Showing 57001 words to 60000 words out of 74955 words

Chapter 20 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

faɗa gani kake bansan soba, alhalin kuma kaine nan baka san soba”.
Kwaɓe fuska yayi tare da cewa.
“Toh in ana son juna kuma sai aƙi ɗaukar wayan juna, Kinga ai da tunaninki hakanne da baza ta ƙi amsa kirana ba”.
Da sauri tace.
“Wata ƙil rashin nuna kana sonta ne yasa tayi fushi da kai, tukun nama daya kuka rabu ko ka mata wani laifi”.
A hankali ya fara mgnar zuci da baisan tana fita ba.
“Ni ba laifin da nayi mata, kawai dai nayi mata nasihar tayi aure ko dan sa mahaifinta farin ciki, domin ya shaida min baya jin daɗin zamanta haka”.
Sai kuma yayi saurin kallon Addawa jin tana cewa.
“Hmmm Allah ya kyauta, in tayi tsami ai kwa fitar da ita in kunji yana gab da kasheku”.
A hankali ya miƙa mata hannunsa tare da cewa.
“Bani wayarki”.
Miƙa mishi wayar tayi tare da miƙewa ta nufi kitchen.
Shi kuwa number Ishmah yasa tare da kiranta bugu ɗaya ana biyu ta amsa kiran.
“Assalamu alaikum Addawa”.
Cikin sanyi ji murya a narke yace.
“Kiyi haƙuri dan Allah kada ki hukuntani, da nesanta kanki dani, kada ki hanani jin muryarka Please abotarmu bata cancanci hakaba Maeeshah”.
Sassayan numfashi ta fesar tare da cewa.
“Taj kainefa ka bani shawarar inyi aure ko?”.
A hankali yace.
“Ehhhh”.
Tana mai rumtse idanunta tace.
“Toh shiyasa na fara nesanta da kai domin in nayi auren ai bazai yiwu muci gaba da abotarmu ba”.
Cikin wani irin damuwa yace.
“Kin mance cewa, kince ni dake ba abota bace ƴan uwantaka ce”.
Da sauri tace.
“Amman ai duk da haka in dai nayi aure mgnar da mukeyi zata haramta”.
Cikin sanyi murya yace.
“Dan Allah ki bar mgnar nan Maeeshah ki bari in kinyi auren nayi miki alkawarin nida kaina zan nesanta dake, irin nesantar da bazaki sake jina da ganina ba”.
Yayi mgnar da jin cewa kamar nesanta da ita zaisa ya nesanta da rayuwa.
Jin yadda yaketa mgnar cikin sanyi ne yasa tace.
“To ba matsala yanzu dai lokacin salla yayi sai anjima zamuyi waya”.
Da sauri yace.
“Kinyi al'ƙawari”.
Cikin jin bazata taɓa yi nesanta da shiba tace.
“Eh Taj nayi al'ƙawari zanci gaba da yin waya da bestie na”.
Daga nan sukayi sallama.

Ganin lokacin salla Magrib yayi yasashi yin al'wala ya wuce gidansu.
Domin in yana gari shike limancin a masallacin kamsusul salawat na ƙofar gidansu.

A daren ranar jirginsu Taj ya tashi zuwa America.

Washe gari da safe, Meymey ce zaune a Parlour tallabe da kafaɗar Laylah daketa kwaza amai gaba ɗaya jinkinta yayi luƙus.
Cikin nuna tsantsar kulawa tace.
“So sorry, tashi mu tafi Hospital aman nan ya isa haka”.
Cikin galabaita da muguwar kasalar da ta kwana dashi tun randa suka dawo Nigeria ta yunƙura ta miƙe.
Da taimakon ta suka tafi Aabet Hospital.

Bayan awa ɗaya da zuwansu ne suka fito kai tsaye gidan su Taj ta wuce da ita.

