Showing 12001 words to 15000 words out of 61789 words

Chapter 5 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

167

ɗakin a rufe yake, jiyowa suhaima tayi tare da sakin murmushi mai sauti sannan tace kada ki damu ta ƙofa zan koma sai ki taso ki rufe muku saboda irin mu irin mu ko,

Kafin taceyi wani wunƙuri suhaima har tafice, takardar hannun ta tabi da kallo wadda suhaima tabata ARAB ESTATE, ARAB ESTATE, saida ta mai maita sunan sau biyu sannan ta fashe da kuka yauni fanteka na haɗu da gamona hajiya zaituna ta haɗani da jaraba,

A a hajiya kukan mekikeyi adaran nan ko dai rashi akayi ne, Larai ce ke magana wadda take ta yatsina fuska alamun baccin bai ishe taba,

Ubanki ne nace Ubanki aka rasa yanzu zaki bar min ɗaki don baki da wani amfani, duk abunda ya faru biki tashiba sai yanxu ko,

Haba uwar ɗakin mu Meye kuma ya faru ni.....

Bansani ba yo ni ai da kasheni za ayi da tuni ankasheni babu kamfanin tayani kwanan nan dakikeyi dole kikoma ɗakin ku yanxu ba sai anjima ba, takai ƙarshen maganar tare da watsawa Larai harara wadda ita dai Larai bata san hawa ba bare tasan sauka,

ARAB ESTATE

Tashi baffa imran yayi bayan dogon lokacin da ya ɗauka yanayi wa sulaim addu'oi, harya yakai ƙofa sai kuma ya jiyo ya ƙara kallon kyakkyawar fuskar sulaim tare da sakin murmushi sannan yafita daga bedroom ɗin,

Da sallama ya shiga yana bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya ya nufi kujerar daya tashi wadda ta kasan ce itace a tsakiyar perlon 3 siter tana fuskantar ko ina acikin parlon, tsayawa faɗar haɗuwar gujerar ɓata baki ne saboda colour ɗin ta ma daban ne acikin kujerun perlon tamkar gadon sarauta hakatake, cikin nutsuwa irin tasa hannun sa riƙe dawani sanda irin na masu ɗan ciwon ƙafa amma shi tashi daga ta gayu ce ta haɗu iya haɗuwa ga ta ruwan gold, ahaka yaqara sa ya zauna kai ka rantse wani babban sarki ne a fadar sa,

Saida ya dai daita zaman sa sosai kafin yayi gyaran murya, hankalin kowa ya dawo kansa da masu magana ƙasa ƙasa, da masu wani tunanin, da waɗan da hankalin su na akan waya, gaba ɗaya suka maida hankalin su kan baffa imran Arab,

Cikin muryar nan ta dattaku yafara magana,

Alhamdulillahi muna ƙara godema Allah abisa komai, kamar yadda muka saba a duk lokacin da ɗaya daga cikin iyalan gidan nan waɗan daba a wannan ƙasar suke ba mukan taru don yi musu barka da zuwa tare da tattaunawa game da al'amarin cikin gida, to Allah mai iko abisa komai ya kawo mu wani lokacin wanda shi Bello yazo tare da iyalansa,

To Insha Allah a yau baza mu samu tattaunawa ba saboda halin da ɗaya daga cikin ahalin gidan nan yashiga gabanin wannan lokacin da muke yanxu wanda hakan ya faru ne agaban idon kowa acikin ku, sai zuwa sanda ya samu sauƙi sosai, ama dadin kowa ina yiwa Bello da iyalansa barka da zuwa,

Ɗan russuna wa uncle Bello yayi daga inda yake zaune yace muna godiya baffa kuma mun amsa,

Jinjina kai baffa imran Arab yayi alamun gamsuwa da batun daddyn Canada,

Sannan ya furta muna yi wa sulaim hameed Arab fatan samun lpy,

Kowa zai iya tafiya haka suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya suna fita amma babban abun mamakin cikin ƴaƴan sa maza babu wanda ya motsa bare a saran zai tashi, da alama haka sukeyi a duk wani taro saboda babu wanda ya damu da hakan kuma shima alhaji imran Arab ɗin bai motsa ko ina ba,

