Showing 30001 words to 33000 words out of 74955 words
Chapter 11 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
rasaki ba domin ina son mallakarki a shimfiɗata, nasan zaki jiyar dani daɗin da babu wata ƴa mace data taɓa jiyar dani,
Bana son rasa ni'imar da nake ganin alamunta a jikinki.
Bana kuma son cutar dake”.
Sai kuma ya tashi tsaye tare da kifa kansa da jikin gini yana ganin surar jikin Ishmah nayi mishi yawo a idanunsa.
Ishmah farar macece ƙal, ƴar duma-duma mai ƙirar jikin da duk wani lafiyeyyen namiji da zai ganta zanji lafiyarsa ta motsa,
Tana da ɗan tsawo dai-dai misali, ƙirjinta irin ƙirjin nanne da yawan shekaru ko yawan haihuwa baya sa ya caɓɓullensu zubewa, a cike suke tib-tib gwanin ban sha'awa tamkar tsada, suke dan fari npls ɗinta kuwa irin mai masifar tsokar mazane domin a tsaye suke cas. Cikinta kuwa a lafe yake, sai hakan ya bawa
Ƙugunta damar bajewa mazaunanta a sama suke, kana masu ɗan motsawane in tana tafiya.
Fuskarta kuwa mai zubin o ne tana da manyan idanu farare masu lumshewa, sai hancinta dai-dai da fuskantar dan bai cika tsawoba sai ƴan siraran Pink lips inta masu masifar taushi da sheƙi kamar kunnen fure gefe duka biyu duka tana da Dimples har a tsakiyan gemunta in tana dariya yana ɗan lotsawa.
Da sauri ya buɗe idanunsa tare da cewa.
“Wallahi bazan iya haƙura da keba Ishmah”.
Ya ƙare maganar yana tuna yadda idanunta kan sauya launi in rauninta ya motsa da sauri ya dauki rigarsa ya zura tare da surar key ɗin motarsa kana ya fito ya nufi gidansu Ishmah yana mgnar zuci.
Zaune suke a Parlour Abbanta, cikin sanyi yace.
“Fushi kikeyi da niko?”.
Kai ta sunkuyar ƙasa tare da cewa.
“Miss calls 37 nayi maka baka ɗauka ba, text message 7 ba amsa, kwana biyar kenan yau baka zoba, baka kirani ba baka bari na ganka a Hospital ba, meyasa ka zabi da ka azabtar dani da hakan?”.
Cikin salon rarrashi ya zamo ƙasa ya durƙusa a gabanta tare da cewa.
“Afwan kiyi haƙuri wai ni kuma nayi hakanne da in gwada ƙarfin soyayya ta a zuciyarki”.
Cikin narke fuska tace.
“Toh ya ka gani”.
Yana murmushi yace.
“Dari bisa dari, fatan dai kina lissafin cewa yau saura.
Kwana 18 arenmu ko”.
Cike da jin daɗi tace.
“Ni da har na fara tunanin in haɗa kayanka da kuɗin sadakinka in bada a maida maka”.
Cikin jujjuya kai yace.
“Azubullahi banji wannan mgnar ba”.
Haka dai sukaci gaba da hirar tsara bikin nasu sai kusan Magrib ya tafi.
Tana dawowa Parlour Dadeey tace.
“Dadeey ba Kinga Dr da bada tsoroba wai gwadani yayi”.
Daddey na miƙewa tsaye tace.
“Haka yace min ai yayi ta bani haƙuri”.
Daga nan suka je sukayi al'wala dan sallan Magrib.
Washe gari, ranar Friday
Misalin ƙarfe 11 ɗaya dai-dai.
Taj ne kwance bisa gadon dake cikin ɗakin binciken lafiyar pilot ɗin da zasu tashi na cikin Istanbul Ataturk Airport.
Lunshe idanunsa yayi da karfi lokacin da yaji Dr na ɗan latsa saman mararsa, sai kuma ya ɗan kalleshi tare da cewa.
