Showing 48001 words to 51000 words out of 61789 words

Chapter 17 - Ahalinmu Daya Book One Complete Book One Complete Hausa Novel

Fauzah   

04 Nov 2025

187

da cewa ba komai kasha kai kaɗai Tunda kai akeso,

Kafin sulaim yace komai sultan din yaɗora da cewa,

Yauwa na gaya maka akwai taro gobe insha Allah za a kawo kayan hawa hadda naka nasa a kawo pls aminina kada kace baza kasa kaba, dayau za ayi taron hawan sai nace Abarshi zuwa gobe saboda kai,

Sulaim wanda yake sauraran Sultan babu abunda ya ce masa kawai ya jisa ne,

*WASHE GARI* 🌅

Wai Meye yake faruwa a masarautar nan ne nake tajin haya niya,

Wata budurwa ce ta tambayi ta kusa da ita itama bazata haura shekarun ɗayar ba,

Lallai ma SIYAMA bakiji sanar warda ake tayi ba tunjiya cewar akwai taron murnar dawowar Yarima Sultan sannan kuma shima kanshi zaiyi Hawa na musamman,

Zunbur wadda aka kira da da suna Siyama ta tashi zaune tare da Faɗin dan Allah da gaske ne ZARAH kinsan dayake jiya ban kwana a nan ba shiyasa banjiba,

Gaskiya Zarah zo kitaya ni duba kayan da zansa order yanzu akawomin fitattatu don bazan yadda wannan GIMBIYAR SHAHEEDAN ta fini kyau ba wlh,

Kinsanta badai iyayi ba kuma nasan kodan YARIMA dole zataje gurin Hawan da zaiyi..!

Share

And

Like fisabilillah 🙏

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

💗💗💗

*Nazari writer's association📚✍️*

_Sarauniyar nazari writer's👸_

*(THE QUEEN👑)*

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 4️⃣3⃣↔️4️⃣4⃣📖

Gaskiya zarah zo kitaya ni duba kayan da zansa order yanzu

Saboda fitattun kaya nakeso dan bazan yadda wannan Gimbiya shaheedan tafini kyau ba wlh,

Kinsan ta badai iyayi ba kuma nasan kodan Yarima dole zataje gurin hawan da zaiyi,

Tana maganar tare da janyo wayar ta ta shiga duba wasu Gowns with veils a media duk wanda ta duba sai tace baiyi mata maba

Laaa zarah matso kiga wata riga tayi kyau gashi veil ɗinta babba ne da sauri wadda akakira da zarah ta matso ta kalli screen din wayar don ganin rigar,

Dariya sosai zarah ta shiga yi kamar wata zautacciya kallon ta siyama tayi tare da fadin Haba zarah kefa baki da kirki Meye kike wa dariya haka,

Saida zarah ta tayi mai isar ta kafin ta ce yanzu ke siyama sai kace biki waye ba yaza ai kice zaki sa MOROCCO 🇲🇦Gown saikace zakije walima gashi veil din ta yayi Miki girma yanda kike hakan nan ba kida tsayi sosai,

Harara siyama tabi zarah dashi tare da fadin kinga naji yanzu Meye shawarar ki,

Yauwa yanzu kikai magana cewar zarah tana gyara zama a saman bed din da suke duk a zaune,

Siyama kinsan yadin karan miski a gidan sarauta baƙaramin tufafi bane mai dara ja ina ganin idan har kikayi shigar sa baƙaramin kyau zakiyi ba yanda kike chocolate colour din nan Idan kikasa kalar haske zakiyi kyau sosai,

Wata kuyanga ce ta yi sallama daga bakin ƙofar bedroom din da suke ciki,

Zarah ce ta amsa tare da fadin za'a iya shigowa

Russuna wa tayi tare da fadin barkan ku da safiya, still Zarah ce ta ƙara amsawa tare da fadin me ke tafi dake?