A Parlour Ummeyn suka zauna.
Bayan ta gaida Ummey cikin girmamawa tace.
“Malam yana cikine”.
Cikin kulawa da jin daɗi Ummey tace.
“Eh yana ciki muje ko”.
Ta ƙare maganar tana kallon Laylah dake kwance tayi luƙus sai kuma ta bita da ido ganin ta miƙe da sauri ta nufi Dinnin area.
Yawu mai yauƙi ta ɗan tofar a washing hand baby dake Dannin area ɗin.
Sai kuma ta dawo ta zauna, ita kuwa Ummeeyshi cike da mamakin irin wasu sauye-sauyen da ta gani tare da yarinyar ta miƙa mata hannun tare da cewa muje ku gaida malam.”

Miƙewa meymey tayi tana mai ɗan latsa wayarta.

A Parlour suka samu Mom Amal da Aryan sai Kabir.
Suna shiga Mom Amal ɗin ta zuba wa Laylah idanu tana ƙare nazartanta.
Ita kuma Laylah cike da azabebben kasalar data buwayi rayuwarta ta tsuke bakinta saboda yawun daya sake cika mata baki so take ta sake tayi ta bawa Ummeey labarin Ishmah dasu Minat da Rahma Amman ina duk ta rasa kuzarinta.
Gefen Ummeey ta zauna tare da lafewa a jinkinta.
Cike da tsananin mamaki Mom Amal tace.
“Ikon Allah bag ɗin Taj ya haka saikace mai laylayin ciki”.
Cikin tsananin sinkewar zuciya Ummeey tace.
“Subahallahi wannan wacce iriyar mgna ce haka Mom Amal”.
Ta ida mgnar tana kallon yadda Laylah ta sake.
Aryan ne yayi saurin cewa.
“Ai kam tayi kama da masu ciki”.
Sai kuma ya kalli Kabir dake cewa.
“Ni kuma gani nayi tayi ƙiba”.
Ita kuwa Meymey tsuke fuska tayi tare da cewa.
“Kai Mom ai sai kisa zuciyata ta buga in mutu da wannan mummunan hasashen naki akan, yar amanan tamu, Malaria 🦟 cefa ta kwatso a Nigeria wata ƙil harda taypot”.
Dai-dai lokacin Malam ya fito daga dakinsa bisa dukkan alamu yaji duk abinda suke tattaunawa a kai saboda jin yana cewa.
“Toh kin kaita asibiti ne Mamana?”.
Cikin sauri Meymey tace.
“Eh Malam yanzuma daga Hospital ɗin muke, kuma ta samu magunguna”.
Cikin gamsuwa yace to Allah ya sauƙawa.”

Da Amin suka amsa baki ɗayan.

Bayan kwana biyar.
Adaya ce tsaye a tsakiyar babban hall ɗin da suke ɗaukan darasin rihazal na gasar rawan da zasu tafi nanda watanni uku zuwa huɗu, wanda shine kaɗai babban burinta.

Wani irin shu'umin waƙa da kiɗi rawarsu na Ethiopia's Gerls aka sake mata, yayinda itace jagorar tawagar shiyasa itace a gaba.
Asina agefen damanta sai kuma Bititi a gefen hagu wacce ita arniyace.
Sai kuma bayansu Izzin ne a gabanta sai wasu maza uku.
Wani irin rawa sukeyi na kafaɗa da kaɗa ƙirji.

Rawa sukeyi kai kace babu ƙashi a jikinsu.
Shi kam Izzin rawar yakeyi cike da ficewar hankali sabo yadda ƙirjin Adaya ke hautsuna mishi lissafi, dan wani irin juyi da tsalle tantsama-tantsaman ƙirjinta ɗin sukeyi tamkar zasu rabu da ƙirjinta su zube ƙasa.
Gigatashi da sukayi ne yasa ya sauya salon rawar tasu, da ƙara kusantarsu ta baya.
Kana yasa hannun damansa ya zagaye lafeffen cikinta, tare da ɗaura na hagunsa kuma saman ƙirjinta.
Haka suma sauran sukayi.
Matse cibiyoyinsa yayi da masifar ƙarfi ya rinƙa tsalle da karya kafaɗarsa haka yasa itama bada ƙaimi, burinta yasa ta gaza tantance abinda yake mata, ya saɓa tunanin.
Sauranma haka suke rawan.
Yayinda couch da sauran fara yi musu tafi da ihu. Haka dai suka kwana wannan jarabar rawar.

