Showing 42001 words to 45000 words out of 74955 words

Chapter 15 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

janye Idanunsa daga kan Ishmah ba.
Gefensa Khalid ya matso tare da faɗin.
“Ina kwana Uncle Taj”.
Ahankali ya ɗaura hannunsa kana Khalid still Idanunsa na cikin na Ishmah yace.
“Lafiya lau My Boy ykk?”.
Murmushi Khalid yayi cikin jin daɗin yanda yake kiransa da My Boy tare da cewa.
“Lafiya lau”.
Kana cikin nutsuwa da takun kamala ya cigaba da tafiya.
Ishmah kuwa har zuwa lokacin tana riƙe da hannun Laylah.

Laylah kuwa murmushi tayi tare da cewa.
“Uncle Taj”.
“Na'am Laylah ”.
Ya amsa batare daya iya cire idanunsa daga kan Ishmah ba”.
Cike da farin ciki tace.
“Uncle Taj kalli kayan da Aunty Ishmah ta ɗinka min ya min kyau ko Uncle Taj??”.
Murmushin gefen baki yayi wanda ke sake fitar da ainihin fuskarsa, kanshi ya gyaɗa mata duk da cewa bai kalleta ba amma yace.
“Masha Allah kinyi kyau sosai Laylah Aunty Ishmah ta iya zaɓi ta zaɓawa Laylah kayan daya dace da ita”.
Cikin farin ciki Laylah ta sake kallon kayan da sukayi mata kyau tamkar dan ita aka halicci Les ɗin tare da faɗin.
“Ta ɗin ka min da yawa akwai wasu ma acikin gida”.
Still Idanunsa na cikin na Ishmah ya gyada kai kana yace.
“Ta kyauta mun gode”.
Akuma dai-dai lokacin ya ƙara sa daf da ita kamar zai gogi jikinta har zuwa lokacin sun gaza janye Idanunsu acikin na juna ahankali yake mirza ƙaramar wayarsa dake cikin hannunsa yayin da ɗaya wayar ke maƙale akunnensa.
Kana adaidai lokacin kuma na wayar ke cewa.
”Hello Afif”.
Bisa duk kan alamu murya ce na ɗaya daga cikin Sanannun Malaman mu na nan gida Nigeria ne.
Jujjuya ƙwayar idanunsa yayi kasancewar baki ɗaya hankalin da baya kan wayar sai kuma yaji wayarma ta katse baki ɗaya.
Cirota yayi daga kunnensa ya zura a aljihun gaban rigarsa ƙaramar wayar ya juya kana ya kai wayar kan kumatun Ishmah ya lakata cikin sanyin murya mai haɗe da taushi yace.
“Wannan kallon fa? Duka na menene?”.
Sai alokacin ta saki sanyayyan numfashi tare da lumshe Idanunta na ƴan sekonni kafin ta sake buɗe su akansa kana ta ɗan ja baya tare da cewa.
_“Fatabarakallahu Fii Ahsanul Khaliƙin”_.
Murmushi yayi tare da kallonta sama da ƙasa kana yace.
_“Masha Allah Fatabarakallahu Fii Ahsanul khaliƙin”_.
Kallonsa tayi kana ta kau da kai tana wasa da yatsun hannunta tace.
“Kaga yanda kayan Hausa Fulani suka yi maka kyau ajikinka? zanso in ganka cikin babbar riga, ka kuwa ga yanda kayi kyau Tajjjj?”.
Ta ƙarashe kiran sunansa cikin wani salo na musamman, domin Allah ya sani tana bala'in son sunansa”.
Murmushi yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa yayi kana ya juya ya kalleta tare da faɗin.
“Saboda komai namu iri ɗaya shiyasa kika iya fahimtar collors ɗin da nake so, da Abinda zai karɓeni da kuma abinda zai zauna ajikina, Nayi mamaki sosai jiya da daddare da Adam ya kawo min kayan, nayi ta mamaki da duka kayan sukayi dai-dai da jikina ban matsuba basu min yadda ɗinkunan ƙasarmu sukeyi ba masu faɗi”
Sai kuma ya ɗan fesar da wani irin numfashi mai cike da tarin Manufofi gami da ma'anonin da shi kaɗai ya sani sai kuma Allah. A hankali ya ɗan motsa lips inshi ya cigaba da cewa.
“Nasan cewa baki taɓa tambaya size na ba amma bansan ya akayi kika san size ɗin takalmina ba duk takalman da kika siya min sunyi daidai da ƙafana ban sani ba ko tef kika samu akaro na farko da muka haɗu kika gwada”.
Ɗan ware idanunta tayi tare da sakin murmushi jin abinda yace.

