Showing 24001 words to 27000 words out of 74955 words
Chapter 9 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
bibiyar comments ɗin, abin al'ajabi naje naci karo da wacce tafi na yar Bangaladash ƙwazo, itama gabatar da kanta ta farayi kana tace ita yar.
Jordan ce, tace tunda take a duniya bata taɓa jin son wani ɗan Adam da muryarshi ba, kamar takaba, tace, ita indai zaka aureta, ta yafe maka sadaki, ka bata haddar Suratul Yusuf da Nisa'i da baƙara, da Khaff sune madadin sadakinta”.
Sai kuma ta sauƙe numfashi tare da ɗan tsagaita wa tana ƴar dariya mai sautin, da yasa Taj jin wani irin yam tsikar jikinsa na amsa amon amintaccen sautinta.
Wani irin narkewa yaji jikinsa nayi lokacin da yaji tana cewa.
“Nice a raina nace, Ni dai na sani, duk faɗin duniyar nan, babu wanda ya kaini jin daɗin muryarka, kasan duk yadda sautin karatunka da muryarka ke sasu nitsuwa basu kainiba”.
A hankali ya buɗe ƴan lips inshi, murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Harda Muryar Dr Nafi'u Kabir Katsina, bata kai miki tawa ba”.
Cikin ƙwaɓe fuska tace.
“Rabani da muryar ba katsinennan, shi sai saurin fushi”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso ƙofar gidansu, dake Airport roud.
A hankali ta dannan hon, cikin sauri, Baba isa ya buɗe mata Gate ɗin,.
Bayan tayi parking ne, tace.
“Alhamdulillah mun iso, sai anjima zamuyi waya, in gayama sauran comments ɗin”.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
“Ok sai kun shiga zan kira ki haɗani da Dadeey”.
Daga nan suka katse kiran a tare.
Ajiyan zuciya mai nauyi Aunty Hauwa ta sauƙe, tare ɗan dafa kafaɗar Ishmah cike da yaƙini tace.
“Ishmah kuyi aure mana ke da Taj.”
Cikin tsananin mamaki da yafi kama da tsoro Ishmah ta zazzaro manyan idanunta tare da dafe hannun a ƙirji kana tace.
“Aure Aunty Hauwa kuma aurenma da Taj, ya Salam”.
Cikin yin mgnar gsky da gsky Auntu Hauwa tace.
“Yess Ishmah kuyi aure da Taj.
Domin kun dace da juna, kamar dan juna Allah ya halicceku, kuma kuna son juna, irin son nan da ɗaya zai iya sadaukar da farin cikin sa ga ɗan uwansa”.
Da sauri ta fara jujjuya kai cikin iyakar gskyar zuciyarta da ƙwaƙwalwarta tace.
“Aunty Hauwa wlh ba soyayya mukeyi da Taj ba, ba wannan mgnar a tsakaninmu, Taj his my best friend, Taj ya zame min tamkar ɗan uwana na jini, Taj abokin hiranane, abokin shawarata, aminina, abokin kukana, Aunty Hauwa ba wannan mgnar wlh”.
Taɓe fuska Aunty Hauwa tayi tare da cewa.
“Yaro dai yaro ne, wato Ishmah har yanzu baki girma ba,
Wai tsakanin ki da Taj kike cewa ba so, to in ko hakane babu wasu masoya a duniya kenan, inma haka kuke gani to ki sauya tunani, domin inma ke haka kika ɗauka shi ba haka yake a garesa ba”.
Ƴar murmushi Ishmah tayi domin bata mantaba Garkuwa ma haka tace mata.
Haka kuma Aunty Maryam ma tace mata, matar yayanta Abubakar kuma ƙanwar Barrister Kamal.
Cikin son fahimtar da Aunty Hauwa tace.
“Shifa Taj yanzu haka matansa biyu, kin manta ɗazu muna tafiya nake baki labarin yadda aka ɗaura masa aure jiya, ga kuma wacce mahaifinsa ya aura masa wata shida baya”.
Dai-dai lokacin suka iso tsakiyar gidan, suna haura barandar Aunty Hauwa tace.