Koda garin ya waye a gajiye ta dawo gida.
“Yanzu kenan Adaya ki rantse lalata rayuwarki zakiyi a banza ki zubda kima da darajarki na ɗiya mace kuma musulma”.
Cewar Umminta hamma mai cike da bacci tayi tare da cewa.
“Dan Allah ki bari in nayi bacci na farka zamuyi mgn”.
Ta ƙare maganar da sake video da sukayi a TikTok.
Sai kuma ta cilla wayar kan gado ta shigo Bathroom.
Ganin haka ne yasa Umminta fita rai cike da ƙuna.

Kwanan Taj takwas da tafi kafin ya dawo, gidansu ya fara wucewa kai tsaye saboda Ummeynshi ta shaida mishi Meymey da Laylah suna gida.

Cikin mamaki yake kallon Laylah da tayi wani irin fari na fitar hankali har wani yellow-yellow tayi, musamman goshinta da yake wani irin ƙelli, kana tayi wata ƙibar da bai santa da shiba.

Cikin mamaki yake lallonta sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Meymey dake haɗa mata tea.
“Yah Salam wai me yake damunta ne?”.
Fuska a tsuke tace.
“Ni ya kamata inyi maka wannan tambayar, tunda ni ba likita bace”.
Cikin tsuke fuska yace.
“Bana son mgnar banza, ba kece kika kaita asibiti ba”.
Sai kuma ya ƙare maganar da jawo hannun Laylah yace.
“Taso mu tafi Hospital”.
Da sauri Ummeeyshi tace.
“Yanzu fa suka dawo daga Asbitin”.
Sai kuma ta kalli Zakiya dake miƙawa Laylah ɗanyen dabino irin mau gafin nan da tace tana so, cikin tsoro Ummeey tace.
“Kai nifa al'amarin nan ya fara bani tsoro, duk fa abubuwan da Laylah keyi na masu juna ne”.
Bai fahimci mgnar Ummeyn ba bare ya damu.
“Zuwa yanzu dai nima na fara zargin da Mom Amal takeyi cewa Laylah nada ciki ne”.
Baima jitaba bare ya fahimci me take faɗa.
So kawai ɗaukar Laylah yayi suka tafi Hospital.
Yayi mata ƴan gwaje-gwaje kuma basu ga matsala tare da itaba.
Sai ɗan Malaria ɗin tsarabar Nigeria daga asibitin gidan Addawa ya wuce da ita.

Kusan ƙarfe goma na dare ne Meymey ta kalli Ummeynshi cikin sanyi tace.
“Hmmm kinga har yanzu bai dawo ba ko”.
Kai Ummeey ta jinjina tare da cewa.
“Bari in kirashi”.
3 miss calls tayi mishi Amman bai ɗauka ba.

Shi kuwa Taj tuni sun koma gida shida Laylah ta wuce ɗakinta.
Shi kuma ya wuce side ɗinsa.
A zatonsa ma Meymey ta dawo.
A Parlour ya zube woyoyinsa bisa senter table dake tsakiyar Parlour shiyasa baiji kiran Ummeeyshi ba.
A hankali cike da alamun gajiya da kasala da nannauyan baccin da yakeji.
Mai ya ɗan shafa kana ya fesa turare, ɗaya daga cikin tattausan towel nashi da sune na baccinsa ya zare tare da ɗaurawa a ƙugunsa.
Bakin gadon ya zauna tare da yin addu'a ya shafa kana ya kwanta kamar yadda ya saba a rayuwarsa daga shi sai Towel ko jallabiya haka yake kwana.
Yana kwanciya bacci yayi awon gaba dashi.

Cikin sanyi Meymey tace.
“Ummeey asa ko Kaber ne ya maidani dan nasan Yah Afif in dai yana tare da Laylah baya tuna komai”.
Ta ƙare maganar da alamun takaici.
Ɗan ƙwaffa Ummeey tayi kana ta kira Kabir ɗin yazo ya maida ita.