“Kamar akwai abinda kake buƙata.
Ya kamata a magance matsalar nan kafin ku tashi, don gudun kada ku tashi sama mararka ta murɗa kaga rayukan mutane zai shiga haɗari”.
Yana ture hannun Dr da ya kasance ɗan asalin ƙasar Turkey ɗine a taƙaice yace.
“Tun shekaru huɗu baya haka nake rayuwa, ka duba bayanan lfyata da Mexico ta tura muku kafin sauƙata, ko ka duba cikekken bayanin wannan abun da kake ganin kamar matsalace a gareri a shafin lafiyar Ethiopia's pilots ɗinmu”.
Cikin sauri Dr yayi saurin juyawa kan na'urorin dake zagaye dashi ya fara dudduba wasu abubuwa cike da mamakin ganin yadda Taj ɗin nasa ke a hanzarce duk da bawai yayi irin azamar neman agaji bane Amman kuma ba a kwance yakeba, tunda gashi har a ta sama wondo suit ɗin dake jikinsa ya nuna hakan.
“Haka kake rayuwa, to kayi aure mana”.
Yana mai miƙewa zaune yace wannan ba matsalarka bace”.
Dan Allah ya sani ya tsani wannan gwaje-gwajen jarabar tsiya da akeyi musu duk sanda zasu tashi.
Daga nan ya fita, shi kuwa Dr cike da kallon mamakin irin zarrar jikin Taj ɗin yake mamaki da jinjinawa lafiyarsa, gashi kuma bisa alamu ba mazinaci bane,
Domin da mazinacine ai da yace akawo mishi mace, a hankali yace.
“Alhamdulillah alah ni'imatil islam”.
Yasan cewa wannan ƙarfin tsarkin addinin Muslunci ne.
11:00 pm jirginsu ya tashi zuwa Ethiopia.
Washe gari ranar asabar, ta kama saura kwana 15 auren Ishmah da Dr Nafi'u,
Kana saura kwana 9 Taj yazo Nigeria.
Ishmah ce zaune a Parlour Garkuwa,
Yayinda suke magana mai mahimmanci a hankali Ishmah tace.
“Nifa tsoron shan magungunan nan nake Garkuwa, saboda gani nake kar in tsuma jiki aure ya watse, abu ɗaya dai nakeson yi”.
Cikin kulawa da sabo da Garkuwa tace.
“Kamar me kenan?”.
Cikin yin ƙasa da murya tace.
“Verging again inaso inje ayi min ɗinki tunda kinga Dr saurayi ne, kuma na haihu har yara uku, sannan yanzu shekara 7 kenan fa ba aure, to kuma ina tsoron ɗinki zafee”.
Murmushin Garkuwar tayi tare da gyara zamanta kana tace.
“Haba dai Ishmah kina tare dani kuma kike batun wani ɗinki ai wlh mun wuce wannan zamanin ke bar min wannan aikin a hannuna na rantse da Allah, zan baki mamaki in sha Allah zan maidaki tamkar ƴar shekara sha shida
Batun kuma bazaki sha magani bata tasoba dolen dole nema Kisha magani, dan dole in gigita Dr Nafi'u in kankaro mana kimarki.”
Sai kuma ta ɗan numfasa tare dacewa.
“Amman batun ɗinkin da kikace, sai kiga Dr sun tabbatar mana cewa, babu ƙarin da kika samu yayin hayhuwa, *domin in dai ƙarine ma'ana yagewar wani sashin fatar HQ yayin hayhuwa ta sama ko ta ƙasa ko gefe more especially ma ace yagewar ta cikine, to zance na Allah dole sai dai ayi miki ɗinkin, domin babu wani maganin ko suplimet da zaija fatar data yage ta rabe da yar uwarta ace kawai a matsa magani ya haɗeta, wannan magana ce kawai ta mutanen mu masu saida magani dan son zuciya da son ciniki, fatar data ya yage kuma har yagun ya warke ace magani ya jawoshi ya haɗa, ni dai a karan kaina a yanzu Ban san wannan maganin ba in akwai wacce ta sani kuma ina biɗa*”.
