Showing 3001 words to 6000 words out of 74955 words
Chapter 2 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
sai gashi cikin ikon Allah yau tafiya ta haɗamu”.
Murmushin Garkuwa tayi wanda ke nuni da karamci da kula ga duk wani Masoyinta tare da kallon Aysha da ta fara yi musu video tana cewa.
“Bari inyi mana video”.
Tafin hannunta tasa ta ɗan kare fuskarta tare da cewa.
“Ya isa haka, muyi addu'a za'a tashi yanzu”.
Kai Maryam ta jinjina.
Ita kuwa Aysha Matawalle wani sabon video ta fara cikin nitsuwa da maɗaukakin jin daɗi take mgna.
“Hi Barrister wannan video en nakane, kaga yanzu zamu tashi, ance 6:00 pm zamu tashi yanzu saura One minute mu tashi, ka samu a addu'a Allah ya kawomu lfy muzo mu sameku lfy”.
Sai kuma tayi saurin juya wayar ta gefen window sit ɗinta.
Tare da zurawa harabar Airport ɗin ido.
A ranta take cewa.
Laaa ashe jirgima kamar mota yake tafiya, da tayoyisa a ƙasa yana fesa gudu, ikon Allah.
Ita ma Maryam window sit ɗinta take leƙawa.
Haka dai kowa da abinda yake yi cike da farin ciki zasu ziyarci ƙasa mai tsarki.
Cikin sauri Aysha ta tasa wayarta a Airplane mode, saboda jin ɗaya daga cikin Hostess ɗin na ce mata, ta kashe wayarta.
Haka yasa ta ɗan kife wayar bisa cinyarta tare da gyara zamanta kana ta gyara saƙala Aepeace ɗin dake kunneta, tana mai jin waƙar IN DA RAI, na sani akwai rabo yana zuwa.
Haka yasa ta gyara zamanta tare da sauƙe sassayan numfashi tana mai hamdala a ranta tare da tariyo dukkan tarin buƙatunta domin wakar kan sosa mata taɓon ƙaddararta.
Yess ai dama in dai da rai akwai rabo duk zafin ƙaddaarka bazaka cire tsammanin warakaba, numfashi mai sanyi ta fesar tana mai mgnar zuci tace.
“Alhamdulillah oh Yah Allah na gode maka, yau nice Aysha zan tafi maka, Yah Allah ka isar damu lafiya, in ganni gaban ka'aba, in ruggumi Ka'aba, in faɗi tarin ƙaddarorina da jarabbobina masu zafi da ɗawainiya da rayuwata inyi addu'a in sha Zam-zam inyi tawassali dashi, in har akwai jinnu ko wata cutar dake tare dani dake hanani samun salama da zaman lfya a rayuwar zaman aurena.
Rabbi ka yaye minshi.
Ka sauƙaƙa min. Jarraba mai zafi, domin Jarrabawar Aure itace Jarrabawar mafi ciwo a zuciyar ƴa mace ba Jarrabawar data fita ciwo sai na cuta.
Yah Allah kasa inyi Hajj Mabrooq Allah ka amsa min addu'o'in da zanje, inyi.
Yah Allah ka takaitamin matsalar rashin nagartar aure kasa in nayi aure da Barrister sai mutuwa zata rabamu.
Yah Allah in dai aurena da Barrister alkhairi ne, Allah ka tabbatar dashi, Yah kasa shirin aurena da Barrister ya tabbata, ko dan farin cikin Mahaifiyata da Mahaifina, ko dan in tsira da zargin mutane dake ganin cewa, nice naƙiyin aure.”
Wannan sune maganganun zuci da Aysha takeyi.
Dai-dai lokacin kuma tayoyon gaba na jirgin ya fara rabuwa da ƙasa, alamun yanzu zasu ɗaga kenan.
A can gaba kuwa wurin pilots ɗin, cikin natsuwa da tsanantan bugawar da zuciyar da Taj keyi, yaci gaba da saita komai na tafiyar, yadda kawai zai zauna ne, yana kallon na'urorin ba tare daya taɓa komai ba, muddin sun ɗaga sama.