“Yess kin gaya min kuma na fahimci aurenma ya yarda an ɗaura da shine saboda ke, saboda tsaida kukanki ya amince da auren, ni kuma na gaya miki Taj na sonki, kuma zamu gani in muna raye”.
Tana tura ƙofar Parlour Dadeeynta tace.
“Nida ga Dr Nafi'u na nan,”.
Sai kuma tayi saurin ƙarasawa cikin Parlour tare da zazzaro idanu...
A can Ethiopia kuwa, yana katse kiran Addawa ta kafeshi da idanun, kanshi ya kauda gefe tare da ajiye wayar gefen Laylah da tuni ta ɓingire tayi bacci, da sauri ya juyi ya kalli Addawa jin tana cewa.
“Afif ka auri Ishmah itace zata baka dukkan farin cikin rayuwa duniya domin itace muradin zuciyarka.
Ka aureta ka haɗa da Meymey in ma, Meymey bata kyautata makaba a wurin Ishmah zaka samu dukkan kulawa, domin kana sonta tana sonka!”.
Tunda ta fara mgnar yaji bugun zuciyarsa ta tsaya cak,
ya gaza koda ƙefta idanunsa, Saida yaji ta dire ayane, yana wani irin fitinenne numfashi da ya maƙale mishi cikin maƙoshinsa tare da fizgo mgnar.
“ni nace Miki, ina sonta? Ni nace Miki aurenta nake nema”.
Murmushin girma Addawa tayi, domin tasan Taj da zurfin ciki da haƙuri gami da juriya da iya sarrafa zuciyarsa, saidai kash duk da wannan zurfin cikin karo na farko kenan a rayuwarsa da idanunsa ke kasa tayashi ɓoye sirrin zuciyarsa, sai jin abinda kakar tashi ta faɗane ya sashi juya idanunsa tare da binne abinda Addawa ke son haƙaitowa, ya lulluɓeshi da zurfin cikinsa kana yace.
“ishmah aminiyatace mai cikekken aminci, bayan Irfan Imran, da Dr Abbas da Dr Amdaz ban taɓa wasu abokai a duniya ba, sai Ishmah, saura wata ɗayama aurenta da wani babban Dr da take aiki a hospital inshi Dr Nafi'u, so ki rinƙa sanin abinda zaki ke nazarta kan mutane, Ni ba komai tsakanina da ita sai aminci”.
Ya ƙarashe mgnar yana mgnar zuci.
“Wai toma ni, ta ina ake fara cewa mace ana sonta, ta yaya ake iya faɗar?”.
Kuwa Addawa kai ta jinjina tare da cewa.
“Uhmmmmm”. Sai kuma ta miƙe ta shiga kitchen ɗinta domin ta sani muddin tasa Zulaihat ƴar ƙaninta, ta kawo mishi wani abu to bazaici komai ba.
Haka yasa ta ɗauko mai gashin da tayi kishi, tare da fruits.
Nigeria
Cike da tsananin jin daɗi Ishmah ta rungume Dadeey data samu zaune a tsakiyar ƙanennenta.
Da kuma ƴaƴanta cikin murmushi itama ta ruggume Ishmah tare da cewa.
“Allah sarki Boɗɗi na, kina can kina yawon nemo min magani ko, Kinga kafin ki dawo Allah ya sauƙaƙamin”.
Murmushin mai tafe da hawaye tayi tare da kallon Aunty Hauwa da ita ta ruggumeta ta gefe, sai kuma ta juya ta kalli Ummominta wanda sun kai 7 duk ƙannen Dadeey ce, sai ɗaya ce yayarta.
Sai kuma Uncle Ali da Uncle Nasir wanda shine ɗan farinsu sai Hajia Aysha da ita ke binshi, sai kuma Dadeey ita kuma Aunty Hauwa ke Binta, saura dai kab ƙannen Dadeey ne, jin jinkinta ya tashi ne yasa, duk suka zo harda ƴaƴansu aurarru.
