Showing 21001 words to 24000 words out of 74955 words
Chapter 8 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
sai kuma Ishmah da ita ko muryarshi taji tana iya gane komai tare dashi.
Ajiyan zuciya mai tafe da raunataccen numfashi ta fesar tare da fara mishi addu'a.
“Yah Allah ka shiga lamarin wannan ɗan nawa Tajuddeen, ya Allah kaine ka halicce shi da zurfin ciki, da haƙuri da jurayar da tasa baya iya fuskantar kowa na duniya ya faɗa masa matsalarsa sai kai, mahaliccin mu, Yah Allah ka shiga lamurran sa ka yaye mishi damursa ka bashi sa'a da nasara akan duk wani ƙalubalen rayuwa, yah Allah ka hana hawayensa zuba a inda bashi da mai sharce mishi su”.
Murmushi nan dai na ƙarfin halin yakeyi yana mai amsa addu'o'in da take jere mishi, hakama Rashida da Maryam da yanzu ta shigo.
Hannunshi ya miƙa Ummeeyshi tare da yin musabaha kana ya miƙe tsaye.
“Bari in tafi”.
Tana miƙewa itama tace.
“Toh Laylah fa?”.
Yana mai ɗan taune gefen lip inshi na ƙasa yace.
“Zamu tafi tare?”.
Ya ida mgnar suna fitowa Parlour, dai-dai lokacin kuma Zakiya da Laylah suka shigo, haka yasa suka fita tare.
Suna isa gidan.
Ya wuce side ɗinsa.
Laylah kuwa cikin sanyi ta nufi bedroom ɗin Meymey dan zata isar da saƙon Halima.
Daga bakin ƙofar ta fara jiyo Muryar.
Amal ƙanwar Taj ƴar Hajia Muhibbat, uwar Kabir kenan wanda itama ƴaƴanta duk matansae sai Kabir kaɗai
Cikin neman mafita da kuma saka gadar zaren da suke shiryawa Taj Meymey tace.
“Ai wallahi ko yaƙi Allah sai ya sakeni, ko shine ƙwai sai na sashi ya magantu, kuma zanyi amfani da zurfin cikin nasa, da ya hanasa fitowa ya butulcewa iyayensa lokacin auren harfa wani cemin yayi nimafa ba sonki nakeba.
Kawai kije ke ki butulcewa naki mahaifin nasan in kikace bakya so Malam zai janye”.
Ƙwaffa Amal tayi tare da cewa.
“Bana gaya miki tun lokacin ba, inda Yah Afif ne, wlh bazai taɓa yiwa Malam musuba, ko ya fito da damuwarsa, haka Allah yayisa.
Shi yasa da wannan halin yasa Malam yakeyi mishi wani irin bayyannen son da bai san cewa fuskarsa bata iya ɓoyewa ba, ke Yah Afif duk nacinka da jarabaar neman mgnarka bazaiyi ma kamar yasan kanayi bare ya kulaka, domin da yana kula mutum da tuni shi da Yah Aryan ko mgna bazasuyi ba, domin a fili yah Aryan yake nuna tsananin tsanar da yake yi masa.
Kuma abin mamaki yanzu haka shi ya ɗauki nauyin karatun Arfa, ɗan Yah Aryan wanda pilot yake karanta in kinji milliyoyin da yake kashewa sai ki riƙe baki.
Ya haɗa da Imran ɗan Yah Hafiz, duk shi yake musu komai suna karatu a Mexico”.
Sai kuma ta zuwa Meymey ido jin tana cewa.
“Uhmmm ai bai haɗu da kaidin macce bane, su mazane shi yasa”.
Da sauri Amal tace.
“Kaidin macce kuma ai in kinsan abinda Mom ke shiryawa a kansa tsawon shekaru yana tsallake wa sai kinyi mamaki.
Kawai dai yanzu zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe ne.
Zan gayyato Yah Aryan da Mom a cikin tafiyar.
