Showing 36001 words to 39000 words out of 74955 words
Chapter 13 - Inda Rai Book 1 Complete Hausa Novel
Ishmah ke kiransa.
Cikin yanayi mai cike da rauni, damuwa, fargabar rashin sanin halin da Ishmah ke ciki ya buɗe idanunsu da rashin bacci da damuwa ya sauya launinsu, zuba mata idon yayi ba tare da yace ƙalaba, ƙara matsoshi tayi tare da cewa.
“Ba dai kace in sha Allah gobe da asuba jirginku zai tashi zuwa Nigeria ba?”.
Kanshi ya gyaɗa mata yana mai rufe idanunsa.
“Toh ka tashi kaci abinci, in sha Allah gobe uwar haka dai kana tare da Ishmah”.
Murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Addawa 3 to 4 Days fa kenan banji Ishmah ba, batayi min text ba, batayi min mgna ta Whatsapp ɗin da tasan domin ta ne, kawai na buɗeshi nake kumayin mgn da ita kaɗai, ban san wani hali Ishmah ke cikiba, ban san me yake faruwa da itaba”.
Ya ƙare maganar yana kife kansa bisa ɗan pillow kujerun.
Ita kuwa Addawa kasake tayi tana ƙara jinjinawa lamarin, domin a iya tsawon rayuwarta Taj bai taɓa jeranta mata doguwar mgna haka ba yankewa ko jan numfashi ba sai akan Ishmah, ta dai san mutum ɗaya kam suna doguwar mgnar datafi hakama tsawo shine marigayi kakansa, wanda kuma mgnar tasu kan ta'allaƙa ne kan karatun ƙur'ani da yake bashi hadda.
Da sauri ta ɗago kanta jin Muryar ɗiyartata da kuma surkinta.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Alhamdulillah kunzo a dai-dai”.
Sai kuma ta kalli Taj ɗin da zubawa iyayen nasa idanu cike da tarin damuwar dake ɓoye can ƙasan zuciyarsa da idanunsa.
“Bismillah ku iso ku zauna”
Cewar Addawa.
Bisa kujerar 3 sitter dake bayan Taj ɗin suka zauna.
“Abana matso nan kusa dani”.
Malam ya faɗa cikin kulawa.
Ummeey kuwa hannun tasa ta kamo hannunsa wanda hakan ya sashi masowa kusa dasu, a tsakiyarsu ya zauna a ƙasa, kusan a tare suka ɗaura hannunsu a kanshi tare da haɗa bakin wurin cewa.
“Meke damunka, Afif ka gaya min”.
Ummeeyshi ta ƙarashe mgnar.
Sai kuma ya ɗago kansa ya kallesu kasancewar suna fuskantar juna.
A hankali ya kalli warshi dake gefenshi, cikin tsananin sauri yasa hannunsa ya jawo wayar tare da yin piking call ɗin sabida ganin sunan Yah Muhammad.
Murya a sarƙafe yace.
“Assalamu alaikum, Yah Muhammad, meke faruwa? Ina Ishmah? Ya jikin Dadeey?”.
Ya jero mushi tambayoyin a lokacin guda ba tare da ya bari ko sallamarsa ya amsaba.
Cikin sanyi murya mai cike da rauni Yah Muhammad yace.
“Wa alaikissalam Taj, Dadeey'mu ta warke cuta ya gagara, ya ɗauke mana ita tun kwana uku baya, Ishmah'nka ta zama tamkar kurma bata mgna sai binmu da idanu, bata bacci.”
Tunda ya fara mgnar jikin Taj ya ɗebi wani irin rawa da tsuma tamkar wanda aka jonawa choking.
Cikin ƙarfin imani da tawakkali ya samu ya fizgo kalmar.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun”.
Sai kawai yayi ta maimaita kalmar tamkar wanda ya fara rasa nitsuwarsa, sai wani sarƙafewa da karkarwa muryarsa keyi.
Da sauri ya rumtse idanunsa tare da kifa kanshi kam cinyar Ummeynshi yayinda hamnunsa ɗaya kuma bisa cinyar Yah Abana.