Cikin gamsuwa Ishmah ke gyaɗa kai tare da maida hankalinta baki ɗaya kan bayanan da Garkuwar ma'aratan keyi mata.
Ita kuwa Garkuwa cikin faɗin gskyr abinda ta sani take da maganinshi tace.
“Sai dai in buɗewace ta Normal hayhuwa, ko sakewa saboda yawan shekaru, ko kuma bazawar dake son sabunta budurci yayin aure, ko wanda iftila'in fyaɗe ya faɗawa, wanda ba yagewar, matsin ake buƙata to wannan bani da haufi akwai Maliƙi da Audugar babbar mace, sai kuma daɗi har maɗiga, su duka uku matsine, bani da haufi in dai matsine to magana ta ƙare, sai kin zama tamkar ƴar 15.”
Cikin sauƙe numfashi Ishmah tace.
“Alhamdulillah na huta da ɗinki kenan, dan last week na je naga Dr Fati, tace min bani da matsalar ƙari, wai ma fa cemin tayi kada in wani sha maganin matsi dan a tsuke nake”.
Murmushi mai sauti Garkuwa tayi tare da cewa.
“Eh fa kin san akwai mata masu jiki, roba ko hayhuwa sukayi a take suke komawa su tsuke su haɗe, kuma kullum a sabbi amare mazansu ke jinsu, to inko ke irinsu ce, nima bazan baki na matsinba”.
Da sauri Ishmah tace.
“A'a ba wanin nan ni ba irinsu bace, ke dai haɗani kawai ciki da waje”.
“Uhhmmm fa Ishmah wlh ni ba ruwana ranar da zaki ji maza”.
Murmushin tayi cike da kunya tace.
“Haba kamar yarinya, ni dai a matseni, kuma a tsumani”.
Kai ta jinjina tare da cewa .
“To taso muje”. Ta ƙare maganar tana jan hannunta.
Wani ɗaki na musamman suka shiga, wanda nanne store ɗin kayyakinta.
Jujjuya idanu Ishmah ta farayi saboda ganin kayan ɗa'a kala da ban da ban, a cike maƙil ita kuwa Garkuwa.
Fara sintar abubuwan da ya kamata tayi tana haɗasu wuri ɗaya.
Cikin 30 minutes ta gama haɗa mata komai wanda ya kai na set ɗin 80k.
Numfashi mai nauyi ta fesar tare da sasu cikin cart ɗin dake gefentakana ta turo suka fito tana cewa.
“Kin dai gana shan maganin Infection set ɗin da na haɗa miki ko?”
Suna shiga cikin Parlour tace.
“Yes na gama shanye shi jiya shiyasa nace bari inzo yau ai”.
Ta ƙare maganar suna zama bisa kujera 2 sitter.
Botikin gumbar riɗi ta miƙa mata tare da robar gumbar ilanwaddihi sai gumbar madara, tana faɗin.
“Su haka nake so ki rinƙa gutsura kina cinsu, ba tare da komai ba, duk da ba daɗi Amman dan Allah ki daure”.
Sai kuma ta miƙa mata botikin gumbar da baya baiwa mai kishiya.
“Shi wannan yana da masifar ƙarfi, kuma da ɗan gafi bazaki iya cinta hakaba, so ki rinƙa damawa da nono ko madarar ruwa kina sha.
Sai kuma wannan garin mallaka ne ga kuma garin Belɗamhi.
Su Kinga dai kamar kakarsu ɗaya green ɗaya ko”.
Kai Ishmah ta gyaɗa.