In sha Allah sai mun tozartashi tozarci mafi muni, sai mun Ƙyamatar dashi a zuciyar Malam sai mun rabashi da wannan soyayyar ta juye ta zama ƙiyeyya, uwarsa kanta da take jin daɗin ɗanta mahaddacine sai ta fara kunyar amsa sunan uwarsa sai tayi nadamar haifarsa”.
Wani makirin murmushin Meymey tayi tare da gyara zamanta suna masu ci gaba saƙa gadar zare.
Laylah da tazo da niyar, isar da sakon Halima na ta cewa Meymey gobe zatazo ta wunin musu.
Jin kalaman da sukeyi ne, yasata tsayawa a bakin ƙofar tamkar an dasata.
Duk da ƙaramcin shekarunta.
Abun ya bugeta, haka nan tsoron Meymey ya ƙara rufeta.
Jin motsinsu alamun zasu fitone yasa tayi saurin fara yin Knocking.
Dai-dai lokacin kuma suka iso bakin ƙofar Amal ce a gaba, ganin Laylah ne yasata ɗan suƙe fuska tare da cewa.
“Lafiya”.
Cikin yin ƙasa da kai ta isar da saƙon Halima, da sauri ta juya da baya saboda tsawar da Meymey ta watsa mata.
“Ke matsa daga nan shegiya ƴar ta'adda ɓacemin daga nan”.
Da sassarfa ta wuce ɗakinta.
Shi kuwa Taj yana shiga al'wala yayi tare zama bisa sallaya, idanunsa ya lumshe tare da fara karanta suratul Khaff.
Sai da ya dire ayar ƙarshe sai kuma, ya saita Camera wayarshi.
Ya karanta aya ta 67-70, ya tura a shafinsa na TikTok
Tare da ɗanyin ɗan guntun rubutu a saman video.
Don't forget to read, suratul Khaff on Friday, Jumma'at Mabrooq to all Muslims Ummah.
A ƙalla yayi kusan stsawon shekara ɗaya da fara hakan, domin tunasar da al'ummar musulmi.
Yanayin Update ɗin video in 5 minutes a ƙalla mutum sama da 1,700 sukayi mishi like, a comment kuma sama da mutum 1000 ne sukeyi, mafi akasari su addu'o'i garesa da jinjina baiwar zazzaƙar muryar da Allah ya bashi.
Follower's kuwa duk ta inda al'ummar musulmi suke a duniya waɗanda ke TikTok ɗin suna biye dashi.
Misalin ƙarfe sha biyu na dare.
Ishmah ce ke kwance bisa gadon ta, tayi da take riƙe da wayarta tana bibiyar comments ɗin da ake yiwa Taj, wanda dama ita ke bibiyar masa comments inshi, duk abinda ta gani na tambaya ko yabawa ko neman haske, takanyi screenshot sai ta tura mishi ta Whatsapp.
Washe gari ranar asabar. Cikin Ethiopia, gidansu Adaya.
Daga bakin ƙofar Parlour wani, irin kiɗinema mai cike da salon kiɗin su na Ethiopia na Damm ke tashi.
Zirya takeyi a tsakiyar Parlour tare da rawa da juyi tamkar mazari, irin rawarsu nan dai na wuya da kafaɗu.
Cikin burgewa da so, ganin sabanin kwarewar ta a rawar, ƙawarta Asina da abokinsu Izzin, suke kallonta, dayi mata video tare da liƙi, jujjuya kanta takeyi, tana tsawo dashi, kamar barewa, sai kuma tayi guntu dashi kamar, kwaɗo tana jujjuyashi kamar maciji, sai kuma fara karkaɗa kafaɗarta na hannun hagu, kai kace jikinta ba ƙashi bane, robace, pantsama-pantsaman nononta kuwa sai rangaji sukeyi cikin yar rigar data matsesu, tamkar zasu bulluƙo waje dan girma da cika, sunyi tumsu tumsu.