Alhamdulillah yanzu kasalar da sauƙi sosai tunda ya haɗa mata magunguna sai yawune dai har yanzu.

Bayan kwana biyu da safe.
Laylah ce zaune kusa da Meymey a dinning table, magungunanta ta ɓare ta bata tare da miƙa mata ruwa.
Amsa tayi tare da shansu.
Fitowan Taj ne yasa ta ɗan zuba mishi ido cike da alamun da yafi kama da tsoro.
“Masha Allah Laylah ya jikin”.
Ya ƙare maganar yana sa hannunsa a wuyanta.
Cike da tsananin tsoro ta sunkuyar da kanta murya na rawa tace.
“Da da dasauƙi”.
Cike da kulawa yace.
“Ya dai Laylah me haka jikinki yake rawa?”.
Da sauri tace.
“B.. ba... Bab.. babu”.
Ita kuwa Meymey idanu ta zuba mishi cike da alamun son gano wani abu.
Dai-dai lokacin kuma kiran Ishmah ya shigo wayarsa.
Amsa kiran yayi yana kallon Laylah da duk ta takure jinkinta.
“Jikin Laylah da sauƙi Maeeshah”.
Ya faɗa tare da motsowa kusa da Laylah kana ya miƙa mata wayar da faɗin.
“Gata”.
Wani irin kallon mai cike da tarin manufofi Meymey ke liƙa mishi.
“Hello Aunty Ishmah”.

“Na'am Laylah ya jikin naki?”.
Cikin sanyi kasala da ya zame mata jiki tace.
“Da sauƙi sosai ma”.

“Masha Allah to Allah ya ƙara sauƙi kina cin abinci kiji ko”.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
“To Aunty ina Minat?”.
Cike da kulawa tace.
“Tana gidansu”.
Daga nan dai sukayi sallama.
Amsar wayar yayi tare da ficewa.
Ya wuce Tajmuh hospital.
Yana isa ya fara aikin CS ɗin da zasuyiwa kusan mata biyar, da taimakon Dr Farida da Dr Adey sukayi komai.

Kwanan Taj goma da dawo kana ya sake wata tafiyar zuwa Bangaladash daga can ya wuce India
Kwana shi biyar ya dawo Ethiopia.

Yau tun safe kuma Laylah ta kuma tashi da amai da zazzafan zazzaɓi.
Haka yasa ta ɗauketa tayi gida da ita.
A Parlour Malam suka samu, mafiya yawan mutanen gidan.

Bayan sun gaisa ne Meymey keyiwa Ummeey bayanin jikin Laylah, cikin taɓe fuska Mom Amal tace.
“Na rantse da zatin Allah ƴannan cikine da ita, in kunƙi kuma kuje ayi muku gwajin cikin zakusha mamaki wlh.
Cikin fara jin tsoro da ganin alamun gskyar Mom Amal Ummeyn tace.
“Gsky dai nima ina gafa gwara aje”.

Dai-dai lokacin kuma Taj dake shigowa yace.
“Ba wani ciki a jikin Laylah dan Allah Ummeey ku daina faɗar hakan, hankali na tashi innaji kuna batun Laylah”.
Ya ƙarashe maganar tare da zira wayar shi cikin aljuhun ba tare da ya katse wayan da yake yi da Ishmah ba.
Kusan duk a tare suka juyi suka zuba mishi idanu.

Malam kuwa wani irin kallon cikin ƙwayar idanun Taj ɗin yake tamkar mai son karantan wani abu.

Ita kuwa Meymey cikin tsoro tace.
“Gsky dai nima zanso ayi mata gwajin cikin nan, dan abin ya fara bani tsoro ayi kawai hankali na ya kwanta”.
Maman Yah Hafiz ne ta jawo hannun Laylah tare da cewa.
“Laylah meke damunki ne?”.
Laylah da batama san menene suke mgn a kaiba jiki cike da kasala ta juya ta fita, yawun bakinta ta zubda kana ta dawo.
Ita kuwa Maman Yah Hafiz cikin sanyi tace.
“Dan Allah ku daina alaƙanta ƴariyar dake da alaƙa da gidanan da wannan mugun abun da bazamu iya ɗaukaba”.
Ta ƙare maganar tana kallon Malam da ya kafe Laylah da kallon dake nuna tsananin tsana da ƙyamar da zata iya fuskanta a tare dashi, domin tasan yadda zuciyar mijinta yake farin sani.