Sai kuma ta kalli gefen ɗaya kuma ƴaƴanta babban dan farin Dadeey kenan Yah Muhammad, sai Yah Abubakar, sai kuma, sai Khadijah ƙanwarta mai Binta wacce a Gombe take aure, sai Adam kana Hafsat sai Hamisu sai kuma autarsu Rahama duk sunyi zobe sun sa Dadeey a tsakiya, kowa da irin kulawar da yake bata.
Uncle Nasir ne ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
“Ishmah babu abinda zamu ce miki sai dai muce Allah ya baki ladan jinyar mahaifiyar ki, mu kuma ƴar uwarmu, tare da yin fatan Allah ya baki mijin aure na alkhairi mai riƙeki da amana da gskya da tausayawa”.
Cikin sanyi tace.
“Amin Yah Allah Uncle Nasir, sai kuma duk sauran umomin nata suka sukayi ta mata addu'a.
Ƴah Muhammad ɗinta kuwa cikin sanyin murya cike da rauni yace.
“Dan rashin auren Ishmah shine ƙololuwar damuwata, sai yanzu na fahimci cewa rashin auren nata ya zama dalilin samun nitsuwarmu wurin jinyar Dadeey domin da ace tana da aure da wuya mijinta ya barta tayi wannan watannin ko ince shakaru a gida da sunan tana jinyar mahaifiyar mu, Amman gashi yanzu ko su Khadijah mata ba sai tazoba, bare mu maza.”
Kai kawai ta sunkuyar tare da fara fito da magungunan Dadeey tana shafa mata a sawunta da hannunta.
Da sauri Rahma ta amsa tare da cewa.
“Yau dai tunda munzo bari mu karɓeki muma mu samu ladan.”
Hajia Aisha kuwa yayar Dadeey fruits take ta bata tana ci suna hira.
Da sauri Ishmah ta amsa kiran Taj da ya shigo, tare da cewa.
“Taj jikin Dadeey da sauƙi sosai, gata muna hira”.
Cikin jin daɗi yace.
“Bata waya”.
Ya faɗa yana kallon yadda Abu Hashim draving ji yake kamar ya amshi tuƙin.
Amsa Dadeey tayi tare da cewa.
“Assalamu Alaikum Tajuddeen”.
Cikin girmamawa yace.
“Na'am Dadeey'nmu ya jiki?”.
Tana ɗan gyara zamanta tace.
“Alhamdulillah Tajuddeen jiki da sauƙi, sosai ma yanzu kam banjin komai ma, sai mutumiyar ka da idonta ke kumbure yayi jazir saboda kuka, dan Allah kayi mata nasiha tasan cewa fa, al'ƙwarin Ubangiji tabbatacce ne, kukantan nan bazai hana komai ba, ta koyi juriya, itace fa babba a mata, kaga daga wurinta ya kamata ƙannenta su samu ƙarfin guiwa, Amman da zaran jikina ya tashi sai tayi ta kuka”.
Cikin sanyi yace.
“In sha Allah zan yi mata mgna Dadeey kuma zata daina.
Allah ya ƙara Miki lfy mai amfani”.
Murmushi jin daɗi tayi tare da cewa.
“Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati, Tajuddeen ngd matuƙa, Allah yayi muku albarka, ka rinƙa ƙarfafa mata guiwa ka hanata kuka”.
Cikin jin daɗi yace.
“Amin Yah Allah”.
Ya ƙare maganar da tare da nufar gidansu.
Abu Hashim nayin parking Laylah tayi cikin gida shi kuwa masallacin ya wuce saboda la'asar tayi.
Bayan sun idar da salla sun dawo cikin gida.
Zaune yake gaban Malam tare da fara yi mishi masaj, cikin kula so Malam yace.
“Kafa san in baka gari burinka kake, cikiwa wato aikin pilot, in kuma kana gari inajin dadin inji kana TAJMUH Hospital, kana cika min nawa burin na zamanka cikekken likita, domin tun a kan Hafiz nake da burin ɗana ya zama likita Amman haka bai samuba, hakama Yusuf da sulaiman da Abduraham dukkansu dai sai a kanka Allah ya cikan burina.”
