda yatsarsa kan buɗa wayar da ba tashi ba.

Kauda tunanin yayi tare da kiran wayarsa.
shiru yayi yanajin yadda wayar ke ringing Amman ba'a ɗaga ba har ya tsinke.
Sake kira yayi a karo na biyu, still ba'ayi piking call ɗin ba, har ya tsinke.

Ita kuwa Aysha cikin baccinta da yayi nisa, take jiyo ringing ɗin wayar, sai dai tana farkawa kiran na katsewa.

Ɗan tsuka ta ja, tare da gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci.

Shi kuwa Taj, time ya duba, ganin, ƙarfe takwas ne na safe, yasa ya miƙe tare da zira wayar a aljihunsa, dan Ummeynshi tace tana son su shiga Oriental Abaya House.
Dan tana son sayawa yar autarta Zakeeya, wata Abaya data fitineta da kira dominsa.

Wannan tunanin ne, yasashi miƙewa tare da fita.
Yana tafe yana mgnar zuci.
“Wannan ina ta shiga ina kira bata ɗagawa, kada kuma inje masauƙin nasu in samu bata nan,
bari dai in fita da wayar, in na dawo in fara zuwa wurinsu in amshi wayata, in bata tata adena takura min rayuwa da kiraye-karayen naci”.
Ya ida mgnar tare da shiga ɗakin da iyayensa suke,
Daga nan suka shiga ɗakin Addawa, wacce kakace a garesa mahaifiyar Ummeynshi.

Malam kuma dama tuni yana Harami.
Daga nan suka nufi inda zasujen


Ƙarfe goma dai-dai Aysha ta farka,
Ido ta zurawa gadon Garkuwa saboda ganin bata nan.
Zama tayi a bakin gadon tare da kallon ƙofar bathroom dan jin motsin ruwa, sai kuma ta kalli Kofar shigowa,
“Yauwa masha Allah, Aysha kin tashi, Please yi sauri mu fita, ga Uncle Ali, yazo mu fita tare dashi, zamufi zararshi”.
Cikin alamun bacci tace.
“Wayeshi ɗin”.
Tana mai kallon Maryam dake fitowa wanka tace.
“Uncle nane ƙanin mamana kuma shine Amirul Hajj namu”.
Da sauri Maryam tace.
“Kai haba tunda muka haɗu nake ta Miki kallon kamar nasan fuskarki, ashe fuskar shi nake tunawa, gsky kuna kama wlh”.
Kai ta jinjina tare da cewa.
“Eh haka dai ake cewa Amman ni ban yarda ya za'ayi mace tai kama dana miji”.
Ta ƙare maganar tana kamo hannun Aysha tana tsayar da ita tare daci gaba da cewa.
“Mu tafi. Yanafa jiranmu yace, shekaran jiyama yazo ya samu, kuna bacci baku gaisaba dan haka yau in tasoku”.
Cikin sanyi Aysha tace.
“Bari in ɗan watsa ruwa”.
Da sauri Garkuwa ta jujjuya mata kai tare da cewa.
“Please kifi, kada kice sai kinyi wanka, kafin muyi baccifa duk munyi wanka”.
Kai ta jinjina kana tace.
“Toh bari inyi al'wala”.

Bayan tayi al'wala ta fitone, ta kimtsa, cikin tattausar Abaya Black collor mai masifar sulɓi, tayi rolling kanta da ɗan kwalin, kana ta zura takalmin snicker nevy blue, tare da ɗaukar ƴar hand bag itama nevy blue wayarta ta zura a ciki kana, ta rataya a wuyanta, irin rata yawar nan ta kai duka.

A jere suka fito.
Cikin kulawa Uncle ya sakar musu murmushi tare da cewa.
“Yaran albarka ya ibada”.
Cikin jin daɗi sakin fuskansa suka amsa da.
“Alhamdulillah Uncle komai lfy Lau”.
Kai ya jinjina tare da yin gaba yana faɗin.
“Masha Allah”.
Suna sauƙa suka samu mota a tsaye driver na ciki bisa dukkan alamu su ake jira.

