Showing 24001 words to 27000 words out of 61789 words

Chapter 9 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

182



Mamaki kuma? Ta tambaya

Eh saboda kamar yadda kika ganki ahaka kin farfaɗo, to bansan komai akan hakan ba, nidai abunda nasani shine kawai na kawo ki wannan asibitin, aka ɗauke ki tun daga harabar asibitin, daga nan bansan inda akayi da keba, likitan da tasa aka karɓe kice, ta ce nabi bayan ta,

"ciki da sa rai nabi bayanta nata domin gani nake muna shiga zasu dubaki, na maman ta da ana maganar kuɗi gashi private hospital Ne, ni bata wannan nake bama kawai kisa mu lafiya shine agaba ne, muka je office ɗinta, suhaima ta kwashe komai tafaɗawa khaltum, hadda labarin wancan asibitin da abunda securities ɗin nan suka yi mata,

Taciga ba da magana, ina zaune ne cikin rashin sarewa da tunanin inda zan samo kuɗin nan zuwa dare, a duba lafiyar ki, nafara tunanin ko inje wajan wannan matar ta gidan da muka sauka, ko zansamu aro, daga baya zanyi aiki tuƙuro nabiyata, ita kaɗai ce wadda muka sani anan, bani da wani fata ko buri, da yawuce ganin tashin ki, sai kwatsam wannan nurse ɗin tayi min magana tace inzo ana kira na,

Khaltum kinsan duk tsananin tashin hankali baya sakani, hawaye bare ma kuka, to amma yau rashin wani akusa da mu, da kuma kaɗai ce yasa kani kuka, khaltum babu godiya atsakanin mu, kece ni nice ke, sanin kanki ne Bamu da kowa sai junan mu, sai mother, Allah Kuma shine gatan mu kuma shine fatan mu, a duk sanda na rasa kwarin gwaiwa, Allah shine fatana, yanzu tunani na ɗaya ne waye ya duba kuma acikin ɗan ƙaramin lokacin nan, da zuwan mu asibitin nan da yi miki aikin ai ba afi awa ɗaya da rabi ba,

Khaltum wadda hawaye suke ta sintiri a fuskar ta Tunda suhaima tafara magana, tace wlh suhaima babu kamar ki, idan ma akwai to za a sha wahalar gaske kafin asamu,

Sannan nima gani nayi kawai na farfaɗo acikin wannan ɗakin sannan saitin zuciya ta yana min zafi, ana cikin haka ne, wannan nurse ɗin data zo dake, ta kawo min wannan tea mai kauri nasha, sannan ta koma ta kawomin wannan tire ɗin kayan marmarin da kike gani, kallon gurin da tire ɗin kayan marmarin yake suhaima tayi tare da ɗaga kai alamar eh tagani, to amma yanzu idan suka ce mu biya su fa ya zamuyi?

Sai ki zauna anan nikuma naje na nemo na biya su, cewar suhaima

To ina zaki sa mesu? Don daki kaɓi aron kuɗi agurin wannan matar gara na mutu don bana sonta (hajiya fanteka)

Hhmm kawai suhaima tace don, gani take tsanar datakeyiwa hajiya fanteka ko kwatanta khaltum batayi mata ita da bata san komai akan fanteka ɗin ba,

Da sallama aka turo ɗakin da suke ciki, amsawa suka yi tare da kai kallon su bakin ƙofar, wata nurse ɗin ce hannun ta riƙe da wani tire ɗin magunguna ne aciki, ƙarasuwa tayi tare da yiwa khaltum ɗin sannu,

Sannan ta bata magungunan da zata sha,

Ta kalli suhaima tace ki kuma kibiyo ni

Tashi suhaima tayi khaltum ta ruƙe mata hannu gam, kallon ta suhaima tayi girgiza mata kai khaltum ɗin tayi alamun kada ta tafi,

Janye wa tayi, tace yanzun zandawo kada kidamu,

Tabi bayan nurse ɗin suka fice, kamar khaltum tabi bayan su haka take ji to amma bata jin ma zata iya tashi ji take kamar ankashe mata jiki, ga ciwo datakeji asaitin zuciyar ta,

