Showing 27001 words to 30000 words out of 61789 words
Chapter 10 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
infaɗa mata yau dai za taga yaya sulaim ɗina a fili ba pic ba, dialing number ɗin malika tayi wadda tayi saving ɗinta da friend Forever,
Fitowa yayi jikin sa sanye da jallabiya ash colour amma irin dark ɗin nan, yawuce abunsa kamar bai san da wata halitta wai saleema ba a gurin ya nufi downstairs, don zuwa masallaci,
Shiyasa yadaɗe ashe har wankama saida yayi, cewar saleema ita kaɗai abunta bata ma damu da wuciwar da yayi ko kallo bata ishe shiba, Oho ita dai aiyau burunta ya cika, bata ɗauke idon ta daga kan sulaim ba harsaida tadaina ganin shi, sannan ta maida kallon ta kan wayar ta, tare da furta, ko gidan ubanwa malika ta ajiye wayar ta Oho, ana kira bata picking,
_________________________
__________________
___________
Cikin murmushi DR.muhibba ke kallon Suhaima, kafin tace wai ke tsoron mu kikeji dabaza kibuɗi fuskar ki muganki ba,
"hhm Suhaima tace sannan yaɗora da cewa a a kawai dai nibana buɗe fuska ta," Allah Allah Suhaima take don jin abunda likitan zata faɗa mata yake don ta samu ta koma wajan khaltum, sannan taji nawa ne kuɗin su, don tafara tunanin inda zata samo su tun a yau ba sai gobe ba kafindai su sallame su, ita fa da tana da kuɗin tabiyasu to ko basu sallame suba, Allah sai sun gudu, 😂
To shikenan, naji yanzu dai, zan tashi aiki, to za a kawo muku abinci, sannan hada kayan sawa saboda kusamu kuyi wanka ko, idan kuna buƙatar wani abu sai kifaɗamin kafin na tafi, ko ita mara lafiyar idan tana buƙatar wani abun,
Cikin tsinkewa da wannan lamarin, na asibitin nan, ta tambaye kanta, to dama wai a asibiti ake bawa mara lafiya da me jinya a abinci??
A a, tabawa kanta amsa, kuma sannan babban abun mamakin wai kayan canza wa idan sunyi wanka, gaskiya wannan abun ya wuce tunanin ta, bari kawai ta tambaye likitan nan duk da tambaya bata ɗaya daga cikin ɗabi ar ta, idan kaga tayi tambaya to tabbas abu ya wuce lissafin ta,
Gashi kuma likintan sai yi mata murmushi take, to ko dai so suke su cutar damu shine suke yimana duk wannan,? Ta sake tambayar kanta,
Kai A a da zasu cutar damu da wani zancan ake ba wannan ba, ya salam tafaɗin jin kanta na neman juyawa,
Muryar DR.muhibba ce ta katse mata hanzari,zaki iya komawa gurin ƴar uwar taki za a kawo muku komai, yanzu, Tunda naga kinyi shiru da alama Baku buƙatar komai,
To kamar umarni haka Suhaima ta amsa gashi taga ita, sannan taga dasu ka haɗa ido da Dr ɗin ko alamun wani sauyi bata gani ba, saɓanin wasu da har gudu wa suke daga kusa da ita bayan tsorata daganin launin kwayar idon ta, amma anan ko ɗaya sai taji son likintan yashi ranta,
Harta tashi zata fita sai kuma ta dawo, amma bata zauna ba kamar ɗazu, "amma dan Allah doctor, Baku faɗa mana kuɗin ba sannan kuma ga wata ƙarin ɗawai niyar ga kuma hada abinci za abamu Tunda nake bantaɓajin irin wannan ba, idan kuma duk acikin kuɗin kune kukeyi mana, to ya kamata ace kunfaɗa mana, don muji ba sai zaku sallame muba,
Faɗa ɗa murmushin ta DR.muhibba tayi sosai kafin tace ki kwantar da hankalin ki Suhaima, Suhaima ko? Eh,
To zanfaɗa miki a taƙaice komai dakikaga anyi muku to a bisa umarni ne sannan kada ki damu da maganar kuɗi, da za akarɓi kuɗin ku, sai kunbiya kuɗin komai kafin ataɓa ƴar uwar ki, idan kikayi hak'uri zaki samu duka amsoshin tambayar ki gobe insha Allah.!!.