Gaba ya shiga ya zauna, yayinda su kuma suka zauna a baya.
Kana motar taja suka tafi.

Cikin kula yace.
“Aysha ya kewan gida”.
Kai Garkuwa ta ɗan jinjina tare da cewa.
“Gaskiya dai kam Uncle ina missing su yan uwa sun samu duk kusan ɗakinsi ɗaya suke ni kuma. Ni ɗaya, irin Maman Khairta kam ma tunda nazo bamu haɗuba. Gwara Mami, Maman Sayyid, da Aunty Nanee su mun haɗu.”
Sai kuma tayi shiru jin Maryam na cewa.
“Toh ba gamu ba, muna ɗebe miki kewarsu”.
Murmushi tayi jin Aysha na cewa.
“Kuma mu jinki muke kamar yar uwa”.
Da sauri tace.
“Wallahi nima haka nake jinku”.
Uncle Ali kam sai murmushi yayi.

Sha ɗaya da rabi dai-dai suka isa bakin.
Riyal Abaya shop.
A kuma dai-dai lokacin Aysha ta ɗan gyara zaman jakarta, tare da zaro wayar dan duba Time, sai kuma tayi arba da miss calls har biyu, da layinta, da sauri ta kira layin nata.
Kasake tayi tana jin yadda wayar keta ruri Amman ba'a dagaba, ƙara kira tayi a karo na uku tana mai sauraron Uncle Ali dake cewa Garkuwa.
“Yauwa shiga ku ɗauki duk abinda kukeso, in kun gama ki kirani ki gaya min, zan biya kuɗin kuma zan turo Usman yazo ya ɗauke ku da kayanku.
Ya ƙare maganar yana miƙa musu.
kuɗi, Dukansu uku kana ya haɗa da cewa.
“Wannan ku ajiye ne, Amman na sayayyar da zakuyi, in kun gama kawai kuyi min mgn”.
Cikin jin daɗi Maryam da Aysha sukayi ta godiya tare da yimishi addu'a.

Da sauri Aysha ta maida hankalinta kan wayar jin, an amsa kira na huɗu data sakeyi.
A takaice yace.
“Kina ina?”.
Da sauri ta ɗago kanta ta kalli rubutun gaban saman wurin tace.
“For naw dai Ina Riyal Abaya shop, kaifa kana ina?”.
Yana mai dudduba jallabiboyin dake gabansa yace.
“Oriental Abaya House”.
Jin haka yasa tayi sauri ta kalli Uncle Ali tare da cewa.
“Ayyah Uncle dan Allah ta ina Oriental Abaya House yake”.
Kai ya dan juyo ya kalleta tare da cewa.
“Can kuke son zuwa ne”.
Da sauri tace.
“Eh Uncle dan zan amshi wayata ne a wurin wani yace min yana can”.
Kai ya gyaɗa kana yacewa.
Driver su tafi can.
Ita kuwa Aysha da sauri tacewa Taj cewa, gata nan zuwa yanzu ya jirata, toh kawai yace tare da katse kiran.

Tafiya kaɗan sukayi suka isa bakin shop ɗin da yaci uban wancan da girma da cika da ƙasaitattun kaya harma da tsaruwan wajen.

Cikin kulawa Uncle Ali ya kallesu bayan sun fita yace.
“Ku kulafa, kada ku tsaya har ku rasa jam'in sallan azahar.
Kada ku tsaya sayyaya ku mance Ibadar data kawomu.
Ni zan wuce, dan zamuyi gaba dan duba ingancin tantunan mu na wurin arfa”.
Cikin girmamawa sukayi mishi godiya kana mota taja ta tafi.
Da ido suka rakashi suna jujjuya kuɗaɗen da ya basu suna kiyastasu da kuɗinmu na nan gida Nigeria ya kai kimanin Naira dubu ɗari da ashirin da biyar biyar harda burbushi canji.
Ga kuma cewa da yayi su ɗau duk abinda suke so zai turo Usman.

