Showing 21001 words to 24000 words out of 61789 words

Chapter 8 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

184

tagama fita gaba ɗaya sannan ya tashi napep ɗin sa ya fice abun sa,

Suhaima tafi khaltum tsayi, hakan yabata ɗan sauƙi wajan goya ta amma gaba ɗayan su basu da kaurin jiki har garama khaltum ɗin tafi Suhaima,

Wai ge wai ge Suhaima tafara yi tana ne man hanyar dazatabi don ganin koda nurse ne, amma ta rasa, acikin kata faran asibitin daya gama tafiya da tunanin ta, masha Allah kawai ta furta aranta tace ai wannan da gurin shaƙatawa yayi kama ba asibiti ba, ga shi ko ina ka wulla idon ka flawer's ne masu kyan gaske wasu green, wasu pink, wasu read, wasu white, da dai sauran su shi kanshi tsarin ginin asibitin ba naƙasar nan bane, abun bugewar ma ko ina fass fass kamar kazuba abinci kaci, haɗuwa iya haɗuwa, ga wasu chairs masu Burgewa tare da wata ƴar runfa kamar bukka, daga gefe,

Saida Suhaima taji kamar zata faɗi, saboda kallo tama manta da khaltum dake abayan ta gashi yamma naƙarayi sosai,

Idon ta ɗan ɗaga sama daga can saman taga an ruta sunan asibitin da manyan baƙi cikin wani salo shima mai ɗaukar hankali,

Tana cikin wannan hali na kalle kalle taji, an daka mata tsawa, runtse ido tayi sannan taboɗe har kwayar idon ta koma rainbow colour, am a bata juya ba,

Kai uban Meye kake yi anan cewar security ɗin dake sanye da uniform a jikin sa, wanda dagani ma kasan ba bahaushe bane ka buɗe fuskar ka mugani kai bakada gaskiya shine zaka shigo nan ko, ko hausar tashi bata fita sosai, ke ba magana akeyi miki ba, cikin hargagi ya ƙara yi mata magana,

Suhaima wadda ko motsi batayi ba bare yasa ran zata jiyo ma,

Wani irin zafi take ji a zuciyar ta tana addu'oi take karantu wa Allah yasa kada yanayin ta ya canza agurin nan, don idan hakan ta faru itama bata san irin abunda zata aikata ba, ita fa babu abunda ke saurin canza mata yanayi irin ayi mata tsawa to ranar ko waye ya tsawa ma mutum sai ta hukunta shi, to ita yanzu burinta kawai a karɓi khaltum a duba lafiyar ta, amma ba don hakaba hmmm kawai tace,

Cikin ikon Allah zuciyar ta tabar zafin sannan kwar idan ta ta koma daidai kamar yadda take ash colour,

Juyawa tayi ta kalli security ɗin sannan tace, sannu fa likita nake son gani, mara lafiya na kawo,

Sai da yaɗan ja baya ganin kwar idon Suhaima ash color, tare da furta a uzubillahi, dayake musulmi ne,

Wannan ba mutun bane, ya faɗa cikin zaro ido _U are monster_ yafaɗi hakan tare da nuna Suhaima,

Mtsss ta furta a fili sannan tace zan nuna maka asalin sheɗan ci idan ƴar uwa ta tafarfaɗo,

Wasu security yayi wa magana daga can bakin gate ɗin asibitin, suka taho da gudu da alama shine shugaban su,

Kufita da wannan yanzu yanzu,

Ganin da gaske suke tunkaro ta yasa Suhaima ƙara runtse ido aƙaro na biyu,

Dr. Anisha Wadda harta buɗe murfin mota zata shiga sai kuma tafasa, taɗan fara tafiya zuwa inda securities ɗin suke, gashi tana hango wata sanye da niƙab ga kuma goyo abayan ta,

Cikin ɗan ɗaga murya Dr.Anisha tace lafiya Meye kuke anan,?

Dakata wa suka yi sannan cikin girmama wa suka ce - good afternoon ma_

Bata ko amsa suba ta ƙara cewa, nace Meye kukeyi anan,?