“Toh ba ɗaya bane, ga wannan farin kuma shine garin maɗi shima yana ɗan tsuke mace kaɗan duk da madara ko nono zakina shansu safe da yamma kullum.
Sai kuma wannan Tsumin riɗi ne da kuma Tsumin makwaranyi da Tsumin goron tula shima yana matsi, su duk sha zakinayi,
Ga kuma Tsumin tsirtai shi sai bayan biki zan gaya miji yadda zakiyi amfani dashi dan yana sa sha'awa”.
Da sauri Ishmah tace.
“Hmmm wlh kuwa kamar kin sani, ni bana jin sha'awa ko kaɗan wasu lokutan har ince ko dai bani da lfy ne, ko kaɗanfa bana jin sha'awa”.
Tana miƙa mata ƴan ƙananan robobin Maliƙi daɗi har maɗiga, da Audugar babbar mace tace.
“No lfyar ki ƙalau kwai kin cire batun namiji a ranki ne shiyasa, shekara 7 har na takwas ba namiji a rayuwarki, kin kuma tsare kanki shiyasa.
Ga wannan kuma maliƙi ne da Audugar babbar mace.
Su duk matsine shi Maliƙi da Audugar babbar mace suna da masifar matse mace, shi yasa ake haɗasu da daɗi har maɗiga domin shi kuma yana da masifar saukar da ni'imane.
Yadda zaki amfani dasu.
“Daɗi har maɗiga zaki fara matsewa, ki tabbatar yatsunki a bushe suke, zaki sashi can ciki.
Sai ki ɗan lakati maliƙi kaɗan, sai ki saka Amman kar ya kai inda kika sa daɗi har maɗiga, sai ki rinƙa ɗan murza yatsarki kina ɗanyin ƙasa da ƴar diddigar haɗin maganin, ki tabbatar a take zakiyi haka dan wallahi kika barshi ya kai, 3 to 5 minutes yatsarki ma bazata shiga ba.
Idan kina son matsewa over, sai ki ɗan yagi Audugar babbar mace kaɗan sai ki ɗan tura, ki barshi na awa ɗaya ki cireshi.
Wlh idan kika barshi ya kwana yatsarki bazata shiga ta daɗi ba.
Shi sai irin kamar saura kwana ɗaya bikin zaki fara yi shi a ƙalla kiyi kwana uku kinayi kaɗan-kaɗan, in kuma ma kina tsoro in kinyi sau ɗaya ya isa.”
Ajiyan zuciya mai nauyi Ishmah ta sauƙe kana tace.
“Hmmm sau ɗaya zanyi ma”.
Ta ƙare maganar tana amsar rogar garin babambaɗe data miƙa mata da butar sirri.
“Wannam butar tsarki zakinayi da ita, wannan kuma jan nama ko kaza zakiyi ta dafawa dashi a ƙalla kiyi sau uku.
In sha Allah zan bada a fara Miki rubutun da zan dafa Miki zuciyar farin rago da kuma kazar rubutu da kuma turarukan wutanki dasu Humra da kulaccar sirri da dai sauransu, ni shine gudumowata”.
Ruggume Garkuwa kawai tayi tare da fara zuba mata godiya.
“Ni dai fatana inga kina aiki dasu”.
Cikin jin daɗi tace.
“In sha Allah kuwa, ngd matuƙa Aunty na ta kaina Allah ya ƙara rufin asiri”.
Daga nan ta harhaɗa su a laida.
“Wai wannan ledar fa ta meye”.
Garkuwa ta tambaya tana nuna mata ledan data shigo dashi.
“Huluna ne da takalma na seyowa Taj”.
Jawo ledan tayi tana duba tsala-tsalan hulunan zannabukar da damanga masu masifar tsada sai kuma takalma duk kala bakwai-bakwai tana mai tsareta da ido tace.
“Ishmah ke da Taj lamarinku na ƙona min ruwan kai fa,
kin ƙi yarda cewa son juna kukeyi ko”.