Yana jin duk abubuwan da Yah Muhammad ke cewa Amman ya gaza iya control ɗin harshensa bare ya samu ya iya faɗin wani abu.
Haka yasa Yah Muhammad ya dawo yana bashi haƙuri sabida fahimtar ya ɗimauce labarin rasuwar Dadeey ya daki ƙahon zuciyarsa.
“Kayi haƙuri Taj, Dadeey addu'armu take buƙata duk yadda muke sonta Allah da ya halittata mana ita, ya bamu ita a matsayin mahaifiya ya fimu sonta, ni na kiraka da ƴa ƙinin kaine zaka iya kwantarwa da ƙanwata hankali ka taushi zuciyar Ishmah”.
Sai a lokacin ya iya cewa.
“Ummeey Ishmah. Ummeey Ishmah Dadeeynta ta rasu, ita kuma bata mgna bata bacci. Ummeey Ishmah! Ishmah!! Ishmah!!!”.
Sai kuma ya kama lip inshi na ƙasa da haƙoransa ya ciza da ƙarfi.
Cikin kulawa da tausayin Ishmah Ummeey da Addawa da Yah Abana suka haɗe baki wurin faɗin.
“Innalillahi wa innalillahi rajiun. Allah sarki rayuwa, Allah ya Ubangijin talikai ya jiƙanta da rahama yasa ta huta”.
Yah Muhammad kuwa katse kiran yayi, fahimtar Taj ɗin yana tare da iyayensa.
Shi kuwa Taj sunan Ishmah kawai yaketa maimaitawa.
“Kayi haƙuri Taj Ishmah zata samu lfy, rashin mahaifiyarta ne ya daki zuciyarta, in ka isa ka taushi zuciyarta ka ƙarfafa mata guiwa ka girgiza imaninta ka hibɓasa mata, aminta da yarda da ƙaddararta.”
Yana mai rumtse idanunsa yace.
“Yah Abana wai bata mgna bata bacci fa.”
Kanshi Ummeeyshi tare da cewa.
“In sha Allah komai zai dai-dai ta”.
Addawa kuwa kai ta sunkuyar hawaye na tsiyaya tausayin Ishmah na ratsata, duk wanda ya rasa uwa shi ne kaɗai yake iya sanin ciwon da zuciyar wanda ya rasa nasa.
Ganin haka ne kuma yasa Ummeeyshi komawa gefen mahafiyar tata tana bata baki, nan dai sukayi ta tausarta.
Washe gari, jirginsu na sauƙa a Abuja. A kuma dai-dai lokacin passingers ɗin jirgin da zai tashi daga Abuja zuwa Yola suke ta shigowa Airport ɗin saboda saura awa ɗaya jirginsu ya tashi.
Saukarsun ba jimawa, suka shiga jirgin da zai kaisu Adamawa Yola ƙarfe ɗaya dai-dai suka dira cikin Yola international Airport.
A hankali suke sauƙowa daga saman steps ɗin da yafi kama da na dakekken kwano.
Hannunsa riƙe da hannun Laylah daketa baza idanu tana kallon yanki ƙasar da bata taɓa zuwaba.
Shi kuwa Taj a hankali yake take steps ɗin tare da lumshe udanunsa, yana mai tariyo da nazarto duk kwatancen gidansu Ishmah, hatta gidajen yan uwanta da sunayen anguwaninsu kab zai iya kai kansa kamar yadda itama zata iya kai kanta gidansu Taj dama duk yayunshi maza.
Yar gajeriyar tafiya sukayi kana suka shigo cikin muhallin da za'a kawo musu kayansu.
Shigarsu ba jimawa, na'urar ta fara juyawa, cikin sa'a a sahun farko jakarsu ce a gaba, hannunshi ya kai da niyar ɗauka sai kuma yayi saurin jenye hannunsa saboda ganin wani ɗan matashi yasa hannunsa ya ɗauke masa jakar tare da sakin yalwataccen Murmushin kana yace.
“Alhamdulillah yau Sheykh Afif Muhammad Taj ne a ƙasata Nigeria kuma jihata mahaifata.
Faɗin hakane da yayi ya jawo hankalin mafi kusa dasu, nan da nan mutane suka zagayeshi, cikin ɗan sakin fuska yake basu hannunsa suna musabaha.