Shi kuwa cikin gaskiya da gaskiya ya cigaba da faɗin.
“Hatta hulunan da kika siya sunyi dai-dai da kaina, hakama Boxers da singlet Why Ishmah ya akayi haka?”.
Da sauri ta janye idanunta daga nashi cike da kunya, haka kawai taji tsikar jikinta na tashi saboda yanda yaja maganar can ƙasan maƙoshi da kuma wani abun da take hangowa cikin ƙwayar idanunsa.
Cikin fesar da numfashi da wani irin yanayi na musamman dake ratsata sassan jikinta aduk sanda taji sautin muryan sa ta narkan da ƙwayar idanunta tace.
“Yadda komanmu ke kasance wa irin ɗaya haka tunanin zuciyar mu ma iri ɗaya may be shitasa na iya fahimtar abinda zai maka dai-dai aranka kuma dama nasani cewa abinda ya min kyau zai maka kyau”.
Kallonta yayi yana mai jin nutsuwarsa na barin jikinsa har ya fara gaza control ɗin kansa, a hankali ya matsa gefenta tare dasa waya ya lakace mata hanci yace.
“Wannan haka yake, kuma in dai in a zaɓine ke ba baya bace in dai kika zaɓi abu, toh abin na musamman ne ba wanda zai iya kushewa”.
Lallausan murmushi ta saki tana mai jin farin cikin yadda ya yabi zaɓinta kana tace.
“Ai kaima na musamman ne shiyasa komai naka ya kasance na musamman”.
Ta ƙarashe Maganar tana nuna masa hanyar dining tare da cewa.
“Bismillah Taj kana son kabar kanka da yunwa kalan ka koma Ummey tace shalelenta ya rame a Nigeria”.
Ɗan ware idanunsa yayi kana yace.
“Saboda me?”.
Agogon hannunta ta duba kana ta langwaɓar da kanta tare da cewa.
“Ganifa kusan 11:00 Am bakayi breakfasts ba gashi har na haɗama lunch”.
Ta ƙarashe Maganar tana taka kan step ɗin dining area yayin da yake biye da ita.

Yaran kuwa a tsakiyar falon suka zabe suna kallon hotuna awayar Ishmah dake hannun Laylah.