Share and more like fisabilillah🙏.
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp channel
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
______Dedicated to aunty salma💎
*Page* 2️⃣7⃣▶️2️⃣8⃣📖
Idan kikayi hak'uri zaki samu duka amso shin tambayoyin ki gobe insha Allah Dr.muhibba, takai ƙarshen maganar tare da miƙewa, tafara haɗawa wasu takaddu, da alama dasu zata tafi,
Ɗan Jim, suhaima tayi kafin tace to Allah yakaimu, mungode,
Karki damu, fatan mu dai shine Allah ya ƙara bata lafiya,
Muje ko sai in duba jikin nata daga nan sai in wuce, zan haɗa ku da doctor ɗin da yake on duty night, nima YAU ina da duty to amma wani dalili yasa, dole zan koma gida, key tayi wa ƙofar sannan suka nufi hanyar da zata sada su da ɗakin da khaltum take,
Shiru suhaima tayi bata ce komai ba, tana biye da likitan, dama ita ba ma abociyar, magana bace, sai wadda tazama dole ayi ta,
Kallon khaltum Dr.muhibba tayi, sannan tace masha Allah jiki yayi kyau, koda abunda kike da buƙa tane? Tayi tambayar tana kallon khaltum ɗin,
Girgiza kai khaltum tayi ala mar, a a
To Allah ya ƙara sauƙi ta faɗa tare da juyawa har takai ƙofa ta jiyo, zafa aka womuku dinner yanzu,Sannan takai hannu jikin madannar fitala, ta kunna take wani haske ya gauraye ɗakin kai kace rana ce ba dare ba, har saida Suhaima ta ɗan runtse ido, kuna zaune a ɗaki babu haske sosai, tana kaiwa nan ta fice abunta,
Duka bayan ta suka bi da kallo, ajiyar zuciya suhaima tayi, khaltum kuwa wadda dama kamar jira take likitan ta fita, da sauri ta kalli suhaima, wannan fa ita ɗin wace?,
"Likita ce, sunan ta Dr. Muhibba,"
To abinci fa naji tace za a kawo mana, to dama hadda abinci suke rabawa,? Khaltum taƙara tambar Suhaima akaro na 2,
Nima haka tacemin kuma wai hadda kaya muyi wanka Musa,
To wai ko dai kinbiya su kuɗi ne bansani ba,?
A a ban basu komai ba, amma dan Allah ki adana tambayar ki sai gobe, zaki samu amsoshin komai, haka Suhaima tafaɗawa khaltum cikin gajiyawa da tambayoyin da take yi mata, aran ta tace ni namafiki shiga ruɗani,
Shiru sukai baki ɗaya kowacce da abunda take saƙawa aranta, Suhaima ce ta tashi tace bari inyi salla naga lokace ma ya fita, dama tunɗazu taga ƙofar toilet ɗin dake cikin ɗakin, daga can wata kusur wa, dake ɗakin yana da ɗan girma, amma kuma duk girman sa gadon marasa lafiya 2 ne aciki,
Ƙofar ta tashi ta nufa wadda daga saman ta aka rubuta, TOILET, kallon toilet ɗin Suhaima tashigayi, sosai tsarin toilet ɗin ya birge ta, komai naci white colour Ne, KO ina tsab tsab gashi sai wani kamshi yake yi, ita tama rasa kamshin Meye, gashi abushe yake kamar ba a taɓa amfani dashiba, gashi da girma, kallon ko ina takeyi, aranta tace aini ko a ɗaki akabani nan ya isheni,😂 amma wai ahaka toilet ne, zancan zucinta ta cigaba da yi, daidai taga hakan bazai fisshe taba sai tamatsa, Tap Don ɗora alwala, jitayi kamar tashiga cikin bottom ɗin tayi Alwalar aciki, sai kuma wata zuciyar tace to ai yanzuma zaki dawo kiyi wanka,
