Showing 60001 words to 61789 words out of 61789 words
Chapter 21 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel
kwalla tace Yaya yarima ƙofar a rufe take,
Baice komai ba tashi yayi ya nufi inda take tsaye saida yaje gab da ita sannan ya tsaya yana kallon ta cikin ido ba shiri tayi ƙasa da nata idon amma tana jin nashi ya mata yawo a jikin ta hawayen idanuwan ta suka fara gangaro wa saman kuma tun ta don ita har ga Allah tsoran shima take yi gani take kamar zai hukunta ta ko yasa a hukunta ta, "ke yanzu ko cewa akayi ki fita ahaka sai kifita biki ga kayan dake jikin ki bane?
Tsintar muryar Yarima tayi cikin kunnuwan ta, take ta fara kallon jikin ta don ita tama manta yadda take cike da jin kunya ta ɗanja da baya, shima juyawa yayi ganin lokaci na ƙure masa gashi yana son ganin Aminin sa Sulaim,
Kayan da me martaba ya aiko masa dasu yafara dubawa cikin nutsuwa komai rainbow colour ne yanayin Gashin ɗawisu, sai rawani launin baƙi sai takalmi irin nasara kai da kwalliyar zinare ajiki, cikin nutsuwa princess salma ta ƙarasa inda yake duba kayan ta tsaya, tare da Faɗin " ama tsayi na na ƙanwar aminin yarima kuma ƙanwa ga Yarima Sultan sarkin gobe da yaddar Allah ina mai roƙon alfarma akan yarima kada yasa kayan dake hannun sa a yanzu, zai fi da cewa ga adalin shugaba yasan wannan kayan zasufi kyau a gareshi ta furta hakan tare da nuna wasu saitin kayan dake ajiye a gefe wanda dama shima kanshi yariman su yayi niyar sawa,
Ganin irin kallon da yarima Sultan yake yimata ne yasa ta saurin cewa tuba nake Ranka shi daɗe Allah ya sanyaya zunciyar Yariman gabas taƙai ƙarshan maganar tare da kama kunnuwan ta duka biyun, har cikin ransa yaji daɗin abunda tayi amma saboda mulki sam babu alamun hakan a kan furkar shi, "dama kawai na faɗi hakanne saboda nasan akwai ƴaƴan sarakuna wanda zasu zo dayawa da ƴaƴan manya kuma dole za asamu wanda yayi shigar ɗawisu saboda shigar sarakai ce, nikuma ina ganin ka fita daban acikin su sai yafi ƙayatar wa,
Ƙasa tayi dakan ta cikin sanyin murya tace dan Allah yaya yarima kabuɗe min ƙofa nima zanje nashirya saboda nasan ummeetha ma nane mana yanzu,
Batare da yarima yace komai ba ya ɗauki wayar sa ya nufi wata ƙofa dake maƙale a cikin ɗakin, aransa yake mamakin Yarin yar nan irin ƙarfin halin ta gashi bata shakkar yi masa magana, take yafara jin haushin kansa taya akai ma ya kawo ta bedroom ɗin sa dayake ta tabbacin babu wata mace da ta taɓa taka hanyar da yake idan ba itaba ko a mazan ma mutum ɗaya ne shine Sulaim banda shi babu wanda ya taɓa shiga sai ita gashi har saman bed ɗin sa, cikin jin zafin hakan ya tura ƙofar ɗakin yashiga, amma kuma sai yaji wani ɓangaran na zuciyar sa na ɗaukar hakan ba amatsayin komai ba, waya ya kara a kunne bugu ɗaya aka ɗaga wayar " Assalamu'alaikum Amincin Allah da rahmar sa su tabbata agareki Mahaifiya ta ina fatan ummul bait na cikin aminci"
Amasawa tayi cikin jin daɗin jin muryar shalelen ɗan nata, " fatan yarima ya kammala shirin sa"
Da izinin Allah zan kammala yanzu ina niman alfarma a gurin ummul bait Yarima nason a turo masa wadda ita iya kwalliyar mata M...... Bai ƙarasa faɗar abunda ya ɗakko ba sauran ya maƙale a maƙoshin sa jin yana nema yayi ɓaran ɓara ma,