Hajiya umma ce ƙarshan fita tabar parlon itama tare da barin alhaji imran da ƴaƴan sa, alhaji hameed, mai girma hasheem, daddyn Canada wato uncle Bello, He excellency Sambo, uncle Mansur, captain Yusuf wanda suke kira da uncle Yusuf , major shaddad, professor Aliyu Arab, sai Abubakar wanda suke kira da uncle A, su kaɗai suka rage a parlon sai baffa imran ɗin duk suna zazzaune ko wannan su da abunda yake tsaqawa aransa,

Sai da suka tattauna sosai game da rashin lafiyar sulaim har wajan 11:30 sannan daga ƙarshe alhaji imran yace kowa ya koma wajan iya linsa shi zai kwana da sulaim ɗin, babu wanda yayi musu acikin su haka kowa ya tashi wasu kam zuciyoyin su fass saboda duk zaman ba acin ma wata ma tsaya ba game da rashin lafiyar sulaim ɗin,

Suka fito kowa yashiga mota yanufi ɓangaran da yake da da Alhaji hameed da daddyn Canada mota ɗaya suka shiga dama kuma tare suka zo,

Uncle Yusuf ne yakai dubansa inda ya jiyo wata irin mahau ka ciyar dariya kamar a gidan boss wazai Gani, mai girma hasheem neke tsaye shida excellency Sambo suna magana,

Girgiza kai yayi kawai ya shege mota abunsa yana Allah wadai da wannan hali na ƴan uwa sa shidai bai san Meye matsalar su kuma ba a taɓa gane gaskiyar su da kuma abunda suke aikatawa, kullum addu,ar sa ɗaya ce Allah ya ganar da su sannan ya ƙara haɗa kansu kodan ƴaƴan su,

In the morning

Ya daɗe yana zaune daga cikin mota idanuwan nan nasa kamar kullum a lumshe suke ware su yayi kaɗan jin kamar a na knocking window din motar, yakai dubansa gurin sannan ya zuge glass ɗin a hankali, murmushi suleem ya sakar wa sulaim shima ya maida masa bayabo babu fallasa,

Yata akai kasan ina nan to ka buɗe mun inshigo sai nafaɗa maka ba musu tabuɗe masa still da wannan murmushin nasa mai ƙara bayyana kyawun sa,

Kallon shi sulaim yayi yana jira yaji ta ina yasan yana nan gurin,

Ƴar dariya saleem ɗin yayi kafin yace, nakira baffa don jin ya jikin ka zan shigo part ɗin Don duba ka sai yace ai ka tashi tun ɗazun kama shirya harka fito, to shine na fito tarbar ka kai kaga yadda kayi kamar bakai bafa,

Kamar mai ciwon baki ya furta, to wayace maka banida lafiya, yanxu daka fito nan jirana idan da ba nanɗin na nufoba fa?

Ya ƙara kafe saleem da ido donjin Meye abunda zaice,

Hhmm saleem ya furta ya manta idan sulaim yafaɗi baya iya tuna komai daya faru gani yake kawai bacci yayi,

Haba amini na wannan duk nameye tambayoyin manta kwai mu ƙarasa ciki muyi breakfast ko?

Dame aikin company kadace ba soja ba wlh bakinka kullum a buɗe kana dariya cewar sulaim cikin ƙara ɗaure fuska,

Dariya saleem yaƙarayi habuɗe baki kenan zai yi magana, sai ya hango suhailat na fito wa zata ta fi school kafin kace Meye har yafice daga cikin motar sulaim ɗin yanufi inda take, shidai sulaim sai hango su yayi tacikin glass saleem yabuɗe ma suhailat murfin mota ta shiga yakarɓi key ɗin a hannun driver yaza gaya ɗayan said ɗin ya zauna,

Wani siririn tsaki sulaim yaja yana tunanin wai duk akan mace yake wannan rawar jikin kafin ya zuro ƙafarsa waje yafara Taku zuwa cikin Part ɗin iyayen nasa,

Kallon parlon yake babu kowa aciki aransa yace ko dai suna sama ne bai gama tunanin ba, yaga mace aga bansa sanye take da wata riga iya gwaiwar ta kamar rigar bacci to amma wannan ta kama jikin ta sosai irin English wears ɗin nan kanta ko hula babu tasake gashin nata tage fe,