A can bayan kuma wurin passingers ɗin.
Cikin sauri sababbin fara shiga jirgi duk suka rurtufe idanunsu kowa da addu'ar da yakeyi.
A gefen First class kuwa.
Da sauri Aysha ta matso gaban kujerar tare da kife kanta da jikin kurejar dake gaban tata kujerar wanda Maryam ce a kai.
Cikin tsananin kaɗuwa da tsoron da mafiya akasarin mutane sukeji a shigan su jirgi na farko.
Rumtse idanunta tayi da masifar ƙarfi lokacin da taji jirgin ya rabu da ƙasa baki ɗaya, ferfelan sun fara aiki na musamman damonin tare iska dan saita hancin jirgin wanda , haka yasa jirgin ke marisa irin dai ƴar marisar nan da manyan jirage keyi in sunzo tashi, dan nasu baya kai na ƙananan jirage irinsu...
Saurin ƙanƙame saman kujerar da Maryam ke kai Aysha tayi tare da riƙewa saboda wani zuuummmmm da taji jirgin yayi tamkar zai rikito ya faɗo ƙasa, wanda hakan yasa taji zuciyarta ta bada sautin zummmm ɗin har takeji kamar hanjin cikinta na barazanar ɓarewa, ya Salam Aysha Farar kura ga tsoro ga ban tsoro.
Wani irin karkarwa jinkinta ya fara yi tamkar mazari, saboda azabebben tsoro da tsinkewar zuciya.
Kar-kar haka jinkinta ke rawa cikin tsananin kiɗima ta fara.
Karanto duk addu'o'in dake zuwa zuciyarta da bakinta.
Da tsananin ƙarfi ta rumtse idanunta lokacin da jirgin ya danyi juyin ɗaukar asalin hanyarsa.
Kiɗimarta da diriricewarta ta tsananta ne saboda jiyo wata babarbariyar dake sit ɗin gaba da na Maryam ta zurma wani irin gigitaccen ihu, da addu'o'i cikin harshen barbarci take cewa.
“Wayyyo Allah hanjina wayyyyyoohhhh zamu faɗi fa”.
Garkuwa kam murmushi mai ɗan sauti tayi, saboda tuno yanayin da ta shiga lokacin forko da ta fara shiga jirgi.
Sai kuma ta kalli Aysha dake wani irin karkarwa jinkinta baki ɗaya tsuma yake.
Hakane yasa ta yunƙura da sauri alamun zata tashi, sai kuma tayi maza ta koma ta zauna saboda Hostess ɗin dake nufosu da tayi mata alamar ta zauna.
Zaman tayi tana mai kallon Aysha yayinda ita kuma ƴar matashiyar balarabiyar ta tsaya gaban babarbariyar nan, tare da zama gefenta ta ruƙo hannunta tana mai kwantar mata da hankali.
Aysha kuwa zuwa yanzu ta saki duk inda ta riƙe saboda jin yadda suke marisa a sama yasata, fara fuzgar numfashinta dake kubce mata.
Shike nan ashe tsananin son zuwanta Makka da takeyi, shine silar rayuwarta, tunda gashi a jirgi zuciyarta zata buga ta mutu, ashe burin iyayenta bazai cikiba, ashe abinda take tsoron mutuwa ba igiyar aure a kanta shi zai sameta, Allah sarki Barrister yana jiran mu isa ashe ni kam bandani.
Sai kuma maganganun zuci da takeyi suka kafe mata, saboda wani zuuummmmm da taji kamar jirgin ya tsinko ya taho ƙasane.
Wannan yasa ta ƙara ƙanƙame sit ɗin da Maryam ke kai, wacce itama gaba ɗaya tayi zuru-zuru da idanunta.
Ita kuwa Aysha ji takeyi tamkar ta ɗaura hannunta bisa tsakiyar kanta, ta rinƙa kwarara ihu da shelanta, a sauƙeta ta fasa tafiyar, toh Amman ta hani kanta da yin hakan saboda sanin ko tayi tasan baza a sauƙanba.
“Yah ilahi ya mujibadda'awati.”.
