Showing 45001 words to 48000 words out of 74955 words

Chapter 16 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel

sauri ta buɗe idanunta tare da miƙewa zaune sai yanzu ta tuna ashe fa yau juma'a ce jin yana karanta suratul juma'a miƙewa tayi tare da tashin Laylah da Minat, kana taje tayi alwala, suma sukayi.
Bayan sun idar da sallah sukayi Azkhar sai kuma ta kalli Laylah dake gaisheta amsawa tayi kana ta riƙe hannunta.
Yayinda hannunta ɗaya kuma ta shafa kan Minat tare da amsa gaisuwar ta, daga nan suka fito falo hannunta na dama na riƙe da Carbi tana Istigfari...

Acan gefen Taj tare da Abba da Yah Muhammad suka fito daga Masallaci suka nufi gefen Abba da kullum suke zuwa shan tea cikin nutsuwa Abba ya kallesa kana yace.
“Muje mu duba mutuniyar taka dan jiya da daddare tana ta rakin cewa hannunta ya ƙone”.
Da damuwa Taj yace.
“Subhanallah amma da dare sosai ko?”.
Kai Abba ya gyaɗa suna cigaba da tafiya yace.
“Eh kusan ƙarfe goma sha ɗaya Naji tanata raki anzo wajena karɓan Zam-zam ta ƙone kasan Ishmah da raki sai da naje nayi mata tofi kafin ta samu bacci, yanzu ma muje nayi mata”.
Ɗan murmushi yayi tare da cewa.
“Toh Abba”.
Kana sukayi gaba su Yah Muhammad na biye dasu bakinsu ɗauke da sallama suka shiga falon zaune a tsakiyar Parlour suka samesu...

Kamar yanda Abba ya sani tana riƙe da hannun tana hura masa iskar bakinta kana tana ɗan yarfewa.
Anutse ta ɗago kanta tare da amsa sallamar sai kuma tace.
“Yawwa Abba ayi min tofi hannun raɗaɗi yake min ya hanani bacci”.
Sai kuma ta maida kallonta kan Khadijah dake cewa.
“Ummm”.
Ashagwaɓe tace.
“Toh me zakice wani ce Ummm?.
Keda kike ta baccin ki baki sani ba ya hanani bacci da kyar na samu nayi bacci”.
Murmushi Abba yayi cike da kulawa yace.
“Shiyasa ma naxo na Miki Tofi Mamana”.
Ya ƙare maganar tare da zama kan kushin kasancewar tana kasa ya kamo hannunta yana mata Tofi su Yah Muhammad sai dariya suke suna faɗin rakinta yayi yawa Taj kuwa kallonta yake cike da tausayi da kuma yanda take shagwaɓe fuska kallonsa tayi sai ta sake kwaɓe fuska shima fuska ya kwaɓe kana ya ɗaga mata girarsa ɗaya.
Abba kuwa bayan ya gama yace.
“Toh ki matso mana Taj ma ya Miki addu'a kinsan kowa da dafa'in bakinsa”.
Juyawa tayi ta kallesa sai kuma ta miƙa masa hannu ya mata tofi tare da cewa.
“Toh Allah ya sawwaƙa”.
“Ameen”.
Ta amsa tare da gaishe da Abba kana ta gaishe da Yayunta da Taj.
Har zasu fita tace.
“Abba in zo musha shayin tare”.
Kai ya gyaɗa tare da faɗin.
“Zo mana Mamana”.
Mikewa tayi tabi bayansu

Atare suka sha shayin da ita.

Ƙarfe sha ɗaya dai-dai Jirginsu ya tashi daga Yola zuwa Maiduguri borno birnin kanuri bayinmu Fulani.
*Sirati sirta moɗa, toh saldori tagga moɗa* kasancewarsu bayi ne a garemu yasa suka koyi karamci da martaba bako, Borno gidan karamci da girmama baƙi tarba na musamman Taj ya samu daga Manyan Malamai Tabbas yaga karamci awajen Kanurai A jiddari aka sauƙe sa bayan ya huta yayi wanka yaci abinci kana akayi masa jagoranci zuwa babban Masallacin Jumma'a Al-Ansar.
Kusan a tare suka shiga yana tsakiyar
Al Sheiky Zharma..
Imam Muchmah. Da kuma Al Sheiky Idee sun sashi a tsakiya yayinda. Dubban musulmai ke dandazon shiga ciki masallacin
shi yayi musu limancin Sallar juma'a na wannan ranan.
Koda aka idar tuni matasan Borno suka zagayeshi nan sukayi ta gaisawa dashi tare da yin hotuna da vidios suna yaɗawa a social media, tuni Nigeria ta ɗauka cewa Sheykh Afif Muhammad Taj na cikin ƙasar.