Taj kuwa cikin lumshe Idanu yace.
“Wa yace Miki banci abinci ba? Tun da muka dawo daga Masallaci Sallar Asbah Abba ya kaini Falonsa ke kina can kina bacci nasha tea tare da Abba sannan kuma naci gashi mai ɗumi bana tare da yunwa shiyasa”.
Ɗan ware idanunta tayi tana Murmushi shi kuwa cikin jin daɗin kulawar da take basa ya cigaba da cewa.
“Naje mun gaisa da Hajja Umma kina can kina bacci zasu ta dake nace su barki kiyi baccinki”.
Murmushi tayi kana tace.
“Uyummm Sai karfe goma na tashi nace bari na maka ɗan abu mai sauƙi. Kaci abincin da nayi maka da hannuna”.
Sanyayyan numfashi ya fesar tare da faɗin.
“Masha Allah Nagode sosai kuwa”.
Ya ƙareshe maganar yana zama akan dining.
Kana itama ta zauna tare da buɗe Warmers ɗin dake farko wanda ɗauke da Gashin kifi tarwaɗane da yaji Vegetables aka zagayesa da source sai kuma Cous-cous da tayi Jollof ɗin sa wanda shima yaji Vegetables a plate ta zuba kana tasa ka masa kifi agefe spoon tasa tare da janyo Mug ta haɗa masa tea ta ajiye gefensa tana mai sakar masa guntun Murmushi dake nuna har lau ƙuncin zuciyar rashin mahaifiyarta na tare da ita, sai danneshi da takeyin da tawakalli tace.
“Taj Bismillah”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh matso muci”.
Kai ta girgiza tana gyara zaman Flaks ɗin tace.
“Aini naci nawa kaine nake muradin inga kaci”.
Ta ƙare maganar cikin yin ƙasa da idanutan sabida ganin wani irin kallon da yake binta dashi, kallon da ta gaza fahimtar na menene.
Shi kuwa Taj cikin sanyi ya motsa lips inshi yace.
“Ok”.
Ya faɗa tare da ɗan matsowa alamar zai fara ci sai kuma ya kalleta jin tana cewa.
“Dawa kake yin waya?”.
Idanu ya jujjuya kana yace.
“Ina waya da Sheiky Isa Ali Pantami”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Masha Allah kace da Manyan Mutane kake waya”.
Yana kai spoon ɗin bakinsa yace.
“Eh saboda munyi dashi idan na zo zamu haɗu sannan zan wuce Maiduguri akwai masallacin juma'a da nayi musu al'ƙwarin zan limamcemu sallan jumma'a, sannan kuma zanje Zamfara akwai masallacin da zan buɗe nayi musu alƙwarin za'a buɗe dani, yanzu kuma Sheykh yace zamuje Kano da Bauchi tare dashi”.
Da sauri ta zare idanunta sai kuma ta langwaɓar da kanta tace.
“Toh rabuwa biyu zakayi?”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Baxan rabu biyu ba amma dole zan bawa ɗaya daga ciki haƙuri zanje na Borno jumma'ar nan, sannan kuma na Zamfara zanje in jasu Khamsus Salawat na rana ɗaya daga nan in wuce Kano nan zanmuyi zama da su Sheykh Aminu Daurawa”.
Rau-rau da Idanunta tayi kana tace.
“Kenan tafiya zakayi?”.
Kallonta yayi tare da langwaɓar da kansa kana ya zura mata idanunsa yana mai jin wani abu na dukan zuciyarsa murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Bakyaso in tafi ne?”.
Numfashi taja kana ta langwaɓar da kanta ta zuba masa Idanu batare da tace komai ba.
Cikin tausasa murya yace.
“Baki ban amsa ba bakyaso in tafi ne?”.
Still shiru tayi amma aranta da zuciyarta tana jin kamar shine farin cikinta ganinsa ya sanyata cikin maɗaukakin farin cikin wanda ya gusar mata da kaso 70 cikin 100 na damuwarta tana ji kamar su dawwama ahaka kai ta girgiza alamar ba haka bane.

Cikin fesar da numfashi ya janye idanunsa acikin nata tare da faɗin.
“Kuma zanje Abuja zamu haɗu da Shugaban izala na ƙasa baki ɗaya”.
Ahankali ta saki nannauyan numfashi kana tace.
“Hmmm?”.
Shi kuwa Taj a hankali ya kai tsokar kifin dake haɗe da Vegetables da ɗan Arish bakinsa, lumshe idanunsa yayi tare da buɗesu a lokaci guda, saboda ɗanɗanon girkin daya game mishi baki.
Hannunsa na hagu ya ɗan dungule tare da yi mata alamar jinjina ya haɗe babbar yatsarsa da manuniya.
“Masha Allah Ashe Boɗɗi Daddy ta iya girki ovar kinci in baki 99.”

Murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
“Nagode”.
Sai kuma ta ɗan kwaɓe fuska tare da cewa.
“Uhmmm”.
Yana shafa yalwataccen sajensa dake ƙyalli yace.
“Menenr faɗi mana”.
Kanta ta sunkuyar ƙasa sai kuma ta ɗago ahankali tace.
“Ai dai wannan lokaci nane zuwanmu ne kayi ko?”.
Kai ya gyaɗa cikin tabbarwa yace.
“Eh zuwanki ne albarkacinki sukaci kuma Al'farman abinda suka nema yana da nauyi bazan iya ƙin yi musu ba saboda manyan mutanene masu daraja, Amman duk da haka in bakya son inje sai mu basu haƙuri ko”.
Kai ta gyaɗa tana mai jin wani irin abu da yafi kama da kewa tace.
“A'a kaje”.

“Yauwa Bestie haka nake son ji”.
Ya faɗi yana mai ci gaba da cin abincin tare da ɗan kurban tea ɗin.

Cikin sauri tace.
“Amman ai zaka dawo ta nan kafin ka tafi ko”.
Yana ajiye mug ɗin tea ɗin yace.
“Ba dole ba, ai dole in dawo nan, sai randa zan bar ƙasar zanbi jirgin safe in koma Abuja, da dare mu tashi”.
Cikin sanyi tace.
“To Allah ya yarda”.
Amin yace tare da gyara zaman yace.
“Jiya da daddare bayan munyi Sallar Isha'i mun dawo falon Abba Ummeyna da Yah Abana da Addawa duk sun gaisa dasu Abba da Yah Muhammad har Khadijah da Hafsat ke kina bacci yanzu bari na kira su ku gaisa”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Toh ba laifi amma yanzu dai ka karasa cin abinci tukunna”.
Kallonta yayi kana ya ida zaro wayar daga aljihunsa yace.
“Um bari na kirata tukunna kuna wayar ina cin abinci”.
Kai ta gyaɗa kana shikuma ya kira Ummey tana ɗagawa tace.
“Ya dai Babana ya Nigeria?”.
Cikin nutsuwa da girmama wa yace.
“Alhamdulillah Ummey Nigeria akwai daɗi”.

“Masha Allah ina Ishmah”.
Kallon Ishmah da itama shi take kallo yayi kana yace.
“Gata nan ma bari in bata ku gaisa”.
Ummey na gyara zaman wayar akunnenta tace.
“Toh bari in mun gaisa in bawa Malam su gaisa dan muna tare”.
“Ok toh shikenan” ya faɗa yana bawa Ishmah wayar amsa tayi kana suka gaisa cikin mutumtaka da nutsuwa tace.
“Ummey ina kwana”.
Cikin jin tausayinta Ummey tace.
“Lafiya lau Mamana ya ƙarin haƙuri?”.
Idanunta na kan dining ɗin tace.
“Alhamdulillah haƙuri ya zama dole”.
“Toh Allah yajiƙanta da Rahama ga Malam”.
Amsa malam tayi kana yace.
“Aysha”.
Cikin nutsuwa ta risinar da kanta tare da cewa.
“Na'am Yah Abana ina kwana”.
Amsawa yayi yana mai jin daɗin sunan data kirashi dashi sunan da kenan daga Taj sai ita kaɗai ke kiransa dashi amsawa yayi cikin kulawa, kana yayi wa Dadaynta addu'oi masu yawa wanda yasa taji nitsuwa kana bayan ya gama ta miƙawa Taj wayar amsa yayi yana kai Spoon ɗin daya ɗebo Cous-cous da kifi bakinsa yace.
“Yah Abanaaa”.
Ya ida maganar cikin tsananin so da shaƙuwa.
Murmushi Malam yayi kana yace.
“Ya dai Babana mai ka samu kake ci haka?”.
Murmushi yayi tare da kallon Ishmah yace.
“Ina cin girkin Ishmah ne fa Yah Abana”.
Kai malam ya jinjina tare da faɗin.
“Masha Allah aci abinci sannan ka kula da kanka kaji?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Toh Yah Abana”.
Daga nan sukayi sallama ya kira Addawa ya bata Addawa na amsawa tace.
“Ishmah”.
Lumshe ido Ishmah tayi cike da son Addawa da kuma rigimarta tace.
“Na'am Addawa”.
Cike da mutumtaka suka gaisa kana tayi mata ta'aziyya sukayi sallama.