Ta faɗa da ƙarfi lokacin da taji jirgin ya harba can sama ya lula alamun ya saita hancin sa bisa da'irar taswirar hanyarsa.
Da sauri Garkuwa ta ɓalle sit belt dinta tare da miƙewa, tsaye ta nufi kan Aysha saboda ganin duk jinkinta ya ɗebi karkarwar tamkar wacce aka jonawa wutar lantarki, kana numfashinta nayi off and dawn, bisa alamufa ta kusa suma.
Da sauri ta riƙo hannunta tana faɗin.
“Hostess help help”.
Jin hakane yasa Hostess biyu dake bayansu saurin isowa kusa dasu.
Ita kuwa cikin kulawa take jijjiga Aysha dake karkarwa gaba ɗaya jinkinta sai ƙirjinta dake ɗagawa sama da ƙasa.
Ɗaya hostess ɗince tayi saurin ɗaga sautin muryata tare da juyawa ta nufi, side ɗin inda suke tana cewa.
“Abata ruwa”.
Da sauri ɗaya daga cikin waɗanda ta haɗu dasu suna turo, ruwan da zasu fara rabawa passingers ɗin ta miƙata goran ruwar, amsa tayi kana ta juya da sassarfa.
A dai-dai lokacin kuma a can cikin wurin su pilot Irfan Imran.
A hankali Taj ya ɗan juyu ya kalli abokin aikin nasa kuma amininsa ɗan ƙasar Palastine.
Murmushin Pilot Irfan Imran yayi saboda ya fahimci me aminin nasa ke nufi.
Haka yasa ya tashi daga inda yake, kana yazo ya zauna inda Taj ɗin ya tashi Taj.
Ɗan miƙa yayi tare da rumtse idanunsa, saboda tsananta da bugun zuciyar keyi, fuskarsa ya ɗan shafa, kana juya ya nufi Bathroom ɗinsu saboda zaiyi al'walan sallan Magrib, dan yaga lokacin sallan Magrib ne ya yayi a ƙasar Nigeria ɗin.
Jim kaɗan da shigansa, ya fito, da alamun yayi al'walan dan fuskarsa dake ƙellin ruwa, wanda babu wani gashi ko ɗan tsilli a saman kekkyawar fuskar tasa face gashin girarsa dana ido.
Da ido ya ɗan zuba wani ɗan na'ura mai haska musu abinda ke faruwa a cikin wurin passingers ɗin,
Hannun rigar jikinsa ya ɗan fara warwarewa saboda naɗewa da yayi kafin yayi salla.
Shiru yayi a tsaye ganin kusan Hostess nasu duk suna tare wuri ɗaya.
“Mitsss.”.
Ya ɗan ja gajere tsaki a saman lips ɗinshi, ganin sun bar passingers ba ko ruwa bare aje ga ɗan wani abun ci.
A hankali ya ɗan daddanan wasu pins ya buɗe ƙofar dake tsakiyarsu da passingers ɗin fist class, wanda kujerar babarbariyar nane firko sai ta Maryam kana ta Aysha.
A gefen dama kenan.
Ganin shine yasa duk Hostess ɗin mimmiƙewa tsaye, cikin tsananin girmamawa da kiyaye tsarin aikinsu.
Maida hankalinsu, a hankali ya haɗe lips inshi da ya buɗe tare da cewa.
“What happened?”.
Cikin sauri ɗaya daga cikinsu tayi mishi bayanin abinda ke faruwa.
Yayin da Maryam da Garkuwa kuwa duk sun kiɗime sai kiran sunan Aysha daketa karkarwar tamkar mazari suke.
Juyowa Garkuwa tayi ta kalli bayanta jin ana ce mata ta matsa ga Dr Taj zai duba Aysha.
Jin haka ne yasa tayi saurin matsawa, tare da jan hannun Maryam, suka bashi fili.
Shi kuwa Taj da sauri ya lumshe idanunsa kana, a hankali ya ɗan sunkuyo kanta, sai kuma yayi saurin datse lip inshi na ƙasa da haƙoransa na sama, saboda wani irin masifeffen harbawa da zuciyarsa tayi tamkar zata ɓallo ƙahon zuciyarsa tayi waje.