Cike da tsananin girmamawa da tarin irin biyayyarnan da kansa son ɗa ya fifita a zuciyar iyayensa sama da ƴan uwansa yace.
“In sha Allah ranar Monday A Tajmuh hospital zan wuni”.
Dai-dai lokacin Mom Amal da Aryan suka shigo,
Wani mugun kallo Aryan ke bin Taj dashi saboda ganin yadda Malam ya wani haɗa kansa da na Taj ɗin har kamar zai kai bakinsa kan kunnen Taj.
Mom kuwa cikin iya makirci tace.
“Babanmu na kanmu Afif dottijon mai halin daddataku, kaine karaminsu kaine kuma babbansu.
Tunda kai ne uban masu gida”.
Ido ya ɗan ɗago tare da ɗan kallonta a fakaice, sai kuma yace.
“Barka da yamma Mom”.
Fuska cike da dariyar baka bana zuci ba tace.
“Alhamdulillah Afif ya surkarmu”.
A takaice yace.
“Alhamdulillah”.
Shi kuwa Malam hannunsa ya miƙa ya kamo na Aryan tare da cewa.
“Matso kusa dani mana”.
Kwaɓe fuska yayi kana ya ɗan zauna kusa dashi.
Nan dai suka kasa suka tsare.
Ganin haka yasa ya ɗan kalli Malam tare tausasa murya yace.
“Yah Abana”.
Murmushin jin daɗi sunan da Taj ɗin kaɗai ke kiransa da sunan a duniya yayi kana yace.
“Na'am Abbana zaka tafi wurin Ummeynka ko”.
Kai ya gyaɗa mishi cikin alamun neman izini.
Kanshi ya ɗan shafa kana yace.
“To ka gaida min Meymey in ka koma ko Abbana”.
Cikin sanyi yace.
“In sha Allah”.
Daga nan ya fito.
Cike da kulawa Ummey ke ce mishi.
“Babana yaushe ne zakayi tafiya, ko ka ɗan samu hutune?”.
Kai ya ɗan jujjuya alamun a'a, ganin yadda ta tsareshi da ido alamun neman ƙarin bayani ne ya sashi ɗan motsa lips inshi a hankali yace.
“Next week ma, zan wuce Mexico City amman kwana ɗaya zamuyi acan zan wuce Istanbul to acan kuma kwana biyu zamuyi zan juyo da Passingers ɗin mu na Ethiopia”.
Cikin jinjina zirga-zirga da yake sha tace.
“Allah ya baka Sa'a ya kaiku lfy ya dawo mana daku lfy”.
“Amin ya Allah Yah Ummeyna”.
Ya amsa cike da alamun zazzafan shaƙuwarson uwa da ɗanta.
Sai kuma suka kalli Zakiya data zauna gefenshi tare da cewa.
“Dan Uncle Taj yanzu ƙasashe nawa kaje a duniyar nan?”.
Kanshi ya ɗan jujjuya mata, alamun shima bai san adadin su ba.
Sai kuma ya ɗan kishingiɗa jikin kujerar tare da ɗaura kansa bisan cinyar Ummeynshi lokaci ɗaya kuwa bacci yayi awon gaba dashi dan, jiya da dare bai samu isasshen baccinba.
Zakiya kuwa hannun Laylah taja tare da cewa.
“Mu tafi Saloon, dan na lura Uncle Taj shine auta ba niba”.
Ita dai Ummey murmushi kawai tayi.
Fahimtar baiyi baccin ba yasa tai ta shafa kansa, dan ta fahimci yana da damuwa zurfin ciki ya hanasa bayyana dama kuwa ta sani bazai bayyana ɗinba.
A can gidansa kuwa, Meymey ce, kwance bisa gadon ta, riƙe da wayarta tana mgna da Dr Zakariyya cikin ƙarfafamishi guiwa tace.
“Zamuyi fa, komai zai tafi dai-dai kada ka tsorita, bazai taɓa fitowa yayi inkarin wanke kanshi ba, kuma in ma yayi inkari ai muna da manyan hujjojin da zamu kafa”.
Cikin shakku Dr Zakariyya yace.