A haka dai har suka fito farfarjiyar da masu tarban mutane ke tsaye.
Da sauri Yah Abubakar ya nufi inda Sheykh Afif ɗin yake.
Yana isa ya ratsa tsakanin mutanen dake zagaye dashi, tare da miƙa mishi hannun.
“Suna Abubakar Abdullahi Matawalle...
Sai kuma yayi shiru jin Taj ɗin na cewa.
“Yah Sadiq”.
Murmushin Yah Sadik yayi fahimtar Taj ɗin yayi masa farin sani a hoto, ruggume juna sukayi, sai kuma ya kalli Mahmud ɗan Ishmah tare da miƙa mushi jakar Taj daya amsa a hannun ƴaron nan.
Da sauri ya riƙo hannun Taj kana juya ya nufi motarsu tare da cewa Bismillah.
Shi kuwa Taj hannun Laylah ya kuma riƙewa, tare da bin bayansa.
Suna isa bakin motar wasu jama'ar suka kuma zagayeshi tare da fara bashi hannun suna kuma matsoshi dayin selfee.
Cikin mutumtaka Yah Sadik ya ɗan kallesu tare da cewa.
“Kuyi haƙuri ku bashi hanya, yana tare da gajiya yanzu ya sauƙo daga Ethiopia ko ruwa bai shaba”.
Yayi mgnar cikin fillancin, jin haka ne yasa suka bashi hanya, tare da buɗa mishi marfin dalleliyar motar Yah Sadik ɗin, yana shiga Laylah ta shiga sai kuma ya jawo hannun Mahmud tare da cewa.
“Shigo nan”.
Cike da nitsuwa yaron ya shiga bayan ya zauna kusa dashi.
Shi kuwa Yah Sadik motar yaja tare da cewa.
“Barka da zuwa Sheykh Afif”.
Yana ɗan kallon Mahmud yace.
“Barka dai Yah Sadik, ya ƙarin haƙurinmu?”.
Cikin sanyi Yan Sadik yace.
“Alhamdulillah”.
Kai ya ɗan juya da kyau yana kallon Mahmud tare da cewa.
“Allha ya jiƙanta da rahama yasa ta huta, mu kuma Allah ya bamu haƙuri da juriyar rashinta”.
Cikin ɗan rage gudun motar Yah Sadik yace.
“Amin Amin Ameeeeeeeen Ya rabbil izzati”.
Dai-dai lokacin kuma suka fito Airport ɗin.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan riƙo hannun Mahmud tare da cewa.
“Yah Miminku tana mgna?”.
Fuska a raunace ya girgiza kai tare da cewa.
“Bata mgna har yanzu, bata sanma kazo ba!”.
Ya ƙare maganar idanunsa na ciccikowa da hawaye.
Kanshi ya shafa tare da jawoshi jikinsa cike da son yaron yace.
“Zo nan my Son karkayi kuka, in sha Allah zatayi mgn”.
Sai kuma ya kalli Laylah da batajin fillancin ko kaɗan sai larabci, turanci, da kuma yarensu na Palastine da Omoro data fara koya wurin su Addawa da Zulaihat .
Saboda bata wani daɗe a Ethiopia ba bare taji fillancinsu da shima ya ɗan bambanta kaɗan da namu, iya gaisuwa kawai ta iya.
Sai dai jin Mahmud nayi larabci ne yasata sakin jiki ta fara mishi mgna.
“Ina Anty Ishmah?”.
Yana kallonta yace.
“Mimina?”.
Sai kuma ta kalli Taj, kai ya gyaɗa mata alamar eh Ishmah ce Miminsa, ganin haka ne yasa tace.
“Eh ita”.
Dai-dai lokacin kuma suka iso kwanan masallacin juma'a na Anguwarsu wanda nanne kwanan gidansu Ishmah tsakaninsu da Airport koda ƙafa zakaje.
Suna isa bakin masallacin ana kiran salla azahar.
Gefen masallacin jumma'a kaɗan ya ɗan rasa ya wuce gaba kaɗan.
Tare da fuskantar Gate ɗin gidan nasu tare da yin
Hon.
