Showing 66001 words to 69000 words out of 74955 words
Chapter 23 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
samu Hajiya Babba agefensa kasancewar yau girkinta ne bayan sun gaisa ne ya ɗan kallesa kana yayi kasa da kansa tare da cewa.
“Yah Abana zan ɗan yi tafiya akwai Passenger da zan ɗauka daga nan Ethiopia zuwa Malaysia kwana biyu zanyi.”
Ɗagowa yayi ya kallesa cikin tsuke fuska ya kawar da kansa gefe tare da nuna mishi hanyar fita.
Jiki amace ya miƙe ya nufi hanyar fita sai kuma ya juya jin Hajiya Babba na cewa.
“Allah ya kiyaye hanya Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya”.
“Ameen”
Ya amsa kana ya fice, kai tsaye Airport ya nufa ɗakin da za'a masa gwaje-gwaje ya nufa gwajin farko da akayi masa kuwa aka samu jininsa ya hau 180 kana ga tsananin masifar ciwon kai ga kuma zuciyarsa dake harbawa da k’arfi, atak’aice dai matsaloli kusan guda biyar aka samu a tare dashi wanda hakan yasa dole aka soke tashinsa da jirgi wanda dole baza a iya barinsa ya tafi da Passenger ba nan dai aka bashi magunguna kana Driver’n sa ya maida shi gida.
Har sun kusa gida ya kalli Abu Hashim tare da cewa.
“Ka kaini gidan Addawa”.
Kai Abu Hashim ya gyaɗa tare da nufar gidan Addawa.
Taj na shiga kiran Ishmah na shigowa wayarsa yana ɗaukar kiran kuwa tace.
“Taj”.
Murya sanyaye yace.
“Na'am”.
Cikin tarin damuwa tace.
“Kayi min bayani, gaba d’aya ka sauya cikin kwanakin nan guda biyar zuwa bakwai na kasa fahimtar ka, sannan ka kasa yimin bayani, Tajj ya kake son inyi da rayuwata hankalina ya tashi zuciyata ya kasa kwanciya kayi min bayani”.
Cikin sanyi ya girgiza kai tare da taune lips ɗin sa cike da b’oye ciwon da yake ji aransa yace.
“Ma'eesha ba komai ki cigaba da yimin addu'a kinji ko?”.
Kai ta gyaɗa kamar yana agabanta kana murya na rawa tace.
“Toh In sha Allah, amma ya jikin Laylah kwana nawa baka haɗani da ita ba”.
Iska mai zafi ya furzar daga bakinsa gami da cewa.
“In sha Allahu zan haɗaki da ita”.
Asanyaye tace.
“Toh shikenan”.
Washe gari ya kasance ranar Laraba,kamar yanda akasani gidan a cike yake saboda kiran Family meeting da Malam yayi na gaggawa. kamar yanda aka saba gaba ɗaya family’n sa dake state ɗin in dai jumma'a ko ya kira taron gaggawan nan gidan suke zuwa maza da mata.
Daidai lokacin da za'a gabatar da Sallah azahar Taj ya tashi daga sahun farko da yake ya kara matsawa gaba sanin cewa muddin yana ƙasar shi yake jansu sallar Juma'a madadin mahaifinsa da kuma kamsutSalawat a masallacin su na gida.
Sai kuma ya danyi sauri yaja da baya ganin Yah Abana ya ɗaga masa hannu alamar ya tsaya ahankali ya koma ya tsaya a sahun farko.
Yah Abana kuwa da kansa ya tada iƙama akayi sallar azahar, bayan an idar da sallar duk gida suka koma Taj kuwa gidan Addawa ya wuce.
Acan gefen gidan Yah Abana kuwa gaba ɗaya yasa Iyalansa suka taru kasancewar Meymey bata zoba yasa Yah Abana ya kalli Kabeer kasancewar shine karami atausace yace.
“Kabeer je ka ɗauko min Laylah da Meymey.”
Kai Kabeer ya gyaɗa cikin sauri tare da ficewa ya nufi Parking space...