Da sauri tace.
“Wallahi ba wannan mgnar a tsaka ninmu kunki ku yarda”.
Ta ƙare maganar tana miƙewa tsaye.
Itama Garkuwa miƙewa tayi tana faɗin.
“Ko ɗazu kafin ki shigo naga wani Video da yayi da Hausa nayi ta mamaki wai yana cewa.
“Assalamu alaikum mutanen Nigeria, ina muku fatan alkhairi ngd da chauraren karatuna da kukeyi, ina sonku sabodda Allah, ina gani nace Ishmah ce ta koya mishi”.
Tana buɗe marfin motarta tace.
“Wallahi kuwa nima ganin video kawai nayi, wani babban Malamine daga cikin malamanmu ya nemi yayi mgn da Hausa kana kuma suna gayyatarsa zuwa Nigeria buɗe wani babban masallacin a Borno da Abuja kin san ni da fulatanci muke magana amman dai zan fara koya mishi Hausar ma”.
Ta ida mgnar ta shiga motar.
“Ki gaida min Dadeyy da jiki”.
Garkuwa tace lokacin da taja mota.
Ethiopia
Meymey ce zaune gaban iyayenta, cikin tsananin so da ƙauna mai tarin yawa Uncle Jibirin mahaifinta kenan yayi gyaran murya tare da cewa.
“Allah yayi miki albarka Meymey na, Ubangijin talikai ya baki yaran da zasuyi Miki biyayya kamar yadda kikayi min”.
Cikin jin daɗi da ƙara kifar da tunanin iyayen nata tace.
“Amin ya Allah Daddy ni ka gama min komai da kayi min zaɓi da miji irin Yah Afif, miji mahaddacin Alkur'ani.”
Cikin tsare fuskarta da ido Mommynta ta zuba mata ido dan san gano gsky ɗiyar tata, domin tafi kowa sanin makircin Meymey kuma sam bata gamsu da sauyinta ba, duk da dama bata taɓa fitowa ta nunawa mahaifin nata cewa bata son Taj ba, sai dai ita Mommy tana ganota.
“Uhmmm Allah yasa da gaskene har ranki Meymey, domin iya gatan duniya dai mahaifinki yayi Miki da ya zaɓa miki Taj a matsayin miji”.
Cikin kwaɓe fuska tace.
“Mommy ai Yah Afif ya canci ko wacce mace ta soshi,
Shi yasa nake alfaharin kasancewarsa mijina”.
“Hhmmmm”. Shine kaɗai abinda Mommy tace.
Dai-dai lokacin kuma Laylah ta dawo daga school, da sauri ta isa gaban Mommyn domin tana nuna mata so sosai, kana Meymey tun randa Taj ya tafi ta sauya sosai take jan Laylah a jiki, kasancewarta marainiya mai sanyin hankali da neman makusanta masu meye mata gurbin iyayenta da danginta data rasa yasa, tuni ta saki jiki da Meymey.
Cikin kulawa haɗi
da nuna bayyanenne so da jinƙai Meymey ta buɗewa Laylah hannun da sassarfa ta faɗa jikinta suka ruggume juna.
“Baby Laylah kin dawo, gidan ba daɗi da kika tafi , Saida su Mommy suka zone naji ɗan daɗi gashi Yah Afif ma, tun ɗazu da ya tafi wurin Malam bai dawo ba”.
Dai-dai lokacin Taj ɗin ya shigo bisa alamu tare suke da Laylah.
“Daddy Barka da zuwa, Mommy yau kene da kanki”.
Taj ya faɗa dai-dai lokacin da ya iso gaban Uncle Jibirin ɗin, cikin so da mutumtaka suka amsa, sai kuma ya juyo cike da mamaki jin Meymey na cewa.
“Sweetheart kamar baka ganniba, saboda kaga Daddy da Mommy ko”.
