Showing 18001 words to 21000 words out of 74955 words
Chapter 7 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
da Maryam dan sune manya a kansu.
Gefenshi suka je suka zauna.
Da sauri ya sa hannunsa ya amshi Trayn dake ɗauke da plates ɗin dake cike da fruit.
Inabin ya fara sinka yana danƙawa yaran ɗaya bayan ɗaya,
Tare da kallon Zakiya cikin sanyisa yace.
Akwai jakar tsarabarsu, tana hannun Baba Abu Hashim, kije ki kwance kowa da sunansa a jikin nasa, ki basu, akwai kuma Chocolates insu, yana mota kije ki dauko duk ki basu”.
To tace tare dasa hannun ta dauki Mahira da Iman.
Haba su kuwa ƴan manyan jin haka keda wuya, duk sukayi ɗuuu suka bi bayan Zakiya suna faɗin.
“Aunty Zakiya a fara ɗauko mama Chocolate ɗin”.
Daga nan duk suka fice.
Kusan duk Parlour da ido da murmushin suka rakasu.
Shi kuwa Taj gyara zamansa yayi tare da kamo ƙafar Malam ɗin cikin sanyin sauti da halinsa yace.
“Yah Aryan bari in karɓeka tausar nima in samu ladan”.
Murmushi duk sukayi, shi kuwa Taj kafar mahaifin nasu ya daura bisa cinyarsa ya fara yi mushi tausa mai cike da iyawa a matsayinsa na likita.
Sai kuma ya kalli Maryam dake cewa.
“Ba abinda kacifa”.
Sai kuma suka kalli Rashida da tayi saurin miƙewa tare da cewa.
“Yauwa kin tuna min na, dama yau nace in sha Allah abincina Malam zai faraci”.
Da sauri kuma suka kalli ƙofar shigowa jin muryar babbar yayarsu mai bin Yah Yusuf tana cewa.
“Ai kuwa bamu yardaba”.
Su dai sai murmushi suke haka ƴaƴan Malam matan da suke cikin Ƙasar Ethiopia a birnin Addis Ababa suka rinƙa shiga wanda yayanshi mata 13 ne cib maza kuma 7. Haka yasa yaranshi 20 ne cib.
Sai kuma mata shi Huɗu, Hajia Halisa itace babba uwar Hafiz, sulaiman, Sai kuma Anty Khaulat sai autarta Hajara, sai kuma Hajia Sumayya itace mahaifiyar Yusuf da Aunty Ni'imatullah da da Aryan da Abdurahan.
Sai kuma Hajia Muhibbat.
Uwar Salma, Madina, Ruƙayya, sai Kabir, da , sai kuma Amal,
Su ukun nada yaya 15 sai kuma Ummeey dake da biyar, Maryam, Rashida, Halima, Taj, Zakiya.
Sune 20 cib.
A irin ya wannan rana yakance da matansa, yau ranar ƴaranshi ne dan haka kada su matsa mishi.
Dan duk ranar jumma'a ta ƙarshen wata duk ƴaƴanshi a tare suke wuni.
Da sauri Rashida ta dauko womers ɗin ta da tazo dasu daga gidanta. Kana ta dawo gaban mahaifin nasu ta zauna tare da zuba mishi abinci.
Halima da yanzu ta shigo hannun rike da womers ce tai ɗan murmushi tare da cewa.
“Allah sarki gida daɗi, kunkam da kuke aure a garina kunji daɗi ai, irina dasu Aunty Ni'imatullah da Madina kam sai in munxo muke samun wannan ladan, dan haka tun da kan su tafi masallaci nayiwa Malam abinda zaici don nima in samu ladan. Yau dai kuyi haƙuri ku bari yaci nawa”.
Murmushi mai cike da farin ciki malam keyi. Tare da kallon ahlin nashi, cikin fara'a Aunty Khaulat tace.
“Gsky fa haka ne Halima to mun haƙura”.
Da sauri Maryam tace.
“Laah Aunty Khaulat ai wayo take mana, muda muke garin ai iya jumma'a jumma'a ne shima sai na ƙarshen wata kaɗai muke samu yaci girkinmu, sufa ƴan nesan nan in sunzo har su koma sukeyi masa girki.