_______________________

_________________

____________

*Back to Arab Estate*

Sannu yaro na da alama yau kagaji sosai, cewar uncle Bello dake zaune yana kallon sulaim a parlon baffa, to ya aikin? ya tambayi sulaim ɗin,

Alhamdulillahi daddy sulaim Wanda ke zaune kusa da baffa ya amsa gabansa kuma laptop ce saman wani ɗan ƙaramin kushin mai tudu an rubuta _Hp_ a bayan computer ɗin, da alama aiki yake yi,

Kallon daddyn Canada baffa yayi kafin yace wai Bello baza ka bamu guri bane,

Ƴar dariya uncle Bello yayi kafin yace to baffa ai mu mundawo nan koro mu fa suka yi,

A a Bello koro shi dai kuka yi ai hadda kai Tunda kana kallo agaban ka suka kore shi, daga Part ɗin su, yanzu kuma shine zaka biyo shi, ai bazai koma ba ya dawo kenan dama anan ɗin yake tun farko, cikin wasa baffa yake maganar don dama shi mutum ne mai wasa da ƴan ƴan shi da kuma jikokin sa, idan suna hira da yaransa sai ka rantse ma abokai ne, amma shi mutum ne mai magana ɗaya ga dattaku, bai kuma yadda ƙarami ya raina na sama dashiba, acikin iyalan sa,

To shikenan baffa yanzu dai zantafi ɗin Tunda kora ta kukeyi amma ataya mu bawa ɗan nawa hak'uri ya dawo,

A sauka lafiya cewar baffa dayake kallon sulaim ɗin don ganin abunda zai yi,

Tashi sulaim yayi ya ɗan matsa kusa da dadin, baffa yayi tunanin binsa zai yi sai kuma yaji yace,

" Allah yabamu alkhairi daddy" nayi missing mommy sosai, zanzo mu gaisa anjima,

Kamar mai ciwon baki yayi maganar,

Murmushi daddyn yayi aransa yana mamakin hali irin na sulaim tabbas idan da lalura to akwai hali, ma wato da gaske sulaim fushi yayi kenan sai sunzo biko,

Ɗan rungume shi daddyn yayi ta gefe sannan yace to yaron kirki sai kazo idan ma bakazo ba muza muzo ai,

Komawa sulaim yayi ya zauna inda ya tashi batare da yace komai ba, shima daddyn kusa da baffa ya matsa yaɗan russuna sannan yace, a huta lafiya baffa,

Jinjina kai kawai baffan yayi sannan shikuma ya fita,

Shiko sulaim wani daɗi yake ji, aransa bayan lokaci mai tsayi, da cire tsammani, amma gashi a yau yayi wa wata aiki kuma cikin nasara da iKon Allah ta tashi ta farfaɗo, ahankali ya furta alhamdulillahi,

Baffa yace sulaim naga kamar kana murmushi,

kallon baffa sulaim yayi, sannan yace, "eh amma Bakomai" ya so faɗawa baffa abun da ya faru sai kuma yaji bakin sa yayi nauyi ya kasa, amma tabbas yasan da ya faɗa masa da baƙaramar murna baffa zaiyiba,

Murmushi kawai baffa yayi, batare da shima yace komai ba,

______________________

Mama bilki ce zaune aka tafaran perlon ta, ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya, lace ne a jikin ta mai tsadar gaske launin sky blue anyi masa kwalliyar stone, sai ɗaukar ido yake, sai babbar ƴar ta mace wato jamila, dake zaune a kujerar kusa da ita, sai uncle Mansur dake fuskantar su, cikin fusata tafara magana,

"Haba Haba na gaji da wannan al'amarin da yaƙici yaƙi cinye wa, Tunda na shigo gidan alhaji imran arab, nake fama da uwar gidan sa, da ƴa ƴan ta ace kullum sune agaba acikin gidan nan, yanzu gashi jinkan tama yana nema yazamar min ciwon ido,