Izzine, ya kalleta cike da sha'awa domin yana masifar gigita da yadda take kaɗa rusa-rusa nonon.
Sai kuma ya haɗiyi yawun , saboda ganin yau ɗin tana cikin tsananin fushi da hatsala tana rawan ne domin shine kaɗai ke sama mata nitsuwa, cikin haki ra
Fuskan cesu, cike da yanayin ƙunci mai gwauraye da tsiwa da gausin baki dake bayyana shagalarta da duniya, ta dawo ta zauna gaban Step Mom ɗinta.
Tare da rumtse idanutan da kukan data kwanayi yayi sanadin kumburarsu cikin yaƙini da ƙarfin aniya cikin harshen Yaren Omoro tace.
“Wallahi tallahi auren nan bai ɗaur....
Wasan da yanzu aka soma, toma me akayi ki biya ki karanta cikin salama.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/7, 12:14 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 5*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Littafin INDA RAI na kiɗine wannan free pages ne, muna gama free page kuma ko kin ganshi a wani wurin to na satane, ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc ne kacal zaku biya jaka ɗaya kenan +22790899076 ga number mommy ta wurinta zaku biya*
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kayana sun iso lfy. Aikin su ya kankama, komai ya zama Available. Duk abinda kake so a cikin wanda zan sako a nan akwaisu Available, kayane masu zafi da tururi kayane da ban taɓa jibgo kamar su da irinsu ba. Ku matso iyayen amare, da amaren da yayun amare da ƙannen amare da ƙawayen amare, Uwar gidaye gareku, tsakar gidaye kuma ban barku a baya ba, mai jego sabon haihuwa ko tsohon jego wato barden goyo, amarya Budurwa ko Bazawarara duk ku taho kowa da zazzafan haɗinsa, ina araha kam duk ɗan karen tsadan da kayan suka ƙara Amman fa ina hana bashi ga number da zakiyi min mgna 08069423567. kaya ne mata mai tsuma jiki da ratsa jiki. Kayana set ne hawa hawane, akwai manyan set akwai ƙananan set ƙanan daga 40k 35k 30k 25k 20k 15k 12k ƙaramin ƙarshen 5k sai kuma manyan set ɗin daga 50k ne zuwa sama 60k 70k 80k 90k sai sha kunɗum ɗin 100k. Kana akwai kayan ƙamshi ma suma haka ne farashin su.
“Ɗauru a kaina ba, na gaya muku, babu aure a jadawalin rayuwata a yanzu, inada burin zama shaharerriyar ƴar rawa a rayuwata, aure zai hanani cika burina, shiyasa duk auren da Abpu ya shirya yi min, nida kaina nake watsashi.
Sannan yau rana tsaka in gama shirya yadda auren zai watse, na kuma yi nasara ya watse, sannan a samu wani jarabbeben mutum ya faɗo sama ta ka, a rana tsaka yace, wai ya aurawa ɗanshi ni, toh wlh tallahi sai yayi nadaman
aurawa ɗanshi ni. Domin asarar kuɗin sadakinsu da goronsu kawai sukayi, ni dai Adaya ba aure a tsarina a yanzu.” ta ƙarashe mgnar tare da miƙewa tsaye taci gaba da wani irin rawa da karya ƙugu tamkar mazari.
Ita kuwa Ummi wacce ƙanwace ga mahaifiyarta, bayan rasuwar mahafiyar Adayan ne aka aura wa babanta ƙanwar mahafiyar tata, domin tazo ta riƙe ƴaƴan ƴar uwarta, Adaya Aminullah, saboda an san abokiyar zamanta mahaifiyarsu Ma'aruf bazata riƙesu ba, saboda tsananin kishi.
Cikin zubda hawayen da suka cika kwarmin idanunta ta riƙo hannun Adaya tare da cewa.