Daga ɗan ɓangaran ummul bait tayi murmushi mai sauti tare da Faɗin angama zaka samu isowar ta yanzu insha Allah batare da jiran abunda zai ce ba ta kashe wayar,
Nannauyar ajiyar zuciya yarima sultan yayi kafin ya ajeyi wayar yafara shirin sa cikin nutsuwa,
Lokacin da yarima yafito bayan kammala shirin nasa baƙaramin kyau yayi ba Princess wadda duk tagama gajiya kayan jikin ta har sun bushe taɗago ta kalle shi masha Allah ta furta wanda bata san ma lokacin da ta fito ba, shiga yayi ta yaran sarakan nahiyar mai ɗauke da tsantsar kyau bai sa kayan da Princess ta zaɓa masa ba sannan bai sa na mai martaba ba, riga da wando ne yasa launin blue mai haske rigar har gwaiwa gaba ɗaya tun daga saman ta harƙasa aiki ne a jiki irin na mutanan ƙasar Pakistan anyi mata ado da duwatsu marasa nauyi, shima wandon anyi masa aiki daga ƙasan shi ƙarshe, yaɗora alkabba fara mai kwalliyar blue mai haske, tare da farin rawani wanda hakan baƙaramin kyau ya ƙara masa ba, ta kalmin sa shima blue irin na Sarakuna sai tashin ƙamshi yake,
Wasu kaya yanuna wa princess alamun ta ɗauka ba musu ta ɗauka tare da bata wata alkabba mai hula yace ta ɗora saman kayan jikin ta hakan kuwa tayi, saida yafara fita sannan tabi bayan sa a parlour suka tarar da mai kwalliyar har ta iso, nan yabada umarnin a shirya princess ɗin zai turo a tafi da ita, baijira cewar su ba yafita, tun daga bakin ƙofar sa shan nasa ya hau doki wanda shima kanshi doki yasa ancanza masa saboda yacanza shigar da zaiyi,
Taro yayi taro kowa na zaune babu wanda ake jira sai yarima Sultan kowa burin sa yaganshi, yana gama hawa doki sai ga Sulaim yafito shima cikin nasa shirin wanda sai ka rantse irin yariman ƙasar yankin Larabawa ne sai dai bai ɗora alkabba saman kayan nashiba, haɗa ido sukai da Sultan take suka sakar wa juna murmushi, yarima saman doki Sulaim ya nufi mota yashiga,
Fadawa ne kijan lizamin dokin da yarima sultan ya hau tunkafin ya isa gurin aka fara kiɗe kiɗe da bushe bushe babu abunda ke tashi sai sautin algaita dakirari ga yarima, saida yarima ya burge kowa a gurin wasu kuwa kamar su mutu don baƙin ciki,
Lokacin aka sanar da iso war yarima dai dai isowar mai martaba sarki, sakko wa yarima yayi daga doki ya nufi gurin sarki ya miƙa gaisuwa, sarki yamiƙa masa hannu da sauri yarima yaƙa yin ƙasa da kansa cikin girmamawa murmushi sarki yayi "fatan komai ya kammala cewar sarki, "eh Ranka ya daɗe insha Allah yanzu za a fara" to Allah yabada sa'a asauka lafiya sarki yafaɗa tare da wucewa mazaunin da aka tanada danshi ya zauna fadawa biye dashi suna kirari,
Komawa yayi gurin manya manyan sarakunan da suka halacci taron ɗaya bayan ɗaya ya kwashi gaisuwa, ga ƴaƴan Sarakuna kuwa gaba ɗaya miƙa musu hannu yayi suka yi musabaha, Yarima yana hawa doki Aka sanar zai fara zamiya ga gimbiya Sultana kafin sarki, ƙara ɗaure fuska Sultana tayi saboda jitaje tamkar ta fashe da kuka saboda ansata tayi shigar ɗawisu, ashe yarima ba ita zaiyi ba,
Ƙarshan filin yarima Yakoma tare da karkaɗa linzamin dokin yana ƙara dai dai ta sirdin sa tare da ƙara gyara zama, kafin kace me doki yafara sassarfa da sukuwa, yafara gudu yana za gane gurin tamkar yarima sultan zai faɗo, da wani irin gudu dokin ya nufi gurin da gimbiya Sultana take bisa mamakin Sultana ta tashi cikin razani da tsira tamkar yau tafara zaminya, ba yarima sultan ba saida ranki wa yaɓaci a gurin bama kamar Hajiya mai soro wadda taji gaba ɗaya kima da darajar su tataɓu dalilin abunda sultana tayi,