Washe gari Asabar bayan an idar da sallan asuba ya wuce garin Zamfara, nan ma yaga karamci.
Kamar yadda ya alƙawaranta haka ya limamcesu kamsusul salawat.
Daga Zamfara ya wuce Kano ta dabo tumbin Giwa.
Jallabar hausa. Ya Salam shine abun da yake faɗa a lokacin da ya dira a malam Aminu Kano international airport, sabida ganin taron masoya mabiya karatuttukan.
Bisa jagorancin Malam Aminu Ibraahim Daurawa da tsaron hukumar Hisba suka tarbeshi har zuwa masauƙinsa na musamman da aka tanadar.
Taj yaga karamci iya ka wurin kanawa.
Dole kwanan sa biyu a Kano.

Ishmah ce zaune bisa kujera riƙe da cup ɗin da da Khadijah ta dama furar mata ta kasa sha, ɗan kwafe fuska tayi lokacin da ta kurbi damun, domin ba daɗi kam to Amman akan ya lalace ai gwara ta shanye musamman in ta tuna gargaɗin Garkuwa gyara riƙon da tayiwa wayarta tayi tare da cewa.
“Yanzu dai ai yau zaku wuce Bauchi ko”.

Yana mai ɗan sunkuyar da kansa kasancewar wayar na aljihunsa ne domin rashin samun lokacin kansa yace.
“Eh yanzuma zamu tafi”.
Cikin kula tace.
“Taj anya kuwa kana cin abinci yadda ya kamata Allah naga videos ɗinka ka ɗan rame, gashi kanawa nan yan al'barka sun zagaye min kai yadda kake ta musabaha da mutane a gajiye”.
Yana ɗan lumshe idanunsa dake cike da tarin gajiya yace.
“Suna da karamci Amman yawan su da yawan son da suke min yasa sun kasa barina in huta”.
Cikin sanyi tace.
“Bari in Barka dan naji yanzuma cikin mutane kake”.
Cikin sanyi yace.
“In sha Allah jibi zan dawo dan yau in munje Bauchi da dare zamubi jirgi zuwa Abuja.
Duk zaman da zamuyi gobe zamu gama a Abuja jibi da sassafe zan iso Yola”.

“Toh Allah ya kawoka lfy Amman Please ka kularwa Meymey da kanka da Adaya”.
Da sauri ya rumtse idanunsa tare da katse kiransa saboda tsinkewa da zuciyarsa keyi a duk sanda ta kira mishi su more especially Adaya.

A ranar suka wuce Bauchi.

Sha biyu dai-dai suka isa Bauchi Yakubu.
Kai tsaye suka wuce gidan, Sheykh Tajuh Usman Bauchi, dottijon malami kuma sannane a cikin ƙasar mu da kewaye baki ɗaya, Shekh Tajuh Usman Bauchi dottijon mai tarin limin addini da yawan shekaru kana da zugar zuriya ƴaƴa da jikoki da jikokin jikoki, malami ne na Ɗarika tsakakkeyiyar ɗarika.
Wanda yake da good understanding da manyan malaman kasarmu na sunan, shiyasa tafiyar ma dasu akayi suna shiga harabar gidan Taj ya lumsh idanunsa tare da sauƙe wani irin amintaccen ajiyan zuciya da fesar da sassayan numfashi kana ya buɗe idanun a hankali yana karewa tsarin gidan da yafi dacewa da a kira shi da fada ko masararuta ilimi isilam domin girmanshi ya wuce ace dashi gida, tsaruwarsa kuwa yafi karfin ace dashi ko sangaya sai dai masarautar.
Isarsu ba wuya akayi musu iso cikin asalin sashin Sheykh Tajuh Usman Bauchi.