“Hummm kinfa san shima Doctor ne daya fini, matakin sanima, tunda shi a ƙarƙashin sa ma, likitoci sama da 8 ke aiki a Hospital inshi”.
Da sauri tace.
“Kada ka damu”. Daga nan taci gaba da ɗaurashi bisa hanyar.
Gab da Magrib Halima da taje gidan Rashida ta dawo, cikin mamaki tace.
“Kai Ummey harda zama ki nitsu yana wani bacci a jikinki, ina matarsa da zai zo ya ɗale mana cinyar uwa”.
Da sauri Ummey tace.
“Toh ai uwar tasa ce shi kaɗai, ku kam duk na bawa Addawa na ku”.
Dariyar Halima ne ta tashesa, kuma dai-dai lokacin aka kira sallan Magrib.
Bayan an idar da sallan, Isha a nan a Parlour Ummey sukayi Dinner shida Laylah kana suka koma gida.
A Parlour ya sameta zaune tana waya da Abbanta Uncle Jibirin kenan ya fahimci haka ne jin tana cewa.
“Eh Abba na lfy Lau muke, gashi ma yanzu ya dawo gidan, Ummey ya tafi ya barni gidan shiru, gashi in baya nan gidan ba daɗi”.
sai kuma ta nufoshi tare da cewa.
“My Love ka dawo”.
Ta ƙare faɗin hakan tana hararan gefen TV.
Da sauri Uncle Jibirin ya kashe wayar.
Ita kuwa Murmushi mai cike da makirci tayi, sai kuma tayi saurin sunkuyar da kanta lokacin da ta ɗago da niyan kallonsa, bazata taɓa iya jure ganin kwayar idanunsa ba, domin suna da wani haiba mai sa makirai rusunar da kai, Fuskantar sa Kuma nasa zuciyar makirai karaya.
Ɗakin Laylah ya wuce, bisa gadon ya kwantar da ita, tare da yi mata tofi kana ya rufeta da blanket sannan ya fita ya nufi ɗakinsa.
Ita kuwa Meymey ƙofar Laylah ta zubawa ido tana Murmushin.
Yau Monday tushen aikin.
A hankali Abu Hashim yayi parking cikin harabar wani tamfatsetsen asibiti na gani na alfarmar, irin asibitin nanne mai tsari na alfarmar ba matsin ko cunkoso.
Daga can sama tsololuwa an rubuta.
*TAJMUH CONSOLATION HOSPITAL*
da manyan baƙi.
Harabar asibitin yalwataccen ne parking spaces ɗin nasu, mai faɗi, wanda a ƙalla zai iya ɗaukan motoci 15, zuwa 20 ba tare da wata ta matsi wata, ko ta gogi wataba.
Sai kuma doguwar katanga da tayiwa asibitin garkuwa, yayinda bishiyoyin dogon yaro ke zagaye dashi iyakar ganinka, sai kuma ƙasansu wasu ƴan dagwai-dagwai ɗin bishiyoyin dabino ne guntaye, masu masifar ƴaƴa da ɗan karen zaƙi, gasu ringiz gwanin ban sha'awa.
Sai daga ƙasan farfajiyar kuma, tsirran flowers ne masu ƙamshi ke zagaye da lungu da saƙo.
Daga saman Benin dake fuskantar gate ɗin kuma an rubuta.
Admin Maternity and Surgery block.
Gaba ɗaya fuska wurin marafen Glass ne mai garai-garai wanda zaka iya ganin kanka ras a ciki.
A dai-dai gaban wurin Abu Hashim yayi parking, yayinda Mai gadi da masu bawa flowers ruwa, sai kuma masu cliners dake ƴan share-share da goge-goge wanda tuni sun kammala aiyunkasu domin da dama moppa suke wankewa, masu tura dozbin na turawa.
Da sauri Maigadin ya buɗe masa marfin motar, shi kuwa Abu Hashim fitowa yayi hannunsa riƙe da briefcase ɗin uban gidan nashi, tare da ɗan tsayawa gefen ƙofar, sukayi jim suna jiran fitowarsa.
Yess in da sabo ai sun saba sun san halin sanyinsa.