Irin Halima gata nan har shara side dinsa in dai tazo ita keyi mishi mu muna samun wannan damar ne”.
Dariya sukayi duka sai kuma suka kalli Amal dake shiga tana cewa.
“Kum tsaya mujadala gashi Aunty Rashida ta riga ta samu shi”.
Ita kuwa Rashida murmushi tayi cikin jin daɗi kasancewar mace mai fara'a yasa Malam kan sake mata fuska sosai, cikin Murmushin ta mika mishi plate ɗin gashin da yaji Vegetables, da sauri Yah Yusuf ya amsa tare da ajiye mishi a gabanshi, Amal kuma Fruit ta ajiye.
Mishi Aumty Khaulat kuwa sauran tarin womers ɗin dake kan Dinnin table nashi tasa su Halima da da Maryam suka jido da tarin plates and spoon's da fork.
Nan duk ta zubawa, kowa.
Hafiz ne ya kalli Taj dake tayiwa maifin nasu, tausa a ƙafarsa dake kusa dashi yana ɗan jan yatsun ƙafar, bisa dukkan alamu, yayi nisa a cikin tunani, domin ana ta mishi mgna yaci abincin Amman bai tan kana.
Shi kuwa gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan wancan al'amarin da ya faru tsakininsa da wacce tsohon nan ya buwaye su da kiran sunanta Adaya.
Allah ya sani yana jin yunwa to Amman ina bazai iya cikin komai ba, domin cikinsa ya cika tib da ruɗani.
“Afif me ke damunka”.
Yah Yusuf ya tambaya cikin kulawa, eh dama Taj ba surutaccen bane kuma baisan kwaramniya Amman yanayinsa na yau ya nuna akwai wani abu tare dashi sai dai zurfin cikinsa ne bazai bari a gane damuwa bace.
Cikin sauƙe nannauyan numfashi ya miƙe tare da cewa.
“Bari inje inga Ummeey na”.
Cikin kulawa Yah Hazif yace.
“Ka zauba muci abinci tu...”
Sai kuma yayi shiru ganin Mahaifinsu ya ɗaga mishi hannu alamun ya barshi, sai kuma yayi mishi nuni da hanya alamun yaje.
Shi kuwa Taj ganin haka yasa ya fita, kai tsaye part ɗin Ummeynshi ya nufa.
A Parlour kuwa cikin Rahama Amal tace.
“Ke ma dai Aunty Maryam mutun da amaryarsa, kika san me ta shirya mishi, zaki wani da mashu da abinci kisa yaci ya koma ya kasa cin nata, kin kuma san Meymey da taɓara.”
Kai Maryam ta jinjina ba tare da tace komai ba, sai mgnar zuci da tayi.
“Uhmmmm Meymey ai ba irin wannan matar bane”.
A can Parlour Ummeey kuwa zaune yake gabanta bisa kan Turkey carpet.
Yayinda kanshi ke kife bisa guiwowinta, cikin kulawa da so tace.
“Afif meke dumunka?”.
Yah Salam wannan tambayar da sukeyi kishi tana kara ɗugunzuma nitsuwarsa, suna tuno mishi abinda ya faru.
Ita kuwa Ummeeyshi ganin yadda jikinshi yake a mace ga idanunsa da su ɗanyi ja ga alamun rashin nitsuwa, sai tayi tunanin ko begen matarsane, haka yasa cikin kulawa tace.
“Toh yanzu dai tashi ka tafi gidanka.
Ka dawo gobe muyi hira”.
Yes Allah ya sani so yake ya kaɗaice, ko zai samu damar da zai yi nazari.
Hakan ne yasashi ɗago kanshi a hankali.
Ido Ummeynshi ta zuba mishi tana nazartar yanayin tashin hankali da ɗimuwar dake cikin eyes ɗinshi.
Ta sani bazai faɗa komai ba saboda tafi kowa sanin tsananin zurfin cikin ɗan nata.