Motar Kabeer na ƙoƙarin fita na Taj na shigowa cikin gidan ahankali ya fito daga motar bayan Abu Hashim yayi Parking hannunsa na riƙe da wata sanda me kyau wanda Sheikh Taju Usman Bauchi ya bashi zuwansa Nigeria yana shiga cikin gida direct Falon Ummey sa ya wuce zaune ya sameta tare da Yayunsa har Aunty Halima wacce itama ayau ta taso tazo saboda sun fahimci kiran taron baya rasa nasaba da ɗan uwansu.
Ganinta yasa ya fesar da numfashi kana cikin yanayin sanyinsa yace.
“Aunty Halima me ya kawo ki Lafiya kuwa?”.
Cikin shesh-sheƙan kuka mai cike da tarin tausayinsa tace.
“Taju ka manta kenan?
Tambayata ma kake lafiya?,ka mance halin da muke ciki?”
Adai-dai lokacin kuwa Falon Yah Abana cike yake da ƴaƴansa jikokinsa da kuma Uncle Jibril da Momyn Meymey saura Meymey sannan Laylah, da kuma Khabeer had’i da ahalin Ummey.
Cikin hakane Aryaan ya shigo falon Ummey tare da cewa.
“Ummey Abba yana neman ku”.
Kai ta gyaɗa kana suka miƙe suka bi bayan Aryaan suka shiga dai-dai lokacin kuma motar Kabeer dake dauke da Laylah da Meymey yayi Parking.
Yah Abana kuwa hannu ya d’aga tare da nunawa Taj gabansa alamar yaxo ya zauna yayin da baki d’aya sauran ƴaƴansa kowa yana inda yake.
Dai-dai lokacin kuma Meymey, Laylah da kuma Kabeer suka shigo falon.
Da hannu Yah Abana ya nunawa Meymey da Laylah tsakiyarsu kan su zo su zauna.
Suna zama Yah Abana ya ɗago kansa ya kalli Taj tare da cewa.
“A yau ɗin nan awannan lokaci nake baka dama ta ƙarshe Akuma yanzu ka buɗe baki kayi min maganar da zan fahimta zan gane.
Wannan itace dama ta ƙarshe da zan iya baka a rayuwata ka faɗa min me gaskiyar abinda ke faruwa ya akayi Laylah take da ciki”.
Idanunsa da suka kuma yin jawur ya rumtse tare da d’an jijjiga kansa, cikin sanyi had’i da bugawar zuciya ya jujjuya kansa tare da faɗin.
“Yah Abana kayi haƙuri ban sani ba….”
Jin abunda yace ne kuma yasa baki ɗaya hankalin Ummey, Aunty Rashida, Aunty Maryam, Aunty Halima, da kuma Zakiyya ya tashi sosai, cikin kid’ima had’i da gigituwa suke kallonsa hawaye na zuba a idanunsu.
Yah Abana kuwa kallonsa ya mayar kan Meymey dake zaune cikin tsukakkiyar fuska yace.
“Meymey me kika ce ranan?”
Baki ta bud’e cikin zubda hawayen munafurci tace.
“Abbah wallahi Yah Afif shi yayiwa Laylah ciki”.
Cikin sauri Hajiya Babba tace.
“Toh me hujjarki Sannan menene Shaidar ki?”
Cikin shesh-sheƙa ta yi wa Taj da kansa ke ƙasa wani irin kallo kana tace.
“Ina da hujjoji da yawa da kuma shaidu”.
Lokaci d’aya Yah Abana cikin rashin walwala had’i da tsuke fuska yace.
“Menene shaidun ki?”
Tana goge hawayen dake zubo mata tace.
“A tambayi ita Laylah ɗin”.
Da sauri Yah Abana ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya maida kallonsa ga Taj.
Taj kuwa juyawa yayi yana kallon Laylah haka zalika duk wanda ke cikin Falon Laylah yake kallo.
Sabanin Momyn Meymey data zubawa ƴar Tata Idanu tana mai Binta da wani irin kallon tuhuma.
Laylah kuwa kanta ta sunkuyar ƙasa.
Cikin murya mai cike da damuwa da tsantsar tashin hankali daya bayyana asaman fuska Yah Abana ya kalli Laylah tare da cewa.