Kusan a jere a jere suke tafiya cike da kamala da nitsuwa da ilimi addinin Musulunci ya sakar musu, yayinda yan agajin da kuma jami'an hukumar Hisba ke zagaye dasu.

Kusan duk a tare suke sauƙe sassauke numfashi a hankali da tsuka ratsa tsakiyar wani mashahurin Parlour na alfarmar.

Sai kuma duk suka ɗan tsaya saboda, ganin ɗaya daga cikin masu yi musu jagoran ya ɗan buɗe musu wata babbar ƙofa tare dacewa Bismillah.
Manyan malaman sunan a gaba, yayinda suka sa Taj a tsakiya sai yan agajin dake baya, kusan duk a tare sukayi sallama
Ya Salam.
Shine abinda Taj ya faɗa a lokacin da suka iso tsakiyar Parlour da yafi dacewa da a kira shi da holl, sai kuma ya lumshe idanunsa saboda hango Sheykh Tajuh Usman Bauchi dake zaune a tsakiyar ƴaƴansa da jikokinsa gami da kuma amintattun ɗalibansa duk sun zagayeshi tamkar sarki a tsakiyar waziransa.
Haka nan sai yanayin yayi mishi kama da yadda suke sa Yah Abana a tsakiyar duk ranar jumma'ar ƙarshen ko wanne wata, komai na zaman da tsarin gidan yayi mishi tuni da gidansu.

A hankali ya buɗe idanunsa tare da diresu kan kekkyawan farin dottijon.
Kusan a tare shi da Dottijon suke rufe idanunsu Saboda wani irin fitinenne bugun zuciyarsu da yayi a tare.

Yayinda sauran kuwa duk sun zube a tsakiyar Parlour a gaban dottijon da duk ya girme su, yana haifesu wasuma yayi jika dasu.
Yayinda sauran yaransa kuwa duk suka juyo suna kallon inda mahaifin nasu ke kallo.

Malaman Sunnan kuwa da sukazo cike da girmamawa suke gaida Sheykh Tajuh Usman Bauchi.
Amman ina hankalinsa baya kansu.
Ido ya zuba wa Taj tamkar zai mannesu a jikinsa.
Shi ma Taj idon ya zuba mishi yana mai ɗan matsowa kusa da abokan tafiyar tasa.
Sai kuma duk taron jama'ar da suka samu a Parlour suka juyo da sauri suka zubawa Dottijon idanu jin yana mgna cikin muryar girma da nitsuwa da tsufa mai nagarta yace.
“Inajin Ƙamshin Mahmoudu na, ƙamshin Mahmoudu nakeji”.
Ya ƙare maganar da miƙawa Taj hannunsa tare da cewa.
“Afif Muhammad Taj ne yau a sangayata”.
Da sauri Taj ya miƙa masa hannunsa.
Jawosa kusa dashi,
Da sauri Taj ɗin ya ɗan rusuna tare da direwa bisa guiwowinshi,
Shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, kan Taj ɗin ya ɗaura bisa cinyarsa, sai kuma ya sunkuyi tare da cusa hancinsa cikin sumar kan Taj, tare da shaƙar ƙamshin jikinsa.
Numfashi mai sanyi ya fesar tare da ɗago kanshi ya kalli baƙin nasa tare da cewa.
“Izala ƙanwar ɗarika yau kun kawo min baƙo na musamman, bakon da nake jin jini da zuciyata sun aminta dashi”.
Sheikh Jabeer sani Maihula ne yayi ɗan murmushi cikin sokkotancinsa yace.
“Malam ai ayanzu Sunnan ce abbabba ɗarika ce aƙƙarama, kawai kui mubaya'a ku yarda mune ag gaba gareku”.
Murmushin Dottijon yayi tare da cewa.
“Yoh aiko ɗan hodiya mancewa yayi a sauka Sokoto da Bauchi zaizo”.
Dariya sukayi mai sauti sai kuma duk suka fara gaisawa, har lau dai Sheykh Tajuh Usman Bauchi bai saki Taj ba, yayinda ƴaƴan da jikokinsa kuwa kab idonsu na kan Taj.