“Babana meke faruwa ne ka gaya min mana”…
Cike da juriya ya ƙaƙalo murmushi dole wai dan ya kwantar mata da hankali cikin sanyi yace.
“Ummey na ba komai fa kwai gajiyace”.
Kai ta jinjina tare da ɗago hannunsa kana tace.
“Toh muje ka gaisa dasu Hajia Babba sai ka wuce gidanka ka samu ka huta”.
Ba musu ya bita a baya suka shiga sashin matan baban nashi sai dai basa ciki alamun sun tafi wurin Malam haka yasa suka wuce can.
Bayan ya gaida su ne yayi musu sallama.
Kana Ummeey da da yayunshi Rashida da Maryam da Aumty Khaulat suka rakashi.
A bakin motar suka tsaya suna ɗan hira saboda, hango Abu Hashim dasu Baba Idi suna cin abinci.
Shi yasa suka ɗan zauna suka jirasu.
Suna gamawa Abu Hashim yazo.
Kana su Ummeey suka koma ciki.
Motarsu na gab da fita motar Uncle Jibirin na shigowa.
Haka yasa Taj cewa.
“Abu Hashim tsaya”.
To yace kana ya tsaya shi kuwa da sauri ya fito tare da nufar motar Uncle Jibirin da tuni sunyi parking har driver'nsa ya buɗe masa ƙofa ya fito, Dottijon ne da bazai gaza Malam ba.
Cikin tsananin sakin fuska ya nufi Taj yayinda shima Taj shi ya nufa.
Rusunawa yayi ya gaidashi.
Ya amsa a mutumce kana ya ɗaura da cewa.
“Amman Mamana bata san ka dawo bako Taj, dan yanzu haka can gidan naka na fito bata gaya min cewa ka dawoba”.
Kai ya ɗan rusunar tare da cewa.
“Ai isowata kenan. Ko Malam bai san zan dawoba ganina kwai sukayi, yanzu zan wuce gidan”.
Motsawa Uncle Jibirin ɗin yayi tare da ɗan bubbuga kafaɗarsa kaɗan kana yace.
“Toh aje a huta”.
Daga nan shi yayi cikin gida, shi kuwa Taj ya koma cikin mota suka nufi gidansa da ba wani nisa sosai dan kusan sashin layin wurin duk su ya sune, gidan babansu suka sa a tsakiya duk su mazan gidajensu na zagaye da na babanne”.
Uncle Jibirin, aminine ga Malam wanda duk wanda yasan Malam a Ethiopia ya sanshi ne da Jibirin, bashi da kowa a duniya da ya aminta dashi sama da Jibirin bashi da abokin shawara a duniya sama da Jibirin.
Shine iya kar wanda Ƴayansa kab suka sani wai wani na jikin mahaifin nasu, basu san kowa nashi a duniya ba.
Sai Uncle Jibirin, shine madadin Babpansu kakansu kakarsu. Wanda sunayensu kadai suka sani, wanda Taj yaci sunan kakansu na mijin.
Halima kuma taci sunan kakarsu macen.
Wannan yasa komai na abinda ya shafi aure Uncle Jibirin keyi musu da kuma Sheykh Adam wanda shine kuma amini na biyu a wurin Malam kuma shi ke ja mishi baƙi.
Wata Shida Baya Malam da Uncle Jibirin suka haɗa auren Taj da Meymey ɗiyar Uncle Jibirin ɗin wacce taci sunan kakanta, wanda bisa dole suka datse soyayyar da Meymey keyi da wani Dr da suka shafe cekara biyu suna soyayya.
Taj kuma baima saniba kawai dawowa yayi ya samu Meymey, wai ai an aura mishi ita, wannan al'amari yayi misifar hautsuna mishi lissafi ya watsa mishi dukkan wani ƙudirinsa.
Toh Amman su kansu dan sanin biyayyarsa da haƙurinsa ne, yasa sukayi mishi haka, koda ya dawo kuma Malam da kanshi ya kaishi gidan da aka shirya mishi matarshi kuma take can.
Ita ko Meymey ta lashi tokobin sai ta kashe auren ko ta wacce hanya.