Sai ta cigaba da Alwalar ta kawai, shikan shi Tap ɗin bata taɓa ganin irin saba Tunda take,
Fitowa taye tare da tema kawa khaltum don itama ta samu tayi alwala suyi salla, dai dai fitowar su suka ga wata nurse tsaye da alama ma su take jira,
Kallon su tayi kafin tace, ga abincin kunan wannan kuma kayan sawa ne, ta nuna musu daga gefan gadon cikin wata jakar leda mai kyau ta ƴan gayu, wadda aka rubuta, *BARAKAT STORE*, ajiki kayan abinci asaman wani dogon table mai tayoyi, da alama turo shi ma tayi ta shigo dashi don wannan ai bazai ɗakku ba Suhaima wadda ke ta zance zuci ita kaɗai abunta,
cikin nutsuwa nurse ɗin ta fara tura wannan table ɗin zuwa kusa da wani shima ƙarami ne daga ɗan gefan gadon kai kace a irin hotel ɗin nan, tafara jere musu kayan abincin daya bayan ɗaya, saida ta sauke komai, hada bottle water da 5alive drink babba sannan ta, tura table, tafice abunta,
Suhaima wadda mamaki ke neman halakata, batabi ta kan komai ba ta ɗauki, mayafin da khaltum ta rufe fuska dashi, ta shimfiɗa musu, takalli khaltum wadda ta shagala da kallon wannan ledar da aka ajiye musu burinta kawai taga Meye aciki, Suhaima ce ta katse mata hanzari, ta hanyar cewa ki saka hijabinki muyi salla ko,
"firgigit, khaltum tayi tana kallon Suhaima wadda har ta tada sallah,
Hijab ɗin tasaka Sannan ta sakko daga saman bed ɗin ahankali Saboda bata jin kwarin jikin ta, zama tayi domin gabatar da sallar bazata iya a tsaye ba,
_____________________
______________
_________
Sulaim da sallama ya shigo parlon saman, amma saboda a ciki ciki yayi sallamar saleema bata jiba, kallon shi take tare da furta barka da shigo wa yaya sulaim,
Batare da yace komai ba ya wuce bedroom ɗin sa aransa yana mamakin, shin tayi salla ne, a a, batayiba, saboda ai babu hajab ɗin da zata yi sallar dashi kuma da alama bata ko tashi daga inda take ba, zuciyar sa ce ta bashi amsa, a lokacin da yake tura kansa cikin bedroom ɗin tare da taɓe baki haɗi da ɗaga kafaɗa irin na _I don't care_ ɗin nan,
Saleema baiwar Allah harta fara fidda rai, sulaim bazai fitoba idanuwan ta sunciko da hawaye tab,
Kamshin dadda ɗan turaren sa dabaya taɓa ɓuya ya bayyana na zuwa cikin hancin ta da sauri ta ɗago tana kallon hanyar bedroom ɗin inda, take ta kallo tunɗazu har ta gaji,
Awwwn😍 saleema ta furta a hankali,