“Adaya ki zauna, ki saurareni, da kunnen basira zaki gane cewa, mahaifinku gata yayi Miki, duk ranar da baya raye, zakiyi kukan da babu mai share Miki hawayenki, wannan rayuwa da kikeson sa kanki bafa rayuwace ta Musulmin ƙwaraiba, na roƙeki da Allah Adaya ki duba makwancin ƴar uwata mahaifiyarku, ki zame mata al'waladussaliha kamar yadda Aminullah ya zame mata”.
Sai kuma ta rumtse idanunta saboda jin Adaya ta janye hannunta tare da cewa.
“Ummi ba aure a tsarina, kuma ko zanyi aurema ai sai a bari sai lokacin da nayi ra'ayi na kuma fidda wanda nakeso, bawai haka nan auren haɗiba, kijifa Izzin yana ce min, roƙo da magiya da kuka Abpu ya rinƙayi a cikin Masallaci sai kace irin na zame mishi masifa da bala'i a gidansa Allah Allah yake ya rabu dani”.
Sai kuma taje gaban kayan kiɗin nasu tare da ƙure sautin.
Ita kuwa Ummi juyowa tayi ta kalli Izzin cike da tsanar abotarsa da Adayan, domin shine yake ƙara ingiza ta, gashi Adaya da ɗan karen taurin kai da kafiya, duk zafin mahaifinsu da tsananinsa akan yara ta buwaye sa, ya gagara tan kwarawa, zuwa yanzu gani yake aurene kaɗai matakin ƙarshe da ya rage na samun damar tankwaratan.
Sai kuma Asina da ita kanta Ummi bata gane alƙibilar Asina.
Cikin tsuke fuska tace.
“Izzin an kira sallan azahar ya kamata ka tafi masallaci”.
Ta ƙare maganar fuska a haɗe, hakanne yasa Izzin kallon Adaya tare da ɗanyi mata signal kana ya ɗan kai hannunsa bisa kunnensa alamun sai sunyi waya.
Ita kuwa Asina jan hannun Adaya tayi suka nufi bedroom ɗinta.
Ita ma Ummi nata Bedroom ɗin ta nufa.
Suna shiga Anisa ta kalli Adaya, tare da yin murmushin tace.
“Mrs Tajuddeen, ko ya yake Tajuddeen ɗin naki, mai ajine ko garma-garma ne, wayeyyene ko kifeffe ne, to wai ma Adaya kin shiryawa zama da namiji a yanzu ne”.
Ciki da takaici da ƙara hatsala tace, koma shi wanne irine zai zo ai ya sameni, daram duk yanayin da naga yake dashi, ai dashi zan yaƙeshi in sashi ya sakeni.
In shi ustas ne, in nuna mishi ni karuwace, zuwan farko in nuna mishi ni mayatacciyar na mijine, in shi mugune in nuna mishi na fishi mugunta, in shi na kirkine in nuna mishi ni ta banzace, Kinga ba ɓata lokacin zai sakeni, kin san gasan rawar da za'ayi a India ina cikin team ɗin ethiopia.“
Cikin jinjina kai Asina tace.
“Nasan kuwa muddin kina cikin team ɗin mune zamuyi nasarar lashe gasarar rawa na duniya baki ɗaya a shekarar nan, domin ke ta musamman ce”.
Daga nan dai sukaci gaba da hirar rawarsun.
A cikin sharara gudu ishmah key tuƙin, ta fito daga Jada ne zata dawo cikin Jimeta,
Gudun takeyi cike da ƙwarewa da iyawa, yayinda waya ke maƙale a kunnenta.
Sai gefen mai zaman banza kuma da Aunty Hauwa ke gefentan ƙanwar Dadeey mai binta.
Dai-dai lokacin kuma Taj ne da Laylah ke zaune a Parlour Addawa,
gefen Taj ɗin ta zauna tare da jawo Laylah jinkinta, cikin tausayawa tace.
“Kin ƙoshi ko?”.
Kai ta jinjina mata, tare da cewa.