To wlh da sake da sake fa bazaiyiwu ba, dole asan abunyi, yanzu nayi waya da, boka zarshima, yana sanar min wai yaron nan da muka daɗe muna aiki akan sa ace, yau yayi wa wata aiki, kunga kenan akwai alamun aiki yafara war ware wa, kuma sannan ya tabbatar min da cewa ya samu kwarin gwaiwa da nasara ne daga ƴar uwar wadda yayi wa aikin, sannan Yace min tabbas yarinyar tananan kuma zata tun karo gidan nan, idan kuma har hakan ta faru to babu ko shakka komai namu zaizo ƙarshe, to nikuma bazan taɓa barin hakan ya faru ba koda ace zanyi yawo tsirara ne to bazan bari iyalai na su wulaƙan taba,

Ai wlh mama lefin kine nace miki akwai wani boka da nasani, aikin shi kamar yankan wuƙa haka yake, kamata yayi mu maida aikin komai gurin shi, da tuni yanzu wata maganar ake bawannan ba aƙasar India yake , cewar jamila wadda tazo gidan a daran jiya saboda, taji labarin saleem ya mari ɗiyar ɗan uwan ta, he excellency Sambo, tana jin labari ya biyo jirgin dare daga Abuja, don zuwa ɗaukar mataki,

Kallon su uncle mansur yayi cikin, matsanancin ɓacin rai ya soma magana wanda saboda tsabar masifa, har shaƙe wa yake wajan cewa, kowa ce wannan yarinyar daza tazamar mana barazana dole ne mudakatar da shigowar cikin ahalin mu,

Kallon shi mama bilki tayi, abunda ya kamata mu fara yi kenan, tun kafin wankin hula yakaimu mu dare,

____________________

Yauwa mommyn yara dama inaso muyi magana, ne cewar ummeetha dake zaune kan super,

To inajinki cewar mommyn,

Dama sonake kafin saleem ya wuce Lagos mu shirya zuwa *MASARAUTAR GABAS*.

*Share and like fisabilillah*🙏

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

*AHALIN MU DAYA*

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

*NAZARI WRITER'S ASSOCIATION*📚

_Sarauniyar👸Nazari writer's association_

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 2️⃣5⃣▶️2️⃣6⃣📖

Dama so nake kafin saleem ya wuce Lagos mu shirya zuwa *MASARAUTAR GABAS*

Eh gaskiya kam ya kamata saboda tun wancan zuwan namu Nigeria🇳🇬 ba wanda ya wuce ba Bamu ƙara zuwa ba, kuma ya kama ta aje a gaida baba Waziri, cewar mommy tana ɗan murmushi,

Sai afaɗawa yaran su fara shiri ko, koya zamuyi da sulaim gashi da yayi mana yaji da gaske,

Murmushi ummeetha tayi, to kuma dai kunga halin ɗan naku ko, dama fa can yana da tsarin komawa Part ɗin baffa, to shine yanzu kawai Yakoma, kuma ko da yana wannan Part ɗin ai ba ganin shi aikeba sai Anne meshi, Sannan DUK sanda ya bushi iska saidai muji labarin yana MASARAUTAR GABAS Din,

Au ashe ma yana zuwa? Mommy ta tambaya

Eh yana zuwa sosai don mayanzu yaɗan rage zuwa Tunda wani couse ya kai *YARIMAN GABAS* Korea 🇰🇷 kusan 1year kenan, to ya ɗan rage zuwa,

Hhm to shekenan, naji ansanar da taron gaggawa anjima idan muka je nidai zanyo bikon kalbiy na,

Suhailat ce ta sakko daga upstairs, cikin shiga mai kyau ta alfarma, material yard ne ajikin ta ɗan uban su wadda ko na faɗa maka ba kasan ba irin nayaku bayi bane, coffee colour anyi masa ɗinkin A shape mai kwala a wuya, abunka da dogon mutum gata fara, sai yadin material ɗin ya haska ta sosai, tayi yafa mayafi brown color Mai haske, ƙafar ta na sanye da plate shoe shima brown colour, tayin kyau sosai,

Ƙarasa wa tayi gurin da su mommy da ummeetha suke a zaune, tace mommy barkan ku da gida,

Barka dai daughter har kunshirya kenan,! "eh mommy"