Da sauri maigadin nasu ya buɗe gate ɗin.
Wani sassayan numfashi mai tsawo Taj ya fesar tare da lunshe idanunsa saboda sassayan iskan gidan dayake cike da shuke-shuke musamman banana da yake ta ko ina, sai kuma flowers dake zagaye da gidan da hakanne yasa gidan yin sanyi mai daɗi a jikin ɗan adam.
Yah Sadik nayin parking Laylah da Mahmud suka fita a tare, sai kuma Yah Sadik ɗin da Taj suka fito a tare dai-dai lokacin kuma Abba, Yah Muhammad Adam, Hamisu, Barrister Kamal, da Mukhtar Bappa Kawai suka fito daka cikin gidan bisa alamu sunyi al'wale dan tafiya salla.
“Masha Allah, Tajuddeen ka iso, sannu da zuwa Nigeria”.
Cewar Abba, sai kuma Yah Muhammad dasu Adam sukayi saurin nufosu suna faɗin.
“Barka da zuwa Yah Taj”.
Shi kuwa Taj da sauri ya nufi Abba tare da ɗan rage tsawonsa kaɗan yana miƙawa Abba hannu sai kuma ya miƙe tsawon nasa ganin Abban ya buɗa masa hannun alamun yazo.
Ruggume juna sukayi cike da mutuntaka.
“Bismillah Sadik kaishi Parlour na, ka kira Auta ta kawo mishi abinci”.
Sai kuma Yah ƙare maganar yana kallon Laylah dake riƙo hannun Taj ɗin tana faɗin.
“Uncle Taj ina Aunty Ishmah”.
Kan Laylah Abba ya shafa tare da cewa.
“Mahamuda kaita wurin Khadijah zata kaita wurin Mameenku!, Sai kazo mu tafi masallaci”.
Sai kuma yayi murmushi jin Taj na maida mata abinda ya faɗa da larabci
Ai da sauri tabi bayan Mahmud suka nufi cikin gida, dai-dai lokacin kuma Khadijah ta fito daga Parlour Dadeey zata nufi part ɗin Yah Muhammad.
Da sauri ta kalli Mahmud dake gaya mata sakon Abba.
Cikin sanyi ta ɗan sunkuyo tare da kama hannun Laylah tare da sakar mata ɗan sassayan murmushi tace.
“Toh zo muje muyi salla, itama Aunty Ishmah tana salla ne”.
Ta ƙare maganar cikin tattaro ɗuk iyakar luggar larabcin bakinta.
Mahmud na juyawa yace.
“Tana jin turanci ai ba iya larabci ba”.
Cikin dauƙe numfashi Khadijah tace.
“Ato da sauƙi”.
Daga nan taja hannunta suka tafi.
A can harabar gidan kuwa, cikin son juya fillancin Ethiopia zuwa na Adamawa Taj yace.
“Muyi salla tukuna Abba”.
Kai Abba ya gwaɗa tare da cewa.
“Toh kuyi al'wala”.
Yana kallon Yah Muhammad dake cewa. “Eh muje kayi al'wala”.
“Inada alwala”.
Jin haka ne yasa duk suka wuce masallacin.
Suna shiga ana ƙoƙarin tada iƙama, ganin shine yasa Limamin yin saurin juyowa ya fuskancesu da kyau cike da son tabbatarwa yasa tafukan hannunsa ya murza idanunsa.
Tare da cewa.
“Wa nake gani kamar Sheykh Afif Muhammad Taj?”.
Sai kuma ragowa mgnar ta tsaya a fatar bakinsa saboda, ganin yadda jama'a suka zagayeshi suna bashi hannun tare dayi mishi Barka da zuwa.
Barrister Kamal kuwa sai murmushi yakeyi, saboda yana jinjinawa amintakar dake tsakanin Ishmah da Taj.
Dr Nafi'u kuwa sai wani tsuke fuska yakeyi.
Shi kuwa Liman da sauri ya matso kusa dasu tare da cewa Abba.
“Alaji Abdullahi yau wa nake gani a masallacin mu kamar Sheykh Afif Muhammad Taj”.