“Amman Uncle Taj bai ciba Addawa”.
Kai jinjina mata tare da cewa.
“Ai indai yana waya da Ishmah baya jin yunwa, sai ya gama zan ɗan gasa mishi nama yaci”.
Murmushin tayi tare da cewa.
“Addawa Aunty Ishmah nada kirki, tana sona, tafi Aunty Meymey sona”.
Murmushi Addawa tayi tare da zuwa Taj idanu tana sauraron hirarsa da Ishmah.
Cikin Lumshe idanunsa tare da tausasa muryasa a hankali yace.
“Wai ina kika jene baki gaya minba Ishmah”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Afwan Taj jikin Dadeey ne ya tashi jiya kwana mukayi bamuyi bacciba, sai ƙarfe huɗu asuba jikin ya lafa, so naje Jada ne amso mata magani”.
Ta ƙare maganar cike da rauni da alamun damuwa.
Sassayan numfashi ya fesar cike da tausayawa da son Dadeey cikin ransa, cike da kulawa yace.
“Ayyah Dadeey Allah ya bata lfy yasa ciwon nan ya zame mata zakkan jiki, kuma kaffara Allah ya yaye mata.
Cikin sanyi tace.
“Amin ya Allah”.
Tayi mgnar tana gyaɗawa Aunty Hauwa kai saboda jin tana cewa.
“Taj ko?”.
Ganin ta gyaɗa mata kai alamar eh shine, yasata yin murmushi.
Gyara zamansa ya ɗanyi saboda jin sosai yau ɗin take da sanyi, ya fahimci sosoi jikin Dadeey ke damunta.
“Kina jina”.
A hankali tace.
“Eh Taj”.
Ɗan Murmushin yayi domin ya gama sanin tana masifar son sunnshi tunda har alƙawari tayi mishi in tayi aure ta haihu zatayi mishi takwara.
“Ko zamu fita India da Dadeey ne?”.
Cikin sanyi tace.
“Hmmm Taj ka mance ne, jinin da yawu da komai na gwajin cuta na Dadeey an ɗiba an kawoma Ethiopia ka gama bincike a kai, ka turashi India aka gama bincike akai, ba'aga me yake damumtaba duk gwajin da akayi result ɗaya yake badawa, bata da matsalar komai”.
Sai kuma ta fesar da zazzafan numfashi tare daci gaba da cewa.
“Kaida kanka da Dr Khumar Kapoor kuka tabbatar min cewa, jinyanta bana asibiti bane”.
Cike da damuwa yake jinjina kai domin ta tuna mishi irin yadda suka binciki kamai na Dadeey Allah baisa sun gano matsalarta ba, kuma sosai ciwon yafi kama da matsalar iska.
Domin yanzu jikin zai riƙece, ko zama bazata iyaba saboda jiri anjima kaɗan ka sameta garau, ga masifar ciwon baya, tafiyarta duk ta sauya saboda ciwon da yake riƙe jijiyoyin ta, hatta hannunta basa iya taɓa ko bayanta duk suna son ƙandarewa.
Cikin sanyi yace.
“Amman kunayi na Islamic ko?”.
Da sauri tace.
“Eh shine”.
Dai-dai lokacin kuma ta iso ngurore zongon baƙi, cike da nitsuwa ta karya kwana tare da ɗaukar hanyar da zai sadata da cikin jimetan.
“Yauwa my Ishmah a kiyaye irin wurin da za'aje neman maganin, domin shi cuta jarrabawa ne, in kayi halattacen jinya baka faɗa wurin bokaye da ƴan bori da masubbataba, to shine sai ya zamewa majinyaci kaffara, kuma kuma ku samu ladan jinya, domin da Dadeey da Abba dake dasu Yah Abubakar da Hamisu dasu Adam duk Allah ya jarabceku da cutar Dadeey ne to kuyi ƙoƙarin cinye Jarrabawar, ta hanya mai kyau in sha Allah watarana zai wuce”.