“Laylah”.
Kanta a ƙasa tace.
“Na'am”.
Sake kiranta yayi amsawa tayi batare data ɗago kanta ba.
Cikin sauƙe ajiyar zuciya ya sake kiranta akaro na uku tare da cewa.
“Ɗago kanki ki kalleni”.
Ahankali ta ɗago kanta ta kallesa.
Yana mai jin bugun zuciya yace.
“Kinsan akan me ake magana?”.
Kai ta gyaɗa.
Ɗan muskutawa yayi tare da faɗin.
“Magana zakiyi”.
Cikin shesh-sheƙan kuka tace.
“Eh”.
Yana mai runtse idanunsa yace.
“Kinsan cewa ance kina da ciki a asibiti?”
Jikinta na tawa tana me kokarin danne kukan dake taso mata tace.
“Eh”.
Cikin sanyi gami da tsoro had’i da fargaba Yah Abana yace.
“Laylah waya Miki ciki?”.
Kusan baki ɗaya zukatan mutanen dake Falon bugawa yake musamman ma masoyan Taj.
More especially Ummey zuciyarta yafi na kowa bugawa.
Laylah kuwa cikin sanyi da rawar murya tace.
“UNCLE TAJJ NE!!”
Lokacin ɗaya Taj yaji baki ɗaya ilahirin jikinsa yana narkewa kamar an shanye jinin jikinsa ji yake tamkar yana zama yashi yana narkewa jin yanda kalmar ya daki ƙoƙon zuciyarsa cikin sauri ya juya ya kalli Laylah sai kuma ya juya ya kalli Meymey da ta saki wani Murmushi wanda daga shi sai Ubangijin daya haliccesa suka san manufarsa.
Da sauri Aunty Halima da jikinta ke rawa ta matsa kusa da Laylah’n cikin tarin damuwa da kuma tashin hankali tace.
“Laylah kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya Uncle Taj ɗinki nefa”.
Kai Laylah ta jinjina cikin zub da hawaye tana me ci gaba da sakin shesh-sheƙan kuka tace.
“Wallahi shine kullum in ya dawo gari aɗakina yake kwana kuma yace idan na faɗa zai yankani…”
A yanzu kam baki ɗaya ilahirin jikin Taj karkarwa yake da tsuma idanunsa sunyi jajur sun kada tamkar wuta, yayinda yake jin kamar ana kwara masa narkakkiyar dalma tun daga tsakar kansa har zuwa k’asan k’afafunsa, tabbas aduk rayuwarsa bai tab’a ganin tashin hankali da masifa irin wannan ba.
Yah Abana kuwa baki daya idanunsa ne suka rikice tare da sauya launi suba farare ba haka kuma su ba jajaye ba, kar-kar-kar haka jikinsa ke rawa.
Laylah’n kuwa kuka ta ci gaba da rerawa batare data kuma yin magana ba.
Yah Hafiz kuwa cikin wani irin yanayi na tsoro da kiɗima jikinsa na rawa yace.
“Meymey kiji tsoron Allah kisan abinda kike faɗa”.
Sai alokacin Uncle Jibril ya dago Kai ya kalli Yah Hafiz tare da cewa.
“Hafiz Mamana bata ƙarya tun tana ƙarama ban shedeta da ƙarya ba”.
Cikin takaici da wani irin yanayi Momyn Meymey ta katsesa da cewa.
“Ɗan Adam yana iya sauya hali akowani lokaci Alh ka daina shaidar Meymey”.
Cikin sauri Yah Abana ya karɓi maganar da cewa.
“Kamar yanda kuma shima Afif dan Adam ne da zai iya sauya halinsa akoda yaushe ba.”
Ummey kuwa cikin tashin hankali marar misaltuwa take kallonsa kana murya na rawa cike da tarin d’imuwa had’i da karyewar zuciya tace.
“Babana kayi magana! kayi magana Afif ka wanke kanka kace wani abu!!”