"Ma dama wannan ne ya shigo kuma anayi mishi magana yace wai yana son ganin doctor ne, kuma dagani ma bashida gaskiya aƙi buɗe fuska aganshi, cewar wannan security ɗin nafarko,

To kai kana ina har ta shigo baka gantaba naje toilet ne, dana fito shine naga shigar sa ta CCB camera shine nabiyo shi,

Bawar Allah lpy kuwa, Dr.Anisha ta tambaye ta,

Ɗan tsaki suhaima taja a zuciyar taci kaji rainin hankali fa ya za ai a tambayi wanda aka gani a asibiti wai lafiya,

Idon ta tabuɗe a hankali batare da ta dubi Dr.Anisha ba tace ƴar uwa tace bata da lpy nakawo ta tun jiya ta faɗi har yanzun bata farfaɗoba munje wani asibiti shine suka turo mu nan,

Meye yake damunta??

*Heart attack* yabata amsa a gajarce saboda tsabar gajiyar da tayi kamar ta kwantar da khaltum a ƙasa saboda bayan ta daya ƙage,

Subhanallah bari mu shiga ciki da dai na tashi aiki amma sai inhaɗaki dawani likitan,

Nagode kawai tace har yanzun bata ɗago sun haɗa idoba,

Hakan Dr.Anisha taji tana son temaƙon ta amma ba don hakaba ta gaji yau sosai fituwar su daga meeting kenan, sannan Kuma yarinyar ta karya dokar hospital ɗin, amma dai ita nata kawai ta temaka musu shine, saboda tasan Dr. Sulaim yana son temako itakuma tana son abunda yake so,

Waya taciro ta danna call cikin ƴan sakanni saiga wasu nurses guda uku 3 suna turo wani gado mai ban sha'awa, ba irin na wancan asibitin ba,

Ji suhaima tayi dama itama aɗakko mata gadon ayita tura ta harsai tayi bacci😂

Kama khaltum suka yi suka ɗora ta saman gadon sannan suka koma da hanzari suna tura gadon,.

Wash suhaima ta furta tare da ɗan banƙare wa kaɗan,

Kallon ta Dr.Anisha tayi taɗan saki murmushi sannan tace biyo ni ciki,

Tajuya suhaima tabi bayan ta, wata haɗaɗiyar glass door suka nufa irin mai 1/2 ɗin nan, dannawa Dr.Anisha tayi ƙofar ta zuge, ta tura kai ciki suhaima ma tabita,

Lumshe ido suhaima tayi saboda wani irin kamshi da sanyi da suka ratsata Tunda jijiya har bargon ta, bin ko ita take da kallo, aranta tace ashe ba komai taganiba a waje na irin tsaruwar da asibitin ke dashi, kallo nanan ciki ashe, wannan ai ko gurin shaƙatawa bai kaishi kyau ba ga wani ruwa fari tass dake gudana a tsakiyar gurin,

Dr. Tunda muka fito meeting nake dubaki harzama na ɗanyi a office ɗinki amma shiru shine na fito, ashe fita kikayi, Dr.jabir wanda suka yi kichiɓis da Dr.Anisha kenan yana kwararo mata bayani,

Eh na fita zanta fi gidane sai na haɗu da wannan ta kawo sister ɗin ta ba lafiya shine na dawo,

Kallon suhaima yayi sannan yace to baza ta iya cire abun fuskar taba ai karya dokan hospital ne wannan to koda face mask mutum yasa yana cirewa aganshi bare wannan baƙin abun,

Nima yi tunanin hakan amma yanzu pls Dr mu koma office ɗina don muji yadda za ai don gaskiya gida zantafi nidai,

Suhaima wadda tayi ƙasa da kanta tana jin komai da suke faɗa, burinta kawai Sufara duba lafiyar khaltum, akan cire niƙab kuma duk tasan yadda zata yi dasu,

Oky

Muje to juya wa yayi suka cigaba da tafiya itakuma suhaima ta cigaba da kalle kallan ta tana kallon nurses da masu jinya da suke ta zirga zirga jefi jefi, tare da ƙara yabawa shugaban hospital ɗin nan wanda tace yayi ƙoƙari ko aƙasar waje bu irin asibitin injita,