Uwar da kina Fulanin sarki ita tace a sanar muku tana son ganin ku yanzu a parlourn ta,

To muna tafe yanzu

Tashi sukai ko wacce ta saka doguwar rigar abaya suna yane kansu da viel din rigar suka fice,

Zama Zarah da Siyama sukai a kusa da ita tare da fadin ranki ya daɗi mun amsa kira gamu,

Kallon su Fulani tayi tana zaune ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya jikin ta sanye da atamfa ɗinki doguwar riga tasha aiki da stone tundaga sama har ƙasa sai alkyabba asama,

Magana tafara yi musu cikin isa da ƙasaita kalma bayan kalma haka ta shiga yi musu magana, kunsan da taro a masarautar nan amma shine kuke kwance a ɗaki har wannan lokacin kuke nan baza ku shirya komai ba ke Siyama har kiran wayar kinayi bata shiga saboda inaso kuzo ku zabi kayan da zakusa,

Saboda akwai manya manyan baki da ƴaƴan sarakuna wanda duk zasu halarci wannan taron ina so sosai Siyama kija hankalin Sultan a gurin akwai kyau tuttukan dana ta nada wanda zaki bashi yayin gabatar da kyauta,

Murmushi sosai Siyama tayi tare da fadin muna godiya ummu Allah ya ƙara lafiya Allah yasa YARIMA SAFWAN shine magajin masarautar nan,

Wani irin daɗi mara misaltuwa Fulani tajiba saboda wannan shine babban burin ta arayuwa naganin babban dan ta wato SAFWAN yazama magajin baban sa sarki Yusuf shareef,

Sai da ta lumshe ido kafin ta amsa da ameen,

Sannan ta ɗan kai dubanta kan Zarah wadda take jira taji ita wane tanadi akayi mata,

Amma ga mamaki zarah taji Fulani tace kuntashi kuje za a kawo muku komai,

Babu musu suka tashi tare da fadin ki huta lafiya,

*FULANIN SARKI WADDA SUKE KIRA DA UMMU SAFWAN*

Ita ce matar sarki ta biyu kuma amarya tana da ƴaƴa guda ɗaya ta rasu dama ita kadai ce mace kuma ta fari sai maza biyu da suka rage Safwan, sai dan uwansa Al'amin suna kiranshi da AMIN,

Siyama da zarah ƴaƴan yayyin tane ta ɗakko su ruƙo, bata da wani bure da yawuce Ganin bayan YARIMA SULTAN Saboda an tabbatar mata idan har yana raye to ɗan ta YARIMA SAFWAN bazai taba gadon sarautar mahaifin saba,

Shine dalilin da yasa take ta neman hanyar da zata gabayan Sultan din ta rasa anbata tabbacin baza a iya kashe shiba saidai ta dalilin matar sa, Sai takeso ta hada Siyama ƴar yayar ta da taɗakko ruƙo da yarima Sultan don cikar mafarkin ta,

Cikin kyakkyawar shiga ta shadda light blue suka fito cikin shirin zuwa fada dan gaisa wa da mai martaba,

Yarima sultan ya dai dai ta zaman Jabbar dake jikinshi fara mai adon ruwan zaiba sai walwali yake a saman kayan nashi kamar jiya sunyi kyau sosai fadawa ne sunkai takwas abayan su domin rakiya zuwa fada,

Fuskar nan ta Sulaim ɗaure tamau tamkar shine Yariman tun kafin su ƙarasa aka sanar wa da sarki zuwan Yarima Sultan magajin karaga,

Sanda suka isa har anfito zaman fada duk wani mai ruƙe da muƙami yana zaune aciki kama daga kan Waziri, Galadima, Hakimi, Liman, da sauran masu karaga,

Kai tsaye suka nufi wajan da mai martaba yake zaune kan karagar sa ta mulki fadawan yarima Sultan ne suka farayi mishi kirare da kambamawa ahankali suka rage tsaye tare da russunawa cikin tsananin Girmamawa,

Sarki yayi murmushi yana amsa gaisuwar da suke yi mishi tare da miƙawa Sulaim hannu alamar suyi musabaha,

Sosai Sulaim ya ƙara yin ƙasa da kanshi cikin girmamawa batare da yamiƙa hannun ba fadawa ne suka amsa da cewa Sarki ya gaishe da ɓaƙon masarautar Gabas kuma amini ga sarkin gobe Yarima sultan ZAKI Dan sarki jikan sarki,