Me zaice? Bazai iya cewa komai ba, bazai iya ba, kansa juyawa yake yana jin kamar mafarki ne, zuciyarsa tayi masa mugun nauyi, yana jin kamar ana caka masa mashi akan k’ahon zuciyar nasa, komai ya riga da ya k’wace masa, baida wani abunyi sai kansa kawai da yake girgizawa, again ya kasa magana jikinsa ne kawai keta karkarwa.
Mom Amal kuwa cikin wata murya me ɗauke da wasu irin manufofi da ita kaɗai tasan ma'anar su tace.
“Wannan ma bai isa hujja ba Meymey idan kina da wasu hujjojin sai ki fito dasu mugani ”
Cikin sauri Meymey ta ciro wayarta ta bud’e tare da shiga Gallery bayan ta shiga kan abunda take son shiga ta juyo da screen d’in wayar zuwa fuskar Yah Abana.
Da sauri Yah Abana ya rumtse idanunsa sai kuma ya miƙe tsaye yayin da numfashinsa ke fusga yana ƙoƙarin ɗauke wa.
Sakamakon ganin hoton Taj da yayi tsaye tsirara Laylah na durƙushe ta riƙe gabansa.
Da wani irin firgita had’i da gigita mai tsanani ya fara cewa.
_“Auzubillahi minarshaiɗanir rajim Auzubillahi da kai Tajudden Subhanallahi da kai Tajuddeen ka ƙazanta ka barranta daga zuri'ata ka barranta daga ahalina.“_
Taj kuwa kansa ya soma girgizawa cikin son yaga abinda Mahaifinsa ya gani da ya kiɗimashi haka.
Uncle Jibril kuwa cikin sauri ya miƙe ya karbi wayar daga hannun Meymey yana kallo cikin tashin hankali yace.
“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Afif ka zama guba ka zama ƙazanta acikin al'umma wannan wani irin nasiface Tajudden wace rayuwa ka zaɓawa kan ka”.
Ya ƙare maganar tare da sake wayar ta faɗi ƙasa, haka yasa ta ɗan sule zuwa gaban Taj ɗin.
Shi kam Taj ya kasa tantance yanayin da yake shin araye yake ne ko ko kuma amace? Saboda ganin tabbas shine a hoton kuma tabbas tsirara yake, kuma tabbas Laylah ce gabansa durƙushe tana riƙe da al'aurarsa, so yake ya rufe ƙwayar idanunsa ya buɗe ko zai daina ganin ɗigon tawadan Allah da yake a saman mararsa wanda yasan duk duniya banda iyayensa da suka raineshi a ƙuruciya babu wanda yasan dashi.
Cikin kuka Meymey tace wlh gashi in ba shi bane ya faɗa.
Cikin wata iriyar muryar dake cike da hargitsi Yah Abana yace.
“Tajjuddeen wai kaine a hoton nan!?”.
Cikin jin ƙahon zuciyarsa na gaba da faso ƙirjinsa murya na rawa yace.
“Eh Yah Abana ”.
Yayi mgnar da iya kar gskyar sanin cewa yess tabbas shi ɗin ne.
Ummey kam kuka mai tsanani ta fashe dashi ta kasa magana haka zalika sauran ƴaƴanta da mafi akasarin Mutanen falon...
Meymey ko gyara zama tayi tana matsar ƙwalla tace.
“Kuma har Video ma akwai”.
Cikin sauri Taj ya ɗago kansa jin yanda Yah Abana ya kira sunansa atsawace.
Ahankali ya ɗago raunatattun idanunsa da suka ciko da k’walla suna sheƙi ya kallesa jin yana cewa.
“Afif ka tashi ka fitar min agidana kabar min gidana bari na har abada bana son ganinka.
Bana son sake kallon wannan ƙazantacciyar fuskartaka arayuwata Afif bana son ka sake shigowa cikin gidana.
Wallahi Allah kenan idanka sake yarda mu kayi ido huɗu Allah ya isa tsakanina da kai!!!”
Cikin tsananin ruɗu mutanen dake falon ke kallonsa.
Passs sautin fashewar glass cup dake hannun Yah Abduraham dake bayan Taj ya ratsa kunnuwansu.
Shi kuwa Malam cikin tsanar halayyar Taj ya cigaba da cewa.
“Kaje na sallamawa duniya kai Afif.