Ummeetha tace to ina saleema? "nayi zaton ta tafi ai, cewar Suhailat,

Kafin ummeetha tace wani abu saiga, saleema itama tana sakkowa cikin salo da yanga, riga da wando ne ajikin ta irin American dress ɗin nan, rigar tata har gwaiwa red colour sai Wasu manya yanyan bottle golden colour da akayi adon rigar da su guda uku, wandon ma golden ne, ta ɗan buɗe daga ƙasa kamar flazo, hannun ta riƙe da jaka irin pos ɗin nan itama black taji stone, GA wani uban glass data saka yacin ye rabin fuskar ta, mayafin tana ɗa akan ta kamar rawani ahaka ta fito, sai tashin ƙamshi takeyi dama bikin ɗiyar uncle ɗin su saleema akeyi yayan mommy uncle tahir to yau suka fara bikin shine zasu yi gaba kafin zuwan su mommyn ita kuma suhailat amaryar friend ɗin tace tare suka yi North West kano , tsaya wa tayi itama a gurin su mommy sannan tace, ummeetha mommy na wuce,

Saikin a dawo lafiya, ummeetha tace mata tare da ɗaga mata hannu alamar bye bye,

Har tafara tafiya mommy ta kalle Suhailat tace to Tunda kunfito tare, driver yakaiku mana,

"No mommy zantafi nida yaya sulaim ne zanje part ɗin grandad ɗin Yanzu sai mutafi tare, kallon Suhailat tayi kafin ta ce," _u can go if you want_"

Mai makon abun yabawa Suhailat haushi sai ma tayi murmushi sannan tace _Don't worry about it saleema till we meet there_ aranta Kuma tace Allah sarki ashe babu rabon yau kije bikin nan Indai yaya sulaim ne zai kai ki,

Atare suka yi hanyar fita daga perlon, ummeetha aranta tana addu'ar Allah ya shirya musu zuri'a atako, mommy da alama hakan ko a jikin ta, don su agurin su hakan Bakomai bane,

Parking space suka nufa tunkafin suƙarasa, saleem dake zaune acikin mota yana jiran futuwar suhailat, tada motar yayi sannan yayi parking a dai dai gaban Suhailat, aiko ta tsaya kafin tayi wani motsi har yafito yabuɗe mata ɗayan ɓangaran, kallon shi Suhailat ɗin tayi da murmushi a kan fuskar ta tace,

"wlh yaya saleem idan kanamin irin wannan abun duk sai narin ƙajin kunya, so kake ace kazama driver ɗina ko," to wlh babu ruwa idan budurwar ka taji labari, takai ƙarshen maganar tare da shige wa cikin motar,

Shima dariya yayi kawai yaza gaya Yakoma driver site, yazauna suka fice daga house din ya hau titin hameed Arab way,

Saleema ma mota ta shiga ta nufi Part ɗin kakan nunsu gurin sulaim,

KO sallama babu haka saleema ta shiga perlon baffa, babu kowa a perlon, sai dadda ɗan hayaƙin turaran wutar dayake, daga cikin boner, ƙara ɗan shiga ciki saleema tayi, still babu kowa aciki, waige waige tafara, saiga hajiya umma kakar su ta fito daga wani corridor, wanda ke ɗauke da hanya ta cikin sa, ƙofar baya kenan, wadda ke sada ka da sauran Part matan alhaji imran ɗin sai kuma na sulaim dake aciki dama part 4 ne, itama hajiya umman daga nata part ɗin take,

Ke kuma Meye kike kallo ina ta sallama, amma kina can kina kallo,

Da sauri saleema tajiyo da alama har tsoro ma taji,

Cikin kwaɓe fuska da cono baki, tace Haba grandma, ni Allah kinbani tsoro, gaskiya,

Eh lallai to maza zoki fita kinsa wani glass yacike fuska kamar ma kauniya, hajiya umma bata fiye wasa da jikokin taba amma tana sakar musu fuska lokaci zuwa lokaci, kika ɗayane, yake yin abunda yake so agaban hajiya umma, amma bata tsawatar masa ba, sulaim,

Oh god, saleema ta faɗa tare da dafe goshi, to aidama ku Baku san kyau ba, yanzu nifa ba wannan ne yakawo niba, pls ina yaya sulaim,?