Fuska ɗauke da kamala Abba yace.
“Ba kama bace shi ɗin nema”.
Jin haka ne yasa liman ɗin saurin miƙawa Taj hannunsa suka gaisa, sai kuma ya ɗan ja baya kaɗan tare da nuna mishi gabanshi cikin alamun mubaya'a yace.
“Yau nima a sahun mamu zan tsaya dan Allah, ka limamcemu”.
Da sauri ya kalli limamin sai kuma yayi gaba saboda jin duk na kusa dasu na cewa.
“Dan Allah ka limamcemu, kaga lokacin na tafiya”.
Daga nan duk jama'ar masallacin sukabi da'ira suka tsaya a sahu tare da dai-dai ta.
Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan gyara tsayuwarsa tare da ƙara matso abun sautin, cikin sanyi murya mai cike da tawali'u ya ɗanyi gyaran murya tare da ɗan rusunar da kansa yace.
“Sahhhhhhu! Sahhhhhuuuh!! Sahhhhhhhuuuuu!!!”. Yana ƙarshen sautin cike da amincin, da yasa gaba ɗaya mamun baya samun nitsuwa sit kakejin masallacin.
Sai kuma ya tada iƙama tare da basmala kana karanta Fatiha da suratul Mulk, a raka'ar farko kenan ta biyu kuma Fatiha da suratul Ala.
Kasancewar sallan azahar ne dole a sirrance akeyinsu yasa in banda wanda ke cikin masallacin da suka ga shigansa babu wanda yasan wake limancin.
Bayan sun idar da sallan ne da sauri Abba yajasu suka tafi gida.
Bayan sunyi gaishe-gashe da jajantawa juna ne, Taj ya rinƙa jero addu'o ga Dadeey.
Bayan sun shafa ne, Abba yacewa ya kaishi BQ.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Abba a kaini cikin gida ina son inga Ishmah”.
Wani irin kallon tuhuma Dr Nafi'u ya watsa mishi ƙasa-ƙasa tare da cewa.
“Kasan ana son ta samu Hutu. Ko ƙwaƙwalwarta zata motsa”.
Bai kalli Dr Nafi'u Bama sai miƙewa yayi yabi bayan Adam.
Barrister Kamal kuwa murmushi dake nuna nitsuwarshi yayi tare da cewa.
“Dr Afif a duba min amaryata da kyau”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Barrister Kamal sai kuma ya ɗan motsa lips inshi.
“In sha Allah yanzu zatayi mgn”.
Cikin tsana Dr Nafi'u yace.
“Nifa Doctor ne, kuma tun randa abin ya faru take karkashin kulawata, ita dayin mgn zata iya kaiwa kwana ashirin zuwa talatin nan gaba”.
Har Lau bai kulashi ba ya tafi.
Suna shiga cikin Parlour, ya zauna gefen Adam dake cewa kakarsu da umominsu Hajja Umma ga Yah Taj, yanxu ya iso.
Nan suka gaisa kana Adam ya miƙe tare da kallon kakar tasun yace.
“Tana ɗakinta ko?”.
Da sauri tace.
“Eh yanzu ta shiga da mukayi salla”.
Kai ya gyaɗa tare da yin gaba yana faɗin.
“Bismillah Yah Taj”.
Jin hakane yasa yabi bayansa.
A hankali ya tura ƙofar tare da cewa.
Assalamu alaikum Adda ga wani baƙo yazo miki gaisuwa.
Ya ƙarashe maganar yana tura ƙofar tare da shiga.
Kwance ya sameta bisa kujera 3 sitter tayi irin ƴar kwanciyar nan mai kama da kishin ƙiɗa idanuta a lunshe.
Yayinda take sanye da Dubai Abaya Black collor mai masifar sulɓi da sheƙi, sai ɗan kwalinta daya zame ya faɗo bisa kafaɗunta sai gashi ta dake tubke da ya ɗan hargitse, kasan cewar numfashinta da yayi ta ɗaukewa tun randa akayi rasuwar shiyasa bata sa bra saboda tana sawa numfashi ke kuma fara yankewa, hakan ne yasa caɓɓullenta yin cirko-cirko suka tsaya cis a cikin rigar.