Sharce hawayenta da ya gangaro mata tayi tare da cewa.
“In sha Allah kuwa Taj, ngd”.
A hankali ya lumshe idanunsu saboda jin muryarta na rawa alamun zatayi kuka, fahimtar hakanne yasa cikin sauri yace.
“Ga Laylah”.
Jin haka kuwa yasa Laylah amsar wayar tare da cewa.
“Assalamu alaikum Aunty Ishmah nayi missing naki, tunda Uncle Taj ya tafi bamuyi wayaba”.
Cikin sauƙe numfashi ta ɗan saki guntun murmushi tare da cewa.
“Miss You to my Laylah Uncle Taj ne ya hanani number Meymey da zanyi ta kiranki ta nan muna gaisawa”.
Cikin jin daɗi tace.
“Toh zan baki number Ummeey mu rinƙa gaisawa da wayarta”.
Cikin sanyi tace.
“To ba matsala”.
Ita kuwa Laylah cekin sonta tace.
“Aunty Ishmah yasu Khalid da Minat”.
Cikin jin daɗi tace.
“Suna lfy yauma zasuzo gida Kinga yau weekends ne”.
“Ayyah Aunty Ishmah in kin koma ki haɗam..”
Bata kare mgnar ba ta miƙa mishi wayar ganin yana miƙo mata hannunsa.
“Uhmmmm komai iri ɗaya ko?”.
Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
“Toh me kuma yayi iri ɗaya?”.
A hankali yayi mgnar murya can ƙasa yadda Addawa ma bazata jiba yace.
“Zuwa yanzu na yarda komai namu ɗaya ne Ishmah, kinga nima banyi bacciba kema bakiyi ba”.
Tana mai ɗan rage gudunta sabida cunkoson ababen hawa tace.
“Uhmmm haka fa, to ni dai fatana abin farin ciki ne nakeso ya rinƙa zuwa mana a tare ba akasin hakaba, kagafa komai sai ka raɓa min”.
Murmushi gefen baki yayi sai kuma ya buɗe manyan idanunsa dake lumshe jin tana cewa.
“Fatana dai ka raɓa min aure, nima in samu aurena da Dr Nafi'u ya tabbata kada ya watse kamar saura”.
Fuska ya tsuke tare da cewa.
“Hghhmmmm”.
Sai kuma ya kauda zancen da cewa.
“Jiya ba'ayi comments bane a video da nayi baki gaya min komai ba”.
Da sauri tace.
“Yauwa kama tuna min”.
Ta ƙare maganar tana dariya tare da kallon Aunty Hauwa dake kallonta cike da alamun nazari.
Sassayan ajiyan zuciya ya fesar, cike da jin daɗin ya fara sauƙar da damuwar zuciyarta yace.
“Uhmmmmm ina jinki?”.
A hankali ta ɗan sauƙe glass ɗin motar ta, dai-dai lokacin da suka iso Welcome to Yola, jami'n tsaron dake bisa hanyar ne ya ɗan leƙa ciki kana ya bata hanya cikin sakin sassayan numfashi tace.
“Uhmmm ai jiya, kaɗan ya hana in kiraki dare-daren in gayama comment ɗin wata, to sai na tuna yanzufa kana da mata, kada taji haushina, gashi ka hanani number ta ma”.
Cikin son kauda mgnar yace.
“Me tace a comment ɗin?”.
Ɗan juyowa tayi ta kalli Aumty Hauwa da ta tsura mata idanu tamkar ta samu TV kauda kai tayi tare da cewa.
“Hmmm wata ƴar Bangaladash ce, ta fara dayin introduceng ɗin kanta ne, harda bada address ɗinta, kana ta ɗaura da cewa, tana sonka, so kuma irin na aure.
Nayi dariya sosaifa ganin yadda ta watso maka emojis ɗin love, Saida na gama dariya ta sai kuma naci gaba da