Daɗi kamar zai kashe gimbiya Shaheedah saboda taji daɗin hakan, Siyama kuwa har saida tayi wani ɗan ihu saboda murna,
Barin gaban ta dokin yayi saboda tafaɗi taji tsoro, cikin harzuƙa yarima sultan ya ƙara kaɗa linzamin dokin da gudu gaban wata kyakkywar budurwa wadda ta iso gurin a lokacin shigar ta sak irin ta yarima sultan komai da komai saidai ita an rufe mata rabin fuskar ta da abun ado na zinare mai kama da sarƙa bawanda ya gane ko wace ce ita da wasu kuyangi guda biyu,
Ganin dokin da gaske kansu yake yi hakan yasa kuyangin darewa da gudu sukabar princess a tsakiyar fili, tunanin kowa budurwa zata razana amma sai suka ga itama tana tafiya a hankali tana tun karar dokin, take akasa ihu gaba ɗaya gurin, dukin yayi wani irin kuka da haniniya tare da ɗaga ƙafa fuwan sa sama kamar zai haye princess salma, wata irin zamiya sukai lokacin Yarima sultan yazaro wata wuƙa a gefan alkabba sa ya cilla ta zuwa sama, ga mamaki kowa sai dokin ya tsaya ita kuma wuƙar ta dawo hannun yarima, kiɗa da busa aka cigaba da yi sabon salo shikuma yarima ya sauka daga saman dokin yamiƙa linzamin zuwa ga wani bafade,
Ihu da kabbara aka shiga yi kowa abun yaƙayatar dashi wasu kuma hankalin su Yakoma kan wace ce wannan Yarin yar haka ko daga wace masarautar ta zo Oho da yawan su abunda ke musu yawo a zuciya kenan gashi tayi irin shigar yarima komai da komai,
Takawa yarima sultan yayi cikin nutsuwa zuwa gaban princess, sai da yaje gab da ita sannan ya tsaya kallon ta yayi sosai, yama rasa Meye zai ce saboda daɗin da yaji na abunda tayi yana mamakin abunda tayi ita da ba ƴar masarauta ba, a saitin kunnan ta yayi magana, "Yarima ya gaishe da ƙanwar sa zamu iya tafiya"
Gaba ɗaya fa kallo ya koma sama murmushin ƙarfin hali princess tayi saboda ƙirjinta da yake ta dukan ɗari da hamsin saboda tsabar firgici da tsoron da ta shiga lokacin da take tun karar dokin jitayi kamar ana bata umarni, ɗan ɗaga mata gira yarima yayi take ba musu suka jera suka fara tafiya gwanin ban sha'awa zuwa mazaunin Yarima,
Sai da gimbiya Sultana taji kamar ta haɗiye zuciya ta mutu kawai ta huta, mamaki ya hana Galadima motsawa daga inda yake saboda ganin yarima yayi hawa kuma ya sauka lafiya kenan gaba ɗaya aikin su ya tashi abanza..!!!
ALHAMDULILLAH!
ALHAMDULILLAH!!
ALHAMDULILLAH!!!
Anan ne na kawo ƙarshan littafi na ɗaya (book 1) acikin wannan labari namu mai takyan _AHALIN MU ƊAYA_ kukasan ce dani acikin littafi na biyu domin jin yadda zata kaya,
Kada kumanta ga Suhaima a Arab estate Shin zasu tsallake wa fansar ta? , komeye fansar ta Oho? , Meye zai biyo baya tsakanin princess da yarima sultan? Shin yarima zai tsallake makircin ahalin gidan su?
Menene asalin AHALIN MU DAYA?
Kubiyo alƙalamin _Fatima Y zakariyya_ _(Oum Ameerah)_ don jin yadda zata kasan ce acikin book 2
NOTE!!!
GA masu tsokaci ko wani ƙorafi ko shawara game da littafin ahalin mu ɗaya zasu iya yimin magana ta wannan number ɗin (what's app only) 08141825210.
Group what's app ahalin mu ɗaya comments section,
https://chat.whatsapp.com/C9sZ6UCsGEHKSALn3SYSqs
_Love u all my fan's❤️💜_