Ita kuwa Aysha zuwa yanzu dai saura ƙiris tsoro ya sumar da ita, duk da jirgin ya dai-da ta kan hanyarsa.
Shi kuwa Taj cikin ƙarfin hali ya buɗe kwayar idanunsa ya tsaidasu kanta, alamunta da yanayin yadda take yi yafi kama da na mai iska.
Domin karkarwar da salatin yasa ta sule tayi ƙasa.
A hankali yasa hannunsa na dama ya riƙo hannunta na dama.
Rumtse idanunsa ya kumayi da ƙarfi kana ya jawota ya zaunar da ita kan kujerar.
Kana ya zauna gefen hannun kujerar, tata ba tare da ya saki hannunta ba.
Cikin gamsuwa da yaƙinin aljanune a kanta ya ɗan juyo ya fuskanceta da kyau
tare da yin auziya kana yayi basmala.
Ya buɗe lips inshi a hankali tare da ɗan ɗaga sautin muryarsa ya fara karanto mata ƙebantattun Ayatush shifa na Alkur'ani.
Ya Salam shine, abinda Garkuwa Da Maryam dama duk sauran waɗanda ke wurin sukace tare da lumshe kwayar idanunsu, saboda jin wani irin amintaccen zazzaƙan sautin muryarsa da yake rero karatun ƙur'ani cikin nitsuwa da cikekkiyar tajweed mai fidda amintaccen Ghunna, Qalqal, iqlab da idgham hadida Ikhfa'a masu sa zuciyar ko wani muminin mutum da aljan samun nitsuwa. Nitsuwar kuwa harda Babarbariyar nan ta nitsu.
Ita kuwa Aysha wasu tagwayen ajiyan zuciya masu nauyi ta fara sauƙe.
Lokacin da taji Ya Kawo ƙarshen.
Suratul Fatiha
Sai kuma taja dogon numfashi jin ya ɗauko,
Ayatul-kursy
A hankali wani nitsuwa ya fara diro mata, wanda yasa jinkinta fara mutuwa. jin ya fara karanta,
Aamanar-rasuulu sai kuma ya ɗauki.
Laqad ja'akum
A hankali tayi luuuh ta ɗan jingina da gefenshi jikinsa lokacin da taji ya fara karanta.
Wattaba'uu ma tatlush shayaɗeenu ala mulki sulaymaan.
Zuwa yanzu ta fara samun nitsuwa. Jinginar da tayi da jikinsa ne kuma ya sa wayarsa dake cikin aljuhun rigarsa sulowa ya fito ya faɗi,
Dai-dai inda wayarta dake kan cinyartan ya faɗi gefen wayarta
Wani ni'imtaccen bacci ne ta fara jiyowa yana diro mata daga sama kanta, numfashin samun nitsuwa ta shaƙa gami da ni'imtaccen ƙanshin turaren jikinsa mai sanyaya zuciya, a lokacin da taji yana karanta.
Qulyaa ayyuhal kaafiruun
Sai kuma ya ɗaura
Qul huwallahu Ahad.
Qul a'uuthu bi rabbil falaq.
Qul a'uuthu bi rabbin-naas.
A hankali ta gyara jinginar ta da jikin kujerar tata yayinda rabin gefen kafaɗarta yake ɗan jingine kaɗan da rabin kafaɗarsa wanda ko ya tashi ma bazata zameba.
Ganin hakane yasa Maryam da Garkuwa dama duk sauran kowa ya koma mazauninsa, ganin tayi bacci.
Shi kuwa Afif Taj, cikeda taushin murya yaci gaba da kawo ayoyin wasu surorin kamar haka.
Suratul isra'i aya ta 81 zuwa 82.
Suratush-shu'ara aya ta 78 zuwa 82.
Suratus-sajadah aya ta 13 zuwa 14.
Suratu aali Imran aya ta 139.
Suratuz-zumar aya ta 18.
Suratul-ankabuut aya ta 41.
Suratul-ahazaab aya ta 22. Kafin yazo ƙarshen tuni baccinta yayi nisa, ta samu cikekkiyar nitsuwa ta falalar Alqur'ani mai girma kenan.