*DR. ANISHA C.E.O. OFFICE*

Aka daga saman office ɗin turawa tayi sannan suka shiga gaba ɗaya suhaima ma ce ƙarshan shiga, anan ma saida tayi kalle kallan don ita wannan kallon FADA Takeyi masa ba office ba,

Tana can ta ɗaga kai tana kallo taji murya Anisha, zaki iya zama Bismillah,

Zama tayi a ɗaya daga cikin kujerun dake gaban table ɗin, shima Dr. Jabir zaman yayi,

Yauwa zanyi magana dake ki cire abun fuskar ki,

"Cikin sanyin murya suhaima tace dan Allah kuyi hakuri kubarni da abuna a yadda kuka ganni wlh niban mai cutar wa bace idan ma haka kuke nufi,

Kallon kallo akashigayi tsakanin Anisha da Dr.jabir,

To yanzu yaki keso ayi mukuma doka ce baza mu duba mara lafiya ba matuƙar fuskarsa na arufe ko kuma tame jinya, idan aka ga fuskar ki zaki iya maida abunki, Dr.jabir ya kai karshen maganar tare da kallon ta,

Suhaima taƙara cewa kuyi hak'uri kuƙaleni Tunda ba dokar Allah kuka takaba, duka ce wanda mutum ya kafata, wanda shima ya kan ƙetare dokar ubangiji awani lokacin kuma ya nemi yafiya da gafa sai Allah ya yafe masa,

To nima ina ƙara haɗaku da girman Allah kuƙaleni da abuna kudaba lafiyar ƴar uwata,🙏

Jikin Anisha yayi sanyi sosai jin yadda ta kai ƙarshan maganar kamar zata yi kuka ahaka ma taga ƙarfin halin yarinyar,

Anisha tace To shikenan, yanzu zakije kibuɗe mata file, sannan zakije (cashier) kibiya duk wani kuɗi da kika gani an rubuta anan, za ai mata charkup ne, ko kitura ta account number ɗin dake jikin file ɗin zaki ganta, sai ki nunawa cashier transaction ɗin, sannan sai ki dawo dasu, nan sai a shiga duba ƴar uwar taki,

Tashin hankalin da ba asamishi date, suhaima ta shiga ganin wasu iyayen kuɗi da tagani rubuce jikin daya daga cikin takaddun da Dr.Anisha tabata, gashi wai ahaka ma wai banda magunguna,

Amma dayake ƙarfin hali gareta sai ta kasa gaya musu bata da wannan kuɗin kawai sai tamiƙe tare da cewa Dr.Anisha ai bansan duka guraran ba dazan je ba,

"Oky idan kika fita kiyi tambaya za anuna miki inda zaki buɗe file ɗin da sauran guraren,

Har ta kai bakin ƙofa sai tajiyo muryar Dr.jabir bakuzo da wani babba bane?

Eh" kawai tace batare da tajiyo ba, ta fice abunta cikin tsantsar tashin hankali, sannan ita fa har a lokacin bata bare sunga cikin idon taba saboda batason tambaya,

Amma bakya ganin yarinyar nan kamar bata da gaskiya? Naga fa ko cikin idon ta batason agani sannan kuma banga alamar tana da waɗan nan kuɗaɗan ba,

Eh to ba zamu iya gane komai akan taba yanzu, nidai kwai naji inason temaka mata ne, kuma sannan ma koda da cutar war ma tazo ai bata isa tayi mana komai ba sannan maganar kuɗi da bata dashi ai da zata faɗa mana ku taƙi tashi ko kuma kasani zata fita ta kawo ne?, koma dae Meye ina ruwan mu,

Eh haka ne kuma, Dr.jabir ya furta a hankali, zuciyar sa ce tafara zuga shi wajan cewa gadama tasamu, kafaɗa mata abunda ke cikin zuciyar ka,

"_No I can't_

Ai baza saurari niba a wannan yanayi gashi tagaji sosai,

Shikenan tabbas kuwa zaka yi biyu babu, ka tsaya jira,

Dr. Lafiya ina magana ka tafi dogon tunani",



Na fahimci fa tun ɗazun kamar bakada lpy _what's wrong_?

