Showing 51001 words to 54000 words out of 61789 words
Chapter 18 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
ina ma zakai wani farin jini kullum fuska a haɗe dunkum kawai kurma,
Gwaggo Murja Takai karshe tare da wullawa Sulaim Harara,
Dariya ummeetha tayi cikin ranta tace lallai gwaggo tana son korar min yaro yanzun nan,
"Princess kuwa har dafe baki take saboda jin sunan da gwaggon ta kira yayan nasu dashi wai dunkum kurma abun baƙaramin dariya yabata ba amma tasan bata isa tayi ta a fili ba,
Abun mamaki Sulaim ko kallon inda gwaggo take bai yi ba saima tashi da yayi daga gurin mommy ya nufi inda ummeetha take zaune,
Kusa da Yarima Sultan ya zauna shima yayi kamar zaman da yariman yayi,
Gaishe da ummeetha yayi tare da yi musu barka da zuwa,
Duk wanda yake cikin parlourn nan saida yayi mamakin Yarima sultan bama kamar waɗan da basu taɓa ganin saba saidai suji labarin sa,
Basuyi tunanin haka yake da sauƙin kai ba ba kamar sauran ƴaƴa ƴan Sarki ba,
Hatta ummeetha da tasan shi tun yana yaro saida tayi mamakin girman da yabata a yau duk da yana girmama ta,
Amma sai ta alaƙanta hakan da abotar Yarima Sultan da ɗan ta Sulaim ne shine dalilin hakan,
Barka da zuwa Yarima sultan yayi wa mommy duk da bai santa ba amma ya yi mata barka da zuwa,
Taji daɗin hakan sosai har cikin ranta wanda tasan badan albarkacin Sulaim ba dabaza ta samu hakan ba,
Ummeetha dan Allah kuntashi mu shiga cikin masarautar nan muzagaya saboda wlh ina so nagan cikin ta,
princess ce tayi maganar dai dai satin kunna ummeetha amma tamkar a kunnan Yarima sultan Tayi saboda yana kusa da ummeetha gashi ta ɓangaran da yake tayi maganar,
Kallon mutane ba ɗabi'ar Yarima Sultan bace amma sai yaji yana son ganin wace ce wannan tayi magana,
Kallon princess ummeetha tayi kafin tace wai nikam Auta yau kika fara zuwa masarautar nan ne da zaki damu mutane,
Kwaɓe fuska princess tayi cike da Shawagwaɓa tace dan Allah ummeetha wlh ina son gani ne,
To naji ga mai masarautar nan zaune da alama ko gaisuwa biki iya ba,
Da sauri princess ta russuna A gaban Yarima Sultan tare da Faɗin Allah ya temakeka Barka da Rana,
Kallon ƙasan ido yarima Sultan yayi mata batare da yace komai bai ɗaga kai kawai yayi alamar ya amsa,
Baƙaramin haushi princess taji ba take taji bata son shi saboda bai amsa mata gaisuwa ba aranta tace Mai ban haushi kawai ashe halin ku ɗaya da yaya Sulaim,
Tashi tayi daga gaban sa tare da komawa ta zauna,
Tashi yarima Sultan yayi tare da Faɗin Na Barku lafiya Ummeetha Sakon Ummul Bait zuwa gare ku yanan isowa,
Murmushi ummeetha tayi sannan tace Acewa Uwar gidan sarki Allah ya ƙara lafiya zamu shigo Gabatar da godiya,
Baice komai ba yana Tashi Rafiq da Taufiq suka ƙarasu tare russuna wa cikin girmamawa sukace yaya Yarima barka da warhaka,
Murmushi yarima sultan yayi tare da Faɗin barka dai allah yasa kuna cikin walwala,
Alhamdulillah,
Sai a lokacin Saleema shima ya taso tunkafin ya ƙaraso Yarima sultan yasaki fuska sosai tare da murmushin ƙasa ita irin nasu,
Ganin haka yasa shima Saleem din sakin murmushi Ranka ya daɗe,
Tunkafin Saleem ya ƙarasa Yarima sulaim yamiƙa masa hannu da nufin su gaisa,
Bamu su Saleem yamiƙa hannu suka yi musabaha tare da Faɗin bantaɓa tsammanin ka haka ba muna godiya da karramawa ga Yariman Gabas,
Saleem Canada KO?