Tayiwa kanta alkawarin babu abinda zai rabata da Dr Zakariyya, domin shi takeso, ta shirya ko ta wacce sigar sai ta rabu da Taj.
Wanda shi baima san tanayi ba domin ya lura Meymey makirace, bata saniba shima bawai sonta yakeba, Amman kuma bazai tozartata ba.
A hankali ya tura ƙofar falonta,
Tare da kutsa kanshi cikin Parlour.
Sassayan numfashi ya fesar ganin yadda Parlour ke hargitse bisa dukkan alamu ba ita da Laylah kaɗai bane a cikin gidan.
Cikin ɗan ɗaga sautin murya kaɗan ya fara kiran Laylah ƙawar Amininshi Irfan Imran dan Palastine ɗinnan.
Wace take cike da marci gaba da baya.
“Laylah Laylah Laylah!!!”.
Ya ƙare kiran sunan nata da ɗan ƙarfi.
Wanda hakan yasata fitowa daga kitchen a guje ta nufoshi.
Sai kuma ta tsaya turus a gabanshi.
Tuni idanunta na tsatstsapo da hawaye, tuno yadda Irfan keyi matansa yasashi buɗa mata hannayensa.
Da gudu ta ruggume ƙafafunsa.
Cikin kula da jinta cikin tsatson jinkinsa tamkar yar da aka haifesu ciki ɗaya a tausashe yace.
“Me kikeyi a kitchen?”.
Ya ƙare maganar yana Binta da ido ganin yadda ta rame har ta ƙanƙance.
Cikin murmushi tace.
“Indomei zan dafa inci yunwa nakeji”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da kallon tsakiyan Parlour.
“Ina Antynki?”.
Da yatsa ta nuna mishi bedroom ɗin Meymey.
Kafaɗunta ya ɗan riƙe tare da ɗan matsar da ita gefe, kana ya nufi inda ta nuna mishin.
Tura ƙofar yayi a hankali tare da shiga da sallama a bakinsa.
“Assalamu alaiku....”.
Sai kuma rogowar sallamar ta maƙale a tsakiyar maƙoshinsa bata koma cikiba kana bata fito wajeba.
Sai kuma ya tsaya tamkar an dashi idanun sa kuwa sai neman rufewa sukeyi da kansu, saboda sai ƙanƙamcewa sukayi, ya kuma hanasu rufuwan ya saitasu, kan Meymry dake ruggume da Dr Zakariyya!
Wani irin tsuma da tashi yaji tsikar jikinsa nayi.
Wanda yake da yaƙinin bakwai na kishi bane, sai na tsananin mamaki da jin tsoron lalacewar Meymey, eh ya sani makirace, Amman bai taɓayin zato ko tsammanin cewa lalacewarta har ta kai matsayin tayi wannan muguwar ɗabi'a da kuma igiyoyin aurensa a tsakiyar kantaba baisan cewa rashin tsoron Allah ta ya kai wannan mata kinba ta shigo mushi da gardi fasiƙi mazinaci har cikin gidansa,.
Dr Zakariyya kuwa, wani irin fitinenne fitsari tsorone ya tsinkomishi.
Saboda kwarjini da haibar Taj ya tsinka mishin hanjin ciki da zuciya.
Wannan yasa tuni fitsarin ya fara ɗiso mishi cikin sauri yayi ƙasa da kanshi domin bazai iya kallon tsarkakkun idanun Taj da nashi ƙazanrattun idanunba.
Ita kuwa Meymey cikin wani irin tsaurin ido da tson ɓoye ainihin firgita da gigitar da tsoron idanun Taj daya sakar Mata, tasa hannunta da sauri da nufin kamo hannun Dr Zakariyya daya janye jikinsa da nata, yayinda gaba ɗaya jikinsa yake ta rawa tamkar mazari.
Sai kuma ya nufo hanyar fita yana wani irin yin fiki-fiki da munafukan idanunsa.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan jungina da gefen ƙofar tare da harɗe hannunsa a ƙirji kana ya ɗan ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya.
Kululu'ulllllllluuu. Cikin Dr Zakariyya da Meymey suka bada sautin a tare.