Ƙanƙantar da idanunsa yayi tare da cusasu cikin nata idanun yana nazartan sauyinta da ya samu tunda ya dawo.
“Hmmmmm”. Yace a ransa a fili kuwa cewa yayi.
“Neman tabarraki nake, kin san Allah da girma iyaye da girma, ka bisu ka dace ka saɓa musu ka taɓe”.
Ya bata mgnar da kurman baƙi da ita yake.
Sai kuma tayi murmushi tare cewa.
“To bari dai in kawo maka ruwa”.
Jim kaɗan ta dawo da goran ruwa mai sanyi tare da cup amsa cup ɗin yayi.
Yana kallon Laylah dake maƙale da Mommy tana cewa.
“Mommy mun kusa zuwa Nigeria nida Uncle Taj, zanje Afirka inga Black peoples, kinsan ana cewa Black is beauti wai sun fimu kyau ko?”.
Da sauri Uncle Jibirin yace.
“Sosai ma kuwa”.
Nan dai suka ɗanyi hira kana su Uncle Jibirin suka sallamesu suka tafi suna sa musu al'barka.
Washe gari Ishmah ce ke draving a hankali saboda Dadeey tace yau so take taga Hajiyarts mahaifiyarta kenan.
Shiyasa Ishmah ta ɗauki Dadeey dan ta kaita wurin mahaifiyarta su kuma kakarsu.
A hankali taƙe ɗan motsa lips inta tana cin gumbar riɗin da robar ke gefe, lunshe idanunta tayi tana jin garɗin riɗin na mata daɗi, jin alamun saƙo ya shigo wayarta ne yasata ɗan duba a fili tace.
“Kai Dadeey kallifa kuɗin da Taj ya turo min har dubu ɗari takwas.”
Cike da mamaki Dadeeynta tace.
“Ikon Allah to na menene haka kuma”.
Tana danna mishi kira tace.
“Bari in tambayeshi”.
Bugu ɗaya ana biyu ya ɗaga dai-dai lokacin da yake fitowa daga side ɗinsa ya nufi babban Parlour da dole ta nan zai fita.
“Taj wannan kuɗinfa na menene?”.
Cikin sanyinsa yace.
“Ki saya waya, ne dan nasan wayarki zata samu matsala”.
Da sauri tace.
“Saboda me”.
Cikin tunano mafi akasarin lukata abubuwa kan farun musu a tare kamar yadda mafi akasarin abubuwan su iri ɗaya ne.
“Saboda wayata ta faɗi ɗazu ta fashe, ko kin manta komai namu a tare yake zuwa”.
Cikin dariya tace.
“To meyasa kayi aure ni banyi ba?”.
Ido ya lumshe tare da cewa.
“Eh Amman kuma ai inada matsaloli akan aurarrakin da kuka cusamin kamar yadda kike da matsala kan aure”.
Cikin sanyi tace.
“Yanzu ina driving in mun isa zan kiraka Dadeey ta gaidaka”.
“Ina amsawa, ina zakije baki nemi izinina ba”.
“Afwan Dadeey zan kai wurin Hajja Ummanta”.
Dai-dai lokacin da ya iso Parlour yace.
“Toh sai anjima”.
Daga nan suka katse kiran.
Suna isa Ishmah nayin parking tayi saurin fitowa dan buɗewa Dadeey ƙofa, da sauri ta riƙe kanta saboda jin tasss wayarta dake kan cinyarta ta faɗi kan intalok ɗin, idanutan ta zubawa wayar ganin yadda screen ɗinta ya fashe yayi ratsa-ratsa.
Taj kuwa cikin mamaki yake kallon Meymey dake zaune bisa kujerar 3 sitter, Laylah na kwance kan kujerar tayi pillow da cinyar Meymey, ita kuwa Meymey tana...
Hmmmm wasanfa na musamman ne ni kaina tsumani yakeyi!
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > [email protected]
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************
[1/8, 5:26 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 8*