Cewar yarima Sultan yana kallon Saleem,
Na'am nine,
Ina maka barka da zuwa Daular Sultan,
Murmushi saleem yayi tare da Faɗin ina godiya sarkin gobe ya furta hakan tare da dunƙule hannu alamar jinjina,
Batare da Yarima sultan ya ƙara cewa komai ba yawuce gaba Shida Sulaim Fadawa suka rufa musu baya tare da ikirari ga Yarima Sultan,
Banyan fitar su Ganin Saleem bai fito ba hakan yasa Sulaim kiran shi a waya,
Muna Mota ka fito mu tafe ko zaka zauna cikin mata ne cewar Sulaim,
Dariya Saleem yayi tare da Faɗin gani nan zuwa to Rafiq da Taufiq Fa su sai su zauna cikin matan?,
A'a Haisam zai aiko a tafi dasu batare da Sulaim ya jira cewar Saleem ba ya kashe wayar dan yasan zai ƙara Faɗin wani abun,
Ɓangaran Suhailat kuwa Tunda saƙon saleem ya risketa hankalin ta yatashi ta rasa Meye yake yi mata daɗi tabbas kalmar saleem ta ƙarshe acekin saƙon da ya tura mata tahana ta sukuni daya ce mata, _but one day if you see me with someone else I hope you understood_ amma ta rasa Meye dalilin?,
Zuciyar tace ta bata amsa da kinfaɗa soyayyar shi Ne,
Jijjiga kai tafara tamkar da wani take magana tare da furta _No_ afili ni soyayya kuma da yaya Saleem A'a
To shikenan a lokacin da kika ganshi da wata sannan zaki tantance,
Take Suhailat taƙarajin kanta ya kulle to Meye hakan ke nufi idan ma na ganshi da wata sai me,
Tayi wa kanta tambayar,
To amma wai Meye dalilin ki naƙin shi Meye ya rasa ko bai kai aso shi bane,
"saleem ɗan gayu ne ga kyau, ilimi, son mutane, dukiya uwa uba yana da kyakkyawar zuciya"
Duk abunda ake buƙatar ga mijin aure yana dashi zai kula dake Suhailat sosai ya kula dake a matsayin ƙanwa ma bare a matar shi,
Gaɓa ɗaya wannan zuciyar Suhailat ce ta karanto mata su game da saleem take taji wani irin tausayin sa ya kamata, to dama ai banida wanida dalili baƙin yaya Saleem Amma dai ina jin kunyar sa sosai ita kaɗai take maganar ta cikin Bedroom a kwance samon gado irin na mai rufe asaman sa na gidan sarauta,
Take taji zuciyar ta tayi sanyi tunanin da yanata sukuni duk ya tafi wayar ta ta ɗaukko tafara rubuta masa Amsar saƙon da ya turo mata,
_....Barka da rana Yayana Allah yasa kana lafiya, kayi hakuri bisa abunda ya faru narasa maka mane,_
_My apologies and I love you more yaya Saleem,_
_...From today I will never live you we will be together every moments and forever😍_
Sai tasa emoji na alamar kunya saida taduba rubutun da tayi kusan sau uku tana bita kamar karatu sannan ta tura cikin da kunya tamkar yana gabata tare da tura wayar ƙasan pillow tana jin wani irin nishaɗi acin ranta,
Wanda ta rasa dalilin sa,
Lokacin da saleem ya fita don bin bayan su Sulaim Motar da Yarima Sultan yashiga shida Sulaim har ta tashi sai wadda ke biye dasu yashiga,
Kai tsaye Yarima Sultan yawuce babban parlourn sa Shikuma Sulaim da Saleem suka zauna a center parlour,
Sai lokacin Sulaim ya ciru wayar Sa yakunna wadda kowa da kowa zai iya samun sa a ita,
Tun baro warsa Kano Baiqara kunna taba sai yau idan kaga Yana waya to da special Sim card din shine Shikuma wannan private ne numbers din da suke ciki basufi 12 ba,