Shi kuwa ido ya kafe Meymry dashi ba ko kebta wannan ne kuma ya sakar mata da rawan jiki.
Shi kuwa Dr Zakariyya cikin fellewa a guje ya raɓa gefen Taj ɗin ya wuce.
Yana matse da hantsar wonɗonsa da tuni ya jiƙe da fitsari.
Da wani irin kallon da yasa hantar cikin Meymry kaɗawa ya raka Dr Zakariyya dashi.
Sai kuma ya dawo da lannsa kanta, ko ƙala bai ce mata, sai irin kallon nan.
“Ke najasace, kuma ke baki da amincin da zuciyata zata aminta dake bare inji kishinki, sai dai inji kishin saɓawa Allah da kikayi a cikin gidana”.
Duk da ba mgna yayi da bakiba Amman idanunsa sun nuna mata kallon ƙazantacciya kuma ƙasƙantacciya yakeyi mata.
Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfi lokacin da taga ya juya ya fita.
A Parlour ya samu Laylah riƙe da plate ɗin indomei.
Hannunta ya kamo kana ya juya suka fito.
Ganin ya shiga Motane yasa Abu Hashim shigowa ya ja motan tare da cewa.
“Ina zamuje?”.
A taƙaice yace.
“Gida”.
Koda suka isa cikin gidan, kai tsaye part ɗin Malam Laylah ta nufa, shi kuwa part ɗin Ummeynshi ya shige.
Laylah na shiga Halima ta buɗe mata hannun da gudu tazo ta, ruggume sai kuma tayi saurin sake Halima ta ruggume Ummeey tare da cewa.
“Ummeey yunwa nakeji”.
Cike da tausayin tarin maraicin dake dabai-baye da rayuwar yarinyar Rashida tayi sauri sa mata abinci.
Maryam kuma kama hannunta tayi ta zaunar da ita.
Nan take ta faraci, hannu baka hannu ƙwarya, fes ta cinye ganin haka Rashida ta ƙara mata.
Shima tas ta cinye, za'a ƙara mata ne, tace a'a ya ishe ta.
Cikin kulawa Halima dace.
“Laylay kin rame kinyi doshe da yawa”.
Kai kawai ta jinjina tare da ɗaukar Iman suka fita, ta nufi gardin ɗin gidan.
Ganin lokacin sallan la'asar ya ƙaratone yasa.
Malam da Uncle Jibirin da suke ɗaya Parlour suka fita suka tafi masallaci kamsussalat dake cikin gidan.
Haka yasa suma duk mazan suka fita.
Su kuwa mata hira suka ɗan ci gaba dayi saboda da ɗan sauran lokacin.
Sai da suka ji an kira sallane, kana duk suka miƙe suka yi sallan la'asar ɗin a nan Parlour Malam, bayan sun idar ne kuma duk suka miƙe suka nufi sashinsu.
Maryam da Halima ɗakin da Haliman ta sauka suka nufa, Rashida kuma bayan Ummey tabi, dan zata kimtsa mata durowarta.
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fahimta Ummey ta ke kallon Taj dake zaune bisa alamu yanzu ya dawo daga masallacin.
Zaune yake a ƙasa yayinda ya kife kansa bisa gadon, tare dasa hannunshi duka biyu ya rumtse kanshi dake mishi wani irin fitinenne sarawa, sam shi lamarin Meymey baya cikin kansa, sai wannan gangancin da yafi kama da wasan kwaikwayon da ya aikata ne, ke gab da fasa minshi kai, a hankali ya ɗan murza kanshi kaɗan ya gyara wayar dake manne da kunnenshi.
“Uhmmmmm”. Ya fidda wani sauti mai kurman baƙi.
Aysha kuwa gyara zamanta tayi, tare da gyara wuyan ɗan ƙaramin baby hijjab da su Doctors suke yawan ta'ammali dashi.
Sai kuma ta lunshe idanunta tare da gyara riƙon wayar d takeyi da Taj ɗin, cikin sassayan murya tace.