Miƙa masa hannu tayi da nufin su yi musabaha, kamar ƙaramin yaro haka yabita da kallo tare da maida hanna yansa ƙirji ya goya, murmushi tayi tare da daga kafaɗa irin na ko a jikin ta ɗin nan itama ta ɗauke nata hannun, tare da furta masa,

Hii I'm saleema Bello Arab by name,

Jinjina kai yayi shima ya furta can ƙasan maƙoshin sa,

Welcome Nigeria saleema, and I'am sulaim Arab yana kawa nan yara ɓata yawuce abunsa, princess dafitowar kenan taga duk abunda ya faru jitayi kamar ta fashe da dariya don dama tasan Indai yaya sulaim ne ba ataɓa burgeshi.

*Wannan kenan...!*



*💕AHALIN MU DAYA* 💕

*🖊️🖊️ALƘALAMI YAFI TAKOBI* ⚔️

*Story by°°°*

*💞Fatima Y zakariyya*💞

_😍Oum Ameerah_😍

_Taku har kullum_❤️

*Sarauniyar🫅 nazari writer's association*📚

_Muje zuwa_✍️✍️✍️

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*✍️📚Nazari writer's association✍️*📚

_Kyakkyawan nazari kafin rubutu na ɗanfare da bin ƙa ido jin rubutu_

_Cikyakkyan nazari kafin rubutu kan Ƙaya ta duniyar adabin hausa_

*Dukkan yabo da godiya su tabbata ga allah mahaliccin ko wa da komai Allah kayi dadin tsira abisa shugaban mu annabin mu annabin rahma Muhammad (s.a.w)*

*Ina roqon Allah yadda nafara rubuta wannan littafi Allah kabani iKon kammala shi lpy abun da na rubuta dai dai allah kabamu ladan Wanda nayi kuskure Allah kayafemin Ina roqon Allah kaqarawa iyayen mu lpy Imani da nisan kwana* 🤲



👍 JINJINA GA YAN FREE GRP

* Ummu safwan💝

* Mrs Muhammad s🤩

* Bin abdurrahman🌹

* Nanjid👩‍❤️‍👩

* Nusaiba M zakariyya✨

*💖 SPECIAL GIFT 🎁 TO MY BIG BROTHER Abba Maifata💯*

*AHALIN MU DAYA*

*NA*

*💞Fatima Y zakariyya*💞

_{😍Ummu ameerah_😍}

*Sarauniyar👸👸nazariwriter's association*📚

_____ Dedicated to aunty khadija matar uncle na 10😍🙏

*Page* 1️⃣5⃣▶️1️⃣6⃣📖

Hii I'm saleema Bello Arab by name

Jinjina kai yayi shima ya furta can ƙasan maƙoshin sa,

Welcome Nigeria saleema, and I am sulaim Arab, yana kaiwa nan yaraɓata tagefan ta yawuce abunsa,

Princess da fito warta kenan taga duk abunda ya faru ji tayi kamar ta fashe da dariya tasan dama Indai yaya sulaim ne ba ataɓa birge shi, ban haushi gare shi,

Yana gab da hawa upstairs yaji ankira sunan shi, tsaya wa yayi cak kafin yajiyo yaga waye mai kiran nashi, uncle Bello ne cikin nutsuwar sa yanufi dinning ɗin, kai tsaye yanufi kujerar da uncle Bello yake zaune russuna wa yayi daniyar gaida shi kamo hannun sa uncle Bellon yayi yaja masa kujera kusa dashi yayi mishi alamun ya zauna, babu musu yazauna sannan yace,

Daddy barka da safiya,

Barka dai ɗana ya katashi,

Lpy daddy,

To bari ayi saving ɗin ka,

Nayi break daddy Alhamdulillahi,

Good Morning yaya,

shiru princess taji Harma tafidda ran bazai amsata ba sai kuma ta tsinci muryar sa,

Morning,

Iya abunda yace kenan, ya maida hankalin sa kan wayar sa yana natsawa,

Kallon shi ummeetha tayi aranta tace oh ni maryama naga ta kaina, Allah ka kawo sauƙi acikin lamarin sulaim saboda taga yau abun nashi yafi na kullum sai wani haɗa fuska yake yi gashi yana magana daƙar duk da tasan haka yake to amma kullum abun gaba yake, ko ita da ta haifeshi rabon da taga dariyar sa har baza ta iya tuna wannan lokacin ba,