Yayinda duk sauran kuma suka zurawa Laylah ido murya a raunace tace.
“Nima ban saniba, bana iya cin abinci kuma yawuna ba daɗi in na haɗiye amai nakeyi”.
Da sauri Mom Amal tace.
“To me kikeson ci?”.
Tana zamewa kwance tace.
“Abu mai tsami”.
Yah Salam shine abinda Taj ya iya faɗa zuwa yanzu shima tsoro mai yawa ya rufeshi musamman da ya ƙura mata idanu a matsayin sa na likita ya gano alamun ciki.
Cikin sauri duk suka kalli Malam da yaja wani firgitaccen numfashi tare da cewa.
“Kai Hafiz ɗauketa ka kaita a gwada min ita yanzun nan nake jiran amsa”.
Ya ƙare maganar cikin tsananin tafasowar fusatar zuci
Da sauri Yah Hafiz ya miƙe.
Meymey miƙewa tayi tare da tallabe Laylah kana suka nufi waje.
Cikin so da kulawa Malam ɗin ya kalli Taj daya juya da nufin zai bisu.
“Zo Babana ka huta, yayanka zai kaita, yanzu ka dawo ko ruwa baka sha ba”.
Wani irin mugun kallo Mom Amal da Aryan suke mishi ƙasa-ƙasa.

Mamin Aryan kuwa da ido ta tsare ɗan nata ganin kallon da yakeyiwa ɗan uwan nashi, cikin mmki da tsanan hali irin na Aryan ta miƙe ta bar Parlour.

Nigeria Abba ne zaune a Parlour shi bisa dukkan alamu waya yakeyi da Yayanshi Bello.
“Ya gajiyar ibada kuma”.

“Alhamdulillah ai yanzu kam gajiya tabi lfy, yau wata ɗaya gudafa kenan da dawowarmu, in sha Allah ma nanda mako biyu dai ina nan tafe zan shigo Adamawa, ɗazu nayi waya da Ishmah nace mata ta shirya”.
Cikin girmamawa Abba yace.
“To Masha Allah, Allah ya kawo ka lfy, ba ruwana
Kaida ɗiyarka”.
Ya ƙare maganar cike da kara.
“Ɗazuma ma Adam ke cemin wai ashe Dr Nafi'u ma, yabar ƙasar jiya ko?”.
Yana gyara zaman hularsa yace.
“Eh yace wai ta ɗan jirashi in ya dawo zasuyi auren”.
Cikin faɗa Uncle Bello yace.
“Bamuyi wannan alƙawarin ba, wlh ina zuwa Adamawa zan ɗaura mata aure, da duk wanda yake buƙata, idan kuma Mukhtar yace yana sonta wlh aura mishi ita zanyi.
Dan yaron yana da mutunci dan koda na dawo Umrah yazo min sannu da zuwa”.
Kai Abba ya jinjina domin ya sani tabbas.
Mukhtar (Bappa Kawu) yana da mutunci da Kamala ko shi bazai ƙi aurenta da Mukhtar ba.

A cikin gida kuwa.
Cikin tarin damuwa Ishmah ke jin duk maganganun da akeyi a Parlour Yah Abana ta wayar Taj dake cikin aljihunsa.