Taj kuwa abinci ya cigaba daci bayan ya gama sukayi hira har kusan Azahar kafin ta fita.

Washe gari ranan Alhamis akayi sadakan bakwai kasancewar ana amfani ne da yini na rasuwar yasa akayi sadakan a yau ɗin.

Da daddare zaune suke a falon Daddy Taj ya kalli Ishmah tare da cewa.
“In sha Allahu gobe zan wuce Maiduguri”.
Idanunta ta lumshe kana ta buɗe su tace.
“Maiduguri fa?,nina ma manta fa Taj”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Eh akwai jirgin da zai tashi daga Yola zai wuce Maiduguri ya ɗauki Passingers ɗin Abuja, a Maiduguri kafin su Wuce Abuja so Ni kuma zan bi wannan sai in sauƙa a Maiduguri ”.
Cikin gamsuwa tace.
“Allah Ubangiji ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya amma ai baza ka daɗe ba?”.
Kai ya gyaɗa kana yace.
“Eh in Sha Allahu in na daɗe ɗin ne inyi kwana huɗu in dawo”.
Da sauri tace.
“Har kwana huɗu?”.
Yana kallon Rahma dake ajiye masu womers a gansu yace.
“To ai tagiyarce da yawa daga Birnon zan wuce Zamfara, sai in dawo Kano daga Kano kuma zamu wuce Bauchi daga can sai mu koma Abuja muyi zaman, muna gama zaman kuma zan dawo nan, kafin mu wuce”.
Sai muka ya kalli Laylah da Minat dake shigowa yace....


*WOHOHO IN KAJI ANA ƘI GUDU TABBAS SA GUDU NE BEZO BA*

_Ina kuke Ma'aurata masu sha'awar ganin sun zama taurari kuma fitilu a idanun mazajensu Uwar gida,Amarya,Tsakar gida,hadda tan kaɗen gida Shararriya kuma ƙasaitacciya data saba kawo muku nau'ikan sirrin sahihan magungunan ma'aurata wato *AYSHA ALIYU GARKUWA* Garkuwar Marubuta ayau ma ta dawo muku da Ingantattun magungunan mata masu kyau da inganci domin gyara kanki ki zamto tauraruwa a idanun mijinki...Muna da Ingantattun Abubuwa kamar haka_ :_Munada Garin mallaka, garin maɗi, garin Hakkin mayi, garin ɓelɗamhi Garin ilanwaddihi, Gumbar da ba'a baiwa mai kishiya, Gumbar kolli mai kellin al'khairi, Gumbar Riɗi wato 3 in 1, Gumbar makwaranyi, Masin Maliƙi mai masifar ƙarfi da matse mace, ka masin Daɗi har Maɗigan Akwai, kwanon ƙasaitacciyar mace mai masifar kyau da ratsa jiki da samar da inƙantacciyar ni'ima yanada abubuwa masu kyau haɗinsa, Zumar goron tula mai masifar kyau, tsumin dabino, mai ratsa jiki, tsumin Riɗi mai ƙarfi, Furar Mata mai tsastsafo da ni'imantaccen damshi, Cida kaza, Ciccibi Abodi, Tsumin Ɓaure, tuwon ɓauren, kana akwai maganin sanyi sadidan, da dai sauransu...Se kuma fannin ƙamshi kasance da Shu'umin ƙamshi wanda ze gigita ƙwaƙwalwar Oga tare da jin ko wacce mace bata kaiba...._ _Shin ko kina da labarin Miskilinci da ƙasaitar Rayyan Naaan amma lokaci ɗaya ya zamto zautacce sakali akan soyayyar Jannart bakomai Jannart ta riƙe ba face sirrinkan gyara da kuma shu'uman humran da kulaccar sirri na Aysha Aliyu Garkuwa(Tubali) tabbas taga tasirin haka domin Naanunta ya zame mata tamkar bawa_
_Shin ko kinsan sihirtaccen haɗin da Aysha ke sha kenan ta zamto tauraruwa a idanun Hamma Yusuf(Miwasmiti)...Tabbas Mahmud ya zamto zautacce kuma makaho akan sauyayyar Bazawara wato khadijarsa duk da kuwa gashi da budurwa(Namiji Baya Kaɗan) ko kinsan hakan nada alaƙa da amfani da sahihan maganin da kuma shu'uman humran Aysha Aliyu Garkuwa??.Nasan ba zaka ku manta da irin kima da kuma darajar da Aysha ke dashi acikin Idanun Sheik Jabeer ɗin ta duk da kuwa shekaru sunja anma jinta yake tamkar budurwa 'yar sha bakwai(Garkuwa) sirrin hakan na tare da Ingantattun kuma sahihan magungunan Aysha Aliyu Garkuwa Wato Garkuwar Marubuta da kuma Ma'aurata na tabbata kunsan da cewa basirarta ba'a iya rubutun littafi ya tsaya ba hadda inganta rayuwar ma'aurata ta hanyar kawo musu Nagartattun abubuwa Ga duk wacce ta shirya saya seta tuntuɓi number ta 08069423567 muna iya tura kayan mu aduk inda kuke afaɗin Nigeria harma da ƙetare Dan Allah 'yar uwa idan baki shirya siyaba kada kiyi min magana muɓatawa kanmu lokaci...._



🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🥰😘sai.kunzo. sayan na gari maida kuɗi gida,



NA
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/10, 3:23 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK ONE PAGE 10*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*LITTAFIN INDA RAI NA KUƊINE, 1k ne cal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853278, ku kuma mutane Niger 1000fc jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076, ku biya mu tafi tare domin mun kusa gama free pages*

Tsaya-tsaya fa kiji yar uwa.
Zuwa yanzu na gama nazari da fahimtar ƙorafe-ƙorafen wasu daga cikinmu mata da kan zomin da kukansu ire-iren haka👉.

Garkuwa mijina baida kuzari!
Garkuwa mijina yana fin sati biyu ko uku bai buƙaceni ba!.
Garkuwa mijina baya gamsar dani in an fara 2 minute yakeyi.
A'a Garkuwa wlh abin oga yana ƙanƙancewa.

To ku taho ku kuma yi shiru.
In sha Allah, da yardar Allah da kuma izininsa da faɗinsa bai sauƙi ko wanne ciwoba Saida ya sauƙi maganin cutar, sai dai in ba'a ganoshi ba.
Yar uwa kizo da yaƙini da yarda in Sha Allahu kukanki ya ƙare.
Domin akwai haɗin maganin maza.
Na basir da sanyi.
Domin mafi akasari matsala biyun nanne ke sasu wannan matsalar.
Bayan maganin matsalar kuma, akwai zazzafan haɗin maza.
Mai magance matsalar ƙanƙancewar gaba, mai ƙara masa kuzari, da girma, gami da iya juriyar daɗewa lokacin raya sunna, da samawa iyali gamsuwar da zata ƙara zaman lfy da inganta farin cikin dararen ma'aurata.
Akwai maganin na gargajiya da kuma na Bappa Nasara...


“Laylah najin daɗin garin nan fa, ita cewa ma tayi wai in koma in bar mata ke”.
Murmushin tayi tare da ruggume Laylah data faɗa jinkinta.
Cikin sanyi ta ɗan lumshe Idanunta tare da cewa.
“Toh Allah ya kaika lfy y dawo da kai lfy ni ina nan tare da Laylah na”.
Ameen ya amsa. Yana mai kallon Minat da saboda kamar ta da Ishmah yasa yake jinta har ransa.

Washe gari da Asbah can cikin bacci Ishmah ta fara jiyo sanyayyan sautin muryan sa na ratsa dodon kunnenta daga Masallacin ƙofar gidansu yana karanta Suratul Juma'a.
Cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login