Yakan iya kai 3 minute zaune a cikin motar duk da yasan sun iso, a da can baya ma, bare yau a kuma cikin yan kwana kin nan.
Dai-dai lokacin kuma a can cikin Reception ɗin nasu, wata Nurse ce ta shiga cikin Pharmacy dinsu, tare da kallon wacce ta samu a ciki, tare da juyawa ta kalli bayanta sai kuma tace.
“Hajara albishirinki dama Dr Taj a cikin hospital nan”.
Cikin rumtse idanunta Hajara ta ɗan ɗaura rafin hannunta bisa ƙirjinta dake, jin yadda Heart ɗinta ke beating so fast, sai kuma ta buɗe idanunta tare da cewa.
“Zuciyata ta rigaki sanarmin”.
Murmushin wacce ta shigo ɗin tayi tare da cewa.
“Wlh kina bani tausayi, sai dai kuma wasu lokutan in naga Dr Taj ko naji Voice ɗinsa nakan ce dole, ƴan mata su rikice su ɗiwauce da sonshi, saboda ya kai a soshi, haibarsa kuma da nagartasa ta isa ta hana ƴan matan sabun damar isar da sonsu, toh suna da suke da aure ai sai dan kariyar Allah da darajar aurene yake hana shaiɗan samun damar farma zuƙatansu.
Da sauri ta fito daga Pharmacy ɗin, ta koma Registry, inda nanne wurin aikinta.
Ita kuwa Hajara ta gyara zamanta tayi, dai-dai lokacin kuma Dr Abbas ya fito daga Consultings room 1, ganinsa yasa duk suka nitsu.
Patients insu wanda a ƙalla sun kai 9 ya kalla tare da yi musu, ya masu jiki.
Kana ya wuce ya nufi hanyar fita.
A bakin ƙofar fita Reception ɗin ya tsaya tare da zuwa aminin nasa idanu yana mai sakin murmushi.
Cikin da nitsuwa ya fito daga cikin motar cikin shigar suit Morning sky color masu masifar kyau, da sheƙi, yayinda long sleeve shirt dake ciki ya ƙara ƙawata shigar tasa, net ɗin dake zagaye da wuyanshi shima maroon color sai ratsin Morning sky, sai kuma Half cover shoe dake saeunsa, na kamfanin Gucci shima maroon color.
Wani irin ni'imtaccen ƙanshin mai masifar daɗi yake bazawa, na turaren kamanin Gucci, intense Oud.
sai ɗan siririn glass farin ƙal, dake manne kam kekkyawar fuskarsa da saje yayi mata ƙawanya, ya ƙara mata haiba da kamala.
Kusan duk a tare Ƙananun ma'aikatan nasa sukayi mishi zobe, suna kwasar gaisuwa kamar yadda ya saba haka ya fara, amsawa yana mai jinjina musu da basu ƙarfin guiwa yake cewa.
“Aikin ku yanayin kyau, manyan ma'aikatana”.
Yayi mgnar da iya kar mutumtaka tare da ɗan jujjuya ƙwayar idanunsa ganin ko ina na cikin Hospital ɗin yayi fes-fes gwanin kyau.
Maigadin ne yace.
“Sir kar Doctors su Doctors inmu suce kana bamu matsayinsu fa”.
Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.
“Matsayin ku ya ɗara na Doctors and Nurse's ai, domin in babu ku a asibitin, ƙazanta zata sa babu Dr da zai yarda yayi aiki anan, bare kuma patients su zo”.
Cikin jin daɗin karramasun da yake yi, suka rinƙa godiya kana suka juya kowa ya koma bakin aikinsa.
Shi kuwa Taj juyawa yayi ya ɗan fuskanci gefen gabas, inda wani tamfatsen gini na musamman yake shimfide daga sama an rubuta Reception. Da manyan baƙi,
Cikin sauƙe numfashi ya nufi ƙofar shigan. Abu Hashim na biye dashi a baya, riƙe da briefcase inashi.
Murmushin mai nuna cikar jin daɗin Dr Abbas yayi tare da cewa...
Ba editing kunsha typing errors.