Maganar mommy ce ta katse wa ummeetha tunanin da takeyi,

My ƙalbiy barka da shigowa, mommy ce tafurta hakan tana kallon sulaim wanda Tunda yazo gurin bai yiwa kowa magana ba sai iya daddyn Canada,

Ɗan Jim yayi kafin yaɗago saboda yasan shi kaɗai mommy take cewa ƙalbiy,

Gani yayi duk shi suke kallo aransa yace kamar wani TV shifa baya son kallo ko ka ɗan,

Cikin jin kunyar abunda yayi ya furta mommy amun afuwa dana bari kugama cin abincin ne sai mu gaisa,

Murmushi tayi tace ai baka laifi ƙalbiy na nima nayi tunanin hakan daga gareka,

Shima murmushin yayi mata sannan yace ina godiya a madadin uwa ta,

Abiiy barka da asuba ya faɗa yana ɗan kallon mahaifin nasa alhaji hameed wanda cin abincinsa kawai yake yi kamar bai san duk abunda suke yi ba,

Kallon tsaf yayi yiwa sulaim ɗin kamar mai son gano wani abu a tattare da shi, sannan yace,

Yauwa fatan katashi lpy, alhamdulillahi Abiiy,

Har ya maida kallon sa kan wayar dake hannun sa sai kuma ya ɗago da sauri,

Ummeetha wai laifin Meye nayi ne naga sai harara ta kukeyi ni dama nasan kindaina sona ya kai ƙarshan maganar cikin kwaɓe fuska alamun shagwaba,

Babu wanda baiyi dariya agurin ba saleema da dama shi take ta kallo Tunda ya zauna agurin, dafe baki tayi alamun mamaki a slowly tafurta Awww Allah yayi halitta wai dama haka yaya sulaim yake wayyo Allah maƙurar kyau, ita bata san ma maganar tafito fili ba,

Shiko in seriously yayi maganar sa bai ga wani abun dariya ba, sulaim shagwaɓaɓɓene na bugawa a newspaper baya taɓa duba ya girma saboda tsabar gatan dayake samu a gurin kakannin sa da iyayen sa,

Ummeetha wanda murmushi yaƙi dauke wa daga kan fuskar ta saboda baƙaramin dariya abunda sulaim yayi yabata ba ba yau tasaba ganiba amma dai da alama wannan yayi mata daɗi,

Meƙewa sulaim yayi yace Allah bazan ƙara dawowa part ɗin nan ba har sai kun ne meni Tunda yanzu ba asona shifa da gaske yake yi,

Allah ya tsare hanya kafi ruwa gudu mu mabiyo ka idan muna son ganin ka yanzu dai kada ka ƙara dawo mana Part Tunda banaka bane,

Haba ummeetha yazaki rinƙa yiwa ɗana haka to gaskiya nima saidai inbishi duk Yakoma har sai kunxo biko,

Abiiy ma dai dariya kawai yake yi,

Yanxu ina kayi ne ɗana sulaim ya jiyo muryar daddyn Canada,

Tsayawa yayi batare da ya jiyoba wai shi a dole yayi fushi, daddy office nanufa,

To jirani muje ina so inga abokin aikin ka DR. Jabir,

Daddy Yayi hakanne don yana so ya tattauna sosai da sulaim ɗin dangane da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar sa dan su samu mafita game da lalurar tasa,

Muje ko ganinan zuwa yacewa sulaim ɗin mu dai muntafi Tunda kun kore mu, idan saleem ya dawo ya sameni shima a hospital ɗin,



Abiiy yace to idan kunje kutare acan amma banda yarona saleem, murmushi daddy yayi yace to mu dai munji ai nawa ba irin naku bane, da haka dai daddy da sulaim suka fita daga area dinning ɗin cikin jin daɗin hirar tasu,

Taɓan garan sulaim ba wani daɗin hakan yajiba don shi baya so a turke shi yafiso koda yaushe ya kasan shi kaɗai yabaya son Magana kwatakwata wannan ma don iyayensa ne ahaka gani yake yau baƙaramin surutu yayi ba wanda hakan yasa kanshi yafara ciwo,

(SAMBO IMRAN ARAB STREET).