Na barrantarwa duniya kai na cireka daga cikin ƴaƴana daga yau ka fita acikin ƴaƴana.
Tajudden daga yau Allah ya isa idan har ka sake ambaton sunana a bakin ka matsayin mahaifinka”.
Cikin tsananin kaɗuwa mai gauraye da ruɗani Yah Hafiz da Yah Yusuf suka runtse idanunsu suna masu girgiza kansu Yah Abdurrahman kuwa wani sanyayyan kuka ya saki mai cike da ɗimuwa ganin halin tashin hankali da ahalinsa ke ciki.
Su Aunty Maryam kuwa, tamkar an daskarar dasu da dusar ƙanƙara haka suka zama.
Ummu Aryan ko da Hajia babba riƙe kai sukayi.
Mommyn Meymey kuwa da ƙarfi tace.
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”.
Yah Abana kam cikin ƙunan zuciya da tsananin fushi ya cigaba da cewa.
“Daga yau ka yanke sunana daga cikin bakinka bana buƙatar ka acikin rayuwata na barrantar da kai daga cikin zuri'ata ku kuma kuji ku shaida dalilin da yasa na taraku”.
Sai kuma ya dire maganar yana kallon ƴaƴan nasa.
Rai cike da ƙunci ya sauke ajiyar zuciya tare da juyawa falon yana kallon ƴaƴansa yayin da numfashinsa ke sama da ƙasa alamar yana son barin gangar jikinsa yace.
“Ku kuma kuji ku shaida duk wanda ya sake mu'amala da Tajudden Allah ya isa ban yafe masa ba, na kuma tsine masa duk wanda ya sake mu'amala dashi bani bashi, ku kuma Matana duk wacce ta kiramin sunan Tajuddeen zata ga fushina, kai kuma Tajuddeen ka tafi kai bazan tsine maka ba, kuma bazan maka baki ba, dan laifin da kayi ya isheka tsinuwa, kawai ni sharaɗin tsinuwana idan ka sake yarda mukayi ido biyu da kai to akan igiyar auren mahaifiyarku kuma bazan yafe maka ba muddin kayi sanadin rabani da Fatima”.
Wani irin kuka mai gunji Aunty Halima, Aunty Maryam, Aunty Rashida suka sake suna masu shiga ɗimuwar jin abinda mahaifin nasu ya faɗa.
Haka ma sauran Matan Mom Amal kuwa fuskarta ba yabo ba fallasa baza ka gane shin farin ciki take ko akasin saba.
Tajudden kuwa kansa na ƙasa ji yake tamkar almara ne ji yake shin mafarki yake ko ko afarke baki daya ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa sun gaza auna kalaman Yah abanansa...
Yah Abana kuwa cikin wani irin kunci zuciya mai tafe da nadamar kasancewar Tajudden jininsa ya cigaba da cewa.
“Idan ka sake yarda kayi ka nunani a matsayin mahaifinka Allah ya isa ban yafe maka ba idan ka yarda ka sake shigowa gidan nan ko kuma ka sake magana da ɗaya daga cikin Ahalina ban yafe maka ba kuma akan igiyar Auren Mahaifiyar ka...
A dai-dai lokacin da yake fadar haka kuma Ummey taja wani dogon numfashi mai nauyi take ta fadi asume.
Lokaci ɗaya kukan Aunty Maryam Aunty Halima Aunty Rashida ya sake tsananta
Yah Yusuf da Yah Hafiz kuwa da rarrafe suka isa gaban Mahaifinsu kana suka riƙe ƙafafunsa tare da cewa.
“Yah Abana kayi haƙuri Tajuddeen bai cancanci wannan abin ba,Wannan hukunci ya masa tsauri kuma muma ya mana tsauri Yah Abana kayi hakuri kada ka yanke wa Tajuddeen hukunci cikin fushi”.
Yah Abdurrahman kuwa da ƙarfi ya matso yana buga kafaɗar Tajuddeen tare da cewa.
“Afif kayi magana Tajudden ka wanke kanka Tajuddeen ka wanke zargin da Mahaifin mu yake akanka Nasan cewa baka aikata ba”.