“Bismillah mu shiga, dan nasan Yah Usman yanzu zai fara ƙorafin lokacin salla yayi bazai zoba”.
Garkuwa ta faɗi haka tana gaba, suna biye da ita Maryam tace.
“Waye Usman ɗin kuma?”.
Suna shiga cikin wurin Garkuwa tace.
“Yayana ne, kuma shine PA ɗin Uncle Ali”.
Kai suka jinjina kana suka ƙarasa kutsawa cikin shop ɗin.

Suna tafe suna dubu tsala-tsalan Abayoyi na alfarmar waɗanda suke da farashi na musamman.
Cikin yabawa Aysha ta kai hannunta kan wata Black blue ɗin Abaya da ta amsa sunanta, tace.
“Wow Masha Allah, kinga wannan Abayar”.
Jinjina kai Maryam tayi tare da cewa.
“Kai tayi kam sai tsada kalli kuɗinta fa, in an juya da kuɗinmu kusan dubu dari uku da hamsin nefa”.
Cikin kula Garkuwa tace.
“Laa ba matsala wlh, ku ɗauka, kema Maryam in kinga kalar da tayi miki ki, ɗauka.”
Cike da poolaku Aysha tace.
“Kai Garkuwa haba, ai sai kuma abin yayi yawa, ai akwai kuɗi a hannunmu, kin manta jiyama Barrister ya bamu kuɗi ai wannan sai musa Uncle Ali ya samu matsala a kan kujerarsa”.
Da sauri tace.
“Wlh da kuɗinsa halal ɗinsa ne zai mana hidima ba da kuɗin ƙungiya ba, kada kuji komai ai shi yace mu ɗauka”.
Haka dai tai ta basu baki har suka ɗauka kana suka fara duba Vails kuma.
Sai kuma gefen bags da takalma.
da sauri Aysha ta zaro wayarta jin, tana ringing.
Tana amsa kiran taji yana cewa.
“Please dan Allah kefa nake jira, na gaji da zaman wurin ga lokacin salla na ƙara towa, kizooohhh”.
Wani irin yam taji saboda yadda ya ƙarashe mgnar da wata iriyar gajiyeyyiyar murya kana kasalalelliya”.
Murya a tausashe tace.
“Ta wanne side ɗin kake”.
A takaice yace.
“Side ɗin Dubai jallabiya na maza”.
Jin haka ne yasa taja hannun Garkuwa Da Maryam suka nufi can.
Tare da ce mishi.
“Gamu nan ma kusa da wurin”.

Shi kuwa a hankali ya zaro ɗaya wayar tashi ya amsa kiran da kakarsa Addawa keyi mishi.
“Tajuddeen wai ina kake ne mun gamafa kai muke jira.”
Cikin sanyin Muryasa yace.
“Afwan Addawa gani nan zuwa ina duba wata jallabiya ne”.
Kai ta jinjina kana ta fara nufo inda take zaton nan yake dan ta lura in ba ta jawoshi ba fitowa zaiyiba, ta rasa menene ya tsai dashi.

Maryam ce a gaba sai kuma Aysha yayinda Garkuwa ke baya,
Kusurwowin ciki, Aysha da Maryam suka fara lelleƙawa.
Da sauri Aysha ta juyo jin Maryam na cewa.
“Aunty Aysha gashi nan”.
A tare Aysha da Garkuwa suka nufi inda yake, tsaye wani daga cikin ma'aikatan wurin biye dashi a gefe yana tura cart da ya zuba abubuwan da ya tsitstsinta.

Kasan cewar yana fuskantar ta inda Aysha ta shigone, yasa sukayi ido cikin ido.
Wani irin ɓoyeyyen numfashi mai sanyi ya fesar tare da ɗan buɗe lips inshi kaɗan.
Kana ya ƙanƙamce amintattun idanunsa, tare da ɗan kawar da fuskarsh gefe, kamar ba ita yake kalloba, sai kuma yayi ƙasa da kwayar idanunsu, daga kan rumfar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login