“To Alhamdulillah sannu ku da isa lfy”.
Sai kuma ya ɗan kalli gefen damansa tare da cewa.
“Ku isa kusha ruwa kuzo muyi muƙabala”.
Da sauri Sheykh Daurawa yace.
“A'a Malam zafa kayi mubaya'ar nan da baka sonyi in mukayi muƙabala”.
Sai kuma suka kalli Sheykh Janeer dake cewa
“Awoh haɗimai Gsky dai, domin hujjar aggaremu gaba gareku, kuna gani da ajjiyarku zaku dawo baya garemu, ko ku zam kuna ɗumi”.
Dariya sosai sukeyi musamman sokotancin da Sheykh Jabeer ke zubawa.
A hankali ya yunƙura tare da fara kiciniyar miƙewa, da sauri Taj ya tallabeshi tare da taimaka mishi ya miƙe, sai kuma yayi saurin amsar sandar da mutumin dake gefensa ya miƙa mishi.
Amsa yayi tare da bawa dottijon shi kuwa Sheykh Tajuh Usman Bauchi cikin tarin girma da isar kamala yace.
“Ni bana gaisawa da baƙo har sai na bashi abin sha da ci yaci ya sha, dan haka Bismillah ku iso nan ya ƙare maganar yana nuna musu Dinnin area.
Wani tamfatsetsen Dinnin table ne na alfarmar wanda ke da kujeru goma sha huɗu.
Yayinda saman table ɗin ke cike maƙil da kayan marmari da kuma manyan womers na alfarmar sai plates, bowls, mugs, and spoons.
Sanin YESS bazai tsaya yayi mgn ba sai sun sha wani abune yasa suka nufi Dinnin area ɗin bisa jagorancin babban ɗansa.
Sheykh Tijjani.

Ga mamankisu kuwa sai gani sukayi yaja hannun Taj.
Sun bi wata ƙofa ta musamman sun tafi.

Kusan duk yayansa kallon kallo suka farayiwa juna, fuskokinsu ɗauke da maɗaukakin mamaki.

Su Sheykh Jabeer kuwa.
Bayan sun ci sun shane, duk sukayi al'wala saboda jin an kira salla.

Daga nan suka wuce masallacin sangayar.
Murmushin Daurawa yayi lokacin da suke tsaye a sahun forko sai kuma ya kalli Sheykh Musa Yusuf Asadussunah na faɗin.
“Toh yau maji ma gani wa zai limamce, izala zata limancin ɗarika ko ɗarikace zata limancin izala”.
Murmushin Sheykh Isa Ali Pantami yayi tare da cewa.
“Mu mun basu dama”.
Da sauri Sheykh Janeer yace.
“Anya ko munefa gaba garesu”.
Murmushin Sheykh Tijjani yayi yana kallon mahaifinsa ganin yana jawo hannun Sheykh Afif Muhammad Taj.

Ga mamakin duk al'ummar Annabi dake cikin yankin jin Dottijon yana faɗin.
“Yau ba ni zan ja sallaba
ya faɗa tare da ɗan matsawa gefe kana yaci ga da cewa.
“Alhamdulillah dai ga Afif Muhammad Taj, a ƙasar Nigeria a kuma jahar Bauchi a tsakiyar tsagayata a kuma sahun limamcin masallancimu.”
Ya ƙare maganar yana jawo hannun Taj ya tsaida shi da'irar limancin kana ya koma ya tsaya a sahun forko.
Shi kuwa Taj zuwa yanzu al'amarin dottijon ya daina bashi mmki kawai dai yana jinsa har cikin jini da tsoka ƙashi da bargo jiki da zuciyarsa, wani irin son dottijon yakeji yana game jiki da zuciyarsa.
Cikin sanyi ya gyara tsayuwarsa tare da gyara maek ɗin cikin nitsuwa gami da cikir kamala ya ɗanyi gyaran murya tare da cewa.
“Sahoohhhh! Sahoooohhh!! Sahooooooohhhhh!!!”.
Kusan gaba ɗaya mamun nasa lullumshe idanu sukayi saboda yadda sautin Muryasa yake ratsadu, sai kuma duk suka gyaggyara tsayuwar sahun.
Ajiyoyin zuciya suka rinƙa sauƙewa tare da bubbuɗe kwayar idanunsa lokacin daya fara tada iƙama.
Da yawa sunso ace jam'in sallama Magrib ko Isha ko asuba zai jasu dan suji zaƙin muryasar.