Sulaim ne ya fito cikin shirin sa na alfarma, kamar wani ango, wani bowl ne ajikin sa launin blue black, black shoes irin saucikin nan amma basu rufe baya ba sai ƙalli sukeyi, ga wata hula daya kafa akansa, wadda kai ko ance kayi mata kuɗi baza ka iyaba, itama black colour ce, komai nashi black ne, watch shi ka ɗaine, jikin sa launin silver, ba ƙara min kai yayi ba, abunka da farin mutum ga fatar kullum ƙara murjewa take kamar mai wanka da ruwan madara, sai ya haska kayan da yasaka, ga tsayi, ga kyau, ga kwarjini, rannan nashi ahaɗe kamar dai kullum, ƙakkyawan lips ɗin, nan nasa brown ya wani ƙara ɗan cizawa, shape ɗin su yaƙara fitowa, sai ƙalli suke yi kamar wanda ya shafa musu, whitelips, har yazo ya wuce saleema, tana can ta shagala wajan kallon sa, sai taji duk ta raina kanta, da tasan irin kyan da sulaim zai yi da batayi irin wannan shigarba, har ƙara kallon kanta tayi, da sauri ta tashi tabi bayan sa,
Kyawawan dogayen ya tsun hannun sa nadama yakai kan dogon wuyan sa ya shafa, tare da furta ya salam, ya manta bai ɗakko key ɗin motar saba, gashi har sun sakko perlon ƙasa, cigaba yayi da tafi batare da yabari saleema ta gane komai ba, ita dai kawai binsa take abaya tana kallon sa kamar wani TV,
Ahankali yake taka wa, saleema da taga haka kuma sannan bata ga alamar key, a hannun saba, sai ta ɗan wuce gaba da sauri, ta nufi motar da tazo da ita, ƙirar (4MATIC DRM) ce ta buɗe masa gidan gaba itama tazaga ya bangaran driver site tabuɗe, Wai yau saleema ce da buɗewa wani ƙofar mota, tab lallai so daban ne, to ko daddyn su bata jin, zata iya buɗe masa ƙofar mota gaskiya,
Kallon ta sulaim yayi ƙasa ƙasa aran sa yace, Yarin yar nan tana da rawar kai waini zatai draving, a fili kuma, miƙa mata hannu yayi alamar taba shi key ɗin, babu musu tamiƙamasa, ta koma ta shiga ɗayan site ɗin, tanajin wani irin daɗi kanta yaƙara girma, wai yau yaya sulaim ne zai yi driving ɗin ta, tab gaskiya ni mai sa'a ce acikin mata, tana ta faman zancan zucinta saiji tayi ya tashi mota, tare da,
furta mata address"
Da sauri ta ɗakko ɗan katin bikin ta duba, tace masa, *STATE ROAD MILLINIOM EVENT CENTRE* tabashi amsa a taƙaice, take ya ɗauke hanya, ita kuma taciru wayar ta ta turawa malika sms,
Saleem ne zaune cikin mota yana kallon suhailat, tare da cewa mata wai Meye yasa kike son mutafi gida tun yanzu kina ganin mafa wasu yanzu suke zuwa ko?
"Eh nidai gaskiya yaya saleem mutafi kawai
"yadda tayi maganar ashagwaɓe ne, yabashi dariya,"
" sannan yace, kefa ba auta bace shine kike yin shagwaɓa ko,
Rufe fuska tayi da ta fukan hannayen ta alamar kunya"
Dogayan yatsun ta yabi da kallo wanda, ɗan jan lallan dake jikin farcen tane ya ɗauke hankalin sa,
Oh wai nan kunya ta kike ji kinga kawai kibuɗe fuska muyi magana, ni dama inaso na tambaye ki wani abu,
Buɗe fuskar tayi amma kanta a ƙasa tace inajin ka yyn,
Shikam yana jin daɗin wannan sunan da take kiranshi dashi yyn, idan ta faɗa har cikin birnin zuciyar sa take ziyar ta,
Am dama wanda naganki dashi jiya, ya kike dashi,?
Kallon shi ta yi tace babu komai kawai meet ɗi nane,
To gaskiya kirinƙa janye jiki daga irin waɗan nan mutanan ban so,
Yaya saleem amma ai hafeez ba ruwan shi kawai, abunda bansani bane muke yi tare, saboda ya iya......