A hankali ya ɗan kalli gefen fuskarta kana, ya ɗan yunƙura ya miƙe, yana mai ɗan shafa aljihunsa, sai kuma ya kalli gefenta, hannunshi yasa ya ɗauki waya.
Dai-dai lokacin kuma hankali sa.
Na kan Hostess ɗin su dasukaci gaba da rabawa passingers ɗinsu abinci da sha.
Daga nan sukaci gaba da tafiya, suna keta hazo.
Ƙarfe goma dai-dai agogon Nigeria Niger Cemaroon da Chadi wanda yayi dai-dai da ƙarfe sha biyu da minti uku kacal, jirgunsu yayiwa King FAHD international Airport dirar mikiya, dora kuwa irin wacce ba zato ba tsammani domin duk da sun san da sauran jirginsu ɗaya a Nigeria bai hanasu cuku-cukun rufe Airport din ba kamar yadda sukace.
Shi kuwa Taj.
Da sauri ya kutsa kan jirgin bisa da'irar da suka bashi damar saukan 12:00 duk da kuma ganin alamun gargaɗin da suke yi mishi, hakan bai hanashi sako kai gadan-gadan ba, wanda bisa dole yasa suka fara shirin tarbarsa cikin gaggawa, domin da har sun fara datse na'urarorinsu.
Murmushi mai sauti Balaraben dake can cikin dogon gidan da suke iya ganin gilmar koda tsutsace aƙasan wurin ko sama.
Ya sani wannan aikin Taj ne, domin matashine mai jini a jika, wanda burin rayuwarsa na duniya pilot, haka kuma babu abinda ke sashi karsashi da shauƙi sama da ya ganshi yana sarrafa jirgi.
Murmushin yayi tare da bashi umarnin dirowa,
Duk da yasan Taj ɗin zai fuskanci ƙalubalen tuhumar dalilinsa na wuce lokacin da aka bashi da kuma yi musu kutse cikin Airport insu.
Sau ƙintama shi ma'akacinsu ne, Amman yasan duk da haka da wuya in bai fuskaci dakatarwaba, bisa gargaɗi mai ƙarfi.
A nan cikin jirgin kuma Irfan Imran ne, ya saki wani zazzafan numfashi.
Jin gubbbb alamun tayoyin jirgin sun dira ƙasa.
Aysha kuwa wannan ƙugin shi yasata rumtse idanunta, tare da ɗauka wayar gefentan tasa a cikin hand bag dinta, sabida jin Garkuwa nace.
“Alhamdulillah mun isa lfy”.
Murmushi tayi tare da buɗe windo gefentan tana kallon cikin Airport ɗin da yake tamkar rana saboda haske.
Zururuuuuuuuuuuu haka jirgin ke fellawa da gudu, bisa da'irar da dama itace ƙarshen rufewa saboda ana tsammanin sa.
Mamakin yadda jirgin ke gudu ya cika mata zuciya.
A hankali ta juyo ta kalli Hostess ɗin data ɗan daga kafaɗarta tare dace mata.
“Yau kinyi babban raɓo, lallai ke mai Sa'a ce Captain Taj Afif ke jan jirgin nan, kin samu taimako na musamman badon shiba da suma zakuyi, tunda ko Doctors inmu sun dubaki matsalarki ta junnuce”.
Cikin sauri tace.
“Kai nifa banda aljanu kawai tsorone”.
Murmushin tayi tare da cewa.
“Ke dai ki godewa Allah ki kuma godewa Captain Afif Taj.”
Ta ƙare maganar dai-dai lokacin da jirgin ya tsaya gis.
Daga nan duk passingers suka mimmuƙe Hostess na bubbuɗe musu durowowin jirgin suna ɗaukan jakukkunamsu, ana buɗe musu ƙofa suka fara fita.
Bayan awa ɗaya da daƙiƙu arba'in da biyar, duk passingers ɗin, sun bar cikin Airport.
Ƙarfe biyu da minti goma dai-dai,
Su Aysha suka isa masauƙinsu.