Bayan an idar da salla suna sake koma ciki.

Nan suka tattauna duk abinda ya kawosu.
Kasan cewar Sheykh Afif Muhammad Taj da Isa Ali Pantami da Sheykh Jabeer Sani Maihula da wasunsu Abuja zasu wuce, kuma sai tara na dare jirginsu zai tashi ne yasa suka kai dare.
Saura kuma tun bayan la'asar suka juya suka koma Kano.

Sit kakaji masallacin da lokacin da yake jansu sallan Magrib babu abinda ke tashi sai sautin muryarsa bayan ya karanta suratul Fatiha kana ya ɗaura.
Daga forkon Suratul Yoosuf
“(Aliflamrah tilka ayatu alkitabi almubinu)”.
Daga nan yaci gaba da kawo ayoyin har yaje aya ta 10 kana sukayi sujjadar forko, kana suka miƙe dan.
Cikin aminci ya karanta suratul Fatiha kana ɗaura da Suratul Yusuf ɗin ya ɗauka daga aya ta 11.
(Qaloo ya Abana ma laka la tamanna Aaala Yoosufa wainna lahu lanasihoona”.)
Wasu irin tafassasun hawayene suka zubawa Sheykh Tajuh Usman Bauchi, Dottijon mai cike da wani miki a zuciya, yayinda shi kuwa Taj haka nan yaji tsoro na diro mishi cikin danne rauninsa ya kawo aya ta 12.
“( Arsilhu ma'AAana ghadan yartaAA wayalAAab wainna lahu lahafithoona”.
Numfashi mai nauyi ya fesar a hankali tare da baddashi cikin taƙib kana yaci gaba da kawo ayoyin Saida yaje aya ta 20. Kana suka tafi ruku.

Haka dai sukayi sallan cike nitsuwa da amcin mu'ujizar Alqur'ani mai girma.
Koda suka idar basu fitaba sai da sukayi isha, anan ma duk a Suratul Yusuf ya jasu, wanda duk aya goma goma ya rinƙa kawowa haka yasa aka samu ayoyi 40 kenan

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu ya tashi zuwa Abuja.

Cikin alfarmar darajar Alqur'ani mai girma. Aka ɗaukesu kai tsaye gidan Sheykh Isa Ali Pantami suka wuce.
Taj yaga kara da mutumci iyaka a wurin wannan Bagombe ya nuna mishi kuma lallay Gombawa ɗiban farine, ba'a kwana dasu ba a tashi dasu.
A dare ranar yaga karrama.

Washe gari da safe, cikin mutuntawa Sheykh Isa Ali Pantami ya shiga masauƙin baƙon nasa. Shi kuwa Taj a dai-dai lokacin waya yakeyi da Ummeey ya kuma haɗa comfrence call ne da Ishmah sai dai Ummeeyshi bata saniba.
“Babana wai sai yaushe zaka dawo ne? Ko ka mance cewa ka tafi ka bar mararka ne, yau fa sai nan tazo muka kwana, tace gaba ɗaya ƙasar Ethiopia batayi mata daɗi in baka nan”.
Sai kuma ta ɗanyi shiru.
Shi kuwa Taj a hankali ya gyara tsayuwarsa tare da ɗan gyara zaman hular kansa yana mai nazari kan wasu ababen sauye-sauyen Meymey da sam a zuciyarsa bai aminta da itaba.
“Hello Babana kayi shiru, ɗazu munyi waya da Laylah tace wai bakusa ranaba me haka ke nufi?”.