Taj kam ya kasa motsa laɓɓansa bare ya iya sarrafa harshensa wajen magana.
Aryaan da Kabeer kuwa duk da irin tsanarsa da kuma haushinsa da suke ji sai da hukuncin da Yah Abana ya ɗauka ya girgizasu...
Cikin sauri Taj ya miƙe jin Yah Abana na cewa.
“Ba naso ka ƙara koda 5 minute ne acikin gidana idan ka ƙara ban yafe ba Tajuddeen in ka sake kusanto inda mahaifiyarka take ban yafe ba kuma wallahi akan igiyar Aurenta su Maryam kuma na rabaka dasu”.
Ya kai ƙarshen maganar tare da faɗawa kan kushin .
Cikin kifewar tunani da cushewar zuciya gami da rashin sanin abinyi Taj ya juya tare da ɗaga ƙafarsa dan fita.
Kan glass cup ɗin da ya fashe a hannun Yah Abduraham ya dire ƙafarsa ta hagu.
Cikin sauri Ummu Aryan tace.
“Ya Salam Taj glass ka taka fa”.
Ina baya jinta bare ya iya tsayawa, hasali ma zogin zuciyarsa ya hanasa jin zogin sukan glass ɗin.
A haka yaci gaba da takawa yayinda tuni jini yake meye gurbin shatin sawun nashi.
Da gudu Aryaan ya shiga ɗakin Yah Abana ya ɗauko maganinsa kana ya basa.
Aunty Maryam da Aunty Rashida kuwa Ummey suke jijjigawa.
Ganin haka yasa Yah Yusuf cicciɓan Ummey ya nufi asibiti Aunty Maryam da Aunty Rashida na biye dasu.
Taj kuwa Ahankali ya ɗan kuma juyowa tare da zaro sandar da Sheikh Tajuh Usman Bauchi ya bashi ya ajiye agaban Mahaifinsa tare da faɗin.
“Yah Abana gashi wannan saƙone daga wurin Sheikh Tajuh Usman Bauchi Nigeria daya bani in baka ban samu na baka ba sai yau”.
Cikin tsawa Yah Abana yace.
“Ka fita daga nan bana son ganinka ka ɓace min da gani idan ka sake minti biyar acikin gidan nan Allah ya isa ban yafe maka ba kuma zan tsine maka!!!”
Da sauri ya miƙe tsaye sai kuma ya tsaya jin Yah Abana na cewa.
“wannan ɗin kuma da kayiwa ciki kai zaka ɗauketa kasan yanda zakayi da ita,' saboda cikinka ne bana uban kowa ba.
Kuma dama kai ka kawota cikin ahlina so yadda ka kwasota ka kawo haka zaka kwahseta ku tafi tare da abin kunyarku.
Sannan ka saki Meymey ƴar Aminina ba zata zauna da ƙazamin mazinaci ba ka tabbatar a yau ɗin nan ka saketa”.
Idanunsa dake gane masa duhu ya rumtse tare da mik’a hannunsa ya kamo hannun Laylah suka fita.
Tafiya kawai yake amma baisan inda yake sa ƙafarsa ba, hasalima baya cikin hayyacin sa, meye zaiyi ko ina zai dosa duk baisani ba, ahaka ya ci gaba da tafiya k’afarsa na zubar da jini sannan yana rik’e da hannun Laylah dake ta kuka haka suka dinga tafiya da sawayen su har suka k’araso gidan Addawa...
Cikin murya mafi rauni da sanyi yace.
“Addawa ga Laylah nan ance cikine da ita kuma ance wai ni nayi mata cikin kuma itama ta tabbatar da hakan”.
Hankali atashe Addawa ta kalli Laylah murya na rawa tace.
“Laylah waya miki ciki?”.
Da sauri da kuma alamun tsoro Laylah ta matsa gefen Addawa, again murya na rawa tace.
“Uncle Taj ne”.
Cikin tashin hankali marar misaltuwa Addawa tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Afif meye gaskiyar maganar? menene gaskiyar lamarin”.
Kai ya girgiza kana cikin rauni, had’i da k’unan zuciya me tsanani yace.
“Nima ban sani ba