“Please ka daina wannan damuwar, in sha Allah ba wata matsala da zata faruwa, yadda ka tsaida hawayen dottijon nan, Allah zai cika maka rayuwarka da farin ciki ya tsaida ma hawayenka, na sani yanzu ko abinci baka ciba”.
Sai kuma ta buɗe idanunta jin muryar Dr Nafi'u Kabir Katsina ya turo ƙofar Office ɗinta tare da cewa.
“Hi Sweetheart me kikeyi ne, har yanzu baki tafi gidaba?”.
Wani ɗan gajeren tsaki Taj yaja saboda jin Muryar Dr Nafi'u Kabir Katsina.
Sai kuma yayi saurin sakin sassayan numfashi tare da mgnar zuci.
“Wai kai Taj meyasa kake tsanan kusancin Dr Nafi'u ne, da Ishmah duk da kasan cewa ta tsaidashi a matsayin mijin aurenta, wanda yau saura wata ɗaya ne rak aure nasu”.
Sai kuma yayi saurin buɗe idan shi jin Muryar Ummeynshi.
Zama tayi gefenshi kanshi ta ɗan ɗago tare da ɗaurawa bisa cinyarsa, cike da kulawa tace bani wayar.
Ba musu ya miƙa mata
Katse kiran tayi domin bata san da waye yake mgna ba, sai kuma ta kalli Rashida data zuba musu ido.
“Jeki duba a fridge din Dinnin area akwai fruits salat da na haɗa, ɗazu ki kawo min”.
To tace tare da juyawa ta fita.
Jim kaɗan da fitanta ta dawo hannunta riƙe da wani bowl mai ɗan kare kyau, da spoon a ciki, amsa Ummeynshi tayi tare da ɗan janye guiwowinta, kana ta fuskanceshi da kyau, ɗiba tayi tare da kai mishi baki.
Kai ya ɗan jujjuya sai kuma ya miƙa mata hannun alamu ta bashi, zaisha da kanshi.
“Ka tabbatar?”. Ta tambaya cike da so ƙauna kulawa irin na uwar, uwarma da shi kaɗaine ɗanta na miji.
Ganin ya gyaɗa mata kaine yasa ta miƙa mishi.
A hankali ya kai spoon ɗin bakinsa.
Spoon biyu yayi sai kuma ya ajiye, ganin haka ne yasa Ummeynshi amsa ta fara bashi, dole ya fara amsa saboda ganin alamun rashin cin abincin nashi na damunta.
Saida ta bashi kab kana tace.
“Zuwa yanzu zurfin cikinka, ba damuna yakeyi ba, cutar dani yakeyi, Afif ina cutuwa da zurfin cikinka da haƙurinka.
Zuciyata na ƙuntata a duk sanda naga tarin damuwa tare da kai, Amman sai kaƙi faɗa.
Har kwanan gobe nasan cewa ba son Meymey kakeyi ba, Amman tsananin haƙurinka da zurfin cikinka yasa mahaifinku gaza gane abinda kakeso da wanda baka so, har ya aura maka matar da ranka bayi so.
Still yanzu kuma naga tsananin tashin hankali a cikin ƙwayar idanunka da ɗimuwa, Amman kayi shiru ka binneshi a ranka ya kakeso inyi ne Afif?”.
Wani makararren murmushi ya ƙaƙalo ya ɗaura bisa fuskar da bata taɓa riskar irin yanayin damuwa da yake cikiba sai lokacin da aka aura masa Meymry da kuma yau.
Cikin son kwantar mata da hankali da gudun ɓacin ranta yace.
“Ummey na ba abinda ke damuna fa, kwai gajiya ce, so nake nayi bacci”.
Da sauri tace.
“Toh me ya dawo da kai bayan ka tafi gidanka”.
Cikin sanyi yace.
“Laylah ce na samu, bata ci abinciba Ummey shiyasa na taho da ita taci abinci in kuma yi sallan la'asar da Yah Abana”.
Ido kawai ta tsura mishi tana son nazartarsa, Amman ina shi har idanunsa kan iya ɓoye ainin matsalarsa duk duniya ita ɗince ma kaɗai kan iya fahimtar yana cikin wani yanayi ma,