Ganin kiran Bappa Kawu ya shigo wayarta ne yasata katse kiran Taj ɗin kana ta amsa cikin sanyi tace.
“Assalamu alaikum, Bappa Kawu”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ni dan Allah na tuba a dena cemin Bappa Kawu nan ko Hamma ki kirani ba sai kince my price ɗin ba”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Wannan ai tsohon suna ne”.
Da sauri yace.
“Ni kuma so nake a sabunta minshi, To my princess, ai ni so nake ki aminta dani fiye da amincin da kikayi dani a baya domin a yanzu da yaƙinin aure na dawo da ƙarfi na”.
Cikin sanyi tace.
“Bappa Kawu ka dawo ka kuma yin wasa da zuciyata kenan ko?”.
Ta ƙare maganar tana jin son da tayi mishi a baya na tasowa.
Allah ya sani taso Mukhtar rabuwan su haukane kaɗai batayi ba.
Cikin salon so ya rinƙa isar da soƙonsa.

Ethiopia.

Kusan duk ma zauna Parlour ido suka zubawa Yah Hafiz da ya zauna gaban Malam yayi ƙasa da kansa hawaye na kwaranya a idanunsa.
Ganin haka ne yasa Taj yin mutuwar zaune saboda koma menene yasan ba labari mai daɗi bane.
Kana ga Meymey a durƙushe a gaban Malam ɗin tana sakin shesh-sheƙan kuka.
Laylah kuwa jikin Ummeeyshi ta faɗa tana karkarwa.

Ita kam Ummeeyshi tuni ta fara karkarwa.
Mom Amal kuwa cike da zaƙuwa tace.
“Hafiz mgn zakayi ba kuka ba, me likita yace?”.
Ta ƙare maganar da kallon Malam da fuskarsa ta sauya daga fara zuwa jazir kana idanunsa sunka ƙanƙance suka kuma sauya launi daga fari zuwa fatsu-fatsi.
Cikin Muryar dake nuna tsananin fusata da tashin hankali yace.
“Hafiz me likita yace?”.
Cikin raunin murya Yah Hafiz yace.
“Dr yace tana da ciki har na tsawon wata uku”.
Wani irin masifeffen harbawa zuciyar Taj tayi lokaci ɗaya zufa ya karyo mishi.
Da sauri kuma ya rumtsa idanunsa jin Malam na cewa.
“Waye yayi mata ciki?”.
Kusan gaba ɗaya Parlour juyowa sukayi a kaɗe suna kallon Meymey da ta saki wani irin kuka mai cike da shesh-sheƙan kuka.
Cikin tsananin tsoro kaɗuwa Yan Hafiz, Yah Yusuf, da Abduraham, kana da iyayensu mata suka zubawa Meymey ido jin abinda take cewa.

Shi kuwa Taj dimmmm yaji kunnuwansa sun toshe zuciyarsa ta tsaya da bugawa idanunsa sun daina gani a lokacin da yaji Meymey na cewa.
“Yah Afif ne yayi mata c....”




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 13*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Page biyu kacal suka rage mu gama free pages bayan wannan, ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276, kuma mutan Niger 1000fc ne rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076.*



Cikin shesh-sheƙan kuka taci gaba da cewa.
“Yah Afif ne ya mata ciki babu wanda zai mata ciki a duniya bayan shi,shine ya maidata tamkar matarsa”.
Wani irin karkarwa da rawa jikin Yah Abana ya ɗauka maganar tazo masa abaxata baiyi zato ko tsammanin jin irin waɗannan kalaman ba.
Rawa zuciyarsa keyi domin sam bata yarda ba kuma bata amince ba lokaci ɗaya yaji jinsa na ƙoƙarin ɗaukewa..

Yayin da Taj kuwa tunaninsa, nazarinsa da ƙwaƙwalwa suka tsaya daga bugawar da suke haka zalika kunnuwansa sunyi dif daga sauraren abinda suke kana idanunsa sunyi dulum daga kallon abinda suke babu abinda yake gani face duhu haka nan yaji numfashinsa na ƙoƙarin barin gangar jikinsa fahimtar yana gab da sumewa In yayi garajene yasan ya ɗan gyara zamansa cikin ƙarfin hali yayi saurin fisgo salati da tasbihi daga cikin zuciyarsa zuwa harshensa duk da bai fito kan lips ɗin sa mutane sunji ba amma da taimakon kalmar _Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun Allahumma Ajirni Fii musibati Wa'alhlifli khairan minhaa_ da yake naimaitawa ya bawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login