Allah yasa ba wani abu ke damun kaba kake boyen mun,

A a babu komai wai Meye kika ce?

Cewa nayi idan yarin yar nan bata dawo ba nan da 10 min zantafi gida saidai kaji da ita, ko kasa DR. Muhibbah ta kula da ita saboda naga tana night duty yau,

Ba matsala amma saidai kifaɗa mata kinsan bana son koda magana ne ta haɗa ni da ita,

_Omg look_ Dr.jabir Meye yasa kake son wulaƙan ta DR.muhibbah Meye laifin ta kawai don tana sonka shine kuskuran nata, kai dai bi a hankali baka san Meye so bane haryanzu idan Allah ya jarab ceka da son wata a time ɗin ne zaka gane abunda nake faɗama,

Hmm kawai yace mata,

Suhaima bayan fitar ta daga office ɗin tafiya take batare da sanin inda zata je ba, guri tasamu daga can nisa da mutane ta zauna,!

Tare da rab ka wani abun tagumi hannun biyu duka, ya rabb, kai ne mafi sanin komai, kaine maji ɓancin lamura, ni baiwar kace mai rauni, ina roƙon da da sunayenka tsarkaka siffofin ka ma ɗauka ka, ka kawo min mafuta Allah kabawa khaltum lafiya, da dukkannin wani mara lafiya,

Ace kawai yanzu kinrasa khaltum yazakiyi zuciyar tace taraya mata hakan,

Hak'uri zanyi mana ai Allah yafi ni son ta kuma dama shi Yabani ita, a fili tayi maganar wasu zafafan hawaye nabin kuncin ta wanda Tunda daga jiya har zuwa yau batayi koda kwallaba sai yanzu,

Suhaima kenan yarin yace amma me ɗauke da abubuwa na ban mamaki kala kala ga tawakkali, ga ƙarfafawa kanta gwaiwa Ako da yaushe bata taɓa sarewa game da wani abu da tatunkara ba, walau takar wannan abun ko kuma shi ya karta haka take bata taɓa sarewa,

Ji tayi andafa kafaɗar ta, ɗagowa tayi ahankali don ganin waye ya da fata, wata nurse ce sanye da uniform white complete,

Yauwa kizo ana kiran ki yanzu kubiyo baya na ɗan janye hannun ta nurse ɗin tayi tare daja baya tana ɗan zaro ido ganin irin kwayar idon suhaima, sai kuma ta ɗan ke idon ta tajiyo kubiyo ni, amma fa maganar gaskiya taji tsoro don ba yadda zata yi ne,

Tashi suhaima tayi jiki babu kwari kuma ba musu tabi bayan wannan nurse ɗin suka cigaba da tafiya tun suhaima na saran sun kusa har ta fidda rai, gani tayi sun nufi saman bene, gani tayi stairs ɗin da suka takai bai wuce goma ba, saiga su abakin wani ɗaki, daga sama an rubuta *(THEATER ROOM 7)* tura ƙofar nurse tayi sannan tace shiga ko, ba musu suhaima tashi duk da babu wani wada taccen haske aciki amma ko ɗar bata ji ba azuciyar ta,

Tana shiga kwafar ta koma ta rufe, tsaye suhaima tayi tana kalle kalle ko ina tsaf tsaf ga wani sanyi mai ratsa zuciya mai daɗi yana shigar ta, sai taji ma kamar ta kwanta a gurin don suhaima bai dai son sanyi ba sanyin ma irin na A.C,

"suhaima

Ji tayi ankira sunan ta ahankai, waiwaye ta fara yi don ganin wace wannan take kiran ta, amma tasan ko a bacci taji wannan muryar zata shaidata, cikin ɗan ɗaga murya itama, tace, "khaltum,Tabbas wannan muryar khaltum ɗin tace.