“Bismillah ka shigo”.
Adam ya faɗa yana zama bakin gadon ta.
Ita kuwa Ishmah a hankali ta ɗan buɗe kwayar idanunta tare da zubasu kan ƙofar shiga kasan cewar nan take fuskanta.
A hankali ya ɗan turo ƙofar tare da kutsa kai ciki.
Wani......!
Littafin nan dai na kuɗine ki biya ki karanta cikin aminci 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa.
mutan Niger kuma 1000fc ne rak jaka ɗaya kenan
+22790899076.
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[1/9, 5:51 PM] Leematu: 📝🕋✈️💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK ONE PAGE 9*
NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Littafin nan na kuɗi ne ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc ne zaku biya jaka ɗaya kenan rak zaku ta wurin Mommy +22790899076*
Wani irin maraitaccen numfashi ta fesar tare galabaitaccen yunƙura ta tashi zaune tare da zuba mishi maraitattun idunta masu cike da rauni kana murya can ƙasan maƙoshinta tace.
“Taaj”.
Sai kuma ta feso wani irin fitinenne numfashi daya fito daga ƙasan zuciyarta ya fito da zazzafan kukan da bata samu tayishi ba sai yanzu.
Shi kuwa Taj wani tasasheshen numfashi mai cike da rauni ya fesar tare da dire kwayar idanunsa a kanta yana saurin ƙarasowa cikin ɗakin, bisa kujerar da taken ya zauna a gabanta.
Cikin wani irin raunataccen kukan daya kwabce take sakin shesh-sheƙan kuka murya cike da rauni, da ɗimuwa tace.
“Taj Dadeey na, ta tafi ta barni bataga aurena ba, Taj Dadeey na ta rasu banyi aureba, Taj Dadeey na ta rasu bata ganka ba ta rasu da burin ganink.”
Sai kuma mgnar ta kakare saboda wani irin karkarwar da jinkinta ya farayi da wani irin fitinenne rauni daya carke mata murya ya cikashi da yanayin da mai jinta da ganinta zaiga shagwaɓarta a fili yayinda numfashi take korar juna ƙirjinta na yin sama da ƙasa dan gunjin da takeyin.
Shi kam Adam sai kife kansa yayi shima yana sassayan kukan daya ingiza na Ishmah.
Shi kuwa Taj ido ya zuba mata yanayi mata wani irin amintaccen kuma raunataccen kallo a yanayin da bai taɓa ganin taba, na zama irin sakewa a cikin gida kuma a ɗakinta, idanunsa da ya zuwa fuskantar zuwa kan wuyanta da ta maida kanta ta jingine bisa jikin kujerar hakan ya bawa ƙirjinta damar bayyanan da yasashi lumshe idanunsa yana mai jin tamkar ya jawota jikinsa yayi mata ruggumar da sai ya rabata da dukkan ƙuncin zuciya dana duniya ya tausashi zuciyar ta irin tausasar da sai tayi murmushi koda hawayenta basu tsaya ba.
Dai-dai lokacin kuma Khadijah da Laylah suka shigo,
Ganinshi ne yasa Laylah saurin zuwa gareshi tare da zubawa Ishmah ido murya na rawa tace.
“Uncle Taj meyasa Aunty Ishmah take kuka”.
Yana mai ɗan tallabo kanta yace.
“Laylah Aunt Ishmah ta rasa mamanta, bazata sake ganintaba”.
Ido na cikowa da hawaye Laylah tace.
“Kamar yadda Mimina da Abbuna da Yah Irfan suka tafi, tafiya na har abada”.
A hankali ya gyaɗa mata kai.
Sai kuma ya kalli Hajja Umma da Aunty Hauwa da suka shigo yanzu suna faɗin.
“Ishmah kiyi haƙuri ki bar kukanan, gashi Kinga kinsa ƙannenki kuka”.
Suka ƙare suna nuna kallon Khadijah da Rahman da suka zauna gefen Adam suna zubda hawayen.
Hannu ya ɗan ɗagawa Hajja Umma kana yace.
“Barta tayi kukan”.
Laylah kuwa da sauri ta matsa kusa da Ishmah tare da faɗawa