Ya isa nifa bawai na tambaye kibani wani abu dan gane dashi bane, kawai dai kada ma nasake ganin ku tare, kinjini ba,
Yeah" ta furta aranta tana mamaki wannan abu, tab to Meye ruwanka da shi, aranta take maganar a fili kuma ta cono baki,
Murmushi tayi kawai ya tada mota saboda shima yafison su koma gida baya son a rinƙa kallon suhailat ɗin ko da yaushe bama kamar acikin taro,
Dai dai fitar su, shi kuma sulaim ya turo hancin motar cikin Ƙaya taccan gurin bikin wanda ya gaji da tsaruwa tun daga bakin gate zaka gane gurin ba na ƙananan muta ne bane,
Amma saboda kowa hankalin sana akan abunda yake yi babu wanda yaga kowa, Suhailat cema taso ganin saleema amma batasan da waye suke tare ba, aran tace lallai ke kuma sai yanzu,
Cikin ƙanƙanin lokaci saleem suka koma gida shida suhailat, har tabuɗe mota zata fita saboda, dama taƙagu su dawo, yau haushin yaya saleem ɗin take ji saboda ya hana ta kula hafeez, ko kula shi ma batayi ba ahanya har suka zo,
Kamo hannun ta saleem yayi da sauri ta jiyo ta kalle shi,
Babu komai akan fuskar shi, yace mata saboda na hana ki kula saurayin ki shine kike fushi dani ko to kiyi hakuri,
Hannun ta ta zame daga nasa, cikin jin nauyi da kunya tace wlh yaya saleem shi ɗin ba saurayi na bane kawai, muna mutun cine fa, takai ƙarshan maganar kamar zata fashe da kuka,
It oky Suhailat kada kiyi kuka kinji zankira ki bayan kin huta akwai maganar da nakeso muyi mai mahimmanci,
"To Insha Allah" ina jiran ka
Zaki iya tafi kawai yace mata,
Fita tayi ta rufe ƙofar yabi bayan ta da kallo
Tare da ɗan zame wa ya maida kansa baya ya lumshe ida nuwan sa,
________________________
__________________
____________
Suhaima ce ta shiga buɗe kwani kan abincin da aka kawo musu, wanda tun tana salla takejin wani irin dada ɗan ƙamshin na fuzgarta sai a lokacin ta tuna rabon ta da abinci, jitayi tamkar zata iya cinye abincin nan ita ƙadai saboda tsabar yunwa sai sannan taji, har wani jirjiri take ji saboda tsabar yunwa,
Food flaks ɗin farko ta fara buɗewa, wata hada ɗiyar fried chicken, ce aciki Wadda taji kayan lambu, ga naman kazan.nan kamar zasu yi magana, sai wani fish pie and salad, acikin wani food Cher ping Mai kyan gaske silver colour, GA wata lafiyayyan bread bugger, acikin wani kwali, komai Suhaima ta taɓa sai taji zafi, kamar yanzu aka sauke, saida taboɗe komai aciki, tana haɗiyar yawu saboda yunwar da takeji, plate ta ɗauka guda 1 tayi saving khaltum taba ta sannan itama tayi saving kanta, da Bismillah tafara ci cikin nutsuwar ta...!
*Comment, share and more like fisabilillah* 🙏
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp channel
*AHALIN MU DAYA*
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚
_Sarauniyar👸Nazari writer's association_
______Dedicated to aunty salma💎
*Page* 2⃣9️⃣↔️3️⃣0️⃣📖
Tsaye yake cikin wata shiga ta baƙakyan kaya cikin wani, ɗaki mai duhun gaske, wata ƙaramar fitila ce an kunna ta a an ajiye a ƙasa irin, aci bal bal ɗin nan,
ta ɗan haska iya inda yake tsaye, magana yake cikin kaushin murya, baza ka taɓa gane cewa, mai girma hasheem ba ne saboda adon kwallin da yayi wa fuskar sa, Indai ba sanin sa kayi sosaiba, gashi ɗakin babu wani wada taccan haske aciki, magana yake a gaban wani dogan mu dubi, baka iya ganin komai na cikin mudubin shi kaɗai ke iya mu tumin da yake magana dashi,
Daga cikin mudubin ne aka fara magana, hasheem kasani dole zaka yi abunda ƙungiya keso Idan ba haka ba, hukunci ne zai biyu baya zaɓi fa aka baka har biyu, amma shine kake wasa da da mar ka ko, dole kasa mu HATIMIN nan shine kawai zai sa mu mallaki ƙarfin iKon da babu wata ƙungiya da take da irin ta acikin ƙungiyoyin (secret).
Kafin mai girma hasheem yace komai wani duhu ya kawo ya mamaye cikin madubin,
Wani irin dogon numfashi mai girma hasheem yaja kafin ya ɗauki wani jan ƙalle ya lulluɓawa fuskar madubin, sannan ya matsa daga gabansa, yana muzurai a fili ya furta bazai yiwu ba dole ni zanzama mai ƙarfin iko na farko acikin ƙungiya,
Takawa yafara yi zuwa wani ɗaki domin ya