*Share and like*

*Beside on creative life story*

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

*AHALIN MU DAYA*

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

_______Dedicated to anty salma💎

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚

_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

*Page* 2️⃣3️⃣▶️2️⃣4️⃣📖

"Suhaima"

Ji tayi ankira sunan ta a hankali, waiwaye ta fara yi don ganin wacece wannan take kiran ta, amma tasan ko a bacci taji wannan muryar zata shaida ta, cikin ɗan ɗaga murya itama, tace, " khaltum, Tabbas wannan muryar khaltum ɗin tace,

Eh nice fa kinganni anan, a iya sanin khaltum tasan suhaima tafi gani acikin duhu, duhun ma sosai, amma Meye yasa yanzu bata gantaba, hannu takai kan irin moonlight ta gefan bed, ta danna ma dannin dake ajiki, take haske ya bayyana ɗakin ya ƙara haske yadda mutum zai iya ganin komai,

Mamaki, al'ajabi, kullewar kai, farin ciki, gaba ɗaya suka lulluɓe suhaima, wadda take a tsaye kyam tana fuskantar gadon marasa lafiya da khaltum take zaune a tsakiyar sa abunta hannun ta ruƙe da ayaba (banana) tana ci tana yiwa suhaima wani Ƙaya taccen murmushi,

"Karo na farko da tunzuwan su cikin garin Kano fuskantar khaltum tazama abuɗe, al'wala da wanka ne kawai suke sasu buɗe fuskokin su saboda kada agansu, al'walar ma a toilet suke ɗauro ta,"

Khaltum fara ce amma ba irin can ba, mai yalwatacciyar, gashin gira, dogon hancin ta harba ka, ida nuwanta ma kai ɗai abun kallo ne, wani irin shape gare su mai jan hankali, ga ɗan ma dai dai cin bakin ta, wanda take motsa shi a hankali tana cin ayaba, masha Allah, irin ƙana nan kyau ne da khaltum, wanda, idan kana nesa da ita baza ka gane kyan ta yake har haka ba, doguwa ce amma daya ke tana da ƴar ƙiba ƙadan, sai tsayen yaɗan shige,

Kwaɓe fuska tayi, kamar zata yi kuka, tana kallon suhaima wadda ke atsaye, bata da niyyar motsawa gaba ko baya, buɗewa suhaima hannu tayi alamun tataho,

Ba musu suhaima tafara tafiya a hankali, kamar mai tsoron za a kamata, rungume juna sukai sosai suhaima ta rungume ta har saida khaltum tace, "wash" ciwo na, janye jiki suhaima tayi sannan tace sannu aiki akayi miki ne,?



Hannu suhaima khaltum ta kamo, sannan ta kalle ta sosai, tafara magana,

"haƙiƙa ke tada bance acikin muta ne, sannan ke ta mu samman ce aciki ƴan uwa, da ace ko wanne mutum yana da ɗan uwa ko ƴar uwa irin ki da ya ji ɗaɗi, ke ɗin ɗaya ce acikin dubu, irin ki ɗaya ake samu acikin ko wane ƙarni, to a wannan ƙarnin kece tauraruwar,

Murmushi suhaima tayi mai sauti, hannun ta ɗaya ta janye daga cikin na khaltum , ta ɗan ja hancin khaltum ɗin tare da furta kingan ki ko, baki ji

murmushi itama khaltum ɗin tayi tare da faɗin Allah gaskiya ai na faɗa, ni banida wata sauran kalma, wajan yi miki godiya, amma bazan gushe ba ina yi miki addu'ar Allah ya biya miki buƙa tunki na alkhairi, sannan Allah yaba mu nasara akan FANSAR MU, Allah yabaki miji wanda zai kula dake fiye da kansa, mai kyawun zuciya da na fuska, fiye da ke, sai kuma ta tayi shiru ganin suhaima tayi ƙasa da kanta, shikenan nabari iya abun da khaltum kawai ta furta kenan,

Khaltum Tunsan da na shigo ɗakin nan, idanuwa na suka yi tozali dake, amma zuciya ta taƙi gamsuwa dake ɗin ce kuwa, anya? Har sanda kika kira sunana ina kokwanto akan ke ɗince ko baƙe bace, ke kuma kinyi tunanin bana ganinki ne shiyasa kika kunna haske to ba haka bane, zallar mamaki ne ya rufeni,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login