Saleem Yana cikin kallon hotunan Suhailat sai ga shigowar message Nan kamar bazai duba ba ahankali yakai duban sa saman wayar saiga _My Suhailat_ ya baya na cikin ida nuwan sa lokaci daya yaji Wani faduwar gaba Mai qarfi,
Baiyi qasa a gwaiwa ba wajan bude saqon Hannun sa har tawa yake ya bude ya fara karantawa,
Murza idon sa yayi don gani yake tabbas a mafarki yake ganin wannan ba azahiri ba,
Cikin rashin yadda da abunda idanuwan sa suka Gane masa yaqara bin saqon ya karanta daya bayan daya tamkar Mai koyan haruffa,
Aqalla ba a qasara ba yabiya ya Kuma Mai maita wannan message din yakai sau 22 har qara duba number din yayi Yana tunanin kodai ba Number din Suhailat din bace Amma yaga Ita din ce dai,
Cikin wata murya wadda ni (Oum ameerah😍) bansan Saleem da ita ba naji ya furta,
Alhamdulillah ya rabbi tare da fadin I really really love you Suhailat,
Sulaim Wanda tun sanda Saleem yafara sun batun karanta saqon da Suhailat taturo masa,
Kawai ya tsaya Yana kallon iKon Allah take yafara tunanin tabbas Saleem yayi gamo dole a nema masa magani,
Sannan yakasa Gane Ina kalaman Saleem din suka dosa,
Dai dai lokacin Yarima Sultan yadawo cikin shigar sa ta shan iska riga ce Mai gajeran hannu sosai fara tass anyi rubutu a bayan rigar da launin baqi anrubuta *PRINCE*
Sai Wanda short dress din Nan Wanda yadan haura masa gwaiwa sosai Amma baikai qasa ba Kuma budadde ne launin Baki,
Baqaramin kyau yayi ba sai hasken sa yaqara fitowa sosai ga kwarjini kwantaccan gashin sa daya Sha gyara har bisa dogon wuyansa,
Haka yafito cike da qasai ta da izza kujera rar dake fuskan tar wadda Sulaim ke zaune Ita ya nufa ya zauna wadda Ita tamkar gadon karaga haka take,
Kallon shi Sulaim yayi tare da Fadin barka da fitowa Ina fatan Yarima na lafiya,
Murmushi Yarima Sultan yayi tare da Fadin idan Aminin Sultan Na lafiya To tamkar Yarima na lafiya ne,
Allah yasa Aminina Yana cikin Ameenci,
Sai lokacin Saleem ya kula da fitowar Yarima Sultan,
Shima barka da Fitowa yayi masa Yana Mai da dubansa kan wayar Sa don lokacin zuwa lokaci sai yaqara duba saqon Suhailat Kuma har lokacin Yakasa Yi mata Reply,
Yarima Sultan yaga kamar Akwai Farin ciki atattare da Saleem Hakan yasa shi kasa yin hakuri ya furta,
kamar Akwai Farin ciki atare da baqona Kuma aboki na Saleem?
Saleem ya tsinci muryar Yarima Sultan a kunnuwan sa Yana magana,
Qara fadada murmushin shi yayi tare da Fadin Alhamdulillah Yarima,
Jinjina Kai Yarima Sultan yayi alamar gamsuwa dakuma Jin dadin Hakan,
Bayan ya bude laptop 💻 din dake ajiye gabansa saman table yaqara Fadin Yarima zai sojin meye silar wannan Farin ciki da abokin sa yake ciki,
Dasauri Saleem yaqara dagowa ceke da mamakin Yarima Sultan Bai taba tsammanin haka yake ba bashida girman Kai gashi da saurin sabo gashi Yana magana bakamar yadda yayi tsammani ba,
Duk Saleem Yana wannan tunani ne ba tare da sanin waye Yarima Sultan ba Yana masa wannan ne duk saboda Sulaim bugu daqari ma jinin su yahadu, sannan a wasu lokutan Yana son wasa da tsokana,
Aboki na Soyayya tana da Dadi idan ka samu Mai sonka Kuma kaiima kakeso to haka ne yafaru dani a Dan qanqanun lokaci Saleem ne kemagana cike da shauqin abun da yake fada,