Shima wannan flat house Ne Mai ɗauke da Part 3 saɓanin house ɗin alhaji hameed da na mai girma hasheem wanda su Part 4 ne acikin house ɗin su yaɗan fi girma,

(NO. 04 He excellency Sambo Arab house)

Aka rubuta daga gefan gate ɗin shiga ciki,

Parlo ne babban gaske wanda yaji kayan alato na more rayauwa duk wani abun jin dadin rayuwa akwai shi acikin parlon komai na cikin parlon maroon colour Ne Mai turuwa sosai, kama daga kan kujeru, carpet, labulaye, welcome, soper, da dai sauran su duk maroon colour Ne,

Mai girma hasheem uncle Mansur, Sambo, barrister Sulaiman babban ɗa agurin hasheem kuma jikan fari acikin Arab family, suna zaune kowanne hannun sa ruƙe da cup na black tea aciki atsakiyar su wanin ƙaramin dinning ne asaman shi an ajiye ƙaramar teapot, da ƙatuwar kwalbar honey, sai wata doguwar kwalba guda biyu 2 irin na (BER) din nan dagani kasan alcohol ce aciki mai launin whisky strawberry da alama kwalba ɗaya aka buɗe suna surkawa da wannan black tea ɗin. kurɓa suke hankali kowa da tunanin da yake aransa fuskokin nan nasu babu annuri aciki,

Barrister Sulaiman ne ya ajiye nashi cup ɗin sannan ya kalli iyayen nasa ɗaya bayan ɗaya cikin wata murya irin ta wanda ta kai mai karo yashawu, yafara magana Haba abba ai kawai shawar da uncle Mansur yakawo ita ya kamata a bi don yin abunda yadace cikin gaggawa don gaskiya ne na gaji, sonake komai ya dawo hannun mu, har tsawan wana lokaci zamu ɗauka muna bibiyar sa amma kullum jiya iyau, wancan ɗan iskan da ba wata lafiya gareshiba, kullum cikin faɗuwa yake amma an ɗauki abun nan mai daraja da amfani ambashi to kawai idan muka kwau dashi zai fimana sauƙi wajan gano inda wannan (HATIMIN) yake,

Kallon sa He excellency Sambo yayi da ida nuwansa wanda suka kaɗai suka yi ja, hannu yamiƙa kan table ɗin dayake gefansa ya yazaro tsinken karan sigari guda ɗaya, daga cikin wani haɗaɗɗan kwali wanda Indai ba gani kayi ba sai ka rantse tissueee ne aciki ko room freshener, yaba zaro ta tafara hayaƙi alamun ankunna ya kai bakin sa yazuƙa kafin ya busa haƙin sama cikin wani irin salo da kwarewa a harkar,

Kai wana tabbaci kake dashi nakan cewa wannan yaron sulaim akabawa HATIMIN nan wai, don gaskiya ne nafi ganin har yanxu yana hannun ubansa hameed, Sambo ne yayi maganar yana kallon Sulaiman,

Kamar dai ni gaskiya nima ina ganin HATIMIN nan yana hannun Bello ko hameed, cewar mai girma hasheem,

Ina da tabbatacciyar hujja akan hakan, Sulaiman ya faɗa ya taƙaice,

Kada ɗe kana faɗa mana haka idan kanaso mu yadda to kawai ka nuna mana kasan baza muyi abu da kaba ko cewar uncle Mansur dake ƙara tsiyaya black tea ɗin nan acikin cup ɗin sa,

Gashinan ku kunna wannan Kuji, wata ƴar ƙaramar recorder barrister Sulaiman ya ciro daga cikin aljihun wandan sa ya ɗora saman dining ɗin gabansa, kallon kallo akashigayi tsakanin hasheem, Sambo, Mansur,

Kunna muji cewar mai girma hasheem yana kallon uncle Mansur, ba musu ya ɗauka ya kunna saiga muryar mahaifin su alhaji imran Arab (baffa) ta fito yana magana,

"dole ne kai za karɓi HATIMIN nan, idan bakaiba sulaim babu wanda zan iya bawa shi a yanxu, kafin yanzu kasan a hannun mahaifin ka yake to amma na karɓa saboda hakan nane ma yaraba kan iyalan gidan nan nikuma har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login