Miƙawa Yarima sultan hannu sarki yayi alamar su gaisa,

Take Yarima sultan ya cire hular kanshi don ne man albarkar mai martaba kamar yadda suka saba duk sanda yazo haka ce take faruwa,

Fadawan sarki ne suka ƙara fadin sarki ya gaishe da sarkin wata rana a masarautar GABAS, Sarki ya amshi gaisuwar Yarima Sultan,

Mai martaba ya kalli muskar Sulaim tare da jin daɗin yadda yaga tsananin girmamawa daga yaron hakan ya burgeshi duk da ba yau yasan Sulaim din ba amma shi komai yaron yayi yana masa daɗi a rai duk da mulki baya bari ya bayyana,

Duka hannuwan sa biyun yasa tare da ɗago da su daga duƙushan da suke tare da yi musu alamar su zauna zama sukai sosai sai a lokacin yarima ya maida hular kanshi tare da daidai ta zaman ta akan nashi,

Saida suka zauna sosai sannan Sulaim yafara magana,

Baffa yana gaishe ka, yace a miƙo sakon bangirma ga zakin sarki da samun kamar sa sai an tona,

Kamar yadda baffan yabashi sakon haka yakawo shi bai rage komai ba aciki,

Murmushin girma sarki yayi dayake yasan baffa sosai abokin shine duk da baffan ya girmeshi, kasancewar babu wanda yaji abunda Sulaim yace hakan yasa babu ba Fadan da ya tofa albarkacin bakin shi bare su ari bakin sarki suci masa albasa,

Nagode sosai Aminin Sultan, kafaɗawa alhaji Imran Arab sarki ya amsa kuma yana miƙo gaisuwa ga dattijon arziƙi,

Take sarki ya basu umarnin Gaisawa da sauran mutanan fada

Gaisawa yarima Sultan yayi da su cikin girma mawa saboda duk manyane akan shi,

Shima Sulaim haka amma duka sauran ƴaƴan sarkin miƙa musu hannu yayi suka gaisa hakan baƙaramin ɓata musu rai yayi ba bama kamar Yarima Safwan yaji baƙin cikin ganin mai martaba ya sakar wa Sulaim fuska har suka yi magana,

Sannan shi Indai kai ba ɗan mulki bane baka isa yamiƙa maka hannu ba amma gashi yau yayi da Sulaim cikin ƙunar rai ya tashi ya bar Fada batare da mai maitaba ya kula ba,

Bayan sungama Gaisawa da kowa Yarima Sultan ya matsa kuwa da sarki sosai tare da fadin

Allah yaqara Maka yawan nasara muza mukoma

Allah ya albarkaci rayuwar ku zaku iya tafiya,

Munbarku lafiya baba cewar Sulaim tunkafin ya tashi ,

Fadawan Sultan ne suka rufa musu baya Suka nufi Layi Sashen UMMUL BAIT tare da sheda mata isowar su ummeethar,

Bayan sun gaisa Yarima Sultan yasanar mata da isowar tasu tare da sheda mata har antafi airport dakko su,

Sosai taji Dadi tasan ko badon da wowar Dan ta suka zoba Amma dai sun zo din Hakan baqaramin Dadi yayi mata ba,

Umarnin zuwa gaida Fulanin sarki UMMUL BAIT taba su Dan tasan Indai bahakan tayiba Sultan bazai taba cewa suje can din ba,

Aiko Hakan ce takasan ce badon Yarima yaso ba haka ya amsa mata da to cike da tsantsar girmamawa saboda Basu San meye musu da gardama ba biyayya kawai su tashi sukaga anayi ga na gaba dakai,

Suntashi da niyar tafiya saga qannan Yarima Sultan Nan su uku da fuskokin su dauke da kyayataccan murmushu su qarasu ganin su yasa Yarima Sultan komawa saman kujera ya zauna Shima Sulaim din haka,

Saida suka fara gaida UMMUL BAIT kana suka juya gurin su Sulaim,

Har lokacin murmushi ne bisa fuskokin su Hakan ya faru ne sana diyar ganin Sulaim da sukai duk da Basu Wani saba dashi sosai ba Amma dai suna son ganin shi yazo,

HAISAM, Shine kebin Yarima Sultan sai Kuma TASLEEM, da TASLEEMA, Yan biyu ne *(twins)* sune mata suke bin HAISAM Kuma sune auta A gurin UMMUL BAIT