Kamar yadda duk sauran majatta kowa ya isa masauƙinsa.
Tuni kuma sun ɗauki niyya kasancewar sunso a ƙurerren lokacin yasa cikin Makka suka dira.
A can Airport ɗin kuwa, cike da tsananin mamaki Doctors ɗin dake bincika lafiyar su pilot Irfan Imran da Taj.
Suka zubawa Taj ɗin idanu.
Domin wannan shine karo na farko da bincikensu ya nuna musu cewa Pilot Afif Taj yana tattare da matsalar matsananciyar sha'awa mai gigitarwa.
Dan ma kasancewarsa mutum mai tsananin haƙuri, juriya gami da zurfin cikine yasa sam a zahiri babu alamar wannan matsalar tattare dashi ko kaɗan sai suda na'urori suka nunawa, sirrin jikinsa.
Tsuke fuska yayi tare da kauda kanshi.
Da sauri Dr Yace
“Are you okay?”. Cikin takaicin yadda na'urar ke nuna ainihin yadda bukatarsa ke hauhawa kamar farashi yace.
“Yesss! I'm okay!”. Ya ƙare maganar yana amsar mgnin ciwon kan da suke bashi.
Daga nan dai sukaci gaba da bincikan lafiyarsa domin lafiyarsa nada mahimmanci a gare su. Sai ƙarfe biyu aka ɗaukesu zuwa masauƙinsu dake gab da harami.
A hankali Aysha ta ɗan kalli Maryam tare da cewa.
“Ba wayarki bace ke ringging”?
Kai Maryam ta jujjuya tare da cewa.
“Ga tawa a hannunsa ai sai dai ko in taki”.
Ta ƙare maganar tana jawo jakar Aysha dake gefentan gami da cewa.
“Gashi”.
Ita kuwa Aysha Garkuwa dake fito daga bathroom bisa alamu wanka tayi,
kasancewar masauƙinsu ɗaya ne.
Sai kuma ta kalli jakarta tata tare da cewa.
“Kai ai ni kuma ba hakka ringing na yake ba.” ta ƙare maganar tana buɗe jakar tata cikin mamaki take kallon wayar yess gashi dai komai na wayar irin wayarta ce Amman kuma ba ringging ɗinta bane.
Sai kuma ta kalli Garkuwa dake cewa.
“Aa ki ɗauka mana, har ta tsinke”.
Juyo fuskantar wayar tayi ga mamakinta sai taga hoton.
Wata kekkyawar Babbar mace ce, mai tarin kwarjini da haiba kana an rubutu.
Fist Love a saman hoton nata,.
Sai kuma tayi kasake ganin kiran ya tsinke sai kuma poton gaban wayar ya bayyana.
Wannan matar ce a zaune sai kuma Taj da yake durƙushe a gabanta ta daura hannunta a kashi tana Murmushin dake bayyana tsananin soyayyarsa a ranta sai kuma wasu mata dake kewaye dashi.
Da sauri Maryam data leƙo tace.
“Laaa ikon Allah wannan hoton pilot ɗin nanne fa da yayi mata addu'a ta nitsu a jirgi, Aunty Garkuwa ganifa”.
Ta kare mgnar tana nuna mata fuskar wayar.
Ita kuwa Aysha jakar tata ta fara laluba wai ko zata jiyo wayarta, jin wayam ba wayar ne yasa ta kalli Garkuwa dake cewa.
“Ikon Allah tofa inaga kunyu canjin waya da bawan Allah nan”.
Dai-dai lokacin kuma wani....!
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/3, 2:13 PM] Fa'izatu Tsohuwa: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 2*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Kayana sun iso lfy. Aikin su ya kankama, komai ya zama Available. Duk abinda kake so a cikin wanda zan sako a nan akwaisu Available, kayane masu zafi da tururi kayane da ban taɓa jibgo kamar su da irinsu ba. Ku matso iyayen amare, da amaren da yayun amare da ƙannen amare da ƙawayen amare, Uwar gidaye gareku, tsakar gidaye kuma ban barku a baya ba, mai jego sabon haihuwa ko tsohon jego wato barden goyo,