Yarima Wanda duk yaji komai murmushi yayi Wanda harsaida tsiraran haqoran sa farare tass suka bayyana,
Kallon Inda Sulaim yake yayi har lokacin da murmushin akan fuskar sa,
Suna hada ido da Sulaim Wanda duk yanajin su duk da wayar shi yake dannawa kamar baisan sunayi ba,
Cike da basarwa Sulaim ya daure fuska don ya fahimci Yarima Sultan din acikin yanayin wasa yake,
Kuma yasan yanzu sai fara tsokanar sa gakuma yajj kalaman Saleem tamkar Wanda yakamu da ciwone hauka haka ya dauki Saleem din,
Ganin Sulaim ya ya dare fuska ne Yarima Sultan yamai da kallon sa kan Saleem shima Sulaim din yake kallo,
Murmushi suka sake a tare,
Kamar Yarima Sultan bazaice komai ba cikin nutsuwar da ya furta abokina Ashe da gaske ne so Yana da Dadi kenan?,
Saleem yace Eh Nima akwanakin da suka wuce bansan hakan ba wahalar sa da radadin sa kawai nakeji tare da danasanin fadawa ta cikin sa Amma a yau Inajin Babu abunda yakai soyayya Dadi,
Wani irin kallo Mai kama da harara Sulaim yayi wa Saleem danshi har cikin ransa da gaske yake Saleem yakamu da matsalar kwakwalwa,
Murmushi Saleem ya sakarwa Sulaim,
Take Sulaim yamiqe da niyar barmusu gurin,
Ai kana tafiya sai mun bika duk Inda zakaje Yarima Sultan ne yayi maganar Amma idon shi nakan Computer 💻 din gaban shi Yana dannawa,
Dafe Kai Sulaim yayi tare da Fadin Ya Rabb ya koma ya zauna Dan yasan tunda yafada to baza su rabu dashi din ba,
Kafin kowa yaqara cewa komai saqon zuwan jakadiyar sarki yazowa Yarima Sultan Take yabada izinin tashigo,
Zubewa tayi a gaban Sultan tayi gaisuwa tare da kirari kala kala harsaida yada Katar da ita ta hanyar daga mata hannu,
Zaki iya gabatar da saqon sarki zuwa ga Sultan Yarima yafada fuskar Nan tashi tamkar Wanda Bai taba Koda murmushi ba,
Tuba nake ranka ya dade sarkin mu nagobe Allah ya temakeka tare da yawan nasara sarki yace asanar Maka zaku karbi Bakuncin Dan sarkin *DAMATURU* yanzu yasamu isowar saqon,
Sannan maimartaba sarki yaqara dacewa Asanar wa Yarima Yana da damar yin ko wace irin shiga Amma da zaiyi shigar *DAWISU* 🦚 Sarki zai so haka,
Mai martaba yaqara dacewa Yarima Yana da manya manyan baqi a Taron daza agabatar da yammacin a wannan rana Yarima yashiya tarbar su,
Allah yaqara Maka lafiya nagaba tar da saqon sarki,
Cikin Isa Yarima Sultan yace Zaki iya tafiya Asanar wa maimarta ba Adalin sarki Sultan yakarbi saqon sa Kuma Yana godiya,
Nabarku lafiya tatashi tafita da sassarfa,
Yarima Sultan komai wa yayi kamar bashine yagama wasa da murmushi ba yanzun Nan Kyakkyawan Hannun sa yakai Mai dauke da dogayen yatsu yasa ya rufe computer din dake gaban sa da alama Bai kammala abunda yakeyi ba,
Sabo yagama tsara komai hatta kayan dazaiyi hawa dasu zuk ya tsara Amma yanzu anason rusa masa shirin sa dafe goshe yayi tare da Dan zamewa ya jingina bayansa jikin kuje rar,
Sauri sauri gudu gudu haka jakadiya ke tafiya tamkar zata fadi ta nufi sashan gidan Galadima Kallon jakadiya HAJIYA MAI SORO tayi tare da Fadin ke Kuma lafiya Zaki fadamin parlour haka kamar wadda aka koro?