Hannu Haisam yami qawa Sulaim tare da fadin Yaya Sulaim barka da zuwa masarautar GABAS,

Murmushi Sulaim yayi tare da miqamasa hannu suka gaisa tare da furta fatan kana lafiya,

Alhamdulillah yafada Yana janye hannuna sa,

Kusan atare Tasleem da Tasleema suka furta barka da zuwa Yaya Sulaim Allah yasa ka iso cikin ameenci,

Alhamdulillah Allah yasa Kuma Kuna cikin ameencin,

Tasleema ta furta mungode ma allah,

Kallon su Sulaim yayi yace Am kice sai Kuma yayi shiru,

Da sauri Tasleem tace eh nice Tasleem Ita Kuma Tasleema,

Wani kyataccan murmushi Sulaim yayi ba tare da yace komai ba yadda Tasleem din tayi ne yabashi dariya

Shi baya hira da kowa baima iya ba idan kaga yayi doguwar magana to da Yarima Sultan ne da baffa sai Kuma Saleem sai aunty raziqa itama Kuma takuramasa take,

Aransa yace ko Tayaya suke iya Gane yaran Nan komai nasu iri daya tamkar RAFIQ da TAUFIQ Yan uwansa kenan Suma twins ne,

Salma sukayi da su da sannan suka qarayiwa UMMUL BAIT sallama suka fita,

Fulani na zaune aka sanar mata da shigowar Yarima Sultan Layin sashanta Gaisawa sukai Babu yabo ba fallasa suna cikin Gaisawa Siyama tashigo sai Wani faman iyayi take da Yan ga daga bangaran da Yarima yake anan ta zauna tagaishe su batare da daya daga cikin su ya kalli ko inda take ba haka dahaka suka bar parlourn,

Wannan abun baqara min ciwo yayiwa Siyama ba Fulani ko ba a magana daga Kai kawai tayi tare da yin kwafa dama tana Jin haushin tunda yadawo sau daya yaje gaida ta,

🦋🦋🦋

Manya manyan motocine guda 4 launin baƙi kowacce da tambarin masarautar GABAS ajiki wato ZAKI *(SHAREEF EMIRATE)* agaban motocin aga rubuta,

Yarima Sultan ne ya turo a dakko su ummeethar yahado hadda sarkin mota saboda abasu tsaro sosai su iso cikin iKon Allah da aminci,

Saleem yaso ace mota daya suka shiga da Suhailat Amma Ina Hakan Bai samuba sai mommy tace yashiga motar da su Rafiq da taufiq suka shiga baji dadin Hakan ba,

Yaso ko a gidan gaba ne ya zauna aqalla ko Babu komai zagan ta tacinkin glass din motar tunda daga Ita sai Saleema ne a motar,

Haka suka dauki hanya Amma yasa aransa duk yadda za ai sai ya ga Suhailat kodan suyi magana saboda a jirgi yaga ko kyakkyawan motsi batayi saboda kada su hada ido duk ya lura da ita a takure take,

Kaitsaye suka sauka a gidan baba waziri sun samu tarba Mai kyau tare da abinci kala kala abinci na musamman UMMUL BAIT ta aiko musu dashi daga ban garan ta tare da aiko Jakadiyar ta da sakon barka da isowa zuwa ga su ummeethar,

Bayan sun ci sunsha daga nau'in abinci kala kala da abin Sha kowa ya kama masaukin sa sun huta sosai wasu daga cikin su har sunyi wanka,

Suhailat kuwa ko fitowa batayi daga masaukin suba da aka Basu Ita da Saleema tunda suka gama cin abinci tashiga tayi wanka Bata fito ba

Princess kuwa jira kawai take sufita tafara yawo acikin masarautar don tana qaunar tsarin masarauta,

mommy tace wai nikam banga kalbiy na ba haryan zu Wani irin Dadi Saleema taji Wanda dama gabtake da tambayar Sulaim din sai mommyn su tariga ta,

Saleem Wanda hankalin sa nakan hanyar idan da Suhailat tabi Yana jiran ganin fitowar ta,