Cikin sanyi murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Yanzu ina Abuja gobe Thursday zan koma Yola. In sha Allah ranar Sunday zan iso Ethiopia domin in samu in ɗan huta dan inada tafiya ranar Tuesday, kuma Ummeey malam ƙasar ne suka ɗan riƙeni shiyasa.”
Ya ƙare maganar cikin Yaren Amharic wanda shine asalin Yaren Ummeeyshi, yayi mgnar cikin sanyi tare da juyowa jin sallar Sheykh Isa Ali Pantami.
Da sauri ya sallami Ummynsh tare da katse wayar.
Ruggume juna sukayi shida Sheykh Isa Ali Pantami.
Yayinda PA'nsa keta ɗaukarsu hoto, gami da ɗan video.

Bayan sun gaisa ne suka wuce wurin taronsu da manyan malam Sunnan.
Inda suka bashi kyautar murya kira'a mafi daɗi da soyuwa a shekarar.

Washe gari da safe jirginsu ya tashi daga Abuja zuwa Adamawa Yola

Cikin farin ciki da jin daɗin mutumtaka da kima daya samu daga Manyan Malamai da kuma jama'ar Nigeria.

Yah Abubakar ne ya ɗaukoshi a Airport ɗin.
Awaje suka haɗu da Abba wanda ya fito daga Masallaci bisa alamu yayi walaha ne.
Cikin so da kulawa Abba ya ɗan ruggumeshi tare da cewa.
“Barka da sauƙa lfy”.
Sai kuma ya kalli Adam daya buɗe but ɗin motar ya fito da jakarsa yana ɗan ja.
“Masha Allah isa daga ciki, ka samu ka huta, kasha zirga-zirga a titunan ƙasarmun nan da ba cikekken kyaune da suba bare tsaro”.
Kai ya ɗan jinjina domin Allah ya sani a gajiye yake, ga yunwa dake kwaƙular cikinsa haka Allah yayinsa baya iya cin abincin kirki in ba matsa mishi akayi ba, so yake yayi wanka yaci abinci yayi bacci.

Shi yasa yana shiga BQ ɗin kai tsaye bedroom ya wuce.
Adam kuma jakar tasa ya ajiye mishi kana ya nufi cikin gida.

A kitchen ya samu Ishmah tsaye cikin wani tattausan lace pink and sky blue collar mai ɗan ratsin Royal blue.
Ɗinkin doguwar rigace da Idris ɗinta ya watsa mishi ɗinki na alfarmar, sosai ya zauna a jinkinta ɗas da ita.
Sai wani irin fitinenne ƙamshi take zubawa, ta murza daurin a setta tayi kyau sosai a ciki.

A hankali take motsa gas meat and Emargency Sultan chips da yaji naman kaza ziryan ɗinta ba ƙashi ko kaɗan sai ɗan Vegetables kaɗan.
lashe baki yayi tare da cewa.
“Uncle Taj ya iso fa”.
Da sauri ta juyo dan bata san ya shigo ba.
“Ya Salam to miƙo min Food flack' and mug ɗinnan”.
Ta ƙare maganar tana jawo trayn.
Miƙo mata yayi tare da ɗan jawo plate ya miƙa mata kana yace.
“Toh nima a saka min a nan”.

Tana juye Gas meat ɗin a wani kekkyawan food flack's dan madaidacin tace to.
Sai kuma ta juyo Sultan chips ɗin ma.
Kana duk ta jerasu a kan tray ɗin.
Sai kuma tasa plate, bowl, mug, sai spoon and fork.
Duk ta jerasu kana ta miƙa mishi tray tare da cewa.
“Yauwa gashi ka kai kan Dinnin table na BQ sai ka dawo ka amshi naka.
Sannan ka ɗauko min Laylah a gidansu Minat, tun juya suka tafi basu dawoba gashi ya dawo bata nan”.
To kawai yace kana ya ɗauki trayn ya juya ya fita dan sauri yake ya samu ya dawo yaci wannan haɗin.

Ita kuwa Ishmah da sauri ta buɗe fridge Yoghurt fruits data haɗa mishi ta ɗauka tare da faro water ta sasu a tray tare da glass cup.
Kana ta fito, a Falo ta samu Rahman bisa alamu da Khadijah take waya dan jin tana cewa.
“Tunda kika komafa nake ta cewa ki haɗani da Maamah amman kinƙi, Maamah ɗiyar Khadijah babbar kenan”.
Tana fita ne tace mata.
“Please ki gyara kitchen nan, kuma ki maida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login