Yana inda kika ajiye shi Tunda ajiyar sa kika bani, Tunda biki iya gaisuwa ba sai tambaya,

"_Oh sorry um forgot_

_good afternoon_" _and u tell me about yaya sulaim pls_" hada dan kama kunne tayi alamar ban hak'uri,

Wani irin kallo hajiya umma tayi mata wanda yasa saleema saurin cewa, barka da yamma, yanzu fadamin yana ina,?

Ke wlh kifata idona Tunda biki ban ajiyar saba, Tunda baya nan ba sai ki wuce Part ɗin saba,

Ai tunka fin hajiya umma ta kai ƙarshe tuni saleema ta juya da sauri ta nufi Part ɗin sulaim ɗin don ita tama manta dayana da part acikin house ɗin,

Girgiza kai kawai hajiya umma tayi, ta nufi bedroom ɗin baffa don tasan yanzu ya shiga ciki don shirin tafiya masallaci wadda ke acikin estate ɗin donmin ankusa sallar magrib,

Zaune sulaim yake atsakanin kujerun parlon daga ƙasa saman carpet, Don yana son zaman ƙasa a wasu lokutan haka kawai, waya yake yi, hankalin sa gaba ɗaya ya tattara akan wayar,

"DR. Muhibba kitabbata kafin kibar asibitin nan komai da suke buƙata anyi musu, bama kamar ita....

Ganin mutun kawai yayi hakan yasa bai ƙarasa faɗar abunda zai ceba, _Dr I will call you later_" ajiye wayar yayi yana kallon saleema da mamaki, ta shigo masa babu sallama sannan kuma har upstairs batare da neman izini ba, wai ita wannan Yarin yar Meye matsala ta da ita ne tana son shiga rayuwa ta nabaro musu house ɗin su amma sai wani bibiyata sukeyi, a zuciyar sa yayi maganar, ɗauke idon sa yayi daga kanta Yamai da dubansa kan screen ɗin wayar sa yana dannawa,

Ƙaraso wa saleema tayi ta samu guri daga ɗan kusa dashi da zauna daga ƙasan inda yake, yaya sulaim barka da hutawa,

"barka" don ta kalle shiba dabatan abunda yafurta ba saboda motsin bakin sa kwai tagani bawai taji abunda yaceba,

Ya saleem pls so ne dama kara kani gurin wani lady's night, bikin cousin ɗin mu aka fara yau shine nake so muje ta....

Kallon da sulaim ya watsa mata ne yasa ta killace sauran maganar ta data ɗaukko,

Tashi yayi ya nufi bedroom, kallon shi saleema tayi wani sa shin na zuciyar ta yace tabbas idan kika barshi ya shiga ciki to kinyiwa kanki,

Da sauri ta tashi tashaga bansa, da Allah yayana idan ma baza kayi driving ɗin ba ni sai inyi mana, ko kuma driver ya kaimu, glass ɗin fuskar ta tacire tuni hawaye sunfara sintiri a fuskar tata,

Dafe kai sulaim a hankali ya furta ya rbb, baya son hayaniya, baya son abunda zai dameshi, baison kuka kwatakwata, bare ma ga mace, kallon ta yayi sai kuma yaji tausayin ta yakamashi gashi dama tun jiya take kiran shi tayi mishi miss call kusan 25 amma bai ɗaga ba ƙarshe ma sai ya kashe wayar baki ɗaya, "zanje masallaci idan na fito sai muje" kamar mai yin raɗa yayi maganar, tare da raɓawa yawuce don yin alwala,

Wani irin tsalle saleema tayi, jin maganar tashi tayi kamar a mafarki bata taɓa tsammanin hakan daga gareshiba cikin sauƙi,

Hmm yauzan shiga da yaya sulaim cikin family friend ɗin mu sai sun raina kansu da boys friends ɗin su, kuma wa tayi ta zauna tare da ciro wayar ta, tace bari ma inkira malika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login