Yace mommy gashinan zuwa nayi magana dashi yanzu,

Saleema jitayi tamkar ta daka tsalle don murnar jin Sulaim yana hanyar zuwa don ita ba don shiba da bazata zoba,

Hattara dai ga zaki dan dan zaki dan gado yafi dan na koya Allah ya temaki Yarima Sultan sarkin gobe A masarautar Gabas da yadda Allah gafarai Yarima zai shigo,

Muryar jakadiya ce takara ɗe kunnuwan su ummeetha kafin kowa yayi wani kwakwaran motsi Yarima Sultan da Sulaim sun shiga Parlourn cikin wata sabuwar shigar wadda tafi ta ɗazun kyau,

Fadawansa dake biye dasu suka ja suka tsaya a ƙofar shiga babban parlourn baba waziri na saukar baƙi,

Kai tsaye Yarima Sultan ya wuce inda ummeethar ke zaune tana murmushin ganin su,

Russuna wa yayi sosai agaban ta cikin girmamawa ya furta inayiwa Mahaifiya ta barka da zuwa Masarautar Gabas Allah yasa Ummeethar ta iso cikin aminci Allah yasa Mahaifiya ta ta samu kyakkyawar tarba acikin wannan masarauta cikin nutsuwa Yarima sultan ya faɗi waɗan nan kalaman,

Sosai ummeethar taji daɗi cikin fara'a tace ɗana Sultan kuma Yariman Masarautar mu barka da Warhaka ina fatan Yarima yana lafiya,

Alhamdulillah ya furta hakan batare da ya ɗagoba,

Zauna sosai kaji ɗaya

Babu musu yarima sultan Ya zauna shi ko Sulaim gurin mommy yafara zuwa ta rungume shi suka gaisa sosai,

Sannan ya rungume Saleem tare da Faɗin soja mazan fama barka da isowa,

Murmushi Saleem yayi tare da fadin mun sameku lafiya

Alhamdulillah"

Komawa gefe Saleem yayi dan baya cikin hayyacin sa hayaniyar tana kara dagula masa lissafi,

Lallai idan har haka so yake to ya shammace ni ya shigeni lokacin da banshirya ɗaukar matsalolin sa ba but why Suhailat?

Saleem ne ke faman surutan shi a zuciya shikaɗai tare da fito da wayar sa yafara rubuta wa Suhailat saƙo kamar haka

_......Ina son ganin ki yanzu saboda muyi magana ina mai baki hak'uri bisa furta kalmar so agareki hakan ya faru ne batare da nima na shirya ba amma komai ya wuce, still what I know is that I love you Suhailat but for you to love me is not by force, just relax and live your life like everyone oky but one day if you see me with someone else I hope you understood_

Yana gamawa ya tura mata batare da ya duba abunda ya rubuta ba saboda yasa aranshi dole yakawo ƙarshan wannan wahalar da zuciyar sa take ci gara ya fuskanci abunda ke gaban sa na aiki,

Gwaggo murja ce ta kalli Sulaim ta taɓe baki tare da fadin to kar Allah yasa ka kai shine idan baka gaisheni ba ai gyatumar ka ta gaishe ni,

Ka zomin har cikin gida sai faman haɗe rai kake maganar aure ce dole ayi maka baza afasaba kuma mace ko wace iri ce sai munbaka yokai ina ma zaka yi wani farin jini kullum fuska a haɗe dunkum kawai kurma,

dariya ummeethar tayi cikin ranta tace lallai gwaggo tana son korar mun yaro yanzu..!!

*Comment and share fisabilillah*

https://whatsapp.com/channel/0029Van1Keq59Pwb6CDnwe0V

WhatsApp channel

*AHALIN MU DAYA*

💗💗💗

*CREATED AND WRITTEN*

*BY*

*Fatima Y zakariyya*

_😍Oum Ameerah_😍

*Nazari writer's association📚*

_Sarauniyar👸 Nazari writer's✍️_

*(THE QUEEN👑)*

______Dedicated to aunty salma💎

*Page* 4️⃣5⃣↔️4️⃣6️⃣📖

"Ka zomin har cikin gida sai faman haɗe rai kake maganar aure ce dole ayi maka baza a fasa ba kuma mace ko wace iri ce sai mun baka yo kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login