Rankiya dade uwar daki na tuba nake Tafe nake da labari zuwa ga *GIMBIYA SULTANA*
Meke Tafe dake zuwa gare ta hajiya Mai soro takara tambayar jakadiya,
Ina son sanar wa GIMBIYA SULTANA cewa Yarima Sultan shigar DAWISU 🦚 zaiyi a gurin Taron sa na anjima,
Sosai hajiya Mai soro tadawo da hankalin ta kan Jakadiya tare da Fadin wane tabbaci kike dashi akan maganar ki?,
Yanzu Mai martaba sarki ya turani na shedawa Yarima Sultan Hakan,
Aiki Mai kyau jakadiya kije kicigaba da SA idon ki sosai komai kika gani kizo da wuri kisanar min,
Yanzu saka mokwan wannan albishir din kinada kyauta ta musamman zata riskike zuwa jimawa Zaki iya tafiya,
Kihuta lafiya uwar dakina cewar jakadiya tafice,
Wani irin shu'umin murmushi hajiya Mai soro tayi Mai wayar fassarawa wayar dake gefan ta tadauka tareda Danna Kira,
Hajiya Mai soro itace matar Galadima wato qanin sarki Mai suna Murtala Shareef yanada Yara biyu Mudassir da Sultana,
💗💗💗
____---_____ *KANO*
*UNGUWAR KWANDILA*
Suhaima nifa gaskiya inaso kifada min wai Ina kike zuwa kwana biyun Nan Amma kin ƙi faɗamin Kaltum ce tafaɗin hakan cikin zafin rai tare da shan gaban Suhaima wadda ke niyar fita..!!
*Like nd share comments fisabilillah🙏*
What's app channel👇
https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V
WhatsApp group👇
https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs
_AHALIN MU DAYA_
💗💗💗
*CREATED AND WRITTEN*
*BY*
*Fatima Y zakariyya*
_😍Oum Ameerah_😍
*Nazari writer's association📚*
_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_
_(THE QUEEN👑)_
________Dedicated to anty salma💎
*Page* 4️⃣7️⃣↔️4️⃣8️⃣📖
____---____*KANO*
_UNGUWAR KWANDILA_
.......Suhaima nifa gaskiya inaso kifaɗa min wai ina kike zuwa kwana biyun nan amma kinƙi faɗamin, cikin zafin rai khaltum tayi maganar tare da shan gaban Suhaima wadda ke niyar fita, cak Suhaima ta tsaya tare da kai duban ta kan khaltum wadda ke tsaye a gaban ta tana jiran amsa,
Khaltum pls kibani hanya in wuce idan nadawo zakiji komai amma yanzu kina ɓatamin lokaci takai ƙarshan maganar tare da raɓawa ta gefan khaltum daniyar wucewa da sauri khaltum ta ƙara tare ta akaro na biyu, nifa kawai kifaɗamin Indai ba wani rashin gaskiyar kike aikatawa ba....
Kallon ta Suhaima tayi tare da ware manyan idanuwan ta akan fuskar khaltum wanda suka ɗai ake iya gani a fuskar tata kwayar idon ta ƙara zama ash mai turuwa saɓanin ada mai haske ce, da sauri khaltum taja baya tare da matsawa daga gaban ta batare da tace komai ba saboda ganin yadda Suhaima ta canza lokaci ɗaya, ganin tabata hanya ne hakan yaba ta damar sakai tafita da sauri, wata irin nannauyar ajiyar zuciya khaltum ta saki tare da dafe ƙirji ta koma gefan katifar su ta zauna tafara tunani kala kala tasaƙa wannan tawar ware wancan,
Mata ne zazzaune a tsakar gidan Hajiya fanteka zawara wa da ƴan mata kowacce da abunda takeyi batare da Suhaima tabi takan kowa ba ta fito cikin nutsuwa tafara raɓa su tana wucewa kanta a ƙasa, "anty ina yini" Cigaba da tafiya Suhaima tayi batare da tajiyo ba don bata kawo a ranta da ita akeba, da sauri matashiyar budurwar da tayi maganar ta tashi tabi bayan Suhaima sai da ta tabbatar tazo kusa da ita, akaro na biyu ta sake Faɗin " ina yini anty" tsayawa Suhaima tayi tajiyo a hankali tare da kallon mai magana abayan ta,
Oh Sajeedah ya kike Suhaima ce tayi maganar cikin fara'a duk da ba'a ganin fuskar, "lafiya ƙalau anty ashe biki manta niba gashi har sunana kika faɗa, kwana biyu bana ganin ku nayi tunanin ma kunbar nan ne" Suhaima tace A'a muna nan lafiya mun ɗanyi tafiya ne kwana biyu fatan kina cikin farin ciki, "sunkuyar da kai Sajeedah tayi da murmushi tace ina lafiya dama